Sashe 58
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
***
Gidan su Humaira tamkar gidan makoki, babu walwala a fuskar kowanne, Abba kasuwar ma kasa fita ya yi. Mami kuwa ta ƙulle a ɗaka ba wanda ya san me take yi. Ummita kuwa tana kwance shiru kawai har baccin dole ya dauketa sanadin magunguna da ta sha kuma a daren jiya ko kadan fargaba da damuwa sun hana ta runtsa.
Karatun alkur'ani Humaira ta kunna a waya ya karaɗe ɗakin don su samu nutsuwar zuciya. Tana sauraro tana bi a hankali ta hanyar motsa lebɓanta duk cikinsu sun kasa yiwa Ummita kwakkwarar magana don ba su san ta inda za su fara ba. Raihana kuwa kanta ta cusa karkashin pillow tana kuka a hankali tana kuma bin karatun. Ji take yi inama komai dake faruwa a mafarki ne. Amma ina, wannan zahiri ne, shi ne kuma gaskiya mai mugun ɗacin da ke addabarsu.
Hatta da Mubarak ya shiga wani irin hali, komai yake yi Ummita ce a ransa, bisa umarnin Abban ya bi su Yassar shago amma yana zaune cikin mugun ɓacin rai. Ya rasa dalilin da ya sa ta tsaya mishi a ƙahon zuci watakila kuma tsananin tausayi ne da duba da irin kirkin Ummitan yarinya mai kirki da sanin ya kamata. Bai taɓa ganinta ba face da murmushi saman fuskarta, tana da hakuri sosai da sanyi. Dabi'unta abin so ne ga kowane namiji.
***
Mami a hargitse take ta faman danna kiran layin wayar amma abu ɗaya kwamfutar ke nanata mata, a kashe wayar take. Koda ta gaji ta yi wurgi da ita tana mai jan tsaki. Goshi ta dafe cikin tsananin ruɗu. Can kuma ta ji wayarta ta ɗauki ƙara. Ta yi azamar karasawa saman gadon ta ɗauka. Lambar dai da take ta kiciniyar kira ita ce aka kirata da ita. Ta ɗaga cikin sauri.
"Kai Bala! Ina ka shiga ne?"
"Kiyi hakuri Hajiya, chaji na bayar sadda kika kira ba'a É—aga ba sai mai chajin kawai ya kasheta gudun a yi ta kira. Ina fatan lafiya?"
Ta girgiza kai idanu a runtse tamkar yana ganinta.
"Ba lafiya ba Bala, aiki ya ɓaci! Duk inda mutanen nan suke ina buƙatar ganinsu. Wannan karon ni da su zamu tattauna. Sun min ba daidai ba, na fadamusu dama idan har sakamako bai yi kyau ba to sai sun maidomin hatta rabin kudin da na ba su. Ba za su ci komai daga dukiyata ba tunda har kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba."
"Hajiya ban fahimci me kike son cewa ba? Ke ce fa kika ba su umarnin barin wajen koda kuwa kudaden ba su shiga hannunsu ba? Ta ya ya kuma za ki É—ora musu laifi kacokam?"
"Bala sun yiwa yarinya fyaÉ—e, yarinyar da ban so hakan ta kasance da ita ba. Da ace waccan mayyar aka yiwa ba zai dameni ba. Yanzu dai mugun abun da suka yi ya bayar da mummunan sakamako, ciki ya shiga."
Bala ya doka salati mai karfi. Can kuma cikin rage murya ya ce.
"Ciki kuma Hajiya? Toh me ake jira da ba za'a zubar ba?"
Mami ta sauke huci.
"Zubarwa ai wajibi ne. Dole na zubarmata da shi ko don gudun tonuwar asirina. Amma yanzu ni ka nemo min su mutanen ko kuma ka aikon lambar shi Babban nasu sai muyi magana."
"An gama Hajiya, zan kira na sanar da shi sai na hadaku a waya don dama ina shirin ce maki ba ya garin ya dan yi bulaguro zuwa Kaduna."
"Shikenan, sai ka turo."
Tana kaiwa nan ta katse wayar tana ji kamar ta zabga ihu, babu abin da idan ta tuna take takaici kamar rashin cin nasarar mallakar dukiyar Abba da ta kwallafa a rai. Ga kuma shirin tonuwar asirinta da ke son afkuwa, matukar cikin Ummita bai fita ba lallai babu shakka watarana abin ɓoye zai fito fili.
***
Mami ta tabbatarwa Abba lalali sai dai a zubar da cikin Ummita gudun zubewar mutuncinsu a idanun duniya. Tun Abba ya na nuna bai amince ba har dai ta ci nasara a kansa ya yarda.
Ranar da zasu je a daren Mami ta shiga wurin Anna don amsa kiranta. Anna ta dube ta a yamutse.
"Sai wani rawar ƙafa kike yi a cire cikin yarinyar nan, idan an cire wa kike tunanin zai aure ta? Shi Sahabin ko kuwa dai shi mijin naki ya ba babban ɗansa aurenta? Ba kya wannan hangen?"
Mami ta ji kirjinta ya buga da ƙarfi. Wannan zance na Anna ko kusa bai mata dadi ba amma sai ta zaɓi ta ɓoye saboda dalilin da ita kadai ta bar wa kanta sani.
"Idan har asirinmu zai rufu mene ne ciki Anna?"
Daƙuwa Anna ta wurga mata.
"Ungo nan nace! Ni dai da ace a asibiti nayi naƙudarki zan iya rantsewa sauyamin ke aka yi ba ke ce jinina ba. Yanzu ke koda wasa idan mijinki ya ce zai hada auren wannan gantalalliyar da ɗansa abin yarda ne a wurinki? Babban ɗanki wanda bai taɓa kusantar zina ba a duniya shi ne za ki yarda a hada shi da ita?"
Kafin Mami ta kai ga cewa komai Anna ta ji an bata amsa.
"Anna, kar ki kara danganta yan uwana da zina, kowa shaida ne ba zina suka aikata ba, kaddara ce da za ta iya faÉ—awa kan kowa. Sannan idan auren ne ma sai me? Ni ina sonta kuma na rantsemaki a yau Sahabi ya janye da batun aurensa da Ummita to fa ki rubuta ki ajiye ba ta da miji sai ni nan Mubarak!"
Ba Anna kadai ba, hatta da Mami wanda ganin inuwar mutum a farko yasa ta ɓoye abinda ke ranta sai da maganar ta yi mata wani irin duka a kirji. Ta dago tana kallon Mubarak din, sanin da ta yi mishi ba ya taɓa sauya magana. Mutum ne mai magana daya wannan ya yi matukar ɗaga mata hankali har ta kasa siyasar data saba na danne abin a zuciyarta. Fuskarta ta nuna tsantsar ɓacin rai na gaske, idanunta har wani kaɗawa suka yi tsabar bala'i.
"Mubarak! Kar ka kuskura na kara jin makamancin wannan maganar daga bakinka. Wacce kake faÉ—awa ka dinga tunawa ita ta haifar maku ni. Ka kiyayi harshenka!"
Mubarak ya yi shiru kawai yana jin zafin maganganun Anna har lokacin suna tarfafasa zuciyarsa. Anna kuwa ta hau zagin Mami tana fadin ta yi mata shiru ai da sa hannunta a rainin da yaran suka yi mata. Shi dai ya dubi Mamin ya isar da sakon Abba akan ta fito su wuce asibiti sannan ya kaɗa kai ya bar musu dakin. Mami ta mike ba ta ko biyewa maganganun Anna ba ta bar dakin. Wannan kalma ta so da Mubarak ya furta yana yiwa Ummita ya tsayamata a ƙahon zuci, abu ne da har abada ba za ta bari ya afku ba muddin rai.
***
A kokarin zubar da cikin Ummita aka kusa jaza mata matsala, zubar jini sosai ta shiga yi dakyar aka samu ya tsaya. Sai dai cikin hukuncin Allah mai kaddarawa cikin yana nan daram bai fita ba. Haka aka shafe watanni hr biyu ana fama da abu daya amma cikin bai ko girgiza ba wannan dalili ya sanya Abba cewa a hakura kawai amma gudun masu shiga da fita na gidan Ummitan ta rage fitowa falon idan ya so duk abinda take so a kai mata daki.
Ga biki ya matso amma sun kara neman alfarma an ɗaga bisa hujjar kayan dakin da ba a kammala haɗawa ba na Ummitan. Wannan abu mai yiwa iyayen Sahabi da shi kansa dadi ba, ga raɗe-raɗin da aka kawowa uwar Sahabi wai Ummita na da juna biyu, ko kadan ba ta ji ta amince da zancen ba, da hakan ne ai ta san iyayen Ummitan masu dattako ne ba za su ɓoye musu ba. Wannan yasa inda ta ji zancen anan wurin ta bar shi kuma a cewarta ai ciki ba ya ɓuya, idan har akwai to fa zai fito.
Mami ta yi nasarar samun wayar WIZZY. Wayarsu ta farko ya nuna bai ma san zancen da take yi ba don gaba daya hankalinsa ba a nutse yake ba gani yake kamar an hada baki ne don a kai musu cafka.
Sai da aka kwashi lokaci mai tsawo sannan ta kara nemansa a waya ganin dai cikin dake tattare da Ummita ya ƙi fita uwa uba ga wani irin kulawa da Mubarak ke yiwa Ummita wacce har gobe ba ta da walwala. Wannan abu ya tashi hankalinta ya kuma jefa ta cikin rudani da tsoro. Ya tabbata kenan idan ciki bai fita a cikin Ummita ba za ta iya zama rabon ɗanta nan gaba. Ta kuwa gwammace gwara ta sanar da Wizzy cewa Ummitan na dauke da cikinsa har na watanni hudu don su ga matakin da za a dauka a kai.
Cikin sa'a ya É—aga wayar.
"Wai Malama ba mun gama aikin da kika sanya mu ba? Kiran da kike yimin na mene ne bayan kin jaza mana asarar maƙudai?"
"Kaga Wizzy, kar ka yimin rashin kunyar banza da wofi! Ni na jazamaku asara ko kuwa ku ne kuka jazamin? Da na ba ku aiki na ce ku ketawa yarinya haddi ne? Shegen halin akuyancinku ya sanya kun afkamata yanzu yarinya tana dauke da ciki har tsayin watanni hudu."
Wizzy ya kantamo wata ashariya ya saki.
"Ciki kuma?!! Don uwarta ita din akuya ce daga yi sau daya sai ciki!"
Mami itama ji tayi tamkar ta sakar masa ashar, da kusa da ita yake a yadda take ji za ta iya shaƙar wuyansa har lahira.
"Ko mece ce ni ba wannan ne ya sa nayi kiranka ba. Mafita nake so, idan kuma babu to lallai kuÉ—ina ya dawo. Sadik shi ne sunanka na gaskiya, kai din haifaffen Katsina ne. Ina da kaf tarihinka na kuma san inda zan sameka, wallahi muddin ka bani matsala sai na yi maganinka."
Shiru ya É—an biyo baya tamkar ba zai ce komai ba don ba karamin dauremasa baki ta yi ba, ita kuwa Mami ta san komai bisa shawarar Hajiya Lubna, tun ma basu kai ga ba da aiki ba sai da suka sanya aka nemi dukkan bayanan sirri na wadanda suka ba aikin sannan suka amince.