← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 28 OF 101

Sashe 28

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Na bar ki lafiya, ki yi hakuri na adana dukkan wayoyinmu, abin nufi nayi recording tun daga farkon wayarmu har na yau. Hakan kan ɗebemin kewa wasu lokutan idan son jin muryarki ya ci ƙarfin kwakwalwata. Ki dage da addu'a a wannan wata mai alfarma. Ina roƙon Allah ya yi maki zaɓin abokin rayuwa nagari, koda ba Fadeel ba."

Yana kaiwa nan bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta yi ƙuri tana duban wayar, hakan na nufin wayar ƙarshe ce tsakaninsu sai nan da shekara? Ta taɓe baki, ta sani cewa ta ba shi aiki mai wahala. Kuma ba zai ma iya shekara yana wahala a kanta ba. Watakila ma kafin sannan ya yi aurensa. Ta watsar da tunani ta yi jifa da wayar ta mike jin an soma kiraye-kirayen sallar isha'i.

***
Anna ce ke yiwa Mami faÉ—a kamar ta ari baki.

"Kin bari miji ya rainaki ya raina uwarki, dama tun akan batun auren Futuha na san cewa Isuhu ya sauya daga yanda na san shi. Wato yanzun ya ci moriyar ganga ya yar da koren, ke yanzu ban da ke sakara ce wawiya, kina tunanin har wani karfin iko kike da shi a wajensa? Mutumin da ya dubi tsabar idon mahaifiyarki ya ce ba zai janye kudurinsa na aurar da Futuha ba? Toh wallahi Maryama ki shiga taitayinki tun kafin dare ya yi maki, mazan nan dai babu amana bar ganin wai girma ya soma kama shi, don ya dankaro maki kishiya ƴar zamani ba komai ba ne. Tun wuri ki ƙwatarwa yaranki ƴanci a wajen mahaifinsu, ki murje idanunki dakyau ki daina bari yana wulaƙanta min jikokina akan wasu bare can. Ban da ma mutum mai shegen mantuwa, Isuhu ko kare ne ya fito daga gidan su Fatima zai kalla da daraja? Matar da ta nunawa duniya cewa ta tsane shi har kwanciya ciwo take akan sai ya sauwaƙe mata ta koma garinsu? Mts, Allah ya wadaran naka ya lalace."

Har Anna ta kai aya ita dai Mami ba ta ce komai ba banda huci da take furzarwa, daga ita sai zuciyarta ta bar wa sanin abin da take tunani. Dakyar ta taushi zuciyar ta soma magana bayan sakin ajiyar zuciya mai nauyi.

"Anna ki yi hakuri, babu amfanin mayar da hannun agogo baya tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Na ba ki wuƙa da nama akan ƙwatarwa jikokinki ƴanci, ki yi abin da kika ga ya dace. Sai dai ki sani, ni Maryam ba da yawuna ba saboda daidai gwargwado yarannan su na kyautatamin, ba ni na haife su ba amma su na bi na sau da ƙafa fiye da ma yaran da na haifa a cikina. Kiyi hakuri idan maganata ta maki zafi."

Anna ta wurga mata harara.

"Au haka kika ce ko? Toh shikenan, ni zan san abin yi a kai kamar yanda kika ce. Koda kuwa zan rasa kwabo a asusuna, zan kwatarwa jikokina Æ´ancinsu, sai ya zama Isuhu ba ya ganin kowame É—a a gabansa idan ba su ba. Mu zuba ni da ku."

Mami ganin yanda ta ɗauki zafi kawai sai ta miƙe itama ranta a jagule ta bar mata ɗakin. Da ace Anna ta san damuwar da ke cin ranta da ba ta soma ƙara mata fetur a kan wutar da ta riga ta soma babbaka a zuciya da kwakwalwarta ba. Ta ja tsaki ya fi a ƙirga a hanya har ta ƙarasa ɗakinta.

***
Azumi yana ta tafiya har a yau sun kai goma sha shida, lamarin su Tasleem da Abba ya ƙara tsauri musamman da ya fahimci ba su bi zancensa ba na shiga kicin. Futuhar da ta soma shiga, tun bayan faɗan da Abban ya yi ya goyi bayan Humaira sai ba ta ƙara leƙawa ba. Cikin ikon Allah wataran kwatsam sai ga shi a kicin din abin da Humaira za ta ce tun zuwanta gidan banda ranar da ya ji fitar gas ya cika gidan ya shigo, ba ta taɓa ganinsa a ciki ba. Ganin daga ita sai Ladidi da Ummita a kicin din ya shiga bambamin faɗa, a sannan Raihana na fama da Malaria mai zafi har allurai ta sha. Aikuwa har ɗakin ya shiga ya titsa ƙeyar Tasleem da Futuha zuwa kicin din yana gargadin Humaira akan lallai duk sadda ba su shiga ba ta sanar mishi. Tun daga wannan ranar ba su ƙara fashin shiga ba. Sai dai shigar da rashinsa ba amfani don kusan zama suke yi kawai ba sa komai.
Abba ya yi siyayyar kayan sallah, kamar kowace shekara wannan ma da kansa ya yiwa kowa zaɓi idan ka cire samarin da ya ba kowannensu kudi su siya shadda. Yanmatan kuwa atamfa ce iri ɗaya sai dai bambancin kala, sai dubu uku da ya ba kowace budurwa a siya takalmin sallah. Shikenan bai ƙara daga haka ba, su Futuha aka dinga kauɗi ganin Alhajinta ya kawo mata shadda da atamfa har da leshi masu tsada sai kuwa dubu ashirin na mayafi da jaka da kuma ɗan kunne. Tasleem kuwa dayake ta soma shaƙa sai ta budewa Hamza wuta akan ko kyautar biyar bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Ranar shi kansa ya yi mamaki da ta iya karya bille ta tambaye shi kuɗi, aikuwa ya ce ta turo acc no, take ya yi mata transfer dubu goma sha biyar. Tsabar rainin da ta yiwa kyautar ko faɗawa su Mami ba ta yi ba sai dai sun mata amfani ta siya abin da take so. Su Humaira kuwa Mami da kanta ta kara musu dinki, leshi mai kyau na ɗankwarai ta siya musu su uku kala ɗaya. Ana saura kwana biyar sallah sai ga Anti Jannat a gidan. Zuwanta ya yiwa su Futuha daɗi ko ba komai mace ce mai sakin bakin aljihu ga fankama. Burinta ta buɗa ko don ta nunawa Mami ita fa mijinta mai bayarwa ne, yana da kyauta sosai. Daidai da Anna ta fi ji da ita, abinda ya hana ta zama wajen Jannat din bai wuce na ganin surukanta sun nuna ba su kaunar hakan ba. A farko ta gwada amma aka so samun matsala, dole ta tattara ta dawo gidan da ta raina, gidan Abba.
Suna zaune a ɗaki bayan sun kammala gwada dinkunansu na sallah, ya yi musu cif da cif, washegari kuma sai tafiya kitso da ƙunshi. Sai faman tsokanar Ummita suke yi ganin saurayinta ya kira tana kashe murya a waya, koda ta ajiye Raihana ta dube ta.

"Wai ni yaushe za ki ba Ya Sayyadi damar zuwa gidannan?"

Kasancewar zuwa lokacin sun sani ba kowa Ummitan ke soyayya da shi ba face Ya Sayyadinsu na makaranta hakan yasa suka samu abin tsokanarta. Ashe wai dama yawan tashinta da yake yi ta biya musu karatu mai dalili ne. Ummita ta É—an harareta.

"Ke me ya hana ki ba Jafar daman zuwa gida? Ni ai mun kashe magana da shi, na ce ya bari sai nan da shekaru biyu ko ma ince É—aya da rabi idan mun yi candy, tunda yanzu muna SS2."

"Kai Ummita, shekara É—aya da rabi fa? Gaskiya sun yi yawa ina laifin ma shekara É—aya?" FaÉ—in Humaira dake tsaye tana maida kayanta sif. Raihana ta tari numfashinta da sauri ta ce.

"Wai ke ce mai yiwa wata faÉ—an shekaru sun yi yawa? Allah ya ba Fadeel hakuri. Wallahi idan na tuna abinda kika yi masa sai na ji kamar na yi maki dukan tsiya."

Ummita ma kwafa ta yi cikin kunar rai ta ce.

"Bar ta kawai Raihana, nima ba ki ji raina ba. Kuma babu kunya ba tsoron Allah har faÉ—amana take yi ya hakura sai nan da shekara. Shi marar zuciyar ina ne da zai biyemaki ya yi zaman jiranki? Ai tana sane, kora da hali ne kawai ta yi mishi. Ba fata nake maki ba, amma wallahi kafin ki samu kamar Fadeel a maza sai dai tsananin rabo."

Humaira ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki.

"Kanku ake ji, ni na faɗamaku ina so nayi auren ne? Auren ku yake burgewa ba ni ba. Sai me? Idan ba auren zan fasa rayuwata yanda ya kamata ne? Ya yi ma gangancin zaman jirana ya gani idan haƙansa zai cimma ruwa. Ya ƙare rayuwarsa a tuzuru."

"Allah ya kiyaye wallahi, bakinki ya sari É—anyen kashi. Fadeel ya wuce nan, kuma ina masa fatan alheri, ya samu haÉ—aÉ—É—iyar da ta fi ki komai Æ´ar kwalisa in sha Allahu." Cewar Raihana.

Haka kawai sai ta ji zafi a ranta, ta ji tana son yin kukan da ta rasa dalili, kawai sai ta fashe da kukan ba tare da ta yi shawara da zuciyarta ba. Raihana ta dubi Ummita kafin su dube ta jiki a sanyaye. Tun tana kukan su na ganin kamar wasa su na rarrashinta, har dai suka ga kamar kukan ba na lafiya ba ne suka fita da sauri suka yiwa Mami magana. Kai abin tsoro Humaira duk iyakar rarrashin Mami ba ta yi shiru ba, hakanan harafi É—aya ya kasa fita a bakinta. Mami ta juya garesu.

"Meyafaru ta soma kukan?" Nan suka ba ta labarin komai, ta ja hannun Humaira kawai suka fice a ɗakin. Su Raihana za su biyo bayansu ta dakatar da su, can falo suka tsaya yayinda Mamin ta shige ɗaki da ita. Sun yi jugum kuma sai ga Mamin ta fito ta dube su ranta a ɓace.
Chapter 28 · 0% Book details