← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 53 OF 101

Sashe 53

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ladidi ta yi dariya Humaira kuwa ta maka mata harara ta rasa dalilin kuma da aka yi ta É—an dawo da jin haushi-haushin Fadeel, sai lokacin kuma Mami ta yi magana.

"Toh uwarta, ke kuma Humaira meyasa ba ki faɗamin kina da baƙuwa yau ba?"

Cikin sanyin murya da kuma rashin jin dadin ɓatawa Mamin rai da ta yi ta ce.

"Kiyi hakuri Mami, gaba daya na manta ma ya faÉ—amin."

Mami ta sauke ajiyar zuciya, ta sauya yanayinta na farko sannan a sanyaye ta ce.

"Ai shikenan, ba don girkin da ake na Futuha ba da sai dai ta zo ba a yi nata tanadin komai ba kenan. Ladidi ƙaro shinkafar nan kafin ki wanke."

Ladidi dake shirin wanke ɗanyar shinkafa ta zuba a ruwa ta amsa da toh, sai da ta ƙara ruwan tukunyar sannan ta ƙara awon shinkafar da ajiye. Raihana dai ta tsaya jiran Humaira ta dage lallai sai ta sauya shigar jikinta. Mami ba ta sa musu baki ko kadan ba, Humaira har haushin Raihanar ta dinga ji saboda irin wannan nacin ba ta ko fuskantar yanayin fuskar Mamin.

"Ki rabu da ni don Allah." FaÉ—in Humaira cikin haÉ—e gira. Sai lokacin Mami ta sa baki ta hanyar bin Humaira da murmushi.

"Aa Humaira, da gaskiyarta. Maza je ki sauya suturar jikinki. Bai kyautu baƙuwarki ta ganki a hakan ba. Jeki."

Ganin yanayin Mamin har a sannan ba ta gamsu ba, amma ta bi umarninta suka fice da Raihana zuwa nasu ɗakin. Ta iske Raihanar ta fiddo mata wata atamfarta purple mai ratsin fara da baƙi, ta kalle ta. Raihana ta murmusa.

"Ya aka yi? Da magana ne? Ko na sauyamaki kayan?"

Guntun tsaki Humaira ta ja.

"Ke dai yadda kika damu da wannan Fadeel din da ma ke kika aure shi."

Raihana ta ji ba dadi jikinta kuma ya yi sanyi, tana tunanin Humaira ta fara sauyawa daga lamarin nata da na Fadeel sai ta ga abin ba haka ba.

"Allah ya huci zuciyarki tawan." Ta fadi tana riƙo hannun Humaira, sai itama ta ji ba dadi.

"Shikenan. Bari na watsa ruwa na sauya ko don ke."

Sosai Raihana ta ji dadin kalamanta. Ta yi dariya.

"Toh."

Daga haka ta fice ta bar Humairar da shiga bandaki.

***
Murja tana zaune gaban motar ta hakimce yayinda Hannatu da yarinyarta mai shekaru uku da ta ci suna Husna suke a baya zaune.
Tun da Murjar ta ji inda Hannatun ta nufa ta kafe akan sai ta bi ta, a farko Hannatu ba ta so ba don tana da labarin irin son da Murjar ke yiwa Fadeel daga bakin Kausar. Shi Fadeel dayake bai ɗauki maganar da muhimmanci ba ya sa bai ce mata komai a kai ba. A karshe dai ganin yadda Anti Amarya ta nuna ta yi na'am Murja ta raka su ya sa itama ɓoye nata rashin yardar suka tafi tare ba da sanin Fadeel ba.
Karfe biyar na yamma suka shiga gidan. Raihana ta tare su da fara'arta zuwa ciki. Murja sai raba idanu ta ke ta ga inda Humaira za ta ɓullo kuma ta ga yanda ta sauya. Ummita itama ta fito suka gaisa da su, nan suka jajanta musu da addu'ar Allah ya kiyaye gaba. Ba ta amsa ba sai ta mike sakamakon idanunta da suka cicciko da kwalla ta nufi daki.

A duniyarta yanzu babu abin da ta tsani ta tuna kamar abin da ta faru gareta a hannun Kidnappers. Gani take duk ranar da aka É—aura mata aure da Sahabi babu abin da zai hana shi gano komai, Abba ya yi niyyar sanar da shi amma Mami ta nuna kar ya yi hakan. Ita kuma a karan kanta ta rasa ta ina za ta fara gayamishi. Ga wata sabuwar kauna da yake nunamata tun bayan fitowarsu duk domin ya kwantar mata da hankali.
Ganin da ta yi Humaira na É—akin, ta yi saurin share fuskarta ta dubeta fuskar a É—an sake duk da ba kamar can baya da take Ummitarta ba.

"Sun ƙaraso su na falo. Ki je ku gaisa, mace mai kirki da ita."

Taɓe baki Humaira ta yi.

"Toh." Shi ne abin da ta iya cewa, daga haka ta sa kai ta fice. Bayan fitarta Ummita ta tura kai a filo ta yi kuka mai isarta tana mai tausayawa kanta. Wannan baƙin ciki na keta alfarmarta da aka yi ta kasa gogeshi daga kirjinta, ta dai san an gogamata baƙin fentin da har abada ba za ta iya gogewa ba. Amsar da ta kasa ba wa kanta har yau shi ne, wane ne wanda ya sa a yi kidnapping dinsu.

*_Ba don kar asirinmu da na Boss ɗinmu ya tonu ba, da sai na nemi aurenki na killaceki saboda kin haɗu ƙarshe._*

Ta tuna wannan ƙazamin zancen da ya fito daga bakin Wizzy a sadda yake kam ganiyar raba ta da mutuncinta. Kenan dai akwai wanda ya sanya su wannan aika-aikar. Waye shi? Kuma a ina yake? Allah ne kaɗai masani. A karshe dai ta yakice wannan tunanin ta mike ta shiga bandaki.

***
Hannatu ta dubi Humaira har ta ƙaraso ta zauna tana mata ɗan murmushi. Murja kuwa kallon Humaira kawai take yi cikin tafarfasar zuciya tana mai kuma cin alwashin ganin bayanta. Babu wani abu da ya sauya daga kyawunta wannan ne ya ƙara wa Murja baƙinciki a ƙasan rai. Ta kauda fuska tana amsa gaisuwar da Humaira ke yi mata a yatsine. Ita kuwa Humaira mamaki take na dama Murjar ta san Fadeel amma sai ta bar wa cikinta ba ta tambaya ba. Hannatu ta saki jikinta ta yi ta jan Humaira da hira, kasancewar da Raihana a falon ta samu ƴar tayi, tun dai Humaira ba ta saki jiki ba har sai gatanan ta soma murmusawa haƙoranta na bayyana.

Raihana ta kawomusu abin motsa baki da kuma abinci. Husna ta maƙalewa Humaira tana mata hira iri iri na yara. Itama ta dinga biyemata. Can dai Murja ta kasa jurewa ko Mami ba ta tsaya sun gaisa ba ta amsa wayar ƙarya sannan ta dubi Hannatu.

"Ni zan wuce sai kun taho. Ƙawata ce ta zo."

Suka dube ta har Raihana da ta fahimci sauyin fuskar Murjar da irin harare-hararen da take wurgawa Humaira jifa-jifa.

"Shikenan, sai mun taho."

Ranta ya ƙara ɓaci, wato dama so take ta tafi ɗin don haka ta dauki jakarta ko sallama ba ta tsaya yi da su ba ta fice a fusace.

Ba jimawa kuwa da fitarta Mami ta fito cikin shirin fita. Daga ganin yanayinta sauri take kuma fuskarta ya nuna rashin nutsuwa. Hannatu ta gaida ta, ta amsa da É—an sauri. Ganin haka Raihana da Humaira suka tarbi Mamin da neman ba'asi. Guntun tsaki ta ja fuskarta dauke da tsantsar damuwa.

"Wajen Tasleem zan je, sun yi dambe da wannan Fauziyar shi ne fa jini ya ɓalle mata amma sun wuce asibiti."

Hankalinsu su din ma ya tashi. Suka nuna za su bi ta amma fir ta ce aa su zauna da baƙuwarsu sannan ga Futuha dake hanyar zuwa kada a bar gidan babu ƴan tarbarta. Dole suka jajanta suka dawo ga Hannatu aka cigaba da hira. Ba ita ta bar gidan ba sai bayan Magriba. Ta kuwa ajiyewa Humaira leda babba ta kayan kwalam sai ko turarukan da ta yo mata tsarabarsu. Firr Humaira ta ƙi karɓa sai daƙyar sannan ta yi godiya. Lokacin itama Ummita ta fito falon, tare suka yi mata rakiya har gaban motar da suka zo cikinta.

***
Karfe takwas da mintoci sai ga Futuha a gidan, tun yamma ta sauka a garin tana gidanta, Ƙasim ne ya kai musu girke-girken da aka yi musu. Ta shigo gidan gaba ɗaya jikinta a mugun sanyaye. Matasan samarin duka suna falo aka tarbe ta da murna, su Humaira su din ma duka ana zaune ana kallon film din Krissh da ake haskawa a mbcbollywood. Ganin yanayin yadda take amsa musu hirar ya sanya Yassar dibanta dakyau.

"Are you okay?" Ta yi murmushin yaƙe kai ka ce ba Futuhar nan ba ce mai ɗora hotuna iri-iri da murnar zuwa Dubai a tiktok.

"Yes. Mamin ba ta dawo ba?"

"Ta dawo tana É—aki."

Faɗin Raihana. Ta kuwa nufi ɗakin, ban da gaisuwar su Humaira babu wani jimamin da ta yi musu na abin da ya faru. Ƙamshin turarenta da ya cika falon ne ya sanya Ummita jin kanta na juyawa, ta ji tamkar hanjin cikinta ke kaɗawa. Da sauri ta mike ta yi dakinsu, kafin ta ƙarasa shigewa banɗakin wani amai ya tahomata wanda sai da ta amayar da duk abincin da ta ci a ranar. Humaira da Raihana wadanda suka biyo bayanta ganin irin miƙewar da ta yi ta bar falon suka tsaya cak cike da fargaba mai tsanani su ke bin ta da kallo.
  *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Raihana ta karasa cikin sauri bayan fitowar Ummita daga banɗakin ta riƙe ta.

   "Lafiya? Meke damunki?"

Ummita ta yamutsa fuska kaÉ—an.

"Ban sani ba, kawai dai na ji zuciyata tana tashi."

"Allah ya sauwaƙe, ki ɗan kwanta ko za ki ji dadin jikin." Fadin Humaira cikin dauriya da ƙaryata zuciyarta har da jan istigfari bisa saƙe-saƙen da ta jefa mata. Ummita kuwa ɗan murmushi ta yi.

"Kar ku damu, kalau nake. Naga duk kun yi wani sukuku da ku."

Cikin kokarin basarwa Raihana ta zauna gami da jan guntun tsaki.

"Ai dole, ga Tasleem can kwance asibiti dakyar aka tsaida jinin. Wai kawai saboda ta kama Fauziyya na waya da tsohuwar budurwar Yaya Hamza kuma ƴar uwarta tana ba ta labarin rayuwar ita Tasleem din da Yaya Hamza shikenan fa daga cacar baki sai cibi ya zama ƙari. Nima Mami naji tana ba Anna labari. Yanzu dai Maman Hamza ta ƙi zuwa ko duba Tasleem ta ce wai kashe mata ɗiya ta so yi."
Chapter 53 · 0% Book details