← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 35 OF 101

Sashe 35

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Tab, ai  wallahi yanzu a zamanin nan dai babu abin alfahari kamar sana'a, ita fa mace mai sana'a ta huce takaici. Ba ruwanta da jiran sai an bata ko kuma an yi mata, kawai gani za'a yi a jikinta tana fitowa ɗas abinta. Muna nan daku in sha Allahu Humaira sai ta zama abin kwatance, wacce ko mai Masters ba zai nunamata arziki ba. A wannan lokacin kuɗi kawai, ilimi ba a taɓa yin latti da nemansa, ballantana ma me zai damu mutumin da yake neman ilimin Muhammadiyya. Ai shi ne maƙurar ilimi, sauran duka bogi ne."

Jin haka ai sai Futuha ta harzuƙo ta kai wa Raihana bugu, Raihana  ta kauce.

"Shegiya kai! Na sa da ke? Ko kin ji na ambaci sunan wata? Da ke nake magana ko Tasleem, iskanci kawai. Ina magana kina sanyamin baki duka zan maki a gidannan. Kin wani raina mu sai kace sa'o'inki. Kema watarana idan ba mu yi dagaske ba shaƙe mu za ki yi tunda ai zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai."

Ta karashe tana  watsawa Humaira wani banzan kallo ita kuwa ta kauda kai tana murmushi. Aikin banza, idan rashin kunya ne na nawa kuma suna gwada yiwa har Mamin balle a junansu, babu kamar Futuha da yanzun kanta ke bala'in rawa ana lallaɓa ta, hatta da Mami kamar ma tsoron sanya Futuhar aiki take yi a yanda ta lura, ba ta sani ba ko don Alhajinta mai hidima ne ko kuwa dai kawai saboda ta kusa aure ne. Tasleem dama ba koyaushe take wuni a gidan ba, saboda zuwa asibiti.

Ba ta kara bi ta kace-nace da suke yi da Raihana ba ta É—auki takarda da bironta ta koma wurin Ummita wacce itama a yanzu ke kokarin koyamata wasu kalaman na boko irin na yau da kullum da take ji ana É—an faÉ—i. Sosai kanta yana É—auka.

***
Ya lumshe idanu yana taunar samosa,  har ya kammala bai iya ya buɗe ba, sai can ya buɗe gami da kai hannu zai ƙara, caraf Ibb ya riƙe tsintsiyar hannun yana dariya.

"Wai kai na tambayeka, ni da na zo wurinka, ni ka kawowa na ci ko kuwa dai kanka? Tun dazu ka kawomin abu amma ka zage sai ci kake, oh don ban ce a bani nawa kason ba tunda dai a gabana aka ƙulla kasuwancin?"

Fadeel ya harareshi.

"Ban da wanda Anti ta cemin ka ci a can? Wannan kuma ni da kai na kawo wa, idan za ka ci ka ci, ka biyemin kaf zan tashi da shi."

Ibb ya saki hannunsa yana murmushin wannan irin kauna. Shi kuwa bai ko kalleshi ba ya cigaba da kai girkin Humaira bakinsa. Can a gajiye ya dubi Ibb.

"Yarinyarnan tana son kashe ni da raina."

Ya kalle shi da kyau kawai ya ji ya ba shi tausayi. A sanyaye yace.

"Meyasa za ka yarda da hukuncinta? Fadeel ka wartsake daga baccin da kake, sorry to say, amma yarinyarnan ba ta sonka. Idan kuma ba za ka hakura ka cire ta a zuciya ba, toh ka yarda mu samu su Alhaji a je nema maka aurenta."

Fadeel ya girgiza kai yana jin ciwo a kirjinsa idan ya tuna wai Humaira ba ta sonsa.

"No, ba zan taɓa yi mata dole ba, amma zan ɗaukar maka alƙawari ɗaya."

"Mene ne shi?" Ibb ya faɗi cike da zaƙuwa.

"Muddin lokacin da ta ban sun cika, zan sanar da Alhaji a neman aurenta. Idan kuma ba ta amince da ni ba, zan haƙura da ita saboda ta samu nutsuwar zuci."

Ibb ya sauke ajiyar zuciya, shi fa sam ba haka ya so ji ba. So ya yi aminin ya furta kalmar rabuwa wanda ya sani sai dai ya yaudari kansa, ba mai yiwuwa ba ne. Yana kuma ji a ransa, muddin Fadeel ya yi dakon shekara, toh shakka babu ba abinda zai sa ya iya hakuri da rashin Humaira. Amma sai ya bar komai a ransa.

"Shikenan, Allah ya yi maka zaɓi nagari."

"Ameen." Ya amsa shi ma.

"Ba za ka ci ba ne?" Cewar Fadeel wanda zuwa lokacin cikinsa ya ƙoshi amma bakinsa na son ɗanɗanon don haka ya haƙura ya ɗau gorar ruwa. Harararsa Ibb ya yi.

"Oh, bayan ka cinye kenan ko?"

Murmushi Fadeel ya yi ya cigaba da kora ruwa a cikinsa ba tare da ya tanka ba.

***
BAYAN WATANNI BIYAR...*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA. KAR KI MANTA BAYAN NAN AKWAI CAN, ALLAH YA SA MU DACE AMEEN.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Gidan Alhaji Yusuf wanda aka fi sani da Maiagogo sun wayi gari ranar alhamis da shirye-shiryen bikin yaransa biyu, Futuhatul-Khair Yusuf da kuma Tasleem Yusuf wanda kwanaki uku kawai ya rage a fara. An samu sauye-sauye da dama, na farin cikin ya fi kowanne yawa ga Humaira da duk ma wanda ke tare da ita. A wannan watannin ta samu alheri mai yawa daga sana'arta. Babbar customer dinta ita ce Hajiya Rukayya wacce ta hanyarta kaɗai ma ta samu oda na biki da party har ya zamana tana gwada na abinci bayan snacks sai dai gaba ɗaya sau biyu ta gwada abincin taro ba laifi kuma masu shi sun yaba hakanan Hajiya Rukayya ta ji dadi da ba ta ba su kunya ba. Duk abin nan ba su taɓa ganin juna da ita ba sai dai waya. Mami ta sa an buga leda da stickers mai tambarin DEELSHA'S DELICACIES. Suna na musamman da Raihana da Ummita suka ba Humaira a sadda Mamin ta ce ta yi tunanin sunan da za'a sanya a ledar. Sunan ya yiwa Humaira daɗi ko kadan kuma ba ta tambayesu ma'anarsa ba. Mamin ma ta ji dadin sunan, ganin kalmar turancin ya sa ta tambayar wacce ta sa, nan Humaira ta sanar da ita su Ummita ne. Daga haka ba ta kara cewa komai a kai ba.

  A yau da ya rage kwanaki uku bikin yan matan Mamin, gidan nasu ya soma karɓar baƙi ƴan uwan Mami daga Agadez sai ko ƙawayen Futuha waɗanda suka zo daga nesa kasancewarta mai jama'a fiye da Tasleem. Yan uwan Abba kuwa ba wanda ya zo gidan da zummar kwana. Mubarak shima ya zo gari, sai kuwa Anti Jannat. Ya kasance a wannan lokacin gidan ba ya rabo da jama'a, Mami ta sa Ladidi kawo mataimaka a aiki har su uku saboda yanayin cikar gidan da zummar bayan biki za ta sallame su.
  Anko har kala biyar aka fitar, na ƙawaye daban wanda zasu sanya ranar kamu da na daurin aure da yini sai ko na ranar dinnerparty. Na manya su ma kala biyu, na fita kamu sai na ranar daurin aure.

Humaira, Raihana da Ummita daban aka fitar musu da na sisters wanda zasu saka na yini sai kuma na dinnerparty da Mami ta yiwa su Futuha jan ido ta karɓar musu katinsu ta riƙe a wajenta don a farko sun nuna su ko kusa ba su kaunar su halarci dinner din.

   Amare sun sha gyara ba na wasa ba daga mai gyaran jiki na musamman da Mami ta samar musu suke sintirin zuwa. Hajiya Lubna ita da kanta ta ɗauki nauyin gyara su, gyara irin na mata. Ta kashe kuɗaɗe masu kauri kuwa wanda hakan ya burge aminiyarta kwarai ta yaba.  Ba ma ita ɗaya ba, ƙawayen Mami da dama manyan mata masu kudi sun ba da gudunmuwa mai yawa na kudi, kanta ya fasu sosai ta kuna ga fa'idar mu'amala da masu hannu da shuni.
Su Raihana sun karɓi dinkunansu a hannu, sun yo ƙunshi da kitso abinsu sun fito fes.
   A na washegari kamu ne su na zaune suna hira a daki tare da wasu yan uwan su Raihana sa'anninsu da suka zo daga Nijar, Tasleem ta shigo. Fatarta har wani ɗaukar ido yake, ba ta da ƙiba irin na Futuha ita nata jikin daidai misali ne, duban Humaira ta yi fuska ba fara'a.

"Ke Humaira, ke da Ummita ku zo na aike ku."

Humaira ta ji ciwon ke din da tayi kiranta da shi, ita kuwa Ummita ko a jikinta ta miƙe tana murmushi. Hakanan halittarta yake, tana da yawan murmushi, abinda zai sanya hawayenta zuba kuwa, toh fa ba ƙaramin abu ba ne kamar dai akan Humaira ko kuwa wani abun daban. Kamar ba za ta miƙe ba sai kuma ta yi tunanin ba komai ta yi tunda dai aure ma za su yi su bar gidan sai ziyara don haka ta taushi zuciyarta ta miƙe itama. Saƙo ta ba su a leda na ankon Dinner su je su kai can asibitin Malam wajen ƙawayenta kuma abokan karatunta da suka samu dakyar don har ta ƙare. Ta miƙawa Ummita dubu su yi kuɗin mota sai kuma lambar wayar ɗaya daga ciki, Sadiya, sun gane ta, takan rako Tasleem din gida wasu lokutan don ta dauki wani abun ko kuma ta zo takanas ziyara.
   Bayan sun fito waje Humaira ta dubi sararin samaniya yanda garin ya haɗu da hadari ana cida, lokacin uku da mintoci, ta ja guntun tsakin takaici.
 
"Kinsan Allah, sa'ar da ta ci kawai na ganin wannan shi ne aike kusan na karshe da za ta yi mana kafin ta bar gidannan shiyasa kawai zan je, amma ban da haka wannan ke É—in da ta ce wallahi da babu inda zan je matukar ba Mami ce ta sa baki ba."

Ummita dake kokarin cusa ƙaramar lema a jaka ta ɗago tana murmushi.

"Humaira ko rigima, rabu da ita lokaci ne ai wataran sai labari fa. Yanzu kalli, ina Anti Jannat? Ba ta yi aure ba sai dai ta zo kawai ziyara ta tafi? Toh su din ma hakan ce za ta kasance, mu ma watarana sai ki ga mun yi namu auren mun tafi mun bar gidan. Sai a dade ma kafin a ganmu."

Tsaki Humaira ta ƙara ja.

"Ke dai Ummita kina son aure na lura, magana kaÉ—an za a yi da ke sai kin yi zancensa."

Da mamaki Ummitan ta kalleta kafin ta amsa.
Chapter 35 · 0% Book details