Sashe 62
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Mahaifin Ummita ya fi mijina rufin asiri sosai, shi mutum ne mai arziƙi, matarsa duk sabgar dangin miji ta fi kowa gayu da kuma kyauta saboda mijinta yana da kuɗi. Ba ta da taƙama balle wani abu wai shi girman kai, wannan kyawawan ɗabi'unta da na tsana, da su ne ta siye zuƙatan uwar mijina kafin ta rasu, ta yi bake-bake a wurin yan uwan Yusuf, ba a ganina da mutunci sai ita. Duk yawan kirkina saboda mijina ba shi da kudi sai na zama tamkar mujiya. Eh uwar mijina tana sona amma soyayyar da take yiwa Jamila ya wuce gejin nawa. Saboda tsabar yanda tsanar Jamika ya rufemin idanu har gani nake yi ba a nunawa yarana kauna a lokacin alhalin ita ko haihuwar ba ta samu ba daga ta samu cikin sai ya ɓare. Haka na jero yara biyar Mubarak,Yassar, Dawud, Ƙassim da kuma Ke. Wannan lokacin ne kuma Yusuf ya zo min da labarin ƙara aure bayan mutuwar mahaifiyarsa, a sannan kuma ba laifi asirinmu a ɗan rufe yake. Yusuf har shago yake da shi a kasuwa yana siyar da kayayyakin agogo wanda ƙaninsa Muntari ya buɗe mishi. Wannan ma ya ƙara tsananta tsanar Jamila da Muntari a zuciyata ganin wato dai arzikinsu muke ci, da azumi haka Muntari ke sauke mana kayan abinci, da sallah, Jamila ke zuwa ta kawomana kayan fitar sallah wannan abu ya tsayamin a ƙahon zuci. Maijidda ita ce macen da ta soma lura da tarin ƙiyayyar da nake yiwa yar uwarta, akwai sadda ta taɓa ganina muraran ina yiwa Jamila barbaɗen magani a abinci wanda daga shi ne ta tsane ni ta kuma ce Jamila ta yi hankali da ni.
 Toh zuwan da Yusuf ya yi da batun ƙara aure ya yi mugun ɗagan hankali amma damuwa ko ta ɗigo ban gwada masa ba, a farko da na ɓata rai, sai ya rude da rarrashina, sai kawai na fashe da dariyar baƙin ciki na nunamasa tsokana ce kawai amma nikam bani da matsala da aurensa. Da wannan ya auro Fatima wacce ya haɗu da ita a kasuwa ta rako Dadarsu siyayyar kayan auren dan uwanta Umar. Shikenan soyayyar ta kai su ga aure. Anna ba ta tare da ni a sannan saboda mijina ba shi da kudi babu wurin da zamu ajiye ta, ita kanta a sannan zagina take yi wai don me zan maƙale nace sai Yusuf da ba shi da ko keken hawa. Nidai son da nake yi masa ya hana ni karɓar ƙorafe ƙorafenta. Ba ta damu da zuwa gidana ba a lokacin.
Aka yi auren Fatima da Yusuf, jininta ya hadu da Jamila. Madadin ni da muke dan shiri da Jamilar a baya, sai suka dinke da Fatima suka zama tamkar wasu ƙawaye, a sannan ina da cikin Tasleem, na kai zuciyata nesa na danne da taimakon shawarar sabuwar ƙawata Lubna da muka hadu a wurin wani bikin tsohon ubangidan Yusuf na kasuwa, mijinta mai arziki ne lokacin yana rike da matsayin Chairman. Da taimakonta na san Boka Babandi, muka niƙi ƙafa daga nan har Katsina wajensa ba tare da sanin Yusuf ba. Na samo magungunan hana Fatima daukar ciki muka dawo.
Cikinta na farko kuwa ya bi rariya, ni ce mai jinyarta da nuna mata ƙololuwar kulawa. Dadarta koda ta zo ta dinga sanyamin albarka da yabona. Yusuf kuwa tamkar ya haɗiyeni ganin a lokacin ko arba'in din Tasleem ban yi ba na haihuwa amma ina fama da kula da Fatima, wannan dalili ya siyomin sabuwar kauna a zuƙatan yan uwan Yusuf.
 Kamar kuma a mafarki ina dauke da karamin cikin Raihana sai ga Fatima da ciki har watanni biyar ya soma fitowa a jikinta, ba karamin firgita nayi ba da na gani saboda ko kadan ban ga wasu alamomi ba. Kuma na rasa yanda aka yi ko a hira ba ta sanar da ni ba. Hankalina ya yi mugun tashi, sai da na kai zuciyata nesa sosai kafin na iya danne damuwata. Ga wani irin soyayya da Yusuf ke nunawa Fatima har a gabana wanda nake ji kamar na shaƙe su duk biyun na huta. Ganin haka ni da Lubna muka ƙara miƙar hanya wurin Babandi, anan ne na je masa da buƙatar jefa tsanar Yusuf a zuciyar Fatima yanda ko sunansa aka ambata sai ta ji haushi. Babandi ya ban tabbacin ba ma Yusuf ba, kowane namiji sai ta tsane shi a rayuwarta muddin ya haɗa ta da wani arnen aljani. Da wannan na tattaro duka chanjina na ajiyemasa. Muka rabu da zummar zan ga aiki da cikawa, ya kuma ban wani hayaƙi yace duk sadda ta shiga halin ƙunci da kuka marar iyaka na yi mata hayaƙin. Wannan zai ƙara tasirin tsanar a zuciyarta. Da wannan muka rayu, Yusuf ya shiga tashin hankalin sauyin Fatima. Akwai radda ta taɓa shaƙe masa wuya dakyar aka ɓamɓare ta sai da na nemi taimako a waje, daga wannan ne kuma ya aikawa Dada saƙo ta zo takanas daga Nijar aka tafi da Fatima saboda ta rantse muddin aka bar ta ta cigaba da rayuwa a gidan za ta kashe shi ko kuma ta kashe kanta. Na yi kuka sosai kamar raina zai fita a gabansu, na ce su kyale ta ayi mata magani a nan idan har larura ce, Dada ta dinga rarrashina ta ce gwara ta tafi da ita. Daga wannan ranar ne na rabu da Fatima, rabuwar da har gobe ba ta ƙara tako Nijeriya ba. Wannan abu ya yimin masifar dadi, cikina nada watanni shida, Jamila ta haifi ɗiyarta mace mai sunan mahaifiyar Jamila, Rahina suke kiranta da Ummita. Sun yi gagarumin sunan kashe kudin da naji tamkar na dora hannu a ka nayi ihu da kuka ina ji inama Yusuf keda kudin Muntari. Da wannan na soma tunanin duk runtsi sai dukiyar Muntari ta zama rabon Yusuf watarana."
Mami ta numfasa ta karasa ta zauna gefen gado, ganin haka Futuha itama ta nemi wuri ta zauna, wasu abubuwan za ta iya tunawa wasu kuwa ba ta da wayo. Ta dai san Mubarak na yawan yabon mahaifiyar Humaira da kaunar da ta nunamasa, yayinda su Yassar suka tsaneta saboda tsanar da ta yiwa Abbansu. Maganar Mami ya katse tunaninta.
"Haka rayuwar ta cigaba har na kusa haihuwa, Yusuf gaba daya ya rame ya tashi hankalinsa saboa Fatima, ya kai mata ziyara har sau biyu daga nan ne hankalina ya yi mugun tashi, wato soyayyar da Yusuf ke yiwa Fatima ya ninka nawa kenan? Ban yi ƙasa a gwuiwa ba, ban kuma damu da cewar tsohon ciki gareni ba, na bi shawarar Lubna na niƙi ƙafa na koma wurin Babandi. Nan na nemi a yimin aikin da zai sa a raba Fatima da abinda ke cikinta da duniyar ma baki daya. Ya nunamin yanzu haka da muke magana Fatima naƙuda take yi, ya tabbatarmin zaa turamata baƙaƙen aljanun da za su yi sanadin rayuwarta. Na yi murna kwarai, amma abin baƙin ciki ya cemin abin da za ta haifa dole zai rayu a doron ƙasa, nidai ban wani damu sosai ba. Koda ya gama dubansa ya ce aikin zai yiwu haka na tattara na tafi da farin cikin Fatima za ta bar duniyar baki ɗaya. Za ta bar mijina. Sati uku da haihuwar Fatima, labari ya zo mana na rasuwarta. Zo ki ga kuka a wurina kamar zan shiɗe. Na nuna zan je gaisuwa, amma Yusuf ya hana ni saboda cikina ya shiga watan haihuwa, da wannan hujjar ya tafi har ina ce masa ƙafarsa ƙafar jaririyar Fatima ya kawomin ita zan riƙe. Wannan ya sa Yusuf ya ji dadi sosai ya dinga yimin godiya bisa kaunarsa da nake. Har a zuciyata addua nake kada a ba shi Humaira ya kawomin. Aikuwa haka ya dawo babu ita ya cemin wai Dadar ta daukarwa Fatima alƙawarin kula da Humaira, ya yi hakuri. Daga nan fa rayuwa ta dawomin sabuwa fil a gidan mijina. Daga ni sai yarana, na haifi Raihana bayan Jamila ta haihu da kusan watanni shida, Humaira na da watanni hudu itama lokacin. Shekaru suka tafi har aka shekara biyar, zuwa lokacin rayuwar kunci da talaucin ya ishe ni, samun Yusuf ya ja baya sosai. Gaba daya ya zamana hatta kudin makarantar yara daga aljihun Muntari yake fita, wannan ya kara sanyamin ƙiyayya mai tsanani na Muntari da Jamila. Ban samu sukuni ba har sai da na biya wasu yara suka haɗa gobarar da ba a fitar da komai a gidan Muntari ba sai Ummita."
Idanu waje Futuha take duban Maminta wannan karon.
"Ma..ma.." Ta ma kasa magana taabar firgicin da ta shiga da tsananin ruÉ—ani. Tana kara tabbatar da nisan da mahaifiyarta ta yi a fannin da suke ganin sun fi ta. Mamin ta yi yar dariyar mugunta.
"Yes, ni na sanya aka ƙona iyayenta, aka kashe jaririyar da Jamila ta haifa da Jamilar ma. Ban san ya aka yi shegiyar yarinyar ta tsira ba. Haka labarin gobarar ta zo mana, hankalin kowa ya tashi ciki har da ni da na nuna ban san komai ba. Shegiya Maijidda tun a sannan ta nuna ita wallahi ba ta amince gobarar gaske ce ta kashe Jamila ba. Ta ce a bincika amma kowa ya yi burus da ita ga tunaninsu kawai zafin mutuwar Jamila ne saboda irin shaƙuwar da suka yi da juna. Da nayi wani tunani akan dukiyar Muntari sai na shawarci Yusuf akan ya ɗau riƙon Ummita kar a raba ta da dangin mahaifinta. Nan fa ya amince, ya kuwa dage akan lallai shi sai an ba shi Ummita. Sun so yin fada da Maijidda wacce ta dage lallai ita za ta dauketa, a karshe dai da Kawunnansu suka sanya baki dole ta hakura ta kuma kalleni ta bini da Allah ya isa. Na fashe da kuka ina nunawa jama'a Maijidda ta tsane ni, nan aka hau rarrashina har yan uwan Jamila ana ganin baƙin Maijidda. Yusuf har kusan faɗa ya yi da Maijidda a kaina dakyar dai komai ya lafa. Wannan shi ne silar dawowar Ummita hannuna, daga baya kuma Humaira ta zo wannan kin sani."
Futuha ta ja dogon numfashi.