Sashe 90
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Tana kaiwa nan ta yi gaba tana ji yana fadin sai ta yi muguwar nadamar zageshin da ta yi amma ba ta ko juyo ba balle ta ji nadamar kalaman da ta yi mishi.
***
Kamar tare suka isa cikin gida da Futuha wacce ke faman kwara ihu tana kiran wayyo. Mami duk da yanayin tashin hankalin da take ciki sai da ta ji cikin ya yi mugun ɗurar ruwa, idan akwai wani abu da ta tsana a rayuwarta bai wuce ta ji ko ta ga wata masifar ta afkawa yaranta ba. Yaran da ta ci kwakwa wajen ganin rayuwarsu ta inganta. Ta ɓoye ainahinta ga duniya domin ta samu kyakkyawar shaidar yaudarar mutanen da take tare da su duk don ingancin da ta ke son rayuwar yaranta su yi.
"Ke! Meye haka? Wannan wane irin hauka kike yi kina neman tara mana jama'a?"
Futuha cikin kuka take sanar da Mami labarin auren Ƴar Snow da Yakubu. Ta ƙara da faɗin.
"Ni wallahi Mami ba zan zauna da ita ba, na fasa aurensa dama ai bakin cikin abin da ta aikata min na ɓata sunana a soshal midiya ne ya sanya na aureshi. Toh wallahi na gama aurensa!"
Jiri sosai ta ji yana nema ya kayar da ita, daidai lokacin kuma aka buɗewa Fadeel katon ƙyauren gidan ya shigo ya yi parking, ganin Mami ya sanya shi fitowa sai baza ƙamshi yake har wata ƴar ƙiba ya ƙara saboda kwanciyar hankali da murnar samun farin cikinsa. Ya ci ado cikin shaddarsa coffee da hula kalarta.
Mami kallonsa take yi, kallon kai ne silar rugujewar rayuwar ɗiyata Tasleem, kai ne kuma silar da aka kama ƴar uwata Jannat. Shi kuwa a kunyace da kuma ban girma ya ɗan russuna ya gaisheta. Madadin ta amsa sai ta buɗe baki da zummar gasa masa baƙaƙen magana amma ta fasa hango Yassar da ta yi ta baya yana mata alama da hannu, alamar roƙon ta yi hakuri ta bar wa cikinta. Yana jin duk yanda suka yi da Futuha, ta harari Fadeel kawai ta ja hannun Futuha da ta ɗan danne kukan ganin Fadeel din zuwa ciki. Bai yi mamakin hakan da ya gani tattare da Mamin ba don ya lura tun a kotu take shaƙe da shi saboda kama Jannat, amma a zatonsa tunda har dai kauna ta don Allah ta ke yiwa su Humaira ai ya ci ace ta ji dadin tonuwar asirin wanda ya ɓata musu suna. Sai Yassar ne ya ja shi zuwa masaukin baƙi.
***
Suna shiga falon suka yi karo da Humaira ta yi kyau shar da ita cikin lemon green din leshi ta yafa baƙin mayafi. Ba ta yi kwalliyar a zo a gani ba amma fa fatarta ta gogu tas. Ganinsu ya sanya ta gaida Mami gami da yi mata barka da zuwa bayan ta ɗan kula da yanayin tashin hankalin dake saman fuskokinsu har ita Futuhar.
Mami ba ta amsa mata ba sai ta yi gaba, itama Humaira ganin hakan sai ta soma tafiya domin ta fita.
"Ke!"
Ta tsaya gami da juyowa ga kallon Mamin.
"Ki yimin farfesun nama yanzu ina jin yunwa."
Humaira ta É—an yi turus, ta mance rabon da Mamin ta sanya ta koda tafasa ruwan zafi ne. Sai yanzun da Fadeel ya zo sannan za ta kirkiro aiki?
"Ko ba za ki yi ba?"
Tambayar Mamin ya katse tunaninta, jiki a sanyaye ta ce.
"Zan yi."
"Toh wuce ki je."
Daga nan Humaira ta kama hanya ta nufi kicin. Wannan ya faranta zuciyar Tasleem dake zaune har da kyakyacewa da dariya.
***
A can kuwa Fadeel da ke zaman jira shiru, yana kokarin kiran wayar Humaira sai ga Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya ce
"Ba ta fito ba ne?"
Fadeel yana ɗan sosa ƙeya amma bai ce komai ba.
"Shikenan."
Abin da Abban ya furta kenan ya nufi ciki.
***
*Assalamu alaikum yan uwana.* *Nagode da sakonninku na gaisuwa da masu kira da ma whatsapp.* *Nagode Allah ya bar zumunci.*
©Rufaida Umar.*DUKAN RUWA*
_Ba zai hana gwarje amo ba._
Da Raihana ya soma kiciɓus ta fito daga kicin inda ta tarar Humaira ta kama aiki ranta duk a ɓace don ta yi duk iyaka yinta ta bar mata aikin ta tafi amma ta ce sam tunda Mamin ta sanya ta za ta iya yi ta je ta ba wa Fadeel hakuri ya tafi kawai. Ganin Abban itama sai ta ji sanyi ba ta ko gaida shi ba ta tafi kai tsaye kan abin da ke cin ranta.
"Abba ga Humaira ta bar Yaya Fadeel ya.."
"Ya isa, kiramin ita."
Abban ya katse ta, ya yi daidai da fitowar Mami daga dakinta. Ganinsa sai ta haɗe girar sama da ta ƙas, kallo daya ya yi mata ya kauda kai shima ta sa fuskar a ɗaure sakamakon fitar da ta yi ba da izninsa ba a yau, wani abu da ya zame masa baƙon abu wanda ba ya jin ta taɓa yi masa hakan. Humaira ta shigo falon tare da Raihana, hawaye kwance saman fuskarta kafin ma ta kai ga cewa wani abu Abba ya tari numfashinta.
"Shirya ki je kin bar mutum zaune yana ta jiranki."
Jiki a sanyaye ta dauki mayafinta dake saman kujera, Mami itama zuciya a sama ta ce.
"Ni kuma ban miki iznin fita ba! Aiki na sanya ta ai, don me shi ba zai iya jiran ta kammala ba tunda ganinta a yau din ya zame masa tamkar rubutu a saman dutse?"
Humaira sai ta yi turus, Mami dai ba za ta daina shayar da ita mamaki ba. Ƙiyayyarta a fili na wannan auren ta ke nunawa ba ta ko iya ɓoyewa.
"Duk ikonki akan ta bai kai ya ni ba, daga ita din har ke din karkashina ku ke, babu dalilin da zai sa na zuba idanu a mayar da ni sakarai a gidana. Don haka Humaira kar ki yarda na ƙara ba ki umarni na biyu, ki wuce yanzu."
Ambatonta da Humaira da Abban ya yi wanda bai taɓa kwata hakan ba ya sa ta fahimci abin ba mai sauki bane don haka sum sum ta sa kai ta bar falon tana jin Mami na bambamin faɗan wai Abban ya nuna dagaske ba ita ta haifi Humaira ba kuma ba ta ita ta ce mata ta yi, ta yi din ba. Ita dai ta fice da sauri tana share fuskarta.
Abba ya dubi Mami dakyau, kamar zai ce wani abu sai kuma ganin Raihana a wurin. Juyawa ya yi zuwa bangarensa can din ma bin bayansa ta yi.
"Diyarka ta dawo gida saboda maci amanan mijinta zai auri abokiyar faÉ—anta. Nima kuma ina goyon bayanta don ban ga wani dalilin da zai sa ya yi mata wannan tozarcin ba a idon duniya."
Cikin al'ajabin wannan sabon labari da ma rashin fahimtar inda aka dosa Abba ya kalleta kallon tsanaki.
"Wane tozarcin? Wa kuma kike magana a kai?"
Ta harareshi kamar idanunta za su zazzago.
"Matan da ka aurar har su nawa ne? Ina magana ne kan ɗiyarka Futuha. Shi Yakubun ko sanar da ita batun ƙara auren bai yi ba saboda ya san auren cin amana ne. Kuma ni dai Maryam yanda ba zan dauka a yimin ba hakanan ba zan zuba idanu a halakar da kuruciyar yarana ba a hana su walwala da jin dadin zaman gidajen mazajensu. Tana nan gida na kuma hana mata komawa, ta yi zamanta har sai ya zo ya janye batun auren can da zai yi. Ya rasa wacce ma zai aura sai yar iskar Tiktok da ta yi mata ƙazafin zina a baya?"
Tsananin ɓacin rai da baƙin cikin da ma nadamar kyawawan shaidun halayyar da ya yiwa Mami a baya suka bi suka lulluɓe shi, ga kuma zafin da maganganunta suka haifar a cikin ƙirjinsa. Ya miƙe tsaye jijiyoyin kansa sun fito raɗau tsabar ɓacin rai. Wayarsa kawai ya fiddo ya danna lambobin Futuha, umarnin ta zo ya yi mata, ba jimawa ta shigo tana ɗari-ɗari ta zauna can gefe kusa da Mami. Shi kuwa Abba har lokacin yana daga tsaye yana safa da marwa, sai bayan zaman Futuhar ya soma magana murya a kausashe.
"Maryam! Idan har na isa da ke da kuma É—iyar da kike tutiya taki ce, ni Isuhu ba zan lamunci zamanta a gidana ba alhalin da igiyar aure a kanta. Ke kuma na rantse maki kika yi gangancin kwana a gidannan sai na nunamaki ni Isuhu na haifu kuma babu wata É—iya ko É—an da zan haifa a cikina ya yi tunanin zan biyewa son zuciyarsa na banza!"
Mami dama a ƙule take don babu abin da ke yawo a kwakwalwarta sai maganganun Babandi, wani mugun haushi Abban ke ba ta. Ta kuwa miƙe itama a zafafe ta ce.
"Ni kuma nace babu inda za ta je! Ba zan yarda da auren cin amana ba! Idan kai ba ka san darajar abin da ka haifa ba har ka nema mishi ƴanci, ni nan Maryam ban haifar yarana ga wasu ƙattin banza don su tozartamin su ba! Ai ba su tashi sun ga uwarsu da kishiya ba!"
"Ba zan yi mamakin kalamanki ba Maryam saboda a yanzu ne nake sanin ainahinki ba lulluɓin da kika yimin ba a baya, yanzun kike nunamin ke wace ce. Toh ki sani, ni dai gida nawa ne, ban ginashi da kwandalar kowa a cikinku ke da yaranki ba. Wallahi a yau sai Futuha ta koma gidan mijinta ba za ta kwana a gidana ba, idan kuma kika taka umarnina sai dai ki sa ƙafa ki bita duk inda za ta je amma na yi rantsuwa babu kaffara yarinyarnan ba za ta kwana a gidana ba. Ba kuma tsoronki nake ba da kike tutiya da fankamar wai ba su buɗi idanu sun ganki da kishiya ba! Amma ki sa a ranki zan nunamaki ni din namiji ne ba MIJIN MACE DAYA ba."
Kirjin Mami ya buga dam! Maijidda ita ta faÉ—o ranta.
"Me kake nufi?"
Ta tambaya a rude, madadin ya ba ta amsa sai ya sa kai ya shige dakinsa. Futuha kuwa kuka sosai take yi jin irin yanda iyayen ke musayar yawu. Ta miƙe tsaye ta kama hanya.
"Ke, na fa ce babu inda za ki je. Ki shiga cikin dakina kiyi kwanciyarki."