← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 40 OF 101

Sashe 40

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Daga haka ya maida hankalinsa ga Kausar suna hirar aikin Fu'ad da babu hutu. Ita kuwa Kausar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ta gama lura da irin matowar da Murja ta yi a kan Fadeel, ta kuma sani zai wahala ta same shi tunda sam ba ta gabansa. Murja ta shaƙa, saukowar Anti Amarya daga saman bene ya sa ta mikewa. Fadeel ya gaisa da ita. Ta miƙawa Murja kudin tana fadin.

"Ina daɗa roƙonki, na san halinki kar ki je ki zauna don Allah Murja. Kina karɓar snacks din ki biya ki dauko cake."

Ta amsa da toh, ji take inama direban gidan ba ya nan sai ta ce Fadeel ya kai ta. Amma tun dazun yana waje ita yake jira. Fadeel kuwa yana jinsu amma bai sa baki ba. Ba ya son ya zaƙe akan lamarin Humairar har su shinshino wani abu babu ma kamar Murjar da bai gama yarda da ita ba.

***
Ta tsaya daga ƙofar gate din gidan tana ƙarewa gidan kallo, yamutse fuska ta yi. Eh ba laifi su na da rufin asiri amma ko daga waje bai kama ƙafar gidan su Fadeel ba. Ta karasa ta yiwa Maigadi sallama ta kuma faɗi abin da ya kawo ta, iznin shiga ya yi mata kai tsaye don dama yana da masaniyar sana'ar Humairar.

A sadda ta karasa ciki Humaira na zaune tare da su Raihana a falo bayan gama yi mata kwatance a waya, ta sani ba za a É—au lokaci ba za ta karaso tunda a sanda suka yi wayar tana kusa da su.
Sallamarta ya sa gaba daya suka dube ta. Ba laifi tana da nata tsarin daidai gwargwadod. Abaya doguwa ce a jikinta sai mayafinsa, sai ko wani ƙaton gilashi da ta rufe kwayoyin idanunta da shi. Tunda ta shigo falon ya karaɗe da ƙamshin turarenta mai ƙarfi irin wanda ya zama haramun mace ta fesa ta fita da shi. Suka tarbe ta da hannu bibbiyu aka gaisa. Humaira har da kawomata ruwa da ragowar snacks din ta ci. Kasancewarta wayayyiya ta sake da su aka ɗan taɓa hira har Mami ta fito suka gaisa da ita. Murja ta yaba kwarai da tarbar da aka yi mata, ta kuma ji a jikinta Fadeel ba zai so Humaira ba, ba ita ce wacce yake so ɗin ba don dai wannan din ba wata babba ba ce ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba.

"Kina da page a instagram ne?"

Humaira ta gyaÉ—a kai da murmushinta har wushiryarta na bayyana.

"Eh akwai."

"Mene sunan?"

Nan fa daya, ta sani furtawar ne aiki ba ta iya ba sosai. Raihana ta karɓe zancen ta fadi. Murja har sai da ta ɗan kalli Humaira sannan ta kalli Raihanar da murmushi.

"Ok zan yi following dinki. Na ji dadin ganinki na kuma ji dadin É—andanon snacks dinki duk da daman na san É—andanon. Akwai É—an uwana Yaya Fadeel yana kawomana sosai. Ta wajensa muka sanki."

Murjar ta fadi tana mai ƙurawa Humairar idanu don ta ga yanayinta, so take dai ta samu tabbacin babu komai tsakaninsu. Raihana kuwa ɗan jim ta yi a ranta tana tunanin wane Fadeel din? Kodai Fadeel wanda ta sani ne, tabbas ya faɗamata yana odar snacks din Humaira ta hannun wata Antinsa. Ko shi din wannan ke nufi? Idan kuma hakane ita wace ce a wajensa? Ta maida dubanta ga Humaira don ta ga yanayinta, sai ta lura ko kadan ba ta sauya daga murmushin da take yi ba, sai dai jin sunan kamar jikinta ya dan yi sanyi.

"Allah Sarki, na kuwa gode sosai." Abin da ta ce kenan, wannan ya sa Murja kuma sakin jikinta sosai. Lallai wannan ba ita ce Humairar da Fadeel ke mutuwar so ba, wannan da alama ba ta ma san da zamansa ba. Dama ya ce ba shi ke yin odar da kansa ba. Yanzu kam ta yarda. Murja ba ita ta bar gidan ba tsabar shagala da ta yi suna ta kwasar hira da su musamman Raihana wacce ta fi su sanin mutane, kusan ma akwai ƙawayen Raihana na makaranta wadanda duk Murjar ta san su hakan yasa hira ta musu dadi sai da Anti Amarya ta kira wayarta tana faɗan jimawarta ba shiri ta mike, su Humaira kuwa har mota suka raka ta da ledojin. Murja ta karɓi lambar Raihana da zummar a dinga gaisawa duk da ta girme musu don za ta yi sa'ar Tasleem.

***
Sadda ta isa gidan har yara sun fara zuwa Æ´an party. Ta karasa Anti Amarya na mata faÉ—an dalilin jimawarta. Hakuri ta ba ta, ganin Fadeel a wurin wanda ke cin abinci a nutse saman dinning ta ce.

"Wallahi hira muka sha da su Humaira, mutanen gidan akwai kirki kar ki so kiga kamar kada a rabu."

Fadeel ya ji maganar har ransa, ya kuma ji dadi sosai. Bai dai ko É—ago ya kalle ta ba. Yana ji dai tana ta ba Anti Amarya labari ita dai ledojin ta hau buÉ—ewa tana kallon snacks din. Koda ta dandana sun mata dadi kwarai. Nan aka shiga sanya wa a takeaway ana rufewa, Kausar na nan ana aikin da ita.

An gudanar da party cikin armashi, yaran Daddy da Mommy ne suka cika gidan don Anti Amarya sam ba ta barin mara shi ya raɓe ta. Yawanci duk abokan makarantar Abdul din ne sai ko makwaftansu. Hatta a yaran yan uwanta ba kowa ta gayyata ba.

***
Ɓangaren Amare kuwa, Amarya Futuha an ci amarcin sati daya cif ko ƙofar gida ba ta leƙa ba. Hotunansu ita da mijinta kala-kala babu wanda ba ta ɗorawa a Instagram, shi kansa Angon hakan na mishi dadi kwarai bai taɓa hanata ba. Tunda ta zo ba ta taɓa sanya Uwargida a idanunta ba, karshe ma sai Ango Yakubu ke sanar da ita ta yi tafiya Saudia ita da yaranta. Futuha tun da ta ji haka duk sai ta matsa mishi akan ita ma ya dace su tafi hutun honeymoon Dubai. Hakan ya yi mishi dari bisa dari, a lokacin ji yake ko nawa ne zai iya kashewa Futuha saboda dadin angoncin da yake kwasa. Ba ɓata lokaci aka soma shirin yi mata passport da sauran abubuwan da ya kamata ma tafiya. Sai bayan kammaluwar komai sannan washegari ta yi nufin zuwa gidansu ziyara da kuma sallama.

A ɓangaren Tasleem ma, babu laifi Hamza na iyakar kokarin faranta mata, sun ci soyayyarsu yanda ya kamata, ba ta dora koda ruwan zafi daga gidan iyayensa ake kawomusu abincin safe zuwa dare. Sai da ta yi sati cif sannan suka kara shiga ta gaida Mahaifiyarsa da abokan zamanta su uku. Gidan dai babban gida ne mai tarin yara da jikoki. A ranar har gidajen facalolinta sai da ta shiga, wasu sun kata tarbar kirki yayinda wasu kallon tara saura suka dinga yi mata. Haka tattara ta dawo gida.

A ranar da suka yi waya da Futuha take ba ta labarin tafiyarsu Dubai hankalinta ya yi mugun tashi, ji tayi inama ita ce ta samu wannan damar. Ciki-ciki ta yi mata murna, dama tana jin haushin hotunan da take karo da su a media na Futuhar da mijinta yanda kowa ke santin kyawun da suka yi. Futuha ta ce ta shirya za su zo har gida su yi mata sallama. Ba ta ma iya amsawa da toh ba ta katse kiran gami da jan tsaki. Ya yi daidai da shigowar Hamza falon, hannunsa rike da ledoji ya yi mata siyayyar kayan sanyi da kaza. Har ya karaso kusa da ita ba ta san ya yi ba tsabar ta lula duniyar tunani. Sai da ya ajiye ne ya dan zunguri kafaɗarta kadan. Ta dubeshi, murmushi tattausa ya sakar mata, itama ta bishi da na yaƙe. Rungumo kafaɗarta ya yi.

"Tunanin me kike yi ne haka? Har na shigo da favourites dinki amma ba ki lura ba?"

Ta kai duba ga ledojin dake ajiye, har gumin sanyi É—aya yake, sai ta ji ta kasa farin ciki da abin da ya ajiye din duk da cewa a baya har so take ya kawo su ta dinga tsalle kenan tana rungumeshi. A yanzun kuwa ko É—igon annashuwa ba ta yi ba. Sai jikinsa ya yi sanyi, ya kamo yatsun hannunta.

"Wai me ya sauyamin ke haka? Ko bayan fita na kin yi baƙi ne?"

Dama kiris take jira ai sai ta tunzura ta yakice hannunta.

"Me kake nufi?! Na yi baƙi sun zugani ko sun ɓatan rai? Yan gidanmu kake nufin sun zo ko ƙawayena?! Au zargina kake yi akan wani zai iya zuga ni akanka? Ai ba sai an zuga ni b, ni mai zuga kaina ce!"

Gaba daya ya razana, ya yi jim yana kallonta, a iya saninsa babu inda maganarsa ta kai nan. Me ya kawo batun zuga kuma ana zaune kalau? A ina ya ce hakan?

"My Noor, me ya kawo zancen zuga? Ban gane inda kalamanki suka dosa ba?"

Sai a sannan ta É—an dawo hayyacinta. Ta ja guntun tsaki ta zauna. Nan da nan kuma Hamza ya É—an sauya fuska.

"No please, zan dauki komai amma ban da raini, ina maki warning na farko da karshe, bana son tsaki. Kar ki kuma."

Ba ta ce komai ba face turo bakin da ta yi, sai ya ji ma gaba daya ta ɓata masa rai kawai ya mike ya yi daki. Ta bishi da harara, ita ta sani ko wannan motar tasa zai siyar ba zai ishe su su je Dubai har su kashe kudade irin wanda Futuha zasu kashe ba. Ta san muddn Futuha ta yi wannan tafiyar to fa kanta zai fasu, za ta ƙara jin wani girman kai har ma ta dinga yi mata fi'ili iri-iri. Don haka hankalinta ya tashi, ga babu yadda ta iya, nata mijin ba ta tunanin ma ya taɓa taka farfajiyar Airport balle ya shiga jirgi. Ta ja tsaki karo na biyu. Madadin ta kwashe ledojin da ya kawo ta adana komai koda ba lokacin za ta sha ba, kawai sai itama ta bar su anan ta shige nata dakin ba ta ko bi ta kansa ba don har sannan zuciyarta zafi take yi, hassada mugun ciwo ne.
Chapter 40 · 0% Book details