Sashe 64
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Ba ta taɓa jin wani irin sanyi da nutsuwa tattare da kasancewarta da Fadeel ba sai a yau kuma a yanzun da yake kwararo mata waɗannan shawarwarin. Sai gaba daya ya tuno mata da Kawunta da ma Dada, ta tuna da kalar rayuwarta a Nijar, koda wasa idan ta idar da sallah, Dada ba ta barinta ta bar saman darduma sai ta yi nafila ta kuma tsaya ta ga ba ta yi wasa da addu'a ba, hakanan tilawar Alkur'ani, duk juma'a Kawunsu na tattara su har yaransa su yi tilawa, kowacce ta biya inda ta iya. Shaiɗan kwarai ya yi tasiri a zuciyarta da har ya sanya ta yi watsi da dukkan wannan, ta zama daga ta idar da sallar asuba sai bacci ba kamar a farkon zuwanta Kano ba da ma rayuwarta a Nijar inda koda wasa ba ta isa ta koma shimfaɗarta ba har sai rana ta fito bisa koyarwar Dada. A farko tana yi daga baya duk ta watsar. Ummita duk ta fi wannan kokarin. Ita kuwa kasala ya mata yawa.
"Kinji? Please."
Ya kara nanatawa. Ta dube shi sai ta yi murmushin da rabon da ya gan shi saman fuskarta har ya mance. Ta gyada mishi kai.
"Naji, nagode sosai da tunatarwa kuma zan kiyaye in sha Allah."
Ai sai ya ji tamkar an jefa shi wata duniyar ta nishadi da farin ciki, sai kawai ya rasa me zai ce ban da leɓe da ya ɗan lasa yana maida mata martanin murmushin. Ƙarar hon da aka danna da ƙarfi ya sanya suka dubi wajen, har ga Allah shi Fadeel ya ma mance adadin mintocin da aka yi mishi alfarmarsa, balle kuma Humaira da ta lula tunanin sakancin da take yi da addu'a tun zuwanta garin. Tasleem ce da wannan aikin ranta a mugun ɓace.
"Nagode, kije suna jiranki. Sai mun yi waya ko?"
Ta ji tamkar ta ce eh, sai kuma ta fasa ta juya kawai ta kama tafiya, ya bita da kallo sai kuma ya buÉ—e motarsa ya shiga, ya sani Abba ba ya nan balle ya shiga su gaisa. Don haka ya yi ribas aka buÉ—e gate ya fice. Itama tana shiga gaban motar kusa da direba, direban ya ja suna É—agawa juna hannu ita da Raihana.
Tasleem da Futuha a bayan motar zaune sai yare suke yi. Ita kuwa duk ta tsargu amma ta haɗiye ɓacin ranta.
Tasleem ke mitar dole ne ma Humaira ta rabu da Fadeel tunda har ita ba ta same shi ba to kowa ma ya rasa. Yayinda Futuha ta ce ta kwantar da hankalinta soyayyar babu inda za ta kai. Haka suka yi ta gulmar Humaira ba tare da ta tsinci ko harafi ba. Ba ta da haÉ—i da buzaye balle ta fahimci akan abin da suke tattaunawarsu.
Har aka sauke Tasleem, ba ta da walwala, ganin haka itama Humaira ta ja jikinta ko ki gaida gida ba ta ce mata ba.
A gidan Futuha, ɗakin dai da ta taɓa sauka wannan karon ma shi ne ya kasance masaukinta. Ta ajiye jakar kayanta ta faɗa ta ɗauro alwala ganin ana dab da kiran sallar magriba, sai a lokacin ta jawo waya ta kira yar uwarta Ummita. Suka ɗan taɓa hira don ta ƙara kwantar mata da hankali, cikin ikon Allah ma sai ta ga ko a muryarta babu wata damuwa. Koda ta ajiye ta kara tsunduma da tunanin Fadeel, wai me ya yi mata ne ma da har ta tsaneshi hakan? Oho, ta ba kanta amsa, sai kuma ta ja tsaki cikin jin zafin rai, to meye nata ma na tsayawa tunaninsa? Don haka sai ta miƙe ta shimfiɗa darduma jin an soma kiraye-kirayen sallah. Koda ta idar sai da ta yi nafila sannan ta yi salati da istigfari. A karshe ta yi addu'a sosai. Sai kuma ta tsinci zuciyarta da yin wani sanyi tamkar an yayemata wata damuwar. Sabuwar wayarta ƙirar Huawei da Abba ya damƙa musu bayan fitowarsu daga hannun ƴan ta'adda ta yi ƙara sauti mai dadi shaidar shigowar saƙo. Ta ɗauka ta duba.
*_Babu wata damuwa ko baƙin ciki da Allah ba zai iya magancewa ɗan adam ita ba. Ki miƙa dukkan lamuranki gareshi, ki kusanceshi, zai kusanceki. Allah yana son masu ambatonsa safe, rana da kuma dare. Ina miki fatan alheri koyaushe._*
Ta karanta fiye da sau uku, ya yi mata dadi sosai, ta kuma kasa barin murmushi. Fadeel ne, koda babu suna a lambar tana da haddarta saboda kira na yau da gobe da yake yi kuma duk da ita ne. Ta sauke ajiyar zuciya, kwankwasa ƙofar da Futuha ta yi da shigowarta da sallama ya sanya ta ajiye wayar ta dube ta. Murmushi Futuha ta yi mata.
"Yauwa Humaira idan kin huta ki fito ki É—ebi abinci a kicin. Daga gobe za ki soma gwadawa Hafsatu yanda kike tsara abinci da komai, yau kinga sai ki huta ko? Ni zan shiga ciki ba lallai kuma mu haÉ—u ba sai da safe."
Ita dai ta amsa da toh kawai, bayan fitar Futuhar ta girgiza kai. Mamakin wannan rayuwa ta yaran Mami take, tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba, da ace sun biyo Mami hatta da girkin ba su da matsalarsa. Ta rasa menene ribar ɗiya mace idan ta zauna har ta yi aure ba ta iya girki ba. Banda shiriritar Futuha, ta gwammace a koyawa Hafsatu girki ta cigaba da yi mata bauta ita kuwa ta zauna ta miƙe ƙafa. A ƙarshe dai ta watsar da tunane-tunanen da ta tabbatar ba za su yi mata wani amfani ba ta cigaba da ambaton sunayen Allah har aka kira sallar isha'i ta gabatar ta kuma haɗa da nafila ta yi addu'a anan ma sannan ta ninke dardumar ta fita, abincin sam bai yi mata ba. Shinkafa ce dafaduka ta dai ji kaji wadanda daga ka kai saman hancinka sai ƙarni ya bugeka, da sauri ta mayar ta ajiye. Sanin da ta yi idan ta zauna sai ta kwana da yunwa ne ya sanya ta daukar indomie kanana biyu ta dafa ta ci ta sha ruwa.
Saita alarm ta yi ya tashe ta karfe uku, dakyar ta tashi saboda ba ta saba ba ga bacci dake neman fin ƙarfinta, sai da har uku da rabi ta buga sannan ta iya miƙewa firgigit tana ambaton sunan Allah. Hakan ya ba ta wani ƙarfi ta kuwa ɗauro alwala ta dawo ta yi nafiloli ta karanta alƙur'ani bacci na ɗaukarta, dakyar ta daure ta yi sallar asuba sannan ta kwanta anan bacci mai karfi ya kwashe ta.
Sai wuraren takwas na safe ta tashi ta yi wanka ta shirya tsaf ta dora hijabinta ta nufi kicin. Ta sani mutanen gidan ba sa tashi da wuri, maigidan kansa sai ya kai goma bai fita ba. A kicin ta tarar da Hafsatu na zaman jiranta har ta yi gyara ta wanke kwanuka. Suka gaisa fuska a sake, nan suka shiga haɗa kayan kari, kasancewarta babbar mace kuma mai basira tana hankalta kwarai da yanda Humaira ke sarrafa girkinta. Suyar dankali da agada suka yi sai ko sauce da ta haɗa, sai ruwan shayi da ya ji citta da kanumfari. Sai ko farfesun nama da ta yi da ya ji kayan lambu. Kicin din ban da ƙamshi ba abinda ke tashi, komai ta yi daidai gwargwado yanda ta tabbatar ba za'a yi almubazzarancinsa ba. Hafsatu ta fita da shi zuwa dinningtable na Futuha, ita kuwa Humaira bayan ta zuba wa Hafsatu ta ɗebi nata ta yi ɗaki don ba za ta iya jurar har sai su Futuha sun tashi ta karya ba saboda yunwar da ya addabe ta, a ranar kuma ta tashi da wani irin karfin jiki da walwala. Ta ƙara gasƙata cewar Fadeel, babu abin da ibada ba ta ɗaukewa na daga damuwa da ma ƙuncin zuciya. Hamdala kawai ta ke yi bisa yanayin da ta tsinci kanta a ciki.
***
A ɓangaren Fadeel kuwa, sosai suke shirin bikin Ibb da Dakta Salma wanda bai fi sati ya rage a yi ba. Abokansu duk wanda ya ji zancen auren Ibb sai ya tambaya ko an yi na Fadeel? Amsar dai bai wuce nan kusa shima zai yi ba. Kamar koyaushe a kwanakin nan, yau ma su na tare bayan ya raka Ibb wurin Dakta Salma jin tsarin events din da za ta gudanar, Ibb sai faman mita yake yi mishi akan kawai ya kai kudi a sanya aurensu lokaci guda shi kuwa murmushi kawai ya ke yi. Girgiza kai Ibb ya yi.
"Fadeel na sanka, kana da ƙoƙari sosai gun ɓoye damuwa, ba ka fiye son ɗorawa mutane nauyin damuwarka ba, amma ba yanda ka iya, mun taso tare kuma kai ɗin aminina ne dan uwana na maka sanin da wani mafi kusa da kai ɗin bai yi ba. Yanzu a ture zancen wasa, please and please ka yi abin da muke da tabbacin yiwuwarsa, idan yin a yi, idan barin a bari."
Tuƙi yake yi amma sai da ya ɗan juyo ya dube shi.
"Ban fahimceka ba. Me za a bari?"
Ibb ya kauda fuska yana ɗan shan ƙamshi.
"Auren mana, ko dole ne sai ita? Lamarinta ya fara kai ni bango, ita ba ƴar kowa ba a ƙasarnan sai ji da kai da taƙama. Matan da suka fi ta sun nuna su na yi da kai sun kuma nuna sun ji sun gani kowane yanayi ma a tafi da su amma ka nace mata, ka maƙale sai ita. Haba Fadeel, yaushe duk wannan zai wuce? Har yanzu kana da hope din cewa za ta amince da aurenka da bakinta?"
Fadeel bai ce komai ba, amma zuciyarsa zafi take. A duniya bai taɓa yin so ba sai akan Humaira, kuma da son ya tashi kama shi, sai ya yi mishi wani irin kamun dabaibayi wanda ko ya ƙi ko ya so, hakanan zai rayu da shi. Bai dai san abin da gaba za ta haifar ba.