Sashe 49
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Idan ka yi hakan ka taimaki kanka da kuma su. Ka kiyaye sharuÉ—É—anmu ko kuma ka yi dana sanin abin da zai biyo baya!"
Abba kuka yake sosai ya amsa da toh, aka datse layin kiran. Har lokacin bai bar rawar jiki da kuka ba, muryoyin yaransa na mishi amsa kuwwa a cikin kunne, ya rasa me zai yi, mene ne mafita? Ga shi nan dai an hana shi yin furucin ga Æ´an sanda dole haka za su yi shiru da iyalinsa su tattauna a haÉ—a kudaden a biya kudin fansa.
***
 *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
A can kuwa, Wizzy yana kammala magana da Abba ya fidda layin a wayarsa ya kakkarya ya zubar, lokaci guda kuma ya mayar da layinsa. Suka dubi juna suka kwashe da muguwar dariya. Humaira da Ummita aka titsa ƙeyarsu zuwa cikin ɗakin. Babu laifi wajen da suka sauya ya fi wancan kyau, komai tsaf sai ƙura kuma ga dukkan alamu sabon gida ne da ba a kammala aikinsa ba. Banɗakin akwai ruwa har da butar alwala. Wajen dai ya fiye musu ɗayan amma kuma hankulansu ba a kwance suke ba. Ai babu wani gata da za a yi musu alhalin su na hannun azzalumai abin ya yi musu daɗi su samu kwanciyar hankali. Daga Ummita har Humaira tun sadda aka garƙame su a ɗakin ba sa aikin komai sai kuka hakan na da nasaba da jin muryar Abba da suka yi wanda gaba ɗaya sun fitar da ran ƙara ji ko ganin wani cikin fuskokin da suka sani.
Wizzy kuwa bayan dawowar Badboy daga rufe ƙofar ya dube su ya ce.
"Aski fa idan ya zo gaban goshi ya fi zafi, wannan lokaci ne da zamu ƙara zage damtse kuma mu yi takatsantsan don cik umarninta, a ƙarshe mu ma mu kwashi rabonmu, ta sallame mu."
Babba wanda ke faman hura hanci yana fitar da huci ya soma magana a kausashe.
"Wai ni fa bana son rainin hankalin da take yi mana! Matar nan tun da ta bamu aiki ba ta yarda ayi waya da uta sai rubutun saƙo. Ita ba ta san hatsarin da ke tattare da hakan ba? Idan fa ta yi sakaci har wani ya yi ya gani to fa akwai matsala. Sannan ta ƙi ta bayyana kanta sai ɗan aiken da ta ke turowa, ita kenan ko kama mu za a yi ta tsira kenan? Ba mu san wace ce ba, kuma ba mu san komai a kai ba, namu kawai aiwatarwa idan an cafke mu ta ci bulus kenan?!"
Wizzy ya É—aure fuska bai ce komai ba, ganin haka Badboy ya cafe.
"Kai Babba ka iya kalamanka, ka sani koda wasa idan har ba mu ne muka so ba, toh fa ba za mu taɓa kamuwa ba. Mun fi ta iya shege ai kai ka sani. Ni fa duk ba wannan ne damuwata ba, yarannan su na hargitsa lissafina amma kai Oga ka ƙi bani damar gwangwajewa. Kenan haka muna ji muna kallo za mu bar su shikenan sun sha?"
Sai a sannan Wizzy ya kalle shi.
"Ba wannan aka umarcemu da yi ba, asalima don horo ne ya sanya muka kai su tsohon gidan gonar can don kawai su shiha taitayinsu amma tun farko ba ya daga cikin bajat dinmu. Kai ne ka fiye garaje, ai na ce maka akwai lokacin da hakan za ta kasance, mu bari mana har mu samu tabbacin kuɗaɗen nan za su faɗo hannunmu tukunna mana, sai mu yi duk abin da muka ga zamu iya. Mu dai tabbatar ba mu kashe su ba don ba shi aka sanya mu ba."
Suka yi shiru babu wanda ya tanka masa musamman Badboy da ke jin haƙurinsa na dab da ƙarewa akan ƴanmatan musamman Humaira da surarta ke fisgarta.
***
 Hankalin Anti Maijidda (babbar yayar mahaifiyar Ummita ta Bichi) a tashe ta shigo babban falon na Mami da jama'a ke zaune ana jajanta wannan lamari na su Humaira. Ba ta ƙasar gaba daya ta je Umarah sai a jiya ta diro Kanon, ko gida ba ta je ba kai tsaye ta ce a sauke ta a gidan. Tana shiga ta zube jikin ƙanwar Abba, Baba Amina da suka saba tun a baya tana kuka sosai ana ba ta haƙuri. A lokacin ne kuma Mami ta shigo daga ɓangaren Abba cikin dogon hijabinta, ta gama jin yadda aka yi da Abba da kidnappers din akan kuɗin fansa. Jin muryarta su na gaisawa da makwaftan da ba su jima da leƙowa gidan ba ya sa Anti Maijidda miƙewa kamar wacce aka tsiƙara ta hau tafi raf raf har sau uku, wannan ya ja hankulan kowa kanta yayinda wasu suka shiga tunanin kodai ɓatan Ummita ya girgiza kwakwalwarta har haka? Mami kuwa cak ta tsaya kawai tana mai zubamata idanu. Maijidda kenan, macen da ba su taɓa raɓar juna da alheri ba, babu wata jituwa da ta ƙara haɗa su tun bayan rasuwar Fatima mahaifiyar Humaira.
Maijidda ta soma magana murya a É—age kuma a kausashe.
"Ki zuba ruwa a ƙasa ki sha Maryam! Ki tara jama'arki ku yi kiɗa ku yi rawa har da juyi! Yau burinki ya cika! Abin da kika jima kina ƙullawa akan yarannan yau kin cika shi!"
Jin haka Baba Amina ta miƙe a firgice cikin kaɗuwa ta fisgo hannun Maijidda.
"Maijidda ki shiga hankalinki mana! Ki yarda da ƙaddara ki yi imani da ita. Wannan wane irin zantukan banza ki ke yi akan baiwar Allahn da ta riƙi amanar ɗiyar ƴar uwarki da amana da kulawa tsawon shekarunnan koda wasa Ummita ba ta taɓa kokawa da ita ba? Wane irin baƙin ƙazafi kike shirin yiwa baiwar Allahn nan?!"
Anti Maijidda ta fashe da kuka sosai tana nuna Mami da yatsa.
"Har abada ni Maijidda ba zan taɓa kaunarta ba, kuma ba na jin zan yarda da ita koda ace gaba ɗaya mutanen duniyar nan za su taru su yi mata kyakkyawar shaida! Baƙar azzaluma ce! Amina ni nasan wacece Maryam, ni zan ba da labarinta! Don haka idan har bincike ake son yi na gaske daga cikin gida, a soma daga kanta da kuma azzalumar uwarta!"
Wannan ƙazamin furucin ya sa Mami ta fusata sosai. Hannunta na rawa kamar yadda dukkan gaɓɓan jikinta suke yi ta nuna ta da yatsa, daƙyar maganarta ke fita saboda zuciyar da ta taso mata da kuma ruwan hawayen da suka wanke mata fuska lokaci guda.
"Na shanye dukkan baƙaƙen maganganunki na tsawon shekarunnan ba don komai ba sai domin albarkacin ƴar uwarki marigayiya Maimuna da muka yi zaman mutunci da ita! Na kuma cigaba da jure duk wani cin kashinki a dalilin Ummita jinin Maimuna ce da Naziru. Ban da haka ba ki da wata ƙima ko daraja a idanuna!"
Baba Amina da mutanen ɗakin dakyar suka tsawatar aka kashe zancen inda Mami ta fice daga falon cikin ƙunar rai zuwa ɗakinta inda Anna ke zaune kuma tsaf ta ji dukkan abin da ya faru. Allah ya taƙaita lamarin Jannat ba ta gidan, ta fita dubiyar wata ƙawarta da aka yiwa aiki a asibiti, da abin zai fi haka ɓaci.
Anna ta dube ta sai kuma ta yi dariya.
"Maryama kenan, wannan shi ne sakamakon bautar da ki ka yi na riƙon Ummita ko? Wannan ranar nake jira dama, ban kuma zaci zan gani nan kusa ba. Shashashar yarinya! Ga shi nan tun ba a je ko'ina ba kin kwashi kashinki a hannu. Da ace tun a farko kin ji maganata hakan da bai faru ba. Yanzu sai kiyi kuka da kanki akan duk abin da ya faru."
Mami ba ta ce da Anna komai ba, sai ta fidda hijabin da ta zumɓula ta ɗauki wayarta kawai ta zauna ta yi shiru tana aikin dannawa, Anna ta cigaba da zabga ruwan bala'i, da Mami ta ga abin ba na ƙare ba ne, kawai sai ta fice zuwa ɗakin su Raihana ta bar mata ɗakin.
***
Fadeel ya farka gami da ƙurawa silin idanu, shiru ya yi yana ƙoƙarin tunano dalilin kwanciyarsa ciwo, a hankali kuma ya juya kansa ya dubi ɗakin. Ibb ne kaɗai a zaune yana danna waya bai ma lura da farkawarsa ba. Ya lumshe idanunsa lokaci guda komai ya dawo kwanyar kansa, a firgice ya miƙe zaune.
"Ya Salam!" Ya faɗi da ƙarfi yana mai fisge drip din da aka sa mishi. Furucinsa ya sa Ibb mikewa da sauri ya nufo shi gami da riƙe kafaɗunsa.
"Fadeel yi a hankali mana."
Jin haka ya dube shi da rashin kwarin jiki.
"No Ibb, kwana nawa nayi a nan? Humaira na hannun kidnappers, za su kashemin ita. Ka bar ni na je nemanta."
Daidai nan Alhaji da Daddy suka shigo. Fadeel ya miƙe jiri na kwasarsa yayinda Ibb ke ɗan riƙe shi, Daddy da sauri ya tarbe shi ganin kamar zai faɗi ya ce.
"Fadeel kwantar da hankalinka, in sha Allahu za'a ga Humaira."
Kawai sai ya ji hawaye sun zubomasa, wato za ma a gan ta ba wai an ganta ba? Ya girgiza kai yana kallon Daddy amma sai ya kasa magana.
Suka taimaka suka mayar da shi mazauninsa. Daddy a nutse ya karanta masa duk yadda suka yi da Abba ya kuma ƙara da faɗin.
"Yanzu haka ba mu jima da waya da shi ba, ya tabbatar mana da cewar sun samu kira daga mutanen, sun kuma buƙaci kuɗi. Wannan damuwar ba zai magance maka kowacce matsalar ba, addu'a da kuma sadaka ita zamu duƙufa yi. Yanzu idan ka ce za ka fita nemanta, ta ina za ka fara? Ka san a inda suke ne? Daji, cikin gari, kasuwa, ƙauye, kai ko ma ba a garin suke ba gaba ɗaya wannan sanin Allah ne kaɗai don haka ka samarwa kanka ƙarfin zuciya ka dage da kai wa Allah kukanka. Babu abin da ba ya magancewa."