← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 38 OF 101

Sashe 38

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 6 min read

A gaggauce ta sanya doguwar riga da mayafinsa ta tayar da sallah, Ummita na zuwa suka ɗunguma suka fice bayan kowacce ta dauki dukkan abin bukata. Babu nisa sosai da unguwarsu, Yahaya Gusau sula je gidan wata yayar ƙawar Raihana ta makaranta, ana kammalawa suka shirya a gaggauce matar ta yi musu ɗauri. Tsayawa kwatanta irin kyawun da suka yi ma ɓata baki ne. Idan ka kalli Raihana ka yaba, idanunka na sauka kan Ummita za ka ce ta fi su kyau duk kuwa da cewar ta fi su duhun fata, amma idan kallonka ya sauka ga Humaira sai ka yi saranda. Sun fito fes cikin ankonsu na atamfa na kamu. Raihana ce ta biya kudin kwalliyar ta account dinta, ta dai ce musu Mami ce ta ba su don haka ba su matsa da tambayar ba. Ta ɓoyemusu daga aljihun Fadeel ya fito, shi ne kuma ya matsa mata akan sai ta karɓa yana son Humaira ta yi kyau. Hotuna sosai Raihana ta dauke su, ta tura mishi na Humaira kaɗai.

A  gidan suka bar kayansu suka fice. Kai tsaye Manal Event Center suka nufa. Wurin ya tsaru iyaka, kowa ka gani da irin nasa haɗuwar. Babu laifi kamu ya yi kyau sosai, Humaira tun da ta nemi guri ta ƙame ba ta ko motsa ba ballantana ta yi rawa. Ummita dai ta ɗan fita amsa wayar Sahabinta, ta kuma dawo Anti Jannat ta haɗa ta da ƴan biyu akan ta zauna da su kar su fita, hakanan ta zauna tare da Humaira da wasu cikin yan uwan Abba, su din ma ba duka suka zo ba.

  A gajiye suka koma gida, kowa ya nemi wuri ya kwanta bayan idar da sallah. Su Futuha gaba daya sun bar kwana a dakin, daki daban suka koma tare da kawayensu wanda babu komai ciki, daga shimfiɗaɗɗen kafet sai katifu sai kuwa fanka dake wulwulawa.
 
***
  Tafe yake zuwa sashin Anti Amarya. Kusan kwanaki sama da biyar kenan rabonsu da juna, ba don komai ya dauke kafa daga shiga cikin gidan ba sai Murja da take neman matsawa rayuwarsa da kallo da kuma hirar dole. Tuni ya taka mata burki da zuwa sashinsa tun bayan da Alhaji ya sanar da shi saƙonta.
  Yau ɗin ma, Alhaji ne ya ritsa shi akan Anti Amaryar tana tambayarshi wai ko ba ya gari. Nan fa Alhajin ya yi mishi faɗa sosai ya ba shi hakuri. Don ya wanke kansa ne kuma zai je a yau din. Da sallamarsa a baki ya tsaya har aka amsa sannan ya shiga. Wacce ba ya kaunar ganin ya ci karo da ita kuwa a kwance tana chatting, daga ita sai vest da dogon wando. Ya kauda kai ya juya zai koma, sai ya tsinci muryar Anti Amarya.

"Ah, Fadeel ya za ka juya? Shigo mana. Ke kuma je ki suturta jikinki." Ta karashe maganar ƙasa-ƙasa tana duban Murja. Ta kuwa mike da saurinta ta yi ɗaki, yau ji take kamar an mata albishir da gidan aljanna, ba ta san haka ta yi kewar Fadeel din ba sai da ta gan shi a gabanta yanzu babu zato. Don haka da sauri-sauri ta zumbulo hijabi ta dawo falon. Lokacin ya maida hankali suna gaisawa da Anti Amarya.

"Ai ni Fadeel na rasa laifin da na aikata gareka. Na ma yi zaton ko ka yi tafiya ne ashe kana gidan amma ka ɓuya."

Ya yi murmushi yana ɗan shafar ƙeya.

"Ko ɗaya Anti, babu abin da kika yi. Abubuwa ne suke ɗan riƙe ni, nakan fita da wuri sannan lokacin da zan shigo dare ya yi shiyasa. Amma tuba nake, ganinan yau na shigo."

Ta yi Æ´ar dariya.

"Toh shikenan ya wuce. Dama Alhaji ne na ga kana kawowa Meatpie da Samosa mai shegen dadi, har nake tambayarsa inda kake odarsa. Gaskiya ya yimin sosai, ina so ne a yimin na birthday É—in autanku (Abdulmaleek) nan da two weeks, ko zan iya samun lambar waya?"

Fadeel ya yi murmushi, ya na so a duniya ya ji an yaba da girkin Humairarsa. Kafin ya ce komai sai ga Murja ta tsoma baki.

"Eh wallahi Anti, nima naji dadi. Babu tauri kuma komai ya ji a ciki sosai. Please ki yi order a wurin."

Ya yi shiru kaÉ—an, ya sani ba shi da matsala koda ace ya ba su lambar Humaira tunda dai oda ne zasu yi. Ba ya tunanin kuma Murja ta san wacece, ba ma ita ba, shi kansa Alhajin bai san daga inda Fadeel ya yi odar ba don haka hankali kwance ya ce.

"Toh Anti, zan turomaki ta message sai dai zuwa yanzun suna cikin biki ne ba za a samu ba. Kafin dai zuwa kwanakin da za a yi taron sun kammala."

Anti Amarya ta jinjina kai. Murja dai É—if ta yi da ta fahimci ko ma wace ce dai mace ce yar uwarta. Abin damuwar tana da aure? Sunanta Humaira? Shi ne ba ta da masaniya. Ita a duniya yanzu mai suna Humaira take son gani wacce Fadeel ya mato a kanta. Dama kawai take jira ta buÉ—e wayarsa ta bincika wanda hakan da kamar wuya.

***
 A can gidan Alhaji Isuhu kuwa, yau aka wayi gari da daurin auren yarannasa wanda ya tara dubban jama'a daga wurare daban daban. Babu ma kamar jama'ar Alhaji Yakubu kasancewarsa mutum na mutane.
Cikin gidan ko tun bayan da suka samu labarin an ɗaura auren, nan ya rincaɓe da guɗa da murna. Su Futuha amaren zamani idanun nan ko ɗigon hawaye babu sai ma murmushi da suke dokawa. Sun sha kwalliya da farin leshi sun yi kyau har sun gaji. Su Ummita kuwa shadda ce ruwan madara da aka yiwa kwalliyar stones suka sanya wanda Mami ta yi musu. Duk inda suka wulƙa sai an kalle su an kuma. Ƴan uwan Mami gulmar masu gulmarta suna yi, a cewarsu ta riƙi bare kamar ƴan cikinta, wataran za a wayi gari sun mata butulci. Yayinda a gefe dangin Abba ke yabon Mami da irin yanda ta ɗauka ki Humaira da Ummita, sun sani ba ta da laifi ko kaɗan a rashin zuwansu gidan sai ko na Mahaifiyarta Anna. Shi ma Abban da bai ba su fuskar su shigo jikinsa ba ya sanya suke ja baya. Sam Abba ba mai sakin aljihu ba ne, hakan ya sa yake ganin kamar duk wani da zai raɓe shi a yan uwan toh fa buƙata ce ya zo da ita koda ba hakan ba.

An sha hotuna sosai, da yamma Amare suka kara shiri cikin atamfarsu mai É—an karen tsada. Aka sha yini, sannan bayan Magriba aka hau shirin Dinnerparty.
Nan ma ya yi kyau sosai, Angwaye da Amare sun sha ado, Amaren sun yi shigar golden lace su kuwa angwayen golden shadda. Ƙawayensu ƴan ƙarya kowacce ji take da kanta. Su ma Humaira leshi Mami ta yi musu coffee colour mai ratsin golden. Sun yi kyau kwarai.
Washegari aka tattara da yammaci aka miƙa Amaren ɗakunansu. Gidan Futuha a rijiyar zaki yake. Danƙareran gida ne na Alhaji Yakubu mai ɓangare uku, nashi sai uwargidansa sannan na Futuha a gefe. Yan uwanta sun yaba sosai da gidan, ga kaya na alfarma da Abba ya yi musu bisa jajircewar Mamin akan ya daure ya fita kunya. Koda suka nufi sashin Uwargida suka iske shi a garƙame, sun bubbuga ya fi a kirga amma shiru, dole haka suka juya da ita zuwa nata ɓangaren suna mita. Wasu na fadin tana nan sun ga sadda aka buɗe labule ana leƙen zuwansu daga wani window a sama.

Daga nan suka wuce Kuntau inda anan ne gidan Tasleem yake, babu laifi shi ma ya haɗu. Flat house ne amma an kashe mishi kudi daidai misali. Ita kadai ce a gidanta sai dai gidan iyayen Hamza na kallon gidan, sai da aka shigar da ita wajensu suka karɓe ta da hannu bibbiyu aka yi ƴar nasiha da addu'a kafin a kai ta gidanta.
Chapter 38 · 0% Book details