← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 76 OF 101

Sashe 76

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

A wannan lokacin ma zaune yake a falon Ibb din wanda yake amsa wayar Daddy, ya yi shiru cikin tunanin Humaira yana mai murmushi idanun a rufe ruf. Ba zato ya ji an wurgo mishi filo, ba kowa ba ne sai Ibb.

"Allah ya sauwaƙe maka kai kam Romeo. Ina ce shirin aurenka ake yi da yarinyar nan? Toh mene ne kuma na wannan dogon tunanin kamar ba yanzu ku ka gama waya da junanku ba?"

Fadeel wanda tun jifa da filon ya wartsake, É—an harara ya wurga masa.

"Toh sannu, kai me za a kiraka idan ka kira ni da Romeo? Mutumin da hatta da gabatar da lakca ba ta hana shi amsa wayar Madam kamar ba daga gidan ka fito ba."

Murmushi Ibb ya yi kaÉ—an.

"Ni yanzu ba wannan ba, ya ake ciki kai da mutuniyar taka?"

Shi din ma Fadeel martanin murmushin ya maida masa gami da kwantar da kai jikin kujera.

"Alhamdulillah, akwai cigaba kwarai ba kamar baya ba. Kai ba ka ga alamu ba?"

Jinjina kai Ibb ya yi.

"Na gani tabbas. Amma ba anan gizo ke saƙar ba, mu dai fatan Allah yasa ba ɓangare guda ke so ba."

"Ina da yaƙini da tabbacin yanzu tana sona, sai dai ta kasa furtawa ne saboda dalilinta. Kai ni koda babu son daga fanninta, zan koyar da ita na tarbiyyantar da ita soyayyata. Har yanzu kana tantamar irin kaunar da nake yi mata wai?"

Ibb na Æ´ar dariya ya girgiza kai.

"Ko kusa, na san ai kai tuni ta shafe babin kowace mace a zuciyarka. Hakan nada kyau. Allah dai ya sanya alheri."

Fadeel ya amsa yana sannan ya sanar da shi haihuwar Ummita. Sosai Ibb ya tausaya mata.

"Ya ake ciki batun binciken can?"

ÆŠan yarfa hannu ya yi.

"I dnt know, ban yi waya da shi ba, kuma bai kirani ba. Amma a satin da ya wuce ya bani tabbacin da alamun nasara don suna bincike akan accounts din da aka bude na whatsapp da instagram har da facebook da sunan Feedy Baby. Ya kuma ce an soma samun bayanai akan ta don ba ta rufe akawun din ba na instagram ta cigaba da amfani da shi a ɓoye, hakanan whatsapp, yanzu dai su na monitoring kowane motsinta."

Ibb ya yi fatan nasara, haka suka yi ta tattaunawa har dai Salma ta shigo ta sanar musu abinci ya kammala wannan ya katse su suka miƙe.

***
Mami gaba daya ba a nutse take ba, Wizzy ya jaddada mata cewar sai ya dauki fansa a kanta ko kuma ya tona mata asiri matuƙar ta hana shi gudan jininsa saboda yana tambayarta ko an haihu ko aa ta yi mishi ihun ya rabi da ita babu ruwansa. Wannan ne shima ya fusata shi har ya kaifafa harshe a kanta ya yi mata munanan kalamai. A karshe dai dole haka ta bar asibitin ta kkma gida don samun damar yin tufka da warwara.

***
Ummita kuwa kwanansu ɗaya aka sallamo ta. Ko ta ya ya? Oho, sai ga makwafta na ɓullowa ganin jariri, aka rasa wanda ya sanar da su. Jannat kuwa ko dakin su Ummitan ba ta shiga. Tasleem zuwanta daya ta koma, dalilin jego ne ya sanya Abba bai yi mata faɗan rashin nuna kulawa ga ƴar uwarta ba. Ita kuwa Futuha Abba ya yi rantsuwar kada ta sake a nan kusa ya ga ƙafafunta a gidansa, kuma ya tabbatar mata muddin ba ta goge dukkanin shafukanta na kan yanar gizo ba zai saɓa mata. Dolenta babu yanda ta iya duk da irin tara jama'ar da ta yi a kafafen musamman Tiktok hakanan ta shafe su don Mubarak na lurar wa Abba ko ta aiwatar ko a'a.

Anti Maijidda ta zo bayan Ummita ta cika sati da haihuwa, ta É—an ji dadi ganin yanda ta kwantar da hankalinta ta ke kuma ba yaron kulawa, idan an ce mata kafin haihuwar za ta yi haka ba za ta yarda ba. A ranar Anti Maijidda ta tattara ta bar gidan domin ta rantse ba za ta kwana a gidan da Mami ke cikinsa ba.

***
Mami ce zaune a falon Abba cikin amsa kiran da ya yi mata don su yi magana mai muhimmanci.

"Ina sauraronka." Ta yi furucin ciki-ciki, tun sadda Abban ya ce ba zai taɓa hana Fadeel auren Humaira ba ta ke jin haushinsa ga uwa uba takurar da ya soma yiwa yaranta. Babu dama Yassar ya kai sha biyu a waje sai ya bude masa wuta kamar ya ari baki, wai ina yake samun kudaden da har yake shigar tsadaddun kaya yake yawon fita taɗi? Ga Futuha da gaba daya ya yi mata geji da gidansa, hakanan Dawud shi ma ya hana shi mu'amala da wasu abokansa ɓata gari. Ƙassim kuwa koyaushe yana gidan makwafta wurin abokansa yaran gidan, haka zasu ja shi yawo wuraren shaƙatawa iri iri na masu kudi a yi ta kashe masa kudade yana shigar kece raini, a yau din ma ganinsu da Abban ya yi da matasan gidan uku wadanda aka yiwa tambari marar kyau har ana zarginsu da shaye shaye da abubuwa barkatai, Abban har marinsa ya yi a gaban Mamin, wannan ma ya taɓa zuciyarta kaca-kaca don haka take cika da batsewa ƙiris ya rage ta fashe.

Ga Abba kuwa bai damu da yanayin dake saman fuskarta ba ya soma magana.

"Sanin kanki ne auren Mamana ya zo sai dai yanayin da muke ciki ya hana a yi abin da ya kamata na shirye-shirye, ita dai a satinnan za ta je Nijar ta yi musu sallamar aure, iyayen yaron da shi kansa sun jaddada min ba sa buƙatar koda tsinke daga wajenmu, za su yi mata komai na gidan aure iyaka a kai musu ita amma matsayinmu na masu mutunci ba zamu naɗe hannuwa hakan ta kasance ba, ko ya ya mu yi mata wasu kayayyakin kamar daga na kicin da dai sauransu. Ku ne mata, kun fi sanin abin da ya kamata a yi. Abu na gaba kuma ƙarshen satin nan mai kamawa za su kawo lefe."

Zantukan suka shiga tafarfasa zuciyar Mami, ji take yi tamkar ta yi fiffike ta dira a jikin Abba ta shaƙe wuyansa har lahira. Daukaka dai ɗaukaka wanda ta sani shi ne abin da ya iso rayuwar Humaira? Toh wai tana mene ne haka? Kai jama'a.

"Da sake!"

Ta furta a fili tana wani irin tsuma kamar na zakanyar da ta wuni ta kwana ba ta ci ba. Abba cikin rashin fahimta da yi mata uzurin ɓacin ran da take tattare da shi a yinin ranar ya sanya shi kai zuciya nesa ya jefamata tambaya.

"Ban fahimceki ba."

Ta dube shi tsakar ido, fuskarta muraran ta bayyana abin da ke cin zuciyarta murya a sama ta ce.

"Eh nace da sake! Ba za ta saɓu ba wallahi! Muddin ina raye ba zan bari Humaira ta auri dan iskan yaron nan ba mazinaci!"

Kalmar mazinaci ta yi matukar girgiza Abba har sai da ya ji wata iriyar faÉ—uwar gaba. Salati ya yi da karfi yana nuna Mami da yatsa dake kakkarwa.

"Maryama ki tsoraci Allah, kar tsanar yaron nan ya kai ki da daukar hakkinsa? A ina kika gani da idanunki yana aikata zina? Wai Maryama meke damunki? Wannan sauyin da kike nunawa na menene?"

Ta ɗan yi jim tana girgiza ƙafafa kamar ta karya ta, so take ta ce masa sauyin na ubanka da uwarka ne amma kuma tana tanƙwasar kanta gudun lalacewar aikin shekara da shekaru, don haka sai ta rasa mafita, bakinta kuma ya ɗinke, kawai sai ta fashe masa da kuma.

Humaira dake tsaye a ƙofa riƙe da jug wanda ta yiwa Abba lemun cittar da ya sanya ta, tun sadda Mami ta soma ambaton kalmar Da Sake! Take tsaye kamar an ɗaure mata ƙafafunta ta kasa motsawa. Komai ya shiga kunnuwanta hatta da kiran Fadeel mazinaci da Mami ta yi. A yau ɗaya kuma karo na farko da ta ji a ranta Mami ta ba ta haushi dagasken gaske.

'Mami lokacin da aka nunawa abu tsana, lokacin zuciyata take tafarfasa saboda kaunarsa. Kiyi hakuri, Fadeel koda mazinaci ne zan jure tarayya da shi, ballantana kuma zuciya da ruhina su na karyata kalamanki gareshi.'

Wannan duk zantukan zuci ne da Humaira ke yi lokacin da ta juya ta soma tafiya da nufin maida haɗin firij har zuwa sadda za su kammala tattaunawa. Haka ta koma ɗakinsu zuciyarta a ɓace, Raihana da Ummita da kuma Sa'ade bazawarar ɗiyar Baba Amina dake kula da Ummita suka zubamata idanu.

"Lafiya Humaira?" Har su na haɗa baki wajen tambayar, sai kawa ta girgiza musu kai da murmushin yaƙe bayan ta yi dabarar dauke ruwan hawayen da ke kokarin zubomata.

"Ba komai."

"Haba Amarsu, tun ma ba'a yi komai ba?"

Fadin Raihana cikin son kawar mata da damuwa da bagarar da zancen. Su Ummita suka É—an dara. Ita dai ban da murmushin dole babu abin da ke saman fuskarta.

***
Mami kuwa sosai suka fafata da Abba don ta rantse ita dai ba zaa yi auren ba, wannan ya sa Abba ransa ɓaci suka samu mummunan saɓanin da har sai da ya kira Baba Amina a waya da zummar ta zo ya sanya ta hidimar auren Humaira. A cewarsa shima yana da ƴar uwa.

Mami ta wuce dakinta a fusace ta rufe ruf, kanta take duba ta madubi ta yi kwafa.

"Lokacin da za ka mutu yarana su mallaki arzikinka ya yi Yusuf. Idan hr tsafi gaskiya ne sai na kashe ka."

Ta furta a kaifafe.
Chapter 76 · 0% Book details