← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 56 OF 101

Sashe 56

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Toh Aneesa. Ni dama tsoron mutuwa nake, kada na sha na mutu naji ance masu zubar da ciki mutuwa suke yi."

"Mutuwa ai sai lokaci ya yi, nidai ina ba ki shawarar ki zubar kuma ki je ki yi planning abinki hankali kwance. Matukar dai kina so mu cimma burinmu."

Ta sauke ajiyar zuciya ta jawo ledar magungunan sannan ta ba Aneesa amsa.

"Shikenan, yanzun nan zan sha. Nagode Aneesa, zuwa gobe duk yanda ake ciki zan kiraki mu ji abinda ya dace a yi."

"Shikenan, sai na ji ki."

Daga nan suka yi sallama. Ta ƙurawa magungunan idanu, a wata farar takarda suke, ta yi shiru can kuma kamar wacce aka tsikara ta mike ta dauko gorar ruwa ta bude, ta zazzaga magungunan a hannunta ta shanye su tas sai jiran sakamako.

***
Tana kwance tana juyi yayinda yan uwanta duka ke bacci abinsu. Ta mike zaune ta yi shiru, tashin zuciya take ji sai dai ta rasa yanda za ta yi ba ta kaunar ta yi amai motsin yunƙurin ya tashe su. Zuwa lokacin ta soma shan jinin jikinta, tsoro da firgici ya soma shigarta. Bai fi kwanaki uku watan da suke ciki ya mutu ba amma har yau babu labarin ganin al'adarta. Tsoro iyaka Ummita na cikinsa. Ta kasa jurewa tashin zuciyar da take ji sai ta bude dakin ta fita da sauri zuwa falon bandaki, nan fa ta shiga kelaye amai kamar hanjin cikinta za su zubo. Duk wani kayan kwalam da ta ci a ranar sai da ta dawo da shi. Ta kammala ta wanke fuska ta gyara wurin, ta kuma ɗauro alwala ta dawo falon ta zauna. Sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ga wani irin mugun sanyi da ya lulluɓe ta lokaci ɗaya. Ba ta son koda tuna kalmar da take tunanin shi ya zama damuwarta balle har ta furta.

'Idan ya tabbata haka din ne ya za ki yi da Sahabi?'

Zuciyarta ta watso mata tambayar, ta rike kai sai kawai ta fashe da kuka sosai. Ba ma Sahabin kawai ba, ta ina za ta soma karɓar wannan ƙaddara na rainon cikin da ta same shi ta hanyar fyaɗe? Fyaɗen ma daga ɗan ta'adda?

Tana wannan kukan mai tsuma zuciya ba tare da sanin irin ƙarfin buɗe muryar da ta ke yi ba har sai da ta ga hasken fitila a falon an kunna saboda akwai wuta. Mami ce, kafin Mamin ta ce wani abu sai ga Humaira a gigice ta fito itama. Kusan lokaci guda suka ƙaraso gareta.

"Mene ne ya faru Ummita?"

Humaira ta tambaya jikinta har yana rawa nan da nan itama ta soma hawaye ba tare da sanin ainahin dalilin kukan yar uwarta ba.

Ummita ta rungumeta tana kuka sosai.

"Ciki Humaira, Humaira zan haifi shege."

Da karfi kuma cikin daga murya Humaira ke girgizata kamar zararriya tana fadin.

"Wa ya fadamaki kina da ciki? Karya ne! Karya ne ba ki da ciki!!"

Mami ta dago Ummita.

"Wa ya fadamaki wannan mummunan labarin? Kin ga wasu alamomi ne?"

Mamin ta fadi nata hankalin itama a mugun tashe, nan da nan cikinta ya duri ruwa. Cikin sheshsheka Ummita ta ce.

"Ma..ma.mi, amai nake ta yi."

Ajiyar zuciya Mamin ta sauke.

"Haba Ummita, amai kuma sai aka ce maki yana nuni da cewa kina da ciki kenan? Amai ai alamun cutuka ne da dama, ba lallai sai ciki ba. Lokacin al'adarki ya yi ne?"

"Eh Mami, har ya wuce."

Gaban Mami ya buga da ƙarfi, Humaira sunan Allah ta shiga ambato sakamakon ji da ta yi tamkar an zare mata wani laka na jiki. A durkushe take amma kuma jiri ne ke kwasarta. Tana ji tamkar a mafarki ake wannan diramar ba a farke ba.

"Maryama, meke faruwa ne?"

Suka juya gaba daya, Abba ne sanye fa jallabiya a tsaye a ɗan rikice, ya tako ya ƙaraso ganin Ummita na kuka ya sanya shi ƙara jin rashin nutsuwa sosai.

"Ummita, meyafaru kike kuka?"

Mami ta yi saurin share hawayen da suka zubomata, ta miƙe tsaye.

"Babu komai, ba ta jin dadi ne. Humaira ku shiga ciki. Ki kwantar da hankalinki gobe idan Allah ya kaimu zamu yi test a gani."

Bayan wucewarsu Abba wanda ya daskare a tsaye cikin wani mugun faduwar gaba ya ce.

"Maryama, meye hakan kuma? Na kasa gano bakin zaren wannan tattaunawar da tsakar dare?! Me kike son ki ce?"

Gaba daya ma Abban ya diririce ko kadan ba ya cikin nutsuwarsa.

Mami ta dafe hannunsa.

"Babu komai Abban yara, muje zan maka bayani."

Zai ƙara magana ta hana shi ta hanyar roƙonsa akan su tafi dare ne kar a ji sai kuma ya hadiye maganar ba musu ya yi gaba zuwa ɗaki ta bishi a baya bayan ta kashe fitilun falon.

Ya ji zancen tamkar saukar aradu, nan da nan ya dafe kansa.

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Maryama wannan mummunan labarin da me ya yi kama? Tashi tashi muje asibiti yanzu a dubamin ita."

Mami cikin hawaye ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar dafe kafarsa gami da girgiza kai.

"Aa Abban yara, kar muyi haka. Yin hakan tamkar tonuwar asirinmu ne. Duniya sai ta san halin da muke ciki. Ka kwantar da hankali tunda ana siyar da Pt-strip na awon ciki, gobe da safe mu bayar a siyo a auna fitsarinta don mu ga halin da take ciki. Mu yi fatan alheri da fatan kar zatonmu ya tabbata.

Ajiyar zuciya mai karfi Abba ya saki.

"Innalillahi...Ya Ilahi! Wannan ranar dame zan kirata ni Isuhu? Inama tun farkon fari ban hana Hajiya Maijidda riƙon Ummita ba tun tana ƙarama, da watakila ba zan ga wannan ranar ba."

Wani irin zuciya ya tasowa Mami, ta ji tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Ranta ya yi mugun ɓaci, wato duk hakuri da dauriyar shanye damuwa da bakin cikin RIƘON BARE da ta yi, da wannan sakayyar Abban zai bi ta? Ta so ta furzar da abinda ke ranta sai kuma ta daure kamar koyaushe ta shanye rabi da kwatan ɓacin ranta ta ce.

"Wane irin rashin tawakkali ne haka Abban yara? Ka isa ka hana Allah ikonsa ne akan al'amarin Ummita? Ummita ko bangon duniya ta je idan hakan ya ƙadartu a kanta sai ya afku. Ban da haka ma, kenan kana kaicon rayuwar da ta yi a hannuna? Kana kaico da irin abin da ya fada mata? Ko a tunaninka a sanadina ne aka sace su har kaddarar fyaɗe ya faɗa kan Ummita?"

Ta karasa zancen da wani irin kausasshen murya, ganin ya kalleta da sauri da alama zancen bai mishi dadi ba kuma bai san fassarar da za ta ba shi kenan ba ya sanya ta fashewa da kuka mai tsuma zuciya.

"Dama na sani Yusuf, watarana sai ka ga gazawata akan yarannan duk kuwa da..."

"Haba Maryama, don Allah don Annabi s.a.w ki yi hakuri. Wallahi zafin bacin rai da damuwa da tashin hankali ne ya sanya ni wannan maganganun marasa kyawun ji. Ko daidai da kiftawar ido ban taɓa kawowa za ki cutar da wani a cikin yaran da kika haifa a cikinki ba ma balle a kai ga Ummita. Yarinyar da kika daukaka ta kika kuma riƙe ta hannu bibbiyu tamkar ke kika haife ta a cikinki. Wane irin butulu ne ni da zan yi maki haka? Ki yafemin domin Allah. Na tuba kiyi min uzurin halin rudani da tashin hankalin da na tsinci kaina ciki."

Mami ta mike ta ja guntun tsaki ya yi saurin tarar gabanta.

"Haba Maryama, da wanne kike so na ji ne? Da tashin hankalin nan na Ummita ko kuwa da ɓacin ranki? Faɗamin, me kike so nayi ki huce?"

Jin haka sai kuma ta yi shiru tana goge fuska.

"Kar ka ƙara irin wadannan kalaman naka na rashin tawakkali."

Ya yi murmushin karfin hali ya rungumeta.

"Idan har wannan ne ba zan kara ba. Na ma yi istigfari tun sadda kika ankarar da ni kurena. Mu ji da damuwa daya yanzu."

Ta gyada kai, bandaki ta shiga ta É—ora alwala ta sanya hijabi ta hau saman darduma. Sosai yake jin so da kaunarta a zuciyarsa. Shima sai ya fasa neman wuri ya kwanta kamar yanda ya so duk kuwa da irin sakensa a ibada lokuta da dama. Kusan wannan shi ne kadan daga inda ya kuskuro, rashin tsayawa kai da fata wurin ibada sosai sai idan ya fada matsala babba.

***
Washegari tashin hankalin da suka riski kansu ciki sai ya mantar da su wani batun zuwa kai Humaira asibiti.
Gidan ya zama tamkar gidan makoki. Suna zaune jigum suna jira Mami da Ummita su fita daga bandaki don sanin matsayar Ummita, akwai cikin ko babu. Abba ya kasa fita kasuwa si safa da marwa yake a falon balle kuma Raihana wacce tun jin abinda ke faruwa ta kasa motsawa ballantana ta wuce makaranta. Sai Humaira da ta dau carbi tana jin tamkar an yi mata mutuwa. Mubarak kuwa wanda shi ya fita ya siyo abin awon cikin, sai ya jingina jikin bangon falon ya yi shiru cikin bugun zuciya.

A wannan yanayin Mami ta fito a gigice kuma a guje, gaba daya suka yi kanta har suna rige-rige.

"Meke faruwa?" FaÉ—in Abba yana jin kamar ya kife tsabar jiri.

Mami ta fashe da kuka.

"Mun shiga uku! Shikenan Abban yara asirinmu zai tonu. Ciki ne da Ummita."
Chapter 56 · 0% Book details