← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 94 OF 101

Sashe 94

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Shikenan, ka yiwa Allah kar ka kara kiran wayar Ummita. Zan maka yanda kake so kafin a kammala bikin auren nan."

Ta dinga magiya har sai da ya ce ya ji. Da haka suka yi sallama ta goge lambar bayan ta yi blocking dinta. Kasancewar wayar Ummita babu wani lock da ta sanya hakan ne ya ba ta damar yin yanda ta so kafin kuma ta koma ta ba Raihana wayar. Har lokacin kallonta kawai take yi hawaye na zuba a saman kuncinta. Wai wannan matar da Allah bai raga da komai na kyawun fuska ba sai ko munanan É—abi'unta ita din mahaifiya ce gareta babu yanda kuma za ta yi ta sauyawa tuwo suna.

"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Raihana kin ji masifar dake shirin tunkaro mu? Wai uban Ahmad ne yake son karɓar ɗansa? Lallai ki kiyaye furta wannan zancen ga Ummita, mun samu ta dawo cikin nutsuwarta yanzu, idan wannan magana ta fito bamu san halin da za ta shiga ba kuma."

Mami duk ke wannan zantukan har da fidda hawaye itama ta a share su. Hajiya Lubna  ko sai ƙara jinjinawa irin salon kisisinar Mami take. Gaba ɗaya ta rikiɗe zuwa ta Allah, wanda bai santa ba ma zai ce har zuciyarta dagaske ta ke. Raihana ta kauda kai tayi murmushi mai ciwo lokaci guda tana sa yatsunta ta share fuskarta. Allah ya taimaka ba ta yi kwalliyar hodar foundation ba, babu kuma irin nacin da Ummita ba ta yi mata akan ta yi din ba ta ce ba ta ra'ayi hakan ya ba su mamaki kwarai game da ita don ta fi su ma son kwalliyar sosai.

"Shikenan, ba zan fadamata ba. Ni bari na koma ciki kar a neme ni."

Daga haka ta juya ta bar su a tsaye, suka bita da ido.

"Hajiya Maryam, jikina yana bani akwai wani abu da diyarki ke ɓoyewa."

Cewar Hajiya Lubna. Mami ta girgiza kai tana wani murmushi.

"Ko kusa Lubna, ban gan shi ba. Na san Raihana sarai, da ace akwai abu a ranta ba za ta iya yin shiru ba. Haka take, ba ta ɓoyon abin da ke ranta."

Hajiya Lubna dai ta ji ta amma ba ta yi na'am ba. Daga nan suka rankaya zuwa wurin motar inda direban tuni ya dawo yana jiransu. Hakuri ya dinga bayarwa da Hajiya Lubna ke mishi fada kafin su shiga ta ba shi umarnin ya jira a waje sai ta mishi iznin shiga motar. Dole haka ya bi umarninta ya samu can gefe ya tsaya yana kallon masu shige da fice Æ´an biki. Sai lokacin Mami ta labarta mata yanda suka yi da Wizzy, ta kara da fadin.

"Na riga na yanke zan sa Bala (wanda ya haɗa ta da Wizzy tun farko) ya yi amfani da damarsa wayar yaron nan ta shiga hannunsa ya kai wurin masana kwamfuta a yi resetting ta dawo kamar sabuwa. Wannan damar zai sa ya rasa komai da muka yi tsakaninmu. Kinga koda asirinshi ya tonu wanda nake ji a jikina zai tonun tunda dai an kama budurwarsa an kuma fara harinsa, babu wata shaidar da zai nuna gaban kotu da za'a ce har da ni a ciki. Abin godiyar ma, bai taɓa yin ido hudu da ni ba ballantana ya ce ya san ni. Nima a bangarena zan fidda komai nasa daga wayata."

Murmushi sosai Hajiya Lubna ke yi.

"Tabbas wannan babbar dabara ce. Nima dai akan ta wa matsalar na auren da Honarabul ke shirin ɗaukowa na waccan shuwa arab din dole na je na ga Babandi. A baya ya yi aikin kamar za a fasa amma kinga ashe magana tana nan kuma yan banzan danginsa sun nuna goyon bayansu. Kinsan duk yanda ka kai ga kyautatawa dangin miji tsinannu sai sun ga aibunka. Koda dai bana tsinana musu hatta uwarsa bai isa ya yi mata ba sai da iznina. Watakila wannan ƙarfin da ya bani na iko a gidansa da kuma kaunar da ya nunamin ce ta yi sanadiyyar da suke nunamin hassada da bakin cikinsu."

Fuska Mami ta yamutse.

"Hum, ba ki ga waccan balbelar ba?"

"Wa kenan?"

"Wace ban da yar iskar bazawarar can Maijidda? Nifa ko zan yi yawo tsirara ba zan aminta da aurenta da mijina ba."

Dariya Hajiya Lubna ta yi.

"Kai kai kai Maryam, yanzu ke da bakinki kin ce Babandi bai tabbatar maki da aure tsakaninsu ba. Toh na meye za ki yi wannan irin yanke hukuncin da gaggawa haka?"

Girgiza kai Mami ta yi.

"Uhm uhm Hajiya Lubna. Babandi shegen kansa ne. Ni jikina yana bani zai wahala idan ba dangantaka ta auren yake nufi ba. Sai yanzu ma nake ganin wautarmu na tsayawa kan mutum daya don yi mana aiki. Yanzu gashinan abubuwa ba sa tafiya yanda muke so, ya kamata dai ki lalubo mana wani gwarzo kuma babban malamin da ya shahara da zai iya yi mana aiki."

"Nima nayi wannan tunanin Hajiya Maryam, lallai mu tsaya mu nemi wata mafitar, akwai masu taimakon jibgi guda suna nan. Shi kuma Bala ki yi maza ki kirashi yanzu, ai da zafi akan bugi karfe, gwara ki ba shi wannan aikin da alkawarin manyan kudade idan ya aiwatar kada lokaci ya kure."

Bisa wannan shawarar Mami ta fiddo waya ta kira Bala, ta ci sa'a ba ta sha wuyar samunsa ba. Suka yi magana ya kuma ji daɗin kudaden da aka yi mishi alƙawari ya ce zai yi yanda ta ce. Da haka suka yi sallama.

Sai da suka gama ƙulla-ƙullarsu kafin Hajiya Lubna ta kira direbanta ya zo ya ja suka bar farfajiyar wajen taron.

***
Tasleem kuwa tun da aka sa ƙafa aka tafi wajen biki, ta zari mayafinta jikinta har rawa yake ta wuce gidan Babandi. Ta rasa meke janta zuwa gareshi. Kiranta kawai ya yi ya sanar da ita ta zo yana jiranta ta ji nan duniya idan ba ta je ba akwai matsala, ko makaranta ta kasa mayar da hankali kan jarrabawar karshe da take yi. Haka Babandi ya more ta sannan ya ba ta wani ƙullin magani akan ta yi yanda za ta yi ta sanya a abin ci ko shan Humaira, sai ko wani turare da za ta shafe a kayan da ta tabbatar shi Humairar za ta sanya ranar daurin aure. Da wannan murnar ta dawo gidan. Koda Mami ta tambayeta daliin jimawarta, cewa ta yi layi ta tarar.

***
Washegari ya kama ranar ɗaurin aure da kuma yinin cikin gida sai ko kai Amarya duka. Tun safe jikin Humaira a sanyaye yake, kewar yan uwanta da tunanin sabuwar rayuwar da za ta shiga na aure sun tsaya a ƙoƙon ranta. Tana gani ana ta shige da fice ana shiri, masu wanka nayi masu karyawa suna yi, ita ko ta kasa sa komai a bakinta balle ta samu ta ji faɗan Hajjo ta miƙe ta shiga wanka. Da ta kalli Ummita sai ta ji hawaye na ƙara zuba kamar famfo a fuskarta. Ummitan ma daurewa kawai ta ke yi, ita ko Raihana ma gaba daya ta dunkuke cikin bargo tana kuka. So take ta je ga Abba ta fayyace masa komai amma kuma ba ta son raba masa hankali gida biyu. Ta san yana ta hada-hadar fita zuwa daurin aure. Wannan dalili ne ya sanya ta bar komai a cikinta.

Ɓangaren Anna kuwa, murna har da su rawa saboda kudaden da aka turo mata ya yi daidai da wadanda aka suka rage ta cika wajen fiddo autarta. Ta yiwa Mami magana, suka dunguma har Futuha da ta shigo gidan da safe  zuwa inda Jannat din take. Tasleem ko ba ta bi su ba sai tunanin ta inda za ta shiga dakin ta shafa turare a kayan Humaira alhalin babu ko tsinkenta a dakin. Ga mutane an cika a ciki, gaba daya kanta ya ƙulle. Ta fito falon goye da ɗiyarta a baya wacce ko wanka ba ta yi mata ba ga famfas ya cika sai tashin zarni take yi. Ƙazanta na ɗaya daga cikin halayyarta. Ƙazamar gaske ce har ma fiye da Futuha kai ka ce ba Nos ba.

"Ladidi don Allah yi da jiki ki miƙawa Amarya wannan shayin yarinyar ta ƙi cin komai, ni bari naje na ga ko masu kai kayan can gidanta sun tafi."

Baba Amina ke maganar ba ta ko lura da Tasleem ba, ta fice da sauri Ladidi na amsa mata da toh. Wani irin sauke ajiyar zuciya ta yi tana jin wani sanyi a ranta. Ta yi sauri ta fada kicin din. Suka gaisa da Ladidi. Ta dubi tire din mai dauke da filas da kuma kofi sai kayan shayi da plate wanda aka soya kwai aka rufe.

"Ladidi don Allah dubamin akwai ragowar fulawa."

Ta amsa da toh sannan ta shige store din dake jingine da kicin din tana fadin ba za a rasa ba bari ta duba. Tasleem a gaggauce ta fiddo ƙullin maganinta cikin zanin goyon, ta kunce ta bude kwan ta barbaɗa kadan a sama, ta rufe ta kara bude murfin filas din shayin ta zuba ciki kadan ta rufe ta jijjiga ta ajiye, ganin Ladidi na shirin fitowa ta yi saurin tura maganin cikin zani ta saita tsayuwarta.

Ladidi ta fito rike da karamin buhun fulawa ta ce.

"An ci sa'a kin samu ba yawa, haka mutumin naki kike son ci?" Tana nufin danwake. Tasleem ta dan yi dariya ranta fari sol ganin a saukake ta aiwatar da guda daya saura É—aya.

"Kamar kin sani, don Allah taimaka ki yimin idan kin miƙa saƙon Humairar."

"Ya akai kika san an Humaira ne?"

Tambayar da Ladidi ta jefomata kenan, ta dan ji faduwar gaba kadan, ashe fa ba ta riga da ta shigo kicin din ba sai kuma ta basar.

"Ah, na ji Baba Amina na baki saƙo tana fita."

Sai a sannan Ladidi ta saki fuska.

"Auho, toh bari na kai sai na zo na É—oramaki."
Chapter 94 · 0% Book details