← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 68 OF 101

Sashe 68

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

_"Innalillahi..Kai...Kai..Humaira anya zan rayu? Humaira ko na mutu kar ki bari a jefarmin da gudan jinina. Kar ki bari su yi nasarar rabaki da É—ana._ _Ki kira shi da suna Ahmad sannan ki kularmin da shi tamkar ina raye._ _Wayyo Humaira ga Wizzy nan!"_

_Wai sai ta juya ta dubi Wizzy, riƙe yake da ƙaton adda a hannu yana kiran sai fa ya raba Ummita da jaririn. Kawai sai kuma ta ga jariri a hannunta, Wizzy zai karɓe ta shige gabansa kawai sai ta ga  Mami ta zo ta tureta ta fisge jaririn a hannun Ummita ta damƙawa Wizzy._

"Humaira! Humaira!!"

Sunanta da Raihana ke faman kira tana jijjigata iyakar ƙarfinta ne ya sanya ba shiri ta miƙe daga nannauyen baccin da ya kwashe ta a saman darduma. Gaba ɗaya ta haɗa zufa sharkaf duk kuwa da iskar fankar dake kaɗawa a ɗakin. Ta damƙe hannun Raihana manyan idanunta suka ƙara girma har hakan ya yi mugun kaɗa ƴan hanjin Raihana, tsoronta kada dai aljanun Humairar ne suka tashi, cikin rawar murya ta ce.

"Lafiyarki kuwa?"

"Ina Ummita?"

Ta nuna mata ƙofar banɗaki.

"Wanka ta shiga."

Sai a lokacin ta sauke doguwar ajiyar zuciya cike da tunanin irin wannan mafarkin, me kuma ya haɗa Wizzy da Mami? Ta yi ɗan nisa a tunani muryar Raihana ta ƙara katse ta.

"Mami ta ce ki shirya ku yi abin kari sannan ki ɗorawa Sis Tasleem farfesu ta haifi ɗiyarta mace suna asibiti. Yanzu zamu wuce da Mamin, idan an kammala tace ki ba Yaya Ƙassim ya kawo."

Humaira ta gyaÉ—a kai.

"Toh, Allah ya raya. Ki gaidamin ita."

Raihana ta amsa ta fita a ɗakin, daidai lokacin Ummita ta fito daga banɗakin. Baiwar Allah duk ta rame sai ciki da ya ƙara fitowa, bai fi sauran sati biyu ta shiga watan haihuwarta. Hancinta duk ya buɗe. Ta dubi Humaira tana ɗigar da ruwan wanka.

"Anti Tasleem ta haihu? Naji kamar haka Raihana ta ce."

Gyaɗa kai Humaira ta yi jikinta a sanyaye cikin tunanin mafarkinta, Ummitar cikin mafarkinta tana so da kaunar abin da za ta haifa har tana ba da amanarsa, amma kuma wannan ta tsani ma a yi mata batun abin da za ta haifi duk kuwa da rayuwar da take gudanarwa maƙale da shi a jikinta.

Ummita dake tsane jikinta tana kallon Humaira ta madubi wacce ta zubamata idanu ta yi ɗan murmushin yaƙe.

"Kallona kike kamar irin kina bankwana da ni zan mutu wajen haihuwa ko?"

Maganarta ta girgiza zuciyar Humaira sosai, ta ji nan da nan hawaye sun cicciko mata ta kauda kai daga dubanta.

"Allah ya kiyaye, hakan ma ba zai faru ba da yardar Allah. Don Allah ki daina yawan irin waÉ—annan kalaman basu da dadi. Ke dai ki yi addu'ar rabuwa lafiya da abin da ke cikinki."

Murmushi kawai Ummitan ta yi wanda hausawa ke kiransa da yaƙe daga nan ba ta ce uffan ba, itama Humaira ba ta son zancen don haka ta miƙe ta dauki zani da brush ta yi banɗaki.

***
Yarinyar Tasleem sak mahaifinta har duhun fatar, haka dangin mijinta suka dinga zarya a gidanta don tuni aka sallameta a yammacin ranar da ta haihu wato Asabar domin lafiya lau ta haifi ɗiyarta. Ta so kwarai ta je gida wanka amma Mami tana sanar da Abba ya ce sam aa, babban dalilinsa kuma kada a je a yi ta zuwa ana ganin Ummita ana ƙara mata wata damuwar ta daban. Wannan ya sanya hakanan ba don ta so ba ta zauna sai Ladidi ce ta je mata zaman wanka don dama bazawara ce mijinta ya rasu sai ko marayun yaranta da ta bari wajen tsohuwarta.

Humaira ba ta leƙa ta ba sai da aka yi kwanaki uku, kullum dai ita ke girki ana kai wa. Sai da Mami ta yi magana sannan ta shirya ta je. Raihana na makaranta su na rubuta jarrabawar mock daga nan kuma ba jimawa za ta soma WAEC.

Fuska a yatsine Tasleem ta amsa gaisuwar Humaira gami da fadin.

"Sai yau kika ga damar zuwa kenan? Ai da ma kin bar shi gaba daya."

Ta kuwa ji zafin maganar ta ji dama sam ba ta zo ba. Wato ba ta ga bautar girkin da take yo mata ba ana kawo wa ba sai kawai ƙorafin ba ta zo ba. Don haka ta ƙi tankawa ta miƙawa Ladidi jaririyar don a yi mata wanka. Ba ta wani jima ba ta fice abin ta. Tare suka wuce da Ƙasim a mashin ɗinsa don yanzu sam Abba ba ya kaunar shigarsu Ɗan sahu. Adalilin haka ne ma yake ƙoƙarin siyar ƙaramar motar fita unguwa bayan tasa ta amfaninsa dake gidan.

Wannan haihuwa ta Tasleem ita ce ta yi sanadiyyar zuwan Jannat garin Kano da kyakkyawan albishir na dawowar da zasu yi Kano ita da mijinta da ma yaransu a dalilin sauyin aiki da ya samu ta zo wa Tasleem. Ta kuwa ji dadi don har tsalle ta yi ta rungumeta har sai da ta yi mata tsawa akan ta bi a hankali.  Futuha ma ranar da Jannat ta zo itama ranar ta ƙara zuwa na biyu, nan take ba su labarin gidan da Yakubu ya gina mata a sama kaɗan da su Tasleem. Ko kusa Tasleem ba ta yi wani murna ba sai murmushin yaƙe saboda baƙin cikin cigaban da Futuhar ke ta samu a rayuwa, ita kuwa Anti Jannat sosai ta ji dadi ta taya ta murna.

***
Fadeel ya ƙurawa matashin da ya ci suna Joshua idanu, siriri kuma dogo baƙi wuluk. Kallo ɗaya za ka yi mishi ka san ya ƙare saboda tsabar shan sigari da kuma kayan maye. Sarƙa mai tambarin cross ce a wuyansa. Ya dubi Ridwan ya ce.

"Wannan dai shi ne wanda ya yaÉ—a rumours akan su Humaira?"

Ridwan ciki da tabbaci ya gyaÉ—a kai.

"Shakka babu shi ne, komai na shaidun da muka samu daga abokansa ya nuna hakan kuma shi da  bakinsa ya gasƙata ya kuma ce sanya shi aka yi amma a yi hakuri."

Mamaki ya ƙara kama Fadeel.

"Amma kuma Yallaɓai alamunsa sun nuna tamkar bai ma jin Hausa gaba daya."

Ƴar dariya Ridwan ya yi.

"Haka kowa zai yi zato, amma shegen ko wani Bahaushen ba zai nuna masa Hausa ba. Hatta karatunsa a kwalejin ilimi na Kano abinda ya karanta kenan Hausa da English. Ko ba haka ba?"

Ya watsa tambayar ga Joshua da ya yi tsuru da idanu yana jinsu. Jiki a sanyaye ya amsa.

"Hakane Sir."

Fadeel ya daure fuska. Ya ji tamksr ya shaƙe wuyan Joshua ya huta, ba iyaka haushinsa kawai yake ji ba akan abin da ya aikata aa, har ma da ɓatancin sunan da ya kusan haddasawa ya rasa Humaira gaba ɗaya a wurin Alhajinsa domin ya tabbatar masa idan zargin da ake yi ya tabbata to fa sai dai ya haƙura da Humaira. Ba shi kuma ya samu nutsuwa ba sai da shaidun da suka tabbatar da satar suka rinjayi masu ƙaryatawa. Wannan dalili kuma ya sanya Alhaji ya sauko akan  bakansa ya kuma ce nan da wata ɗaya za a yi aurensa da Humairar muddin dagaske iyayenta suke za su ba shi ita. Shima ya aminta da hakan, hakanan Abba ya san da zancen amma ko kadan bai sanar da wani a gidan ba.

"Yanzun ka shirya faÉ—a mana wacce ta sanyaka aikata hakan?"

Tambayar da Ridwan ya watsa masa kenan. Ya sunkuyar da kai kirjinsa na dukan tara tara amma gwara ya tona asirin ya huta don bai ga hanyar tsira a hannunsa ba. Miyau ya haɗiye maƙwat sannan ya ce.

"Wata ce ta haɗa ni da wata mata mazauniyar ƙasan Egypt ta ce tana da wani zazzafan aiki wanda idan har nayi mata komai ya tafi yanda take so za ta yimin kyautar dubu dari biyu."

Ridwan da Fadeel suka dubi juna sannan suka maida hankula gareshi.

"Ya sunanta? Ka ba mu labari tiryan-tiryan don mu san abin da ya faru."

Joshua ya kasa cewa komai sai zufa.

"Look Joshua, ba wani abu muka ce zamu yi maka ba, muna son mu je root din matsalar ne don mu magance ta. Ka fito ka faÉ—amana su waye ke da hannu a ciki."

Ya jinjina kai cikin aminta da zancen Ridwan ya soma magana.
Chapter 68 · 0% Book details