← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 32 OF 101

Sashe 32

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Humaira ta amsa da toh, daga haka ta watsa mata harara ta shige. Taɓe baki Humaira ta yi, ko kaɗan ta daina jin ciwon ƙiyayyar da suke mata, ta lura ba ƙasa suka kwasa ba. Jinin Anna ne dole su kwatanta halinta. Ban da ma rashin ta ido, ina uwar mace da zuwa gidan surukai ta tare ko tuna asalinta ba ta yi? Mami ce dai ta sha bamban da su.

Tana wannan saƙe-saƙen zucin wayarta ta ɗauki ƙara. Ganin baƙuwar lamba ya sanya ta yin jim tana tunani, tana da tabbacin ba shi ba ne. Mutumin da gaba ɗaya ya sauya bai ko ƙara kiranta ba, ganin wayar na shirin katsewa ya sa ta ɗauka. Muryar mace ce, ta amsa sallamarta suka gaisa.

"Ina magana da Humaira? Humaira Yusuf mai yin snacks?"

Ai sai ta miƙe tsaye ta hau washe haƙora. Ta amsa cikin zaƙuwa.

"Eh, ita ce."

"Masha Allahu, ina bibiyarki a shafinki na instagram, na ga tallace-tallacenki. Ina son snacks ne, za'a iya samu nan da kwanaki hudu haka zuwa biyar?"

Humaira ta ɗan yi tsallen murna sai ta ɗan toshe baki gudun kar dariyar farin ciki ya suɓuce mata, wannan kusan shi ne order din farko tun da suka soma talla. Nan ta tambayeta kalolin snacks din da take so, ta yi mata bayani, a karshe suka yi sallama da zummar Humaira ta lissafa adadin kuɗinta sannan ta turo acc number. Ai don murna tuni ta mance da batun wata Jannat, gudu-gudu ta nufi falon Mami tana kwala mata kira. Amma ina! Ba ta nan tana bangaren Anna, tsabar rufewar idanu kawai sai ta sa kai har cikin dakin Anna tana kwala kiran Mami. Su na zaune su na hira sai ganinta suka yi. Mamin ta nemi ba'asi nan ta hau sanar da ita yanda suka yi da mai order. Itama sai murna da hamdala.

"Kai Alhamdulillah. Dole kiyi murna, maza muje ayi lissafin sai a turamata."

Da murmushinta mai bayyana kyawunta da tsantsar kamanninta da Abba ta amsa da toh. Har ta juya za ta fice ta ji tsawar Anna.

"Ke!"

A firgice ta juyo kuwa, har ga Allah sai a sannan idanunta suka buɗe. Ta tuna inda ta faɗo da kuma kuskuren da ta yi na rashin sallama ballantana gaisuwa. Kawai sai ta durkushe ta gaida Annar, Jannat ta karasa ta ja kunnenta har sai da ta saki ƙara.

"Don ubanki dayake kin raina mutane uwarmu sa'arki ce da har ki faÉ—o É—akinta kamar na uwarki?! Ba aiki na sanyaki a kicin ba? Kema kuma Mami laifinki ne."

Daga nan ta juya harshe zuwa buzanci ta cigaba da sababin faɗa, Anna itama tana taya ta. Daga yanda Mami ta yi shiru ta haɗe girar sama da ta ƙasa Humaira ta fahimci magana suke gasamata. Nan da nan jikinta ya yi sanyi, a gefe guda ga na gorin ɗakin uwa da aka yi mata, ba don darajar Mami dake a idanunta ba sai ta faɗamusu mai zafin da ba zasu ƙara mararin daɗa kwana ko ɗaya a gidan ba idan har su na da sauran kunya.

"Humaira, tashi ki je, ki yi aikin da ta sanyaki kafin na zo." Muryar Mamin ta katse ta. Ta mike tana mai amsawa da toh gami da share kwallar da ta cika idanunta. Bayan fitarta Anna ta ce.

"Maryama ban san irinki ba, ban san wa kike son ki burge ba. Wato har wani girki za ta fara na harkar kuɗi? Wannan naki salon uƙubar ce ko kuwa dai son yarinyar ne fiye da naki yaran ya rufemaki idanu kike son ta kere su a komai ta yi musu zarra? Idan bacci kike ki farka, kin nemawa yarinya har ya zama mai arziki, a kuma yanda naji zaƙin miyarta ina mai tabbatar maki watarana sai ta fi ki kuɗi. Tukunna ma, kuɗaɗen kina nufin ita za ki dinga damƙawa?"

Mami ta yi shiru na ƴan sakanni har Anna ta ƙara tankawa yayinda Jannat kuwa ta ja tsaki don tana jin haushin yayarta sosai, tana abu tamkar a duniya su Humaira ta haifa ba su Futuha ba. Can dai Mamin ta yi magana.

"Ta asusuna kuÉ—in za su shigo."

Murmushi Anna ta yi mai tarin ma'ana kafin ta ce.

"Na sanki Maryama, ni na haifeki. Kar ki zo mini da rainin hankali da wayo kinji ko? Wato ni ga sakara shi ne za ki rufe ni ruf, to ai koda ta asusunki kuÉ—aÉ—en suka shigo a yanda kike nunawa yarinyarnan kamar ki lashe ta, ke me iya yin hidimar ta ce ba naki ko yaranki ba. Kaiconki Maryama, lallai idan ba bi a hankali ba yarinyar nan watarana sai ta watsa maki borkono a idanu. Kina wasa da wuta."

Janant ta kalli Mami, sai kuma ta girgiza kai.

"Anna, zai fi kyau ki bar wahalar da bakinki a kan wannan saboda ɗiyarki ta yi nisan da ba ta jin kira. Ita mai miji, burinta ta nunawa duniya ta fi kaunar ɗa wani sama da nata yaran. Idan kin ji yanda yarannan ke ƙorafin nuna halin ko in kula da take yi musu sai ki rantse ba ita ce ta yi naƙudar su ba a bola ta tsinto su. Babu ma kamar su Yassar wadanda su ubansu bai sakarmusu sun ji dadin rayuwa irin na matasa sa'anninsu ba, su ba su sami wata kyakkyawar kulawa a wurin uwar ba. Ni na rasa irin wannan gidan da rayuwar cikinsa. Ba haka nake rayuwa a gidan nawa mijin ba, shi koyaushe burinsa ya wadata mu da abinda za mu huta ni da yaransa, amma tun da na rayu a gidannan har na yi aure, mijinta bana jin ya kashemin sama da dubu ɗari biyar a rayuwa."

Mami ta miƙe tsaye tana duban Jannat, zuwa yanzu ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci.

"Ya isheki hakanan! Ke tsabar rashin kunya har kya kalli kwayar idanuna ki faɗan magana? A gidan dai da kika raina nan kika rayu sannan ko Yusuf bai kashe maki sama da kuɗaɗen ƙaryar da kika buga lissafinsu ba, ai kin ci kin sha daga jikinsa. Ke yanzu idan da kina can wannan dajin kina rayuwa, har kin isa ki ga shi mijin da kike tutiya da shi ki aura? Ni na isheki! Nan da kike ganina kar nake, na fi ku sanin inda ke mini ciwo. Ba damuwarki ba ce kuma balle ki sani, idan har ba za ki dauke idanu daga lamuran gidana ba, ki tattara ki..."

"Maryama!" Tsawar da Annan ta bugamata ne yasa ta yin shiru tana fesar da huci mai zafi, ta kalli Anna sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Jannat nan ta haukacewa Anna wai Mami ta yi musu gorin zama a gidan don haka su tattara su bar mata gidanta. Anna dai ta dinga lallaɓa Jannat, ta sani muddin ta bi cewarta ta bar gidan to fa komawa can wani ƙauyensu dake garin Agadez ya kamata, yanda ta fito ta ɗanɗani rayuwar daula koda ace bai kai yanda ta ke so ba, ta gwammace ta cigaba da rayuwa a nan. Ta sani babu ta yanda za'a yi shegiyar surukar zamani irin ta Jannat ta amince da zamanta a gidan ɗanta. Dakyar dai ta samu Jannat ta janye ƙudurinta, tsana da haushin Humaira ya ƙara ninkuwa a ƙasan ranta.

***
Humaira kuwa sai ta nemi murnar da take yi na Oda ta rasa, jiki a saluɓe ta yi mata dahuwar dafadukan macaroni mai busasshen kifi. Ƙamshinsa ya karaɗe kicin ɗin da falo. Koda ta kammala ta haɗa komai a ƙaton faranti ta kai mata babu godiya ba kallon arziki, itama ba ta sa a ka ba kawai ta jya da zummar tafiya.

"Ke zo nan!"

Muryar Anna ta ji, ta runtse idanu kirjinta na dukan tara-tara cike da tunanin da wanne kuma Annar ta zo yanzu ta juya ta koma ta durkusa ba tare da ta kalleta ba. Ta soma magana a kausashe.

"Ɗago ki kalleni nan, ni da kike gani dai na fi ƙarfinki. Mun ci dubu sai ceto, zuri'ar Mamman Ɗan Jika daidai nake da kowane bafillace mai taƙama da asiri. Har mu za a gayawa asiri? Tun wuri ina gargaɗinki ki fice a rayuwar ɗiyata, idan ma wani mugun ƙullin aka kawoki da shi don ki shiga tsakaninta da yaranta toh ahir ɗinku, ni dai na fi ƙarfinku balle kuma tsatsona. Ki kama kanki tun kafin na ɗau mummunan mataki a kanki. Ɗan girkin da kike taƙama kin iya ni mai iya juya lamarinki da shi ne, idan kuma kina da ja ki cigaba kar ki fasa. Asir dai ba za ki nunamana ba, mun saka Allah a gaba ne kawai shiyasa muka watsar. Amma muddin kika ce za ki cigaba da juya ɗiyata kamar waina da shiga tsakaninta da yaranta da ta haifa da cikinta ni nan zan nunamaki iyakarki."

Tana kaiwanan ta juyar da kai tana girgiza ƙafa na bala'i. Humaira ta dubi Anna dakyau, an zo gaɓar da ba za ta jure ba sai ta ba ta amsa ko yaya ne. Ƙazafin sihiri ba za ta jure shi ba don haka ta soma magana da wani irin ƙunar rai.
Chapter 32 · 0% Book details