← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 89 OF 101

Sashe 89

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Tana kaiwa nan ba ta jira me Mamin za ta ce ba ta yi gaba da sauri ta fice ta bar kofofin hancin Mamin da shaƙar ƙamshin da ta bari. Bayan fitarta Mami ta ɗan dafe goshi, meyasa? Meyasa ta ke kasa sarrafa kanta a kwanakin nan, gaba daya ta kasa hakurin ɓoye abin da ke ranta. Amma ta sani adalilin wannan daukakar da ta zo ga Humairar ce alhalin nata yaran na watangalili a gidan mazajensu sun kasa samun jin dadi da walwalar da ta so musu.

"Ya zama dole na kula kada taɓarɓarewar abubuwa su fi wanda nake fuskanta a yanzu."

Ta yi furucin a fili, ta kalli wayarta ta ƙi fitar da ita daga plane mode ba don komai ba sai gudun abin da Wizzy zai fesar mata. Ta san ba za ta ji mai kyau da kuma dadi ba don haka ta yi watsi da lamarinsa.

***
Futuha ce kwance a falonta tana danne-danne a waya kamar yanda ta saba, sai ta wuni gida a ƙazance idan har ba yarinyar da ke mata aiki ce ta zo ba. Ba ta kauda ko tsinke, girki ma hakanan take hakuri da yanda yarinyar ke jagwalgwalawa ta kawomata.

Kira ne ya shigo wayarta, sunan ƙawarta Aina'u da ta gani ya sanya ta ɗagawa.

"Marar mutunci, sai yau kika tuna da ni?" Cewar Futuha cikin walwala.

Tsaki Aina'u ta ja.

"Ba dole ba, ke yanzu don wulakanci da daukata da kika yi ƴar iska kika kasa sanar da ni abin bakin cikin da ya sameki, koda dai na ji muryarki ma babu wata alama na ɓacin rai."

Sai tunanin Futuha ya ba ta ko batun Anti Jannat take yi, kasancewar Aina'un ta san Jannat sadda suke gida. 

"Toh banda abinki wannan ai ba abin yayatawa ba ne, don ma dai kudaden da aka buƙata babu wani yawa, just 10millions fa."

Wani uban ashariya Aina'u ta saki ta wayar kafin ta ce.

"Kada dai ki cemin ba ki da labarin auren da Yakubu mijinki zai yi da Ƴar Snow?"

Ai sai ga Futuha a tsaye kirr saman ƙafafunta. Kirjinta wani dukan tara-tara ya shiga yi.

"Wannan zancen banza ne kike yi, Yakubu fa yana Dubai. Wace Ƴar Snow din kike maganar zai aura?"

Wata dariya Aina'u ta saki.

"Lallai Futuha wayonki ya tashi a banza. Toh ita Ƴar Snow din kika san ina take? Wallahi tana tare da shi a can ma suka hade lefen nan da kika ga hotunansu, ina maki magana ba cikin satin nan ya ce maki zai dawo ba? Toh tare za su taho da ita kuma yana zuwa aure za'a daura. Gidan da ya fidda ki a ciki, nan zai ajiye ta har an ƙara yi mata wani mahaukacin gyara ya yi kyau."

Ihu mai karfi Futuha ta saki har sai da ta razana Aina'u.

"Ƙarya kike yi! Ba dai mijina ba! Ke uban wa ya fadamaki duka wannan?! Aina kar ki kashe ni, kirjina zafi yake ina ganin dishi-dishi."

Aina'u ta hau rantsuwa da Allah akan dagaske take yi, kuma ta ce tunda har ba ta aminta ba za ta hankaɗo mata hotuna ta sha kallo. Ko sakanni biyar ba su yi ba da ajiye wayar Aina'u ta aikomata hotunan da Ƴar Snow ke ɗorawa tana rufe fuskar Angonta. Gaba daya Yakubunta ne a hoton. Ta kuwa buga wayar jikin talabijin dinta gami da fasa uban ƙara. A haukace ta shiga daki ta dauki mayafi sai gida.

***
Raihana bayan da ta lura hankalin kowa ya tafi akan Humaira da Hajjo ke yiwa gyaran jiki kasancewar yaran Baba Amina sun zo itama tana dakin, sai ta mike ta nufi bangaren Abba. Mami ta fita unguwa, cikin sa'a ta iskeshi zaune shi É—aya ya kammala shan fura. Ganinta ya sanya shi É—an zubamata idanu da amsa sallamarta.

Ta ƙaraso ta zauna a gefe.

"Rahane (sunan da ya ke kiranta a wasu lokutan), ba ki da lafiya ne kwana biyun nan?"

Ta sunkuyar da kai gami da bude baki cikin sanyin jiki ta amsa.

"A'a Abba, lafiyata kalau."

"Kin kasa cire maganar can a ranki ko? Meyasa ba kya jin nasiha? Nace maki ki bar komai a hannuna tun da na riga da na ankara toh da yardar Allah hakan ba zai ƙara kasancewa ba. Ai wataran za a kuma kwatawa, kinga sai ya kasance muna da shaidu ba kamar yanzu ba."

Raihana da tuni hawaye sun jiƙa fuskarta ta gyaɗa kai da ɗan jan majina.

"Toh Abba, dama na dauki lambar wanda Mami ta kira a ranar ne shi ne nace bari na kawomaka nasan zai taimaka wajen bincike."

"Ya aka yi ta bari kika taɓa wayarta? Na sha gwada yin hakan amma ban samu nasara ba."

Ya fadi cike da jin dadin wannan nasara, ko ba komai za'a bincika a kamo shi yaron da aka sanya ya aikata laifin. Ta ba shi labarin yanda aka yi ta dauka sannan ya fiddo wayarsa ta sanya masa lambar.

"Kiyi hakuri Raihana, na sani daga ni har ke mun kasa yarda da abin da yake a zahiri saboda inda ake zatonsa ba anan aka iske shi ba. Abin ya zo da daure kai da al'ajabi, ina fatan wannan ba zai hana ki cigaba da yin biyayya gareta ba, kema kuma ina fatan da zarar kin kammala jarrabawa ki yiwa shi yaron can magana ya fito a yi magana."

Gyada kai kawai Raihana ta yi, ita yanzu komai ma na duniyar ji take ya sire mata, har kullum fargabarta bai wuce da idanun da za ta dubi Humaira idan wannan É—anyen aikin na Maminta ya fito ba.

Daga haka suka rabu da Abban. Shi ko Abba kai tsaye ya tura lambar zuwa ga D.P.O sannan ya kirashi suka yi magana. D.P.O ya tabbatar masa da yardar Allah za su bincika har su cafke mai wayar. Da haka suka yi sallama.

***
Babandi kenan, baƙin kuma gabjejan ƙato mai tumbi zaune saman kujera ya ci uban rawanin da ko zafi bai yi masa. Mami na daga gefensa a zaune, falon tsaf sai iskar fanka ta ko'ina domin gidan Malam Babandi solar ce ke aiki. Tsohon Malami ne kuma babba da ya ci ya hantse da haram. Ya dubi Mami dakyau.

"Gaskiya Hajiya Maryam akwai matsaloli sosai. Na farko kin yi saken da yaranki suka san komai dangane da abin da kika shuka, wannan idan ba ki manta ba yana daga cikin sharuɗɗan da na taɓa gindaya maki a baya, wato kar ki kuskura a yanda kika faro mu'amalarki da kowa, ki bada ƙofar da wani ko wata zai ji. Idan ban manta ba kwanaki can kin faɗamin kin sanar da ita babbar yarinyarki, koda muka bincika muka ga ba zai haifar da matsala ba amma duk da hakan ai na kwaɓe ki. Yanzu dai ita wannan yarinya taki ta biyu, Yasmeen take ko?"

"Tasleem." Mami ta gyara masa da muryar da ta fito daga can ƙasan maƙoshinta, a duniya ba ta son rashin nasara a kan komai ma ba wai iyalinta ba.

Babandi ya cigaba da zancensa.

"Yauwa Tasleem, yarinya ce mai taurin kai da kafiya a yanda na gani, zai wahala ta iya bar wa cikinta komai."

"Nidai don Allah Babandi a yi dukkan abin da ya dace idan har kwalliya za ta biya kudin sabulu, sannan batun auren ita Humaira da yaron can, kiyi hakuri, ban hango wani katanga da zai yi sanadin rushewarsa ba. Sai dai abu ɗaya, ki zaɓi ta ɓangaren da kike son a musgunawa rayuwarta mu gani ko zai yiwu. Abu na gaba kuma wato mijinki Isuhu, ba zan ce maki ga abin da na gani ba, amma wacece Maijidda? A zuri'arsu akwai wata mai suna hakan ne?"

Gaba daya abubuwan da yake faÉ—i tana jinsa ba don tana fahimtar komai ba, ba ta tashi dawowa hayyacinta ba a gigice sai da ya ambaci Maijidda. Ta ji dam! Wata iriyar faÉ—uwar gaba. Idanu waje take dubansa.

"Me..me kake son ka ce?"

Babandi ya girgiza kai.

"Tambayarki nayi ko akwai Maijidda? Ai ban ce ba tukunna."

"Babu, ba mu da wata Maijidda hakanan shi kansa Alhajin."

Babandi ya yi wani irin murmushi gami da girgiza kai.

"Toh ai shikenan."

Ta dube shi cikin fitar hayyaci.

"Me zai faru da shi Isuhun da Maijiddar?"

Ya É—an zubamata idanu sai kuma ya numfasa.

"Duhu na hanga, ban gane komai ba. Na dai ga wata an kuma cemin Maijidda ce. Ban san manufar hakan ba."

Gumi ne ya shiga kwaranyo mata. Maijidda dai? Toh don uwar Maijiddan me za ta yi a rayuwar mijinta? Kada dai waccan tsohuwar kilakin da duk mijin da ta aura mutuwa yake yi ita ce Maijidda da Babandin ke nufi? Toh ma da take tunanin aure ne zai faru tsakanin shi Isuhun da Maijidda?

"Ina!! Wallahi na rantse maka idan ni Maryama ina raye Babandi ba ka isa ba! Ashe dama kai macucin banza ne?! Wato aure ka hanga tsakanin baƙar annobar can da mijina shi ne za ka yimin na ƴan bariki?! Lallai kai cikakken marar hankali ne da tunani! Ni Maryam kake tunanin ina raye san bari Isuhu ya auri wata bayan ni?!"

Babandi ya ji zafin maganganunta.

"Hajiya Maryam kar ki sake ki zage ni. Ni nace maki na hangi aure ko zama tsakani? Har yau duk da irin shekarun da muka kwashe da ke ki iya kallon cikin idanuna ki kira ni da marar hankali kuma macuci?!"

Idanun Mami sun rufe ruf akan baƙin kishin da ya tasar mata, ji ta yi kamar Abban take gani zaune a gabanta. Babu abin da take haskowa sai tabbatuwar aure tsakanin Maijiddan da Abba. Jikinta kuwa har rawa yake yi don haka a harzuƙe kuma cikin kururuwa ta daka masa tsawa.

"An kiraka ɗin! Nace ka yi uwar da za ka yi Isuhu! Ni ce ma banzar da na zauna sauraron tatsuniyoyinka marasa kan gado. Yo mutumin da yake da mata har huɗu hakan bai isheka ba kana neman almajiranka maza kai zan tsaya ka magancemin matsalolina alhalin kodayaushe lalacewa yake! Ni nan na ishi kaina! Zan yiwa kaina komai! Daga yau idan ka kara ganin ƙafata a inda ka ke kirani da wani sunan ba Maryam ba!"
Chapter 89 · 0% Book details