Sashe 11
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
"Malama na fada! Nace na fada! Kabeer din banza da wofi! Ba zan je ba din akwai abin da za ki iya yi? Ko waye ya tilasta ni shiga lamarinsa sai na gasa mishi maganganun da zai yi dana sani!"
Raihana gaba daya ta tsorata, kamar dai Humaira kamar ba ita ba. Kawai sai ta gifta ta fice daga É—akin ba tare da ta tanka ba don dama Raihana akwai tsoro. Ummita ta mike ta kama hannun Humaira a sanyaye.
"Humaira, lafiyarki kuwa? Me ya yi zafi?"
Ba ta ce komai ba kawai ta zare hannunta a cikin na Ummita, zama ta yi ta yi shiru sai huci ga gumi na tsastsafo mata. A haka Mami ta shigo dakin, Raihana duk ta ba ta labarin abin da ya faru, kallon Humaira take yi a nutse, sai kuma ta karasa ta zauna gefenta. A hankali ta dafe hannunta. Humaira ta kalleta, kawai sai ga mamakinsu ta fashe da kuka.
"Mami don Allah kiyi hakuri, wallahi na tsane shi, ki ganinsa bana son yi. Kiyi hakuri don Allah ki janye batun zuwa mu gaisa da shi."
Wani irin kuka ne da sheshsheƙa tamkar wacce ake kokarin raba ta da numfashinta. Mami da Ummita wacce duk ta firgice suka dubi juna sai kuma ta rungumo Humaira.
"Kar ki damu, ya tafi ya bar gidan ma. Kuma na yi maki alƙawari Kabeer ba zai ƙara takura maki ba. Kin ji ko?"
Sai a sannan ta gyaÉ—a kai ta bar kukan, lokaci guda kuma ta fara dawowa hayyacinta. Ita dai Ummita ikon Allah ta zubawa ido tana kallo. Abin dai kamar a wasan kwaikwayo.06
Dare ne misalin karfe ɗaya da mintoci, ɗakin ya yi shiru ban da munsharin Tasleem ba abin da kan addabesu kullum ba abin da ke motsi. Humaira wacce abu biyu suka hana ta sukunin bacci, ta zubawa tagar ɗakin ido tana kallon farin wata da ya hasko har cikin ɗakin nasu. Garin babu zafi sai iska dake kaɗawa kaɗan kaɗan hakan yasa rashin wutar bai hana mutanen gidan sukuni ba. Ta ja guntun tsaki ta miƙe zaune gami da runtse idanunta.
_'Humaira ba ki kyautata kalamai ga Mami ba. An sani maganar Kabeer kika tsana, sai dai yanayin da kika yiwa Mami magana kamar wata Humairar aka chanja ba ke ba. Idan kin yiwa Raihana wannan dama abokiyar yinki ce, amma ga Mami, kin yi kuskure.'_
Ta tuno kalaman Ummita, wannan na daga cikin abin da ya damu zuciyarta, Mami fa, matar da ta ke ba ta kulawa da zuciya É—aya. Ta maye mata gurbin Dada da Mamarta wacce ba ta buÉ—i ido ta gani ba. Ta kuma zame mata abokiyar hira a lokuta da dama idan tana zaune ita kaÉ—ai a gidan. Hakan za ta dinga ba ta labarin Nijar itama ta ba ta na ainahin garin iyayenta wato Agadez su yi ta nishaÉ—i.
Abu na biyu da ya tsaya mata a rai bai wuce na mamaki da tunanin abin da ta yi ɗin ba. Eh ta san ba ta son Kabeer, ta tsani ma ganinsa, amma tsanar har ta yi yawan da za ta kasa ɓoyewa har haka? Ita kam abin ya sha mata kai.
Tana nan zaune dai ganin ɓatawa kanta lokaci da tunani take yi da b zai magance mata komai ba sai kawai ta maida kai filo a hankali bacci ya sure ra. Duka wannan zaman da ta yi har zuwa kwanciyarta akan idanun Raihana wacce munsharin Tasleem ya hana ta sukunin bacci. Tsoron yarinyar ya ƙaru a zuciyarta, ta kasa kwakkwarar motsi ga fitsari cike fal a mararta amma ina, ga ni take ai tana miƙewa Humaira za ta tashi ta shaƙe ta don ta gama ba zuciyarta cewar iskokai ne da Humairar. A wannan daren dai bacci ɓarawo ne ya sace Raihana.
***
Ta kammala shirinta tsaf kamar koyaushe za ta wuce wurin koyon girki, ta fito falon. Ummita na zaune tare da su Muhsin a falon, Raihana kuwa na gefe ɗaya ta hakimce tana abin da ta saba, latse-latsen waya. Ganin Humaira yasa ta kalle ta sau ɗaya ba ta ƙara ba don ita ba ta so ma su haɗa ido, har ga Allah tun can tana tsoron mai aljanu. Tana kuma shakkar yi musu rashin kunya tun wataran tana jss 2 da wata abokiyar karatunta ta shaƙe ta akan ta zauna a kujerarta ta kuma yi magana amma ta ƙi tashi. Da ta fusata ta shaƙo wuyanta sai da malaminsu ya kwace ta. Abba har makarantar ya je, iyayen yarinyar suka ba da hakuri aka kuma sauya musu aji. Tun daga nan ta ke tsoron duk abin da zai danganta ta da mai iskokai. Ko kusa da su ba ta raɓa.
"Har kin fito kenan?" Ummita ta tambaya tana kallonta fuska a sake. Itama murmushin ta yi.
"Na fito, ina Mami?"
"Tana sashinta." Daga nan ta nufi sashin Mamin, a falo ta iske ta tana waya tana dariya, ganinta yasa ta yi sallama da ɗaya ɓangaren ta ajiye waya. Cike da walwala ta ce.
"Ƴar Mami har an fito?"
Kunya ta kamata, ita kunyar Mamin take ji wallahi, ta karasa ta durkusanta gaida ta.
"To, wata sabuwar gaisuwa ce nan ban da wacce muka yi É—azu?"
Mamin ta faɗi cikin wasa da dariya, Humaira dake sunne kai ta ɗan murmusa, ita ta manta ma sun gaisa ɗin. Mamin ta ƙara magana.
"Au, ashe gidan Laila za ki ko? Bari ma na ba ki saƙonta ki tafi da shi." Mamin daga haka ta miƙe ta nufi ɗaki, can ta fito ɗauke da leda wacce Humairar ba ta san ma ko mene ba ta karɓa. Ta ba ta kuɗin mota tana fadin.
"Abbanki ya riga ya fita na mance ban karɓar maki na motar ba, ki je kawai idan ya dawo sai na karɓa."
Ta gyaɗa kai ta sa hannu ta karɓa da godiya, ganin ta ƙi motsawa balle ta tashi ya sa Mamin tattaro nutsuwarta gareta.
"Lafiya Humaira? Akwai magana a bakinki ko?"
Gyaɗa kai ta ƙara yi a karo na biyu, cikin nutsuwa kuma ta soma magana.
"Mami dama akan abin da ya faru jiya ne, ina neman gafara."
Murmushi Mamin ta yi ta girgiza mata kai.
"Kar ki damu, ni nasan ba laifinki ba ne. Hakan ya sa na yi maki uzuri. Ki cire komai a ranki kedai ki tattara nutsuwarki ki cigaba da maida hankali ga darussanki. Laila na ta yabon kwazonki don haka ki ƙara dagewa, na maki alƙawarin Kabeer ba zai ƙara shiga sabgarki ba, kin ji ko?"
Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta samun nutsuwa, ta amsa da toh daga nan suka yi sallama ta mike ta fita, Mamin ta bita da kallo tana murmushi.
***
Tuƙi ɗan sahun ke yi cike da nutsuwa, sosai tuƙin ke mata daɗi yayin da iskar dake kaɗawa a garin ke ƙara jefa ta cikin walwala. Damuwar da ta kwana da shi a ƙarƙashin ranta, tas ya wanke ya koma annashuwa. Don haka murmushi take yi ma ba tare da sanin tana yinsa ba. Ba zato ta ji ta yi wani irin hantsilawa sai ga ta a bayan ɗan sahun nan hannayenta rungume a kan wuyansa kai kace wacce aka goyo. Shi kuwa ɗan sahun kansa ya ƙumu da jikin gilashin da karfi har sai da gilashin ya tsage, saura kaɗan adaidaitar ta wuntsila amma Allah ya taƙaita faruwar hakan, sai ya koma baya da ƙarfi har tayoyin na bugun ƙasa da ƙarfi, wannan ya sa ta koma mazauninta, lokaci guda ta saki ƴar guntuwar ƙara sakamakon cikinta da ya bugu da ƙarfen jikin mazaunin direban yake mata zafi dalilin buguwar da ta ƙara yi dalilin komawa baya. Ta runtse idanu daidai sadda ta ji salatin jama'a a kansu. Gaba ɗaya ma ta kasa buɗe idanunta tana dafe da cikinta, ta yi shiru kawai don hayaniyar ma ba burge ta take ba.
"Sannu Æ´anmata, sauko."
Ta tsinkayi É—aya daga cikin jama'ar wurin na fadi, wasu kuwa na hayaniya su na fadin ai laifin mai motar ne. Can kuma ta ji an ce.
"Alhaji kai ne da laifi, kai ka bugi motarsu garin cin burki a kurarren lokaci."
Ta buɗe idanunta a hankali jin wani daddaɗan kamshi a gefe, a hankali ta sa hannu ta ɗauki jakarta da ta tarwatse a ƙasa, duk tarkacenta sun zubo. Wani matashi ya shiga tattara mata ita kuwa tana son ta fito a adaidaitar kamar yanda ɗan sahun ya fita ya zauna gefen kwalta, amma ina tururuwar mazan dake wurin ya sa ko motsin kirki ta kasa. Da murya irin ta manyan mutane ya amsa.
"Baba, ba abin zafi ba ne. Na sani ni keda laifi, ina mai ba da hakuri garesu. Zan kuma yi kokarin gyara ɓarnar da nayi. Ku yi hakuri don Allah."
Humaira ta juya ta kai duba ga mai maganar, daidai lokacin da shima ya ɗan rankwafo don ya yi mata sannu da kuma neman alfarma akan ta sauko su je asibiti. Kalma ɗaya ta kasa fita a bakinsa da ya yi nauyi. Ƙafafunsa suka soma ƙoƙarin kayar da shi. Zai iya rantsuwa ba kaffara son budurwar yarinyarnan yake da idan da ace Uwargidansa ta yi haihuwar wuri to fa ya ci ya yi haihuwar fari da ita. A ɓangaren Humaira kallon da ta bishi da shi bai wuce na son ganin marar hankalin da bai iya tuƙi akan ƙa'ida ba har yake shirin kai ta barzahu. Babban mutum wanda ba gigin kuruciya tattare da shi, ya sha manyan kayansa har da babbar riga da hula. Kana ganinsa dai ka ga wanda ya ba arba'in baya. Ganin yadda ya ƙuramata idanu sai nan da nan ranta ya yi masifar ɓaci, ta ja tsaki wanda ya ba Alhajin nan mamaki, ba ta jira komai ba ta sauko daga adaidaita sahun ta ɗaya ɓangaren mutane na mata sannu. Matashin da ya tattara mata kayan ta yiwa godiya ta karɓi jakarta, ba ta so dubawa ba amma da yake ya matsa sai kawai ta duba, komai nata yana nan cif ba abin da ya ɓata. Dakyar take tafiya dalilin gefen cikin da har sannan ke mata ɗan zugi.