← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 10 OF 101

Sashe 10

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Nan ma girgiza kan ta yi. Ganin haka sai kawai Humaira ta mike ta nufi sif dinta, har ta sanya kaya jiki a sanyaye Ummitan ba ta da niyyar cewa wani abu. Ganin haka sai ta ƙarasa wajenta karo na biyu.

"Na tambayeki mene ne kin kasa cewa komai, kuma kina kuka." Jin ta yi shiru ne yasa Humaira fadin.

"Toh bari na kira Mami mai yiwuwa ita za ki faÉ—amata."

Har ta miƙe da sauri Ummita ta riƙe hannunta. Suna haɗa idanu ta girgiza mata kai, itama Humaira tuni idanunta sun cicciko don a duniya ta tsani kukan mutum. Kuka ma irin na waɗanda  ta ke yiwa ƙauna domin Allah. Duk abin da ya shafi irin mutanen nan tana jin abin a ranta tamkar ita ya shafa.

"Kar ki je, zauna na faÉ—amaki." Ta koma ta zauna tana mai zuba mata ido bayan ta share kwallarta.

"Yayar Mamana ce ta kira ni daga Bichi, kwanakin nan duk sun takura akan lallai sai na fiddo miji na yi aure wai karatun ya isa hakanan. Su sam hankalinsu bai kwanta da zamana a gidannan ba. Ita Babbar yayar Mamana, Anti Maijidda cewa take yi wai har mafarke-mafarke take yi a kaina don haka za su yiwa Abba magana a dakatar da karatun nan, ida n ma aure ne dai a yimin. Ni kuwa na dage akan ba zan yi aure yanzu ba, na ce musu ko zance ba na yi, sun ce ai kuwa anan da Bichi ba zan rasa mijin aure cikin ƴan uwa ba, Anti Maijidda har cewa ta yi ga babban ɗanta Yusuf nan, wai ya kammala  gininsa za ta turo shi ya zo mu yi hira mu fahimci juna. Kin taɓa jin wannan irin abu don Allah Humaira? Duka-duka nawa nake da za su ce za su aurar da ni yanzu? Zangon karshe nake a Ss1 zan wuce Ss2, idan ma auren suke buri su ga na yi, ai sa bari dai shekaru biyun da suka ragemin a sakandire na kammala su. Haka kawai don wasu mafarke-mafarken da ba su da tabbas ku rushemin ginin rayuwata? Sun bi sun kafawa Mami karan tsana, ban san hawa ba ban san sauka ba, amma nima su na hantarata akan na mayar da ita tamkar uwar da ta haife ni, gani suke na fifita dangin Babana sama da su. Toh don Allah faɗamin, mutanen nan sai na je wurinsu duk shekara a can nake hutun dogon zango da ake ba mu na makaranta har ya ƙare, amma su ko sau ɗaya ba su taɓa zuwa garin nan da zummar ganina a gidan nan ba acewarsu su da Mami har abada don ba su yarda da zuciya ɗaya ta ke riƙe da ni ba. Akan Mami na sha duka a wajensu idan na je domin duk wanda ya aibata  ta zan buɗe baki nace sam ba haka take ba, to fa anan sai na ɗanɗana kudata. Yanzu wannan matsalar auren da ta taso ki faɗamin Humaira, ta ina zan kashe ta ba tare da na samu matsala da su ba, nikam wallahi gaba ɗaya kaina ya ƙulle."

Humaira ta sauke ajiyar zuciya.

"Wai Allah!" Shi ne abin da ta furta don ita komai ma ya tsaya mata cak, ta rasa me za ta cewa Ummita. Mamaki take yi na yadda suke yiwa Mami kallon baibai alhalin matarnan iyakar kokari tana yi a kansu, irin kokarin da ko mahaifansu na usuli sai haka. Can kuma ta dubi Ummita.

"Toh kodai ki yiwa Abba bayanin komai? Na tabbata zai fahimceki kuma ba zai rasa matakin ɗauka ba yadda zumuncinku ba zai taɓu ba."

Shiru ta É—an yi, sai kuma ta ce.

"Ko? Nima na yi wannan tunanin, wallahi maganganunsu ke hargitsa ni tun wancan satin su ke huran wuta, tun fa ina dannewa har suka soma sanya ni kuka. Amma hakan zan yi kawai, zan faÉ—awa Abba komai, ke nasan ma kai tsaye zai nemi Kakana wanda ya haifi Mama ya yi mishi magana. Shi kaÉ—ai zai iya tsawatar musu, daman tsoro ne ya sa na kasa faÉ—a mishi, amma na tabbatar zai magancemin."

Humaira ta jinjina kai.

"Sai dai don Allah kar ki faÉ—awa Abba zargin da suke yiwa Mami."

Ummita ta kama baki.

"Rufamin asiri Humaira, dama me zai kai ni?"

Murmushi Humaira ta yi. Suka ɗan taɓa hira sannan ta kyale ta don ta yi karatu.

  Aikuwa a daren Ummita ta samu Abban ta zayyane mishi komai, ransa ya ɓaci. Ƙarshe dai ya ce ta tashi ta wuce zai san matakin da zai ɗauka. A ranar kashe wayarta ta yi ta kuma yi alƙawarin ba za ta kunna ba har sai komai ya wuce don ta tabbata zagi ne dai za ta sha a wurin su.

***
BAYAN WATA BIYU...

Gadan-gadan Humaira ta fara zuwa koyon girki, abin da ya burge su Abba da Mami bai wuce irin hazaƙarta ba na saurin ɗaukar abu. Ita kanta Anti Laila sosai take yabawa da Humairar. A farko-farko ne dai idan aka koyar da su ta zo gida ta yi sai ya kasance bai yi dadi ba ko gishiri ya yi yawa ko dai wani abin, har su Tasleem na ci don su yi mata dariya da kuma kushe. Har su na cewa Abba ya yi asarar kuɗinsa. Amma yanzu kam duk da su na kaucewa ba su son nunawa a fili yana musu dadi, to fa a ƙasan zuciyarsu su na son su ɗanɗana idan ta yi. Amma fa ana ci ana yamutse fuska ana nuna ba laifi ya ɗan yi dadi. Ita dai ba ta tanka musu tunda har Abba da Mami da Ummita su na yabon girkinta.

A farko direba ke kai ta, daga baya kuwa Mami ta nemi É—an sahun da zai dinga kai ta kuma ya É—auko ta. Watarana kuwa da aka yiwa É—an sahun rasuwa da kanta ta Mami ta sanya yaron gidan me musu wanki ya raka ta titi ya sanya ta a adaidaita, a dawowa da kanta ta dawo. Tun kuma daga nan ta soma zuwa da kanta ta dawo, a karshe kuma ya kasance koda É—an sahun bai zo ba ita ke zuwa ta dawo. Ganin ta gane hanya ya sa Mami kawai ta sallami É—an sahun ake ba ta kuÉ—in mota.
Komai idan ta koya tana samun É—an littafin da Ummita ta bata ta rubuce tsaf da hausar ajami. Rubutunta mai É—an karen kyau da burgewa har ya kasance Ummita ta yi ta santin handwritting din.

A bangaren Islamiyya kuwa, kusan tare suke tafiya da Ummita a aji duk kuwa da cewar a can karatunta ya zarta na su, akwai abubuwa da dama da ta sani na daga litattafan addini wanda na ajin Æ´an gaba ne. Hakan ya sa idan ba sa komai ta ke zama malamar Ummita. Su yi ta karatunsu musamman yanzu da ake cikin hutun dogon zango na makarantun boko. Idan ka cire Tasleem da Futuha sai samarin, babu wanda ke zuwa makaranta. Gidan sai yake yiwa Humaira daÉ—i fiye da a baya.

Ranar wata Asabar da yammaci su na zaune a É—akinsu, Humaira ke taya Ummita gyaran sif É—inta, gaba É—aya sun sauke kayan Ummitan saman gado. Humaira sai tsokanarta take yi akan da tuni yanzu an sanya ranar aurenta da Yusuf, ita kuwa tana kai mata bugu da ninkakkiyar rigarta. Sai kuma ta ja guntun tsaki ta zauna gefe tana murmushi.

"Ke nifa ina da mijin aure a hannu, kawai dai bai taɓa zuwa gidannan ba, ba na so kowa ya sani sai na kammala karatu."

Humaira ta zaro ido da wani irin zumuÉ—i ta ce.

"Don Allah dagaske? Waye wannan mai sa'ar?"

Ummita ta ɗan harareta sai kuma ta miƙe ta ci gaba da ninkin da take yi.

"Oho, idan ta yi wari kya ji."

Duk irin magiyar Humaira dai ba ta samu Ummita ta furta komai ba, da ta ga hakan ba mai ɓulla bane sai ta sauya ta ce.

"Toh abu ɗaya za ki faɗamin, Allah kuwan daga shi ba zan ƙara tambaya ba. Na san shi, na taɓa ganinsa? Eh ko aa?"

Dariya Ummita ta yi.

"Wai ni za ki yiwa wayo ko me?"

Itama dariyar ta yi.

"Allah ba wayo ba, kawai ina son sani."

Ummita ta ɗan yi shiru, ta sani idan har ta ce mata ta san shi to za ta ƙara damuwa da son ji ita kuwa duk data yarda da Humaira ba ta shirya kowa ya ji yanzu ba. Sai ta girgiza kai.

"A'a toh."

Jin haka Humaira ta taɓe baki.

"Toh shikenan, idan ta yi wari ma ji."

Kafin Ummita ta tanka sai ga Muhsin ya shigo a guje.

"Adda Humaira, ki zo inji Mami za ku gaisa da Yaya Kabeer."

Humaira ta ji kanta ya yi wani dum, wani irin ɓacin rai da bakin ciki na taso mata da ba ta san silarsa ba. Nan da nan ta haɗe fuska tamau kamar ba ita ke dariya yanzu ba.

"Ka ce gatanan zuwa." Ummita ta amsa jin ba ta da niyyar amsawar. Ta sani Humaira ta tsani Kabeer, tun ganin da ya yi mata a gidansu tare da Mami yake bibiyarta. Amma yadda fuskarta ta sauya ita kam ba ta taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba.

"Ke lafiya? Daga ance maki Kabeer ya zo?"

Tsaki ta ja ta miƙe a fusace cike da wata iriyar tsiwar da ita kanta Ummita ba ta san ta da ita ba ta ce.

"Aikin banza da wofi, na tsani naci da takura wallahi. Mutum sai shegen naci, itama Mami ta biyemishi har da wani aikowa a yi kirana." Ta kara jan tsaki. Maganarta na karshe kan kunnen Raihana da ta shigo É—akin tana danna waya, baki buÉ—e take kallonta.

"Ke, Mami za ki yiwa rashin kunya? Har da tsaki?"

Ko kallonta ba ta yi ba ta juya ta ci gaba da ninkin kayan da alama ba ta da ko niyyar tashi balle ta je. Ummita ta kalli Raihana itama ta dube ta, a fusace Raihana ta karaso ta fisge rigar dake hannun Humaira ta yi jifa da shi. Humaira ta mike a zuciye ta ce.
Chapter 10 · 0% Book details