← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 60 OF 101

Sashe 60

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tasleem wacce daga makaranta ta shigo gidan sanye take cikin uniform dinta ga tirtsetsan cikinta dan watanni takwas sai faman taunar aya take yi suna hirar makarantar da Mami, watanni shida kawai ya rage ta kammala karatun gaba daya. Ba ta yi ko mintuna uku ba sai ga Hajiya Futuha ta shigo tana ta faman shan ƙamshi. Tasleem ta harareta ta gefen idanu ta kauda kai tana ɗan huci, fatar Futuha ta kara kyau kamar ka taɓa jini ya fito, kamshin turarenta kuwa ya buɗaɗe falon gaba daya. Ƙasim na rike da jakarta yana take mata baya, babban burinsa shi dai ta ba shi na kashewa.

Yassar ya dube ta.

"Ka ga manya matar Alhaji naku daban da nasu. Irin wannan ƙamshi haka? Gaskiya zan zo a sammin turaren."

Ta karaso ta zauna jikin Mami tana dariya.

"Har ka bani kunya É—an uwa. Idan dai turare ne, ko direba zan aiko ya kawomaka na siyo su kala-kala a Dubai."

Aka sa dariya Dawud na fadin.

"Inyeee! Ka ga Hajjaju mutan Dubai."

Mami dake murmushin jin alfahari ta ce.

"Ya ishe ku hakanan toh."

Tasleem dai ba ta tanka ba sai dariyar yaƙe kamar bakinta zai rabe biyu amma ƙasan ranta ji take tamkar ta kurma ihu.

Shigowar Ummita da su Humaira ya sanya hirar ta tsagaita, suka gaishe su, Futuha ta amsawa Humaira faram-faram don tsakani da Allah so take ta wuce da ita gidanta ko don girki. Tana da mai aiki amma ko kusa ba ta iya abincin da Alhaji Yakubu ke so ba kullum sai ya yi mita wannan dalilin ne ya sanya take son tafiya da Humaira gidan koda na kwanaki ne ta nunawa yar aikinta yanda take sarrafa tukunya.

"Humaira sannu, bayin Allah har kun dawo hayyacinku wallahi."

Fadin Futuha, sai kuma Raihana ta sanyo wani zancen gudun kar a tada abin da zai sosa musu inda ke ƙaiƙayi. Yassar da sun riga sun samu labarin komai kuma har a zuci ba su yi farin cikin ƙaddarar cikin Ummita ba sai ya sanyo hirar abinci yana kiran a kawo a ci ya kwaso yunwa daga kasuwa. Tasleem kuwa ƙuri ta yi da idanunta akan Ummita ba ta ko ƙiftawa musamman ma da Ummitan ta mike tsaye ta sauya wurin zama. Da ta kammala tabbatar da zarginta sai ta ga ta nan a tsaye ta miƙe har ayar da take ci na zubewa a saman kafet.

"Kut! Me nake shirin gani Mami?"

Ta yi furucin har a sannan idanunta na kan Ummitan. Gaba daya suka dube ta, Ummita kuwa ganin idanun Tasleem a kanta ya sanya ta É—ago me take son fadi, wato dai itama ta gane tana da ciki don haka sai ta mike da sauri-sauri ta shige daki saboda kukan da ya tahomata na tsantsar damuwa.

"Me aka yi kike mana ihu? Ita kuma wannan me aka yi mata ta miƙe?"

Futuha ta jero tambayoyinta lokaci guda.  Tasleem ta cafe zancen tana kara hura hancinta da ya buɗe saboda ciki.

"Ciki na gani jikin yarinyar nan."

A razane Futuha ta buÉ—e idanunta ta dubi Humaira da kuma Raihana sannan ta maido hankali ga Tasleem.

"Wa kenan?"

"Ummita mana. Mun shiga uku, shikenan yarinyarnan za ta ɓata sunan gidanmu, image din gidanmu zai lalace a idanun duniya. Meyasa ba a zubar da cikin ba Mami?"

Humaira wani tururi zuciyarta ke yi na ɓacin rai, wato ita Tasleem ba ta ko tausayawa halin da Ummitan ke ciki ba balle tayata jimami. Kamar ta tofa sa kuma albarkacin Mamin dake zaune a wurin ta ja baki ta kuma zuba idanu ga Mamin don ganin me za ta ce. Mami kuwa ta gefen idanu ta ga irin duban da Humaira ke mata don haka nan da nan ta daure fuska.

"Idan ita ba ta ɓata mana suna ba, ke gashinan ai kina ihun da makwafta za su ji su fahimci halin da muke ciki! Wannan wane irin rashin tunani kike aikata mana? Kina haukar tonawa yar uwarki asiri?"

Jin haka sai Tasleem ta koma ta zauna, ta ja guntun tsaki ba ta ce uffan ba. Ita wannan duk bai dameta ba kamar yanda kawayenta da dangin miji da ma abokan hulda da ake kunya za su samu labarin cikin Ummita ya zamar musu abin habaici da zagi. Futuha kuwa, babu abin da take hangowa sai irin yanda labarin zai karaÉ—e social media alhalin ta gama karaÉ—e ko'ina da nuna hotunan su Ummita tana shaidawa duniya su din kannenta ne. Yanzu idan zancen nan ya fita ai ta shiga uku.

Yassar ne ya basu labarin duk fadi tashin da aka yi don ganin an zubar amma abu ya faskara. Tasleem ta ja tsaki karo na biyu.

"Ba dai abi hanyar da ta dace ba. Ni wallahi da tun farko an faɗamin da kaina zan zo na yi mata alluran da na tabbatar sai cikin ya zube. Amma yanzun ma ai ba ta ɓaci ba, me zai hana a markaɗe shi?"

"Wai Sis Tasleem meyasa ba ki da imani ko ƙanƙani? Kina magana babu ruwanki idan an yi ko Ummita ta mutu ta rayu."

Tasleem ta harzuƙa da zancen Raihana.

"Da wannan abin kunyar ba gwara ace ma mutuwar ta yi ba! Ai gwara mu lulluɓe ta cikin sutura a kai ta kabarinta da dai ta haifa mana shege."

"Sai dai ke ki mutu! Ai dama wanda bai sonka ba zai taɓa sonka ba. Na kuma gama gasƙatawa ke din azzaluma ce da ba kya kaunar naki. Ciki kuma ƙaddarar Ummita ce da bai wuce faɗawa kan kowa ba koda kuwa matar auren ce. Nawa aka yi? Yanda ba kya kaunarmu har abada ba zamu taɓa kaunarki ba, yanzun ma albarkacin masu albarkar kika ci da ban ɗaga yatsuna na watsa a saman fuskarki ba."

Humaira ce ke wannan zantukan cikin tsananin rufewar idanu jikinta har tsuma yake yi. Tasleem ta yi laƙwas, ina za ta mance shaƙar da ta yiwa Anti Jannat, me ya yi mata zafi da za ta yarda ta yi katoɓarar da itama za a shaƙe ta ga tsohon ciki. Falon gaba daya aka rasa mai tankawa Humaira, su Yassar wadanda sun soma hankali sun ragewa zuƙatansu ƙiyayyar Humairar ba wanda ya goyi bayan zantukan Tasleem din.
Mami kuwa kamar yanda ta saba danne bakin cikinta da soyayyar yarannata a lokuta barkatai don siye zuƙatan yaran wannan karon ma haka ta yi.

"Koda wasa kar na ƙara jin makamanciyar wannan magana daga bakinki. Kina kiran mutuwa ga yar uwar da ke ganin girmanki. Ban san me yarannan suka tare maki ba. Kina dai kan gaɓar haihuwa ki ji tsoron Allah."

Mami na kai wa nan ta mike tana ɓata rai ta kama hannun Humaira suka yi daki wurin Ummita. Itama Raihana ta mara musu baya.

Tasleem ta ja tsaki.

"Ni ban ga amfanin abin da Mami take yi ba. Duk lalacewar naka, naka ne. Ta guji ranar da wadannan mutanen za su yi mata butulci."

"Uwar biyu kenan, sai kin zauna da su sosai za ki fahimci ba su da kowace matsala. Ni kaina a farko rashin ba Humaira dama ya sanya ni tsanarta amma yanzu da na dan zauna na saki jiki da su na fahimci kirkinta. Wallahi sosai na tausaya musu sadda suka yi nesa da mu, na kuma gane ina kaunarsu a jinina, ba zan iya fasalta yanda labarin cikin nan ya jefa ni ba. Duk da ban kai Yaya Mubarak shiga damuwa ba."

Fitowar wannan zancen daga bakin Dawud ya ba Futuha da Tasleem mamaki, dama akwai ranar da Dawud zai fadi mai kyau akan su Humaira? Yassar wanda shima bai jin ƙinsu ko kuma kaunarsu a zuciyarsa, dariya ya yi.

"Kai babban yaya ai ya faÉ—a, rannan Anna ke fesamin wai son Ummitan yake yi. Tana ta masifa da tsinewa zancen ta ce ko bayan ranta ba da yawunta ba."

"Wallahi ba za ta saɓu ba. Tab! Me Yaya Mubarak zai yi da sauran ƴan ta'adda?"

Futuha ta yi furucin a zafafe. Tasleem kuwa ta ma kasa cewa komai ji take kamar abin da ke cikinta zai fito idan ta ƙara magana saboda tsabar takaici da ya yi mata lulluɓi a ƙirji.

"To sai me? Ni wallahi don ya riga ni furtawa ne amma na ƙudurta ni zan aure ta matukar wancan Sahabi ya guje ta."

Cewar Dawud. Kiran sallar azahar ne ya tashi mazan, Tasleem ta dubi Futuha.

"Me kike tunani akan maganar cikin nan?"

Futuha ta yamutse fuska.

"To me zamu iya yi tunda an binne zancen ba a sanar da mu ba sai da ya fito?"

Tasleem ta yi ƙwafa. Ta ciro wayarta ta kira Jannat ta fesamata abin da ke afkuwa. Jannat ta feshe da muguwar dariya.

"Dakyau! Ki ce abu ya yi dadi? Toh ai wannan maganar ba abin a ɓoye ba ne. Ke ban da abinki tunda har ya afku ai zai fito. Kawai mu juya zancen mu yaɗa cewar dama karuwancinsu suka tafi, itama Humaira an keta mata haddi. Idan har duniya ta yarda ta amince kinga ai shikenan? Ban da Abbanku da DPO akwai wani da ya san an gan su kafin a kama su sun gudu?"

"Aa." Tasleem ta furta da sauri.

"Toh kinga idan ma an bada wannan hujjar zamu ce a kawo shaida, wacce kuma babu ita ba za a same ta ba."

Shiru dai Tasleem ta yi, Futuha ta zubawa Tasleem idanu, so take ta kammala wayar don ta labarta mata abin da Antin ta ce.

"Anti toh dan jira zan kiraki."

Daga nan suka ajiye waya, ta labartawa Futuha yanda suka yi. Tun ma kan akai aya Futuha ta hau girgiza kai.

"A'a, a'a, Tasleem kar ku yi haka. Nidai Futuha babu hannuna ciki. Ba fa sunansu kadai za a ɓata ba kenan har da na gidanmu. Nikam ba za'a yi haka da ni ba gaskiya, count me out!"

Tasleem ta harareta kawai sai ta yi shiru ba ta ce uffan ba. Futuha ta zubamata idanu, ta san halin muguntar Tasleem, shirunta na nufin abubuwa da dama.

"Ina fatan dai ba kina son cemin za ki haÉ—a kai da Anti Jannat ku aikata wannan babban kuskuren ba?"

"Sai aka ce maki bani da hankali ko? Mtsw."
Chapter 60 · 0% Book details