← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 20 OF 101

Sashe 20

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Bai kara magana ba sai mayar da hankali ya yi ga Imran dake nuna mishi wani hoto a waya. Shi kansa Ibb ba mai yawan zance ba ne sai ta kama, don haka bai hanata ba. Shi kuwa gogan kallonta bai kara ba, sai Idris da ya zuba mata ido kamar ya haɗiye ta. Shi dai kam lokaci guda ya ji ta kwanta masa a ƙoƙon rai. Don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya dubi Fadeel.

"Wannan ƙanwarmu ce?"

Tsaf Fadeel ya karance shi, don haka ya gyada kai kawai fuska ɗaure. Ita kuwa da rawar jiki ta miƙa kwanon abinci ga Fadeel. Madadin ya karɓa sai ya dube ta. Ta ji kallon tun daga tsakar kanta har tafukan sawayenta.

"No, ki fara ba su tukunna."

"Kai Malam, idan za ka karɓa ka soma ci ka karɓa. Tun ɗazu ka ke mana raki da kukan yunwa kamar wanda ya shekara bai ci ba. Wannan ta ya ya kake azumtar watan Ramadan?"

Jin haka ya ja filo ya jefawa Imran a fuska, gaba daya aka sa dariya shi kuwa ya shafi sumar kansa yana mai lumshe idanu lokaci daya ya bude su akan Murja, wannan karon sai da ta ji miyan bakinta ya sarƙe ta sai ga shi ta soma tari ba ƙakƙautawa. Idris da sauri ya miƙa mata ruwan roba dake gefensa saman kafet. Ta karba ta sha tana satar kallon Fadeel da bai ƙara dubanta ba sai waya da ya ke faman dannawa. A haka da rawar jiki ta zuba kowa ta miƙa mishi. Friedrice ne da hadin coslow sai chicken pepper. Ta bude firij ta ciro musu lemuka ta ajiye. Daga haka ta sa kai ta fita. Tana fita Idris ya gyara zama ya shiga rantse musu akan ya ga matar aure shi dai yana sonta idan za'a ba shi. Fadeel ba ya fahimtar komai ban da ta cikinsa da ya ke yi, ganin duk da fankar da ke busawa yana gumi kawai sai ya mike ya cire rigarsa daga shi sai dogon wandon shadda da vest ya koma ya zauna. Sai da ya tashi da abincin tas kafin ya ɗauki ruwa ya kora ya dubesu. Kowannensu bai kai ga kammala ci ba, suka kwashe masa da dariya, shi kansa murmushi da tsaki ya yi lokaci guda kuma yana sa hankicif ya goge fuska.

"Ku na da matsala wallahi, ba za ku gane illar da yunwa ke min ba. Yanzu sai ta tayarmin da ulcer."

"Ai mun gane komai ranka ya daɗe. Ko za ka ƙara?"

Saifullah ya faÉ—i da zolaya. Fadeel ya É—an harareshi.

"Saboda na zama rumbu ko?"

Haka suka yi ta zolayarsa shi kuwa tuni ya maida kai kan wayarsa yana kiran abu na biyu da ya tsaya mishi a ƙoƙon rai amma har ta kammala ringing ba a ɗaga ba. Haka ya kira har sau uku, sai a na huɗun, aka ɗaga. Kafin ya kai ga cewa komai ta soma faɗa.

"Wai Malam kai din maye ne?! Na ce ka bar kirana ka ƙi! Dole ne zuwanka gidan namu? Haba, wannan jaraba da naci har ina wai? Mtsw."

Daga haka kit, aka kashe kiran, nan da nan kansa ya yi wata irin sarawa, dama ga ciwon kan da tun ɗazun yake ji. Gumi ya karyo masa saboda tsananin ɓacin rai, idanunsa tuni suka kaɗa. Sauyawar yanayinsa ya sa Ibb ƙuramasa idanu. Sai dai bai ce komai ba ganin ba su kaɗai ne a falon ba. Sai bayan da gaba daya suka fice don gaisawa da Alhaji sannan Ibb ya dube shi, lokacin ya mayar da kai jikin kujera ya lumshe idanu don har su Imran suka fita sun yi zaton bacci ne ya kwashe shi su na mishi tsiya. Shi kuwa duk yana jin su ba shi dai da karfin biyewa shirmensu.

"Fadeel, wai meke faruwa haka?"

Jin muryar Ibb yasa shi bude idanun, ya mike zaune sosai.

"Yarinyarnan nema take ta kashe ni, daga ranar da na gan ta har zuwa yau ban huta ba."

Cikin rashin fahimta Ibb ya dan wurga hannu.

"Wace yarinya ce haka? A rayuwarka har ta hanaka sakat? Wace ce?" Tsakaninsa da Allah ya yi furucin don shi gaba É—aya ma ya manta da wata Humaira.

"Wacce muka haÉ—u da su tare da wannan É—an iskan yaron."

Shiru Ibb ya yi cikin nazari sannan ya dube shi a hanzarce.

"Are you serious? Kana nufin ka kira ta?"

Cikin ido Fadeel ya dube shi.

"Yes, mun yi waya, amma duka ba masu dadi ba ne."

Ya kora mishi bayanin duk abin da ya faru, Ibb ransa ya ɓaci.

"Unbelievable! Yanzu akan mace ne ka shiga wannan yanayin? Fadeel kai ne dagaske dai wanda na sani? Mutumin da gaisuwar kirki abu ne mai wuya a ganka kana yi da wacce ba muharramarka ba, kai ne yau da bakinka ka ke faÉ—in cin kashin da wata shashasha can take maka? Kuma har ka ke tolerating in the name of love? Is this love or madness?"

A fusace Fadeel ya soma magana, tun da Ibb ya jefi Humaira da kalmar shashasha ya ji ransa ya yi masifar zafi.

"Oho! Idan ma haukan ne naji ni na jefa kaina ai ba da sa hannunka ba ko? Ban damu da duk wani tunani da za ka yi ba. Ina sonta, ka zo gabana kana kiranta da shashasha ba zan iya jura ba Ibb! Ina haÉ—a ka da Allah, idan har ba goyamin baya za ka yi ba toh kada ka kara kuskuren zaginta a gabana. Kawai dai ina ji a jikina wataran za ta gane ni din masoyinta ne na gaskiya."

Yana kaiwa nan ya mike ya nufi hanyar ɗaki, Ibb kuwa baki a wangale yake binsa da kallo har ya ɓace masa. Meke damun Fadeel? Ya jefawa zuciyarsa tambaya, a take kuwa amsar ta zo masa, Soyayya ce. A fili ya ce.

"Idan kuwa har wannan ita ake kira da soyayya, ina nemawa kaina tsari da ita. Kai kuma Fadeel ina roƙon Allah ya yayemaka wannan haukan son."

Daga haka ya mike ya fita a dakin domin shi har ga Allah ba ya fatan wannan rashin hankalin da mace za ta zage shi ya kasa daukar mataki a kanta. Ko ƴar uban wace ce ba zai ƙara yi mata kallon wata abar so ba, ballantana har ta ci galabar yi mishi son ranta.

***
Humaira na  kwance a yammacin ranar juma'a ta ji ihun ƴan matan gidan ya karaɗe falo, ta mike zaune tana mutsistsiƙa idanu. Hayaniyar ta mene ne? Kafin bacci ya gama wartsake mata sai ga Ummita ta shiga fuska ba yabo ba fallasa.

"Wai hayaniyar me ake yi?" Fadin Humaira. Tsaki Ummita ta ja haɗi da taɓe baki.

"Aunty Jannat ce ta zo, kanwar Mami."

Humaira ta zaro ido, ba ta taba zama da ita ba amma ta sha jin labarinta a bakin Ummita na irin uƙubar da ta sha a wajenta sadda tana rayuwa a gidan.

"Dagaske? Ki ce mun shiga uku."

Ganin ruÉ—ewae Humairar har ya so ya fi nata ne yasa ta dariyar dole wanda ba ta shirya masa ba.

"Ke da ba ki taɓa zama wuri guda da ita ba? Ba lallai ki fuskanci matsalar da na fuskanta ba ai."

Ita dai Humaira ta ji ne kawai ba don ya zauna a kwakwalwarta ba.[7/24, 9:39 PM] Maman Imaan Nvl Lvrs: *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

Suna nan zaune Humaira na cewa  ita kam za ta so ganin ya wannan Jannat din take mai shegen son mulki sai ga Muhsin da Waleed sun faɗo ɗakin a  guje. Kira ne daga Mami akan su fito a gaisa da Jannat. Ummita ta dafe kirji, yayinda Humaira mikewa ta dube ta.

"Wai ya haka, kinsan fa yarannan akwai daukar zance yanzun sai su fasalta musu yanayinki."

Ummita sai ta maze ta mike. Suka kama hanyar falon, tun kafin ma su kai ga ƙarasa shiga ta hange ta. Kamanninta sak da Mahaifiyarsu wato Anna. Kusan har ta so ta fi Mamin hasken fata, siririya ce ba ta da tsawo duk kuwa da cewar tana daga zaune ne. Yaranta ƴan biyu tamkar an tsaga kara an karya, ba su wuce sa'o'in Muhsin ba. Wato shekaru goma a duniya. Riga da wando ne a jikinta sai abaya dake ajiye a hannun kujera wanda ga dukkan alamu cire ta ta yi. Gashinta ya sha kananun kalba an tufke a tsakiyar kan ya yi kamar ta sa ribos din acuci. Gaba daya iyalan Mami na falon ciki kuwa har da Anna wacce ba kasafai ta fiye fitowa ba. Humaira ita kanta sai da ta sha jinin jikinta ganin Anna a falon, sai da itama ta ji kamar ta ja hannun Ummitan su juya. Aikuwa su na ganinsu Anna ta tamke fuska gami da juya harshe zuwa buzanci. Ko me ta fadi oho, gaba daya suka kalli su Humaira, matasan suka gimtse dariyarsu sakamakon Mubarak dake zaune, sun tabbata muddin suka ce fiddo shi waje to fa kashinsu ya bushe wurinsa.  Hatta da Raihana ba ta ji dadin zancen Anna ba domin har ga Allah yanzu ba ta da matsala da su, ta riƙe su ƴan uwan na gaske kuwa.

Ita kuwa Jannat kallon Humaira ta ke yi kamar wacce ta ga kashi. A yatsine ta amsa gaisuwarta, Ummita kuwa gaisuwar ma ba ta samu ba sai harara da ta watsa mata ta ja tsaki.

"Wai Anti Jannat har yanzu wato kina nan yadda na sanki."

Mubarak ya fadi ransa duk ba dadi, tun daga kalmar agolar da Anna ta kira Humaira da shi har zuwa yanda Jannat ta karɓi gaisuwarsu.  Rai a ɓace ta amsa.

"Toh ko za ka sa hannu ka buge ni ne? Dama ai kai na faÉ—a can dai dangin uba ka biyo ba mu ba."
Chapter 20 · 0% Book details