Sashe 75
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Kai kuma me kake yi anan?"
Ya dubi Ummita gudun kar Mami ta ɓaro wani batun har ta yi sanadin tashinta daga bacci sai bai ce uffan ba ya juya ya fita, Mami ta ɗan dubi inda suke kwance sannan ta juya ta rufe ƙofar ta bi bayansa. Ya sanar da ita saƙon Abban da ma huɗubar da aka yiwa yaron da suna Ahmad.
"Sai kuma a rasa wanda zai yi sai kai? Meyasa zai yimin haka? Ina ruwanka da sabgar yaron da ba a san asalinsa ba?"
Mamaki ya ƙume Mubarak.
"Mami, wai lafiya kwanaki biyun nan ranki duk a ɓace? Haba Mami, don Allah ki bar faɗin hakan kada ki faɗa gaban Ummita abin babu dadi."
Kamar ta kifa masa mari haka ya ji, shi kuwa sosai ransa ya ɓaci. Ga damuwar da Futuha ta jefa Abbansu ciki ga kuma wannan haihuwa da ya tabbatar za a sha daga da Ummita akan duk abin da ya shafi ɗan.
"Toh ubana, sai ka faɗamin abin da ya kamata da wanda bai ma dace ba ka ga ai zan ji tunda kai ka haife ni. Mubarak tun muna mu biyu ina mai ƙara gargadinka akan ka fita hanyar yarinyar nan ka kuma gaggauta cire ta a zuciyarka don na rantse ni dai Maryam muddin ni na haifeka kai ma ba shegen bane ba za ka taɓa aurenta ba."
Ya ji kansa ya yi wani irin sarawa, a duniya ko misƙala bai taɓa fuskantar zai samu matsala daga Mami ba akan Ummita, ya fi tunanin zantukan su Anna da Jannat ne ya sanya ta zama haka amma ba wani abu daban ba. Madadin ya yi magana sai kawai ya ba ta hakuri ya bar wajen don ba ya so su haɗa wata diramar a asibiti.
Da ficewarsa sai ga wayarta ta dauki ƙara, dubawar da za ta yi ba kowa ba ne face Wizzy. Sai da ta yi taga-taga za ta fadi da sauri kuma ta dafa ƙofar ɗakin. Ganin mutane a wajen sai ta yi tunanin shigewa dakin da Ummita take, ta ji Nos ta ce za ta jima tana bacci wannan ya sa kanta tsaye babu shakkar komai ta shiga amsa wayarta.
"Mene ne? Kiran na meye ka ke yimin? Ba nace maka kar ka kuskura ka kirani har sai ta haihu ba?"
Ya yi Æ´ar dariya.
"Hajjaju kenan, kina tunanin za ki yanke alaƙa da ni da wuri alhalin kina tare da abu mafi soyuwa a rayuwata? Ina! Ai ba zai yiwu ba, koda ace yau gudan jinina ya fito a duniyarnan ki sani kin samu jikan da zai kiraki da kaka ko da kuwa daga bangon duniya ne. Ni kiran da nayi shi ne, ya ake ciki? Ina magana a whatsapp sai wani you no care kike nunamin, to idan ba so kike nayi eh yane ba wato na yi dirar mikiya a gidan ki gaggauta sanar da ni halin da ake ciki. Ta fesar da cikin ko kuwa ya na nan a dunƙule?"
Wani irin zufa ya karyowa Mami. Ta ji hatta da jikinta ya ɗau rawa, ta juya inda Ummita ke kwance ganin ta ɗan motsa ya sanya da sauri ta bude ƙofar ta fita ba ta ce masa uffan ba har sai da ta ƙarasa ficewa zuwa farfajiyar asibitin.
A ɓangare Ummita kuwa, tsaf ta ji muryar Mami tana yiwa abokin wayarta magana akan me zai kirata, sai dai ko alama ba ta tsinkayi abin da ya ce ba. Motsin da ta yi na farkawa tana kokarin tashi ya sanya Mamin ficewa a dakin, ta buɗe idanunta tarr ga wani jiri dake kwasarta daga kwance tsabar yunwa. Tunanin maganganun Mamin take son yi amma lokaci guda kukan da jaririn dake gefenta ya tsala ya sanya ta dan karkata kai ta kalleshi. Kallo na ƙurillah, burinta ta hango kamannin Ubansa ko ta samu shaidar da za ta nuna domin a binciko inda yake a cafke shi, sai dai kuma ban da su din waye ya taɓa ganinsa? Kukan yake yi tana jin wani iri a zuciyarta, yanayin da ba ta taɓa hangensa akan yaron ba yana zuwar mata a sannu sannu. Ta kasa miƙewa zaune balle ta samu*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Ta kasa miƙewa zaune balle ta samu damar kai masa tallafi a haka su Humaira suka shigo ɗakin suka risƙeta. Ganinsu sai ya sanya ta komawa ta kwanta sai kawai ta soma kuka a hankali, da sauri Raihana ta ƙarasa ta ɗ an rungume ta tana kokarin maida ƙwallar da ta cika mata idanu.
"Ya isa hakanan don Allah. Kiyi hakuri tunda Allah ya raba lafiya yar uwa."
Humaira kuwa sai ta ajiye kwandon kayayyakin da suka taho da su ta shiga haɗa mata bisa umarnin Mami da suka yi karo da ita za ta fice da waya a kunne, ta dai katse kiran ta musu magana kusan ba a nutse ba sannan ta sa kai ta karasa ficewa zuwa farfajiyar, su kuwa suka yo ciki. Raihana ta saki Ummita ta karasa ga Bebin da ya ɗan jinkirta da kukan ta ɗauke shi ta zuba masa idanu. Can kuma ta kalli Ummita, kamar ta ce kun yi kama sai kuma ta ji tsoron kar ta ji haushinta. A haka aka kwankwasa kofar dakin da sallama suka amsa aka shigo, Baba Amina ce ƙanwar Abba sai ko Abban da kansa a bayansa kuma Mubarak. Abban da kansa ya yi kiranta ya sanar da ita zancen haihuwar wannan ya yi silar zuwanta. Ita ta taimakawa Ummita ta sha shayin ta ci abinci kadan, anan kuma Abban da ita suka hadu wajen yiwa Ummita nasiha da nunamata muhimmancin yarda da ƙaddara. Sosai kuma maganganunsu suka shige ta, sai anan ma take ji Mamin ta je gida ta dawo a bakin Abba. Bayan fitar su Abban da Mubarak ne kuma Baba Amina ta zage wajen taimaka mata ta yi wanka ta shirya tsaf, shima yaron ta wanke shi ta sanya mishi sabbin sutura, wankewar da ya sanya kamannin mahaifiyarsa ya ƙara bayyana muraran a fuskarsa hatta da ɗan baƙin tabon da Ummita keda ahi a gefen kumatunta haka jariri Ahmad ma. Ta yi ta satar kallonsa cike da sha'awa ga wata iriyar ƙauna da ta yiwa zuciyarta ƙawanya. Ba zato ta ji Baba Amina ta miƙa mata shi har ya kusan faɗuwa ba don Allah ya sa ta tarba da hannunta ba.
"Daure kiyi hakuri ki ba shi ya sha Ummi, in sha Allahu wataran zai zamo maki abin alfahari. Kar ki duba hanyar da kika same shi, kiyi hakuri ki yarda wannan wata jarrabawarki ce da ba ki isa kin kufce mata ba. Watarana sai labari da yardar Allah."
Kwalla suka cicciko mata, nan Baba Amina ta taimaka mata yaron kuwa ya cafka ya soma tsotso kamar zai tsige mata fata, haka yana sha tana jin wani irin ciwo a mara ga zafin fisgar da yake yi har hawaye ta soma tana jujjuya kai. Humaira da ta zuba musu idanu sai ƙarar wayarta ta katse ta. Ganin sunan Fadeel na yawo saman screen ya sanya ta fita a dakin fuskar dauke da ƙaramin murmushi. Da sallama ta ɗaga wayar, ya amsa mata a sake.
"Boddona wato idan Fadeel ayyuka suka hana shi kiranki, ba za ki dauki waya ki kirashi ba ko?"
Ƴar dariya ta yi kaɗan da har ya tsinkayo sautinta, ita sau da dama yanayin shagwaɓar da muryar da Fadeel kan yi mata na ba ta mamaki da kuma dariya, shi dai a lallai ta ji tausayinsa koyaushe.
"Oh, dariya ma na baki? Toh aikuwa yanzu zan bar dukkan abin da nake yi ki gan ni da yammacin nan."
Ta dan rausaya idanu kaÉ—an tana murmushi.
"Ka yi hakuri toh, ni ba na ma gida, Ummita ta sauka lafiya muna asibiti."
"Allah Sarki, me aka samu?"
Da sanyin jikin tausayawa yaro Ahmad ta amsa.
"Namiji ne, an masa huÉ—uba da Ahmad."
Ya yi addu'ar fatan alheri gareshi kafin kuma ya ƙara kwantar mata da hankali da nunamata su ne suke kusa da ita, su kasance masu jarumta su dinga ƙarfafa mata gwuiwa. Kamar dai sun haɗa baki da Baba Amina, haka ya yi ta yiwa Humaira nasiha. Hakan ya sanya tsantsar so da kaunarsa wadanda ba ta san mafarinsu ba suka shiga ratsa ta sosai. Ya karashe zancen da fadin.
"Yauwa, kuma bana son kina yin asarar hawayenki musamman da yake bana kusa."
Ta É—an russunar da idanun kamar yana kallonta saboda jin nauyin maganarsa.
"Bari na kyaleki ma yi magana anjima in sha Allah."
"Toh, na gode a gaida mutan gidan."
"Zasu ji, nace ba?"
"Naam?" Ta amsa gami da tattara nutsuwarta don a sautinsa ya nuna ko ma mene zai fadi nada matukar muhimmanci.
"Ina matuƙar kaunarki."
Sai ta sauke ajiyar zuciya har tana jin tsikar jikinta na miƙewa, tana son furta masa ita din ma hakan ce a wajenta amma wani kunya ya hanata aikatawa. Sai kawai ta ji ɗif ya yanke kiran. Ta numfasa kafin ta ja ƙafafunta zuwa ciki duniyar na mata wani irin dadi ga kaunar Fadeel dake ƙara tsuma ta.
***
A ɓangaren Fadeel kuwa, ajiye wayar ya yi jikinsa duk a mace saboda shauki da kewar Humaira da ya mamaye shi lokaci guda, har yanzun yana shakkar kada wani abu ya sauya zuciyarta daga gareshi, sati ukun da kwanakin da suka yi saura jinsu yake tamkar shekaru duk kuwa da cewar a zahiri ga Ibb na ta faman tashi faɗi wurin ganin an haɗa dukkan abin da ya dace dangane da lefe da ma kuma list na wadanda zasu gayyata. Fadeel din shima sosai ya maida hankali ga ginin gidansa wanda an kammala komai sai kayayyakin furniture da yake sanyawa don alƙawari ne ya daukarwa kansa da yardar Allah sai dai Humaira kawai ta shigo gidansa amma ba ya bukatar a yi mishi hidimar da babu wanda zai mora sai shi sai kuma matarsa. Ita din yake so da kauna ba komai ba.