← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 18 OF 101

Sashe 18

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Ban damu da abin da kowannensu zai ce ba, ban kuma damu ko Raihana ta sauya ba ko aa, abin da na sani shi ne, ko a gaban waye, kuma a ko'ina ne, su din ko naƙi ko na so, ƴan uwana ne na jini, ba zan taɓa ganin abin da zai cutar da su na yi shiru na zuba ido ba, sai inda karfina ya kare. Kar mu ja zancen Ummita, ni yanzu damuwata Mami, ta ina zan soma wanke kaina a wajenta? Na mari diyarta har shatin yatsuna sun bayyana ƙarara a saman fuskarta, anya kuwa za ta karɓi dukkan hanzarina? Ni dai na san soyayyar uwa akan nata, dagaske ne Mami na yi mana so na hakika, amma wace uwa ce za ta kara kallonka da ƙima alhalin ka sa hannu ka daki nata?"

"Sai ni nan, Maryam."

Gaba daya suka kalli bakin ƙofar shigowa kicin din, Mami ce wacce ta tsinkayi zantukan Humaira na karshe. Humaira ta zuba mata idanu tana so ta ga ko za ta fahimci yanayinta, ba ta gane komai ba sai murmushin da ta gani kwance saman fuskarta. Kicin din ta karasa shigowa sosai ta ce.

"Sai ni nan Maryam, haba Humaira, kina zaton ba ni da hankali ne? Na sani duk yadda aka yi akwai wani abu da Raihana ta yi kika yi mata wannan hukuncin. Kar ki manta tazarr fitarku ba nisa, da nayi nazari sai na ga kodai wani wurin za ta je da bai kyautu ba kika bi bayanta? Kar ki sa komai a ranki, koda ba ki faÉ—i komai ba ni na fahimceki kinji ko?"

Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. Wai mami wace iri ce acikin matan uba? Komai nata daban ne, kirkinta da kawaicinta akwai mugun yawa. Sai kunya ta lulluɓe ta, ta sunkuyar da kai.

"Kiyi hakuri Mami. Ban yi..."

"Bana buƙatar ji ko sanin komai kinji ko? Komai ya wuce. Ku hanzarta shirya kayan abinci, Abbanku na jin yunwa."

Suka amsa da toh a gaggauce suka ci gaba da aiki, Mami ta fice daga kicin din fuskarta ba yabo ba fallasa.

***
Kwance take saman gadonta tana buga game a waya, hankalinta kacokam ya tafi a game din sai ga kira ya shigo. Ta yi tsam tana duban wayar, lamba ce da ba ta da masaniya a kanta. Ganin haka sai ta katse kiran ta ci gaba da game dinta, aka kara kira, ta katse, a na uku ta ɗaga a fusace amma sai ta danne ta yi sallama. Jin muryar namiji ya amsa sallamar ya sa ta jin wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa yatsun ƙafa, ba ta san ma'anr hakan ba.

"Ina mai ba da hakurin yi maki katsalandan a rayuwa. Hope ba za ki damu ba idan na ce jiya na karɓi numbernki wurin Ibb Gusau."

Shiru ya biyo baya, ita ba ta fahimci komai ba don har ga Allah ta mance da su. Jin shiru ya sa Fadeel ƙara magana a tausashe.

"Ok, ba ki gane ba ko? Jiya ni da abokina da ya ba ki numbernsa akan wannan saurayin ƙanwartaki, Musaddam nake tunanin sunansa ko?"

Nan da nan ta tuna komai, wannan me kama da aljanun ne mai shegen kallo. Ta ja guntun tsaki kaÉ—an.

"Uhm, na gane. Ina fatan lafiya?"

Ya yi shiru yana jin amsarta a wata kala na daban, madadin ta ba shi haushi sai kuma ya ji bai ji haushin nata ba.

"Lafiyar ce ta sa na kiraki. Suna na Fadeel, magana nake son mu yi amma ta fi ƙarfin waya, idan kin ba ni dama ko zan iya sanin kwatancen gidanku?"

Ranta ya soma ɓaci, ta ji wani abu na taso mata.

"Idan maganar ba za ka iya yinta a waya ba don Allah kada ka ƙara gangancin kirana. Hakan zai fi maka alheri, sannan ina bukatar ka goge lamba ta a wayarka, tunda ba wani muhimmin abu ne ya sa ka kira ba."

Tana kai wa nan ta katse kiran, ta yi wurgi da wayar saman gado, game din ma ya fice a kanta. Ita kaɗai ce a ɗakin, sai ga Raihana ta shigo. Ko kallonta ba ta yi ba ta mike ta faɗa banɗaki, koda ta fito ganin Raihanan zaune saman gadonnata yasa ta mamaki. Fuska a ɗaure ta ƙarasa.

"Malama lafiya?"

Jiki a sanyaye Raihana ta soma magana.

"Kiyi hakuri Humaira, na ja an maki faɗa an kuma zalunceki. Don Allah ki yi hakuri. Ina neman gafararki bisa dukkan abin da na taɓa yi maki a gidannan. Ban kara gasƙata kaunarki gareni ba sai a jiya da kika shanye faɗan Abba ba ki faɗi ainahin abin da ya faru ba. Wallahi na ji kunyarki sosai, kiyi hakuri ki yafemin."

Taɓe baki Humaira ta yi tana fadin.

"Ya wuce. Kar ki damu."

"Dagaske kike?"

Ta tambaya da sauri kamar za ta yi kuka don muryarta ta karye, Humaira ta zauna a gefe.

"Ni ban taɓa binku da kallon maƙiyana ba, kallon da nake maku na ƴan uwana ya bambanta da irin wanda ku ke yimin. Sai dai dukkan wannan ba zai sa na ga abin da zai cutar da ku na kasa magana ba. Idan na yi hakan na ci amanar kaunar da Mami ke nunamin. Raihana mutunci da darajar mace ya fi gaban ta tsaya ta siyarwa wani ƙaton banza a waje. Musaddam da kike gani wallahi ba zai taɓa aurenki ba matuƙar kika yarda kika ba shi kanki a waje, ke koda ba ki bayar ba, yaron ba aure ne a ransa ba face iskanci. Idan kuma dagasken auren yake sonki da shi, meyasa bai taɓa zuwa nan ƙofar gidanku da sunan zance ba, kema kin san karya ne kawai. Tun wuri ki yiwa kanki faɗa ki rabu da shi zai fiye maki alheri."

Raihana da tuni ta soma hawaye ta kamo hannun Humaira.

"Toh naji Humaira, amma wallahi ina sonsa, wani irin so ne da ban san yanda zan fara yakice shi ba a rai. So ne da ya rufemin ido naji ko me Musaddam zai nema a wurina zan iya yi mishi."

Sai kuma tausayinta ya lulluɓe ta, tana kuma godewa Allah da bai ɗora mata son kowane ɗa namiji ba balle har ya wahalar da ita.

"Wannan son za ki yaƙa, domin halaka ne a wajenki. Musaddam ba sonki yake yi ba muna nan da ke watarana za ki ban labari. Ki kai kukanki wurin Allah sannan ki shagaltar da kanki wajen duk abin da kika san zai dauke maki hankali daga tunaninsa. Nima kuma zan tayaki addu'a har sai Allah ya amsa, ya rabaki da wannan makahon son. Ke ina kika hango dacewarki da shi wai? Wallahi ta ko'ina ke din ba ajinsa ba ce, ban da ma dai shi son da kike ikrari bai san inda zai je ba, ai sawun giwa ya shafe na raƙumi."

Murmushi Raihana ta yi cikin jin salama, sai kuma hira ta buɗe tsakaninsu, tana ba ta labarin ainahin yanda aka yi ta hadu da Musaddam din. Humaira ta gefen ido na kallon wayarta da ke silent tana ta haske alamar shigowar waya amma ta yi biris da ita. Su na a haka Futuha ta dawo daga makaranta ta iske su, mamaki ya dabaibayeta, ta cire facemask din da ta sa don ɓoye kumburin gefen bakinta da Humaira ta daka, ba ta cewa Raihanan komai ba sai zama da ta yi gefen nata gadon tana ci gaba da kallon ikon Allah. Ita kuwa Humaira ko ta nuna ta san da wanzuwar wata a dakin bayan su. Can kuma Raihana na juyawa tana yiwa Futuha magana ta ga hasken wayar Humaira ta jawo.

"Lah, kinga fa kiranki ake ta yi. Lamba ce. Kodai Ibb ne?"

Jin sunan da ya fito bakin Raihana ya sa Futuha zaro ido waje a razane. Ita kuwa Humaira fuska ta yamutse.

"Waya sani, tun dazu ya kira wai wani kwatancen gidanmu."

"Wane Ibb din kika nufi Raihana?"

Suka dube ta, sam Raihana ta mance, yanzu me za ta ce idan Futuha ta dage akan son sanin komai? Kada dai allura ta tono garma. Ita kuwa Humaira sai a sannan ta tuno ashe fa a hirarsu tana jin Futuha na yawan maganar son da take yiwa Ibb Gusau da haduwarsa. Kodai shi ne Ibb din da take magana?

"Ibb Gusau wanda kika sani."

Humaira ta furta da murmushi saman fuskarta, ta karbi wayarta a hannun Raihana ta katse kiran amma sai ta sa a kunnenta kamar gaske ta hau fadin.

"Assalamu Alaikum, ina neman afuwa ka kira bana kusa. Fatan ka karasa gida lafiya?" Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice daga dakin, sai da ta isa falo sannan ta kwashe da dariyar ganin yanda Futuha ta cika tayi tam har gefen bakinta da ya kumbura sumtum yana kyalli. Ta dai san ta harba mata bomb a zuciya.10

Dariya take yi har ta shiga kicin É—in, Ummita dake amsa waya tana lumshe idanu ta yi azamar katsewa tana dubanta. Humaira kuwa ganin haka ta karasa fuska dauke da walwala tana bin ta da kallon tsokana.

"Waya kike amsawa ko? Shi ne ina shigowa kika yi saurin katsewa. Nidai ya kamata zuwa yanzu na san waye wannan majnun É—in naki."

Ummita dai ba ta tanka mata ba sai maida hankalin da ta yi wajen ɓarar tafarnuwa tana murmushi, sai kuma ta share zancen da hanyar fadin.

"Wai dariyar me kike yi ne?"

Sai a sannan ta tuna abin da ta yiwa Futuha, dariyar ta kuma taso mata. Ta fayyacewa Ummita labarin, baki buÉ—e take kallonta.

"Ke kuma ina kika samu lambar shi?"

Ita shaf ta mance Ummita ba ta da labarin komai, ta yi ajiyar zuciya. Labarin da ba ta so bayarwa ba amma ya zama dole ta sanarwa Ummita don ba ta da yar uwa kuma aminiya sama da ita. Ta labarta mata duk abin da ya faru da sanadiyyar marin Raihana ta kara da jan tsaki da fadin.

"Shi ne wannan mayen ya takuramin da kira fa, toh ita Raihana ta yi zaton ma Ibb din ne. Ni kuma don na shaƙawa ƴar banza shi ne na sa wayar a kunne ina wayar gangan na soyayya."
Chapter 18 · 0% Book details