← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 30 OF 101

Sashe 30

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ladidi dake tsaye tana ɗan tattara kwanuka ta amsa fuska a sake. Daga haka Mami ta juya itama ta bi bayanta. Dakinsu ta nufa, tun kafin ta karasa ta ji ƙamshi iri-iri na turare yana busowa. Hakan sam bai burgeta ba don ta sani Futuha ce da wannan aikin, yarinyar babu ruwanta da haramcin fesa turare mai ƙarfi ita kusan ma turaren maza ya fi burgeta akan masu sanyin ƙamshi marasa ƙarfi. Futuha ce kuwa tana tsaye an ci ado cikin atamfarta super mai kyau sky blue da ratsin fari da ruwan toka mara turuwa cikin wanda Alhaji ya kawomata, ta yafa blue mayafi mai kauri da girma kasancewar sallah za ta je yi sai takalminta mai shegen tsini shi kuma baƙi. Ko mahassadi ya sani ta yi kyau sosai, sai hotuna take ɗauka tana cuno baki. Ita kuwa Tasleem bata kai ga zuwa kayan ba tana tsaye gaban madubi tana gyara fuskarta, Allah ya taimaka an kwana da wutar nepa kuma an wayi gari da shi. A gajiye take likis, ta zauna gefen gado zaman jiran fitowar Raihana daga wanka, babu wanda ya ce mata ci kanki kamar yanda ita ɗin ma ba ta kula su ba. Tun tsawatarwar Abba ta samu suka sakarmata mara kaɗan, duk da a wasu lokutan ana bin ta da baƙar magana ko kuma kallon banza amma ko kallo ba su ishe ta ba. Su din ma ba kasafai yanzun suke shiga harkarta ba, sun fi maida hankali a hirar bikinsu. Kusan kullum sai an shiga instagram an ga tsarin bikin ƴan ƙarya ana cewa irinsa za a yi, ko kuma kayan amaryar sun yi kyau shi za su yi.
     Har ta soma buga hamma bacci na son kwasarta sai ga Raihana ta fito, ta mike Raihana na mata sannu da aiki ta amsa ta ɗau zanin wankanta ta shige. Tana fitowa ta hau shiri, itama Ummita tuni ta yi wanka kafin ta ta je shirya yaran Anti Jannat don haka tana shigowa shirin ta hau yi. Atamfarsu na wurin Abba suka sanya. Sun yi kyau abinsu tsaf kowacce da jilbab wanda ya hau da kayanta. Humaira kalar maroon ne nata, ya fito da farar fatarta sosai ta yi kyau sai rama da fuskarta ta yi ba ma ita kadai ba, dukkansu babu wanda bai rame ba a watan azumi. Itama Ummita ta yi kyau tsaf cikin jan hijabinta mai haske, sai kuwa Raihana da nata brown. Sun yi kyau gaba ɗayansu. Fararen ƴaƴan Mami kamar wasu larabawa. Haka suka jera har su Muhsin da Waleed da suka sha adon babban riga farare tas zuwa farfajiyar gidan. Nan ma su Yassar ne ke faman ɗaukar hoto hannun kowannensu saƙale da darduma. Yaran Jannat ma har da su, mota uku suka yi har da motar Jannat wanda mijinta ya siyamata tun kafin kamawar watan azumi kafin su iso gari saboda zirga-zirga da yaransa. Kasancewar ta iya tuƙi ita ta shiga su Futuha abokan hirarta suka shige motarta sai kuwa yaranta. Ummita da Humaira su na tare da Mami sai motar Abba da matasan yaransa ke ciki. Haka suka jera zuwa masallacin idi kasancewar akwai tazara da gidansu. A mota Jannat suka yiwa Raihana caa akan yanda take shigewa harkar Humaira da Ummita, ita dai ta hademusu rai kawai ta ƙi cewa uffan. Bayan sun yi parking suka karasa da ƙafa.
   Koda suka isa gida nan kuma aka tsaya yin hotuna a farfajiyar gidan, anan ne Raihana ta dinga yiwa Humaira hotuna kala-kala, ita kaɗai ta san me take niyyar yi. Ta kuma ranta sai ta aiwatar. Suna kammala cin abinci ana santin girkin Humaira, Abban da bai fiye kyauta ba shi ne har da ba Humaira dubu uku barka da sallah sakamakon girkin da ya yi mishi dadi sosai. Mami ta zuba na makwafta aka miƙa. Humaira ta ji dadi kwarai na yanda kowa ya ci sai ya yaba, hakanan abokanan su Yassar har da neman ƙari. Ita dai tana kammala ci ta yi daki ta sauya kaya zuwa doguwar riga marar nauyi ta shimfiɗe a gado ta hau ramuwar bacci. A sannan ne Raihana ta shigo ta dauki wayarta dake a gefenta ta fice zuwa falon.
Ummita da ta kammala tattara falon ta dube ta.

"Ke kuma me kike shirin yi da wayarta?"

Ta yi murmushi ba tare da ta kalleta ba ta amsa.

"Lambar masoyinta zan É—auka na turamasa hotunanta. Ko ba komai zai rage zafin takunkumin da ta sanya mishi."

"Um um Raihana, kada fa ta ji babu dadi."

Raihana ta É—an harareta.

"To ke za ki faÉ—amata?"

Taɓe baki Ummita ta yi gami da neman wuri ta zauna.

"Me ya yimin zafi? Ke ce dai abin ji tunda bakinki ba ya shiru."

Raihana dai ba ta ƙara tankawa ba, sai da ta tabbatar ta kwafi lambar Fadeel ta yi mishi sallama ta whatsapp gami da gabatar da kanta sannan ta mike ta maida wayar inda ta ɗaukota, baiwar Allah ba ta san ma meke faruwa a duniyar ba tsabar gajiya da baccin da ke kanta.

***
Mintuna kusan sha biyar da shigowarsu gidan daga masallaci, Fadeel wanda ya sha gayu da babbar riga fara ƙal mai kwalliyar baƙi, ya shige sashinsa ya bar Alhaji anan falon saukar baƙi tare da makwafta an kai musu abinci iri-iri. A duniya idan akwai abin da ke damunsa to fa babbar riga, ya matsu ya cireta. Hakan yasa tun kan ya ƙarasa ɗakin ya cire hularsa ya riƙe a hannu, yana shiga kuwa ya fidda ya ɗora saman kujera. Zama ya yi sannan ya fiddo waya ya hau kan whatsapp. Anan ya tadda missedcalls din ƙanwarsa Hannatu, ya danna mata videocall kamar jira take ta ɗaga. Sun jima su na hira har ya gaisa da mijinta da kuma ɗanta ƙarami kafin daga bisani su yi sallama. Sauka ya ƙara yi ya kira wayar kakansa wanda ya haifi Mamansa, nan ma ya gaisa sosai da ƴan Kamaru har da wasu cikin ƴan uwansa. Bai ajiye wayar ba sai da ya kira Mahaifin Ibb da suke kira Daddy ya yi mishi barka da sallah ya ci sa'a su na tare da Maama, itama sun gaisa ya kuma jaddada musu zai shigo zuwa anjima ganin Maama na faɗin ba ta karɓar miƙe ya zo har gida.
  Koda ya ajiye wayar sai ya ji wata irin nutsuwa ta ziyarce shi, wato dai babu abin da ya kai zumunci daɗi. Wayar ya ƙara janyowa, a hankali yake sarrafata har ya kai kan lambar da babu ranar da ba ya buɗowa. Kewar muryarta ya ke sosai, kullum cikin sauraron phone record dinsu yake amma ba su ƙosar da shi ba. So yake ya ji muryarta a zahiri, da kuma yana da dama ace ya ganta.

"Why all this?" Ya furta a sanyaye yana kallon lambarta kamar wanda yake jiran jin amsa daga garesu. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, damuwar da yake kwana da tashi cikinsa ita ce ta ke kokarin mamayeshi, idanunsa suka kaɗa. Kalmar kora da halin da Ibb yake faɗi ba ya so ya kasance gaskiya. Sai dai kuma ya sani, gaskiyar kenan, mai ɗaci. Amma ya zai yi? Ya kasa raba zuciyarsa da Humaira. Ya kuma kasa yi mata gangancin tura magabatansa kai tsaye wajen nata, ba ya son ta kalleshi a mugu mai son kai. Yana da yaƙini irin su Humaira idan suka faɗa tarkon so su ne masu riƙon alƙawari, zai wahala su ɓata ran masoyi da gangan.

Idanunsa ya sauka saman alamar faɗowar saƙonnin whatsapp da ke nuni ta saman screen din.

"Raihana ce ƙanwar Humaira."

Wannan saƙon shi ya ɗauki hankalinsa daga baƙuwar lamba. Cikin sauri ya buɗo whatsapp din ya shiga. Aikuwa idanunsa suka yi kyakkyawan gani saman hotunan abar kaunarsa. Ya rasa me zai yi don farin ciki da kuma dadi, ya ja filo ya yi jifa da shi ya mike tsaye ya shafi sumar kansa yana bin hotunan da kallo yana murmushi. Wannan zinariyar kuma lu'u-lu'u a cikin mata ita Ibb ke cewa ya rabu da ita? Inaa! Ba mai yiwuwa ba ne, sai ko idan ƙaddararsa ce ta zo a haka. Ya kasa hakuri kawai ya dannawa Raihana kira.

***
A lokacin tana tare da su Futuha a ɗakin Anna, ita kuwa Mami tana falo amsar gaisuwar ƴan barka da sallah yaran makwafta sai wasu a cikin ƴan uwan Abba da suka zo. Mikewa Raihana ta yi da sauri ganin sunan FH a saman screen ɗinta, ta san Fadeel ne. Ƴar barandar dake a wajen ta nufa ta tsaya gami da yin sallama. Ya amsa mata suka kara gaisawa kafin ya ɗora da fadin.

"Kin bani kyakkyawan goron sallah ƙanwata, na kuma ji daɗi sosai. Ki turon acc no dinki nima na ba ki naki goron."

Ta yi Æ´ar dariya.

"Aa Yaya Fadeel, ni wallahi don Allah na maka. Ba abinda ni da Ummita ba mu sani ba game da sharuÉ—É—an da Humaira ta gindaya maka. Ni kuma sai na ga wannan hanyar ce kawai zan yi na ragemaka damuwa."

Ya ji dadi kwarai, ya kuma tabbatar da cewa iyalan gidan abar sonsa su na da kirki kamar ita. Bai yi zaɓen tumun dare ba.

"Nagode sosai Ƙanwata, ki gaidamin Ummita. And please ki turo idan kin bani matsayi ɗaya da Humaira."

Ta amsa da toh sannan ta yi godiya. Koda ta tura ta yi mamakin ganin dubu ashirin matsayin barka da sallah, ya aiko da text ya ce su sha sweet. Ta kuwa hau washe baki da murna har su Futuha da Anti Jannat na neman ba'asi, sai kawai ta mike ta bar su tana dariyar jin su na cewa wai alert ta ji daga saurayinta. A dakinsu ta iske Ummita, karasawa ta yi a hankali ta ja hannunta gudun kar su tashi Humaira, Mami ta ce a rabu da ita ta huta. Sai da suka fito Ummita ta tambayeta.

"Ke wai mene ne?"

Ta nuna mata kuÉ—in da Fadeel ya turomata, Ummita ido waje don ba ta ma fahimci sunan ba ta dube ta.

"Wa ya aikomaki wadannan kudaden?"
Chapter 30 · 0% Book details