Sashe 50
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali har da cewa koda ace kudaden da Abban za su haɗa ba za su kai ba, shi ya ji ya gani zai san yadda za'a yi a cika a bayar don su kuɓuta, balle kuma shi Fadeel din wanda yake jin zai iya sadaukar da dukkan abin da ya mallaka a doron ƙasa don kuɓutar rabin jikinsa daga hannun azzaluman nan. Sosai ya ji dadin zantukan Daddy, da wannan ya lallaɓa ya yi wanka, brush, da alwala, Ibb ya ba shi kaya ya sauya. Daga nan ya hau ramuwar sallolin dake kansa.
Bai kai ga idarwa ba sai ga Anti Amarya tare da Murja sai ko Fu'ad da ya kawo su, hannun Murja riƙe da kwandon abinci. Ta gaida su Abban sannan ta karasa ta ajiye gefen gadon. Gefe ta koma tana satar kallon Fadeel ɗin da a kwana ɗaya kawai ya zabge. Zuciyarta na wata iriyar tafarfasa.
 'Ka yi ka gama Fadeel, na rantse maka koda ace Humaira ta fito ni Murja sai na kashe ta da hannuna. Ballantana ma ba za ka ƙara ganinta ba.'
Ta yi maganar a zuci, su Alhaji suka tafi saboda yamma ta kawo kai yayinda Ibb suka fita don yi musu rakiya. Fadeel na idarwa ya dubi Anti Amarya ya gaishe ta, ta amsa tana mishi sannu. Ido ta É—an yiwa Murja hakan ya sa ta saurin gaida Fadeel, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.
 Nan suka zauna har sai da Fadeel ya ɗan sha ruwan shayi dakyar amma sam ya ƙi yarda da cin abinci, tunaninsa ko a wane yanayin Humaira take? Watakila ma ko abincin ita ba a ba su sun ci ba. Wannan ya daƙilar da shi daga ci.
***
 Sahabi saurayin Ummita kullum sai ya zo gidan ya gaida Abba da Mami, gaba daya ya komaɗe ya rame tsabar tunanin Ummita. Iyaye da ƴan uwansa babu wanda bai shigo jajantawa ba. Hakanan ƴan makarantar islamiyyar su sun zo sun kuma yi saukar Alkur'ani akan Allah ya bayyana su. Hatta da yan makarantar su Ummita na boko sun zo har da malaman makarantar an jajanta. Aka yi addu'a suka tafi.
 Labarin dai yana ta yaÉ—uwa don har waÉ—anda su Abban ba su ma sani ba sun zo sun taya su jaje, da yawansu a social media suka ci karo da shi. Mubarak dake Ghana yana jarrabawar Æ™arshe hankalinsa gaba daya yana Kanon, ba don Abba ya ce kar ya zo ba ya zauna har ya kammala da tuni ya dawo. Hakanan su Yassar ba su zo ba. Amma sosai abin ya taÉ“a su duk da Æ™iyayyar da suke yi musu.Â
 Â
  Æangaren Futuha kuwa Æ´ar Dubai, kasancewarta mai mu'amala sosai da yanar gizo sai ga abin nema kuma ya samu. Bidiyo sosai ta yi tana kuka ga hotunan Ummita da Humaira daga Æ™asa ta É—ora a shafinta tana addu'ar Allah ya bayyana su a Æ™arshe ma har da sanya muryar shahararren Malamin nan wato Sudais yana addu'a. Koda ta É—ora hankalinta kwance ta shiga duba yadda ba a É—auki dogon lokaci ba bidiyon ya yaÉ—u, nan fa jama'arta suka fara jajanta mata su na tambayar dama Humaira mai shafin Deelsha's Delicacies yar uwarta ce? Da yawa ma wadanda ba su san Humairar ba ko shafinta sai lokacin suka dinga followinh dinta, lokaci guda shafinta ya yi jama'a fiye da dubu talatin. Hakanan shafin Ummita ma ya yi jama'a.
Raihana tana kallon duk abin da ke wakana amma ba ta magana, karshe ma sai ta kashe wayarta gaba daya ta ajiye. Tun da Abba ya shaida musu da kuɗaɗen da aka ce a bayar na fansar Humaira da Ummita ta ke jin ƴar nutsuwa, ko ba komai kenan su na lafiya kuma Abban ma ya tabbatar musu ya ji muryoyinsu amma bai ce musu ga a yanayin da ya ji ba gudun tayar musu da hankula.
***
 Fadeel da Ibb suka shirya tsaf a washegari zuwa gidan su Humaira kamar yanda Fadeel din ya nema. Hankalinsa ya kasa kwanciya da zamansa a asibiti alhalin ba a ga Humaira ba, kuma bai je ga iyayenta ba. Wannan ne ya sanya su Alhaji goyamishi baya don haka ana ba shi takardar sallama ya kama hanyar gidan.
Sun samu tarba na mutunci daga Abba, Tasleem tun ganin da ta yiwa Fadeel matsayin saurayin Humaira ya zo jajantawa ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. Kishin nan daɗaɗɗe na Humaira ya taso ya soma cin zuciyarta. Har gobe akwai son Fadeel a ƙirjinta, ta kuma tabbata da ace shi ta aura da yanzu wani labarin ake ba wannan ba.
Kusan lokaci guda suka shigo gidan da Fadeel anan ta gan shi, shi kuwa bangaren Abba suka nufa inda Ƙasim da ya yi musu iso ya raka su ciki. Fauziyya ce ta yi mata rakiya gidan, tana kuma lura da sauyin da ya zo mata lokaci guda sadda Ƙasim ya dawo yana shaida mata ai manemin auren Humaira ne. Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba tana ƙara nazarinta.
 A falon ta bar Fauziyya ta faɗa ɓangaren Anna tana huci. Nan ta tarar da ita zaune da Jannat wacce ke zaune tana taunar gasasshiyar kazar da ta siyo suna hira da Anna kai ka ce babu wani tashin hankalin da ake yi a gidan. Ganin yanayinta ya sanya su dubanta.
 "Toh mai ciki, yau kuma wa ya taɓo ki?"
Ta zauna idanunta suka cicciko da kwalla yayinda zuciyarta ke faman tafarfasa. Kwafa ta yi kana ta amsa.
"Wai Fadeel na gani ya zo jajantawa Abba fa? Har yanzu dama yana tare da Humaira? Shi ne don munafunci Humaira ta ci amanar Mami ta ɓoye zancen?"
Murmushi Jannat ta yi.
"Ke ban da abinki ina Humairar take a yanzu? Kina tunanin shirin na wasa ne za ta dawo, ai daga can inda take sai wata duniyar kuma ba wannan da muke ciki ba. Duk fa wanda ya samu dama ya dama. Kuma da kike wannan maganar ba yanzu gashinan kin auri Hamza ba? Ba kya sonsa kika bari ciki ya shige ki?"
Tasleem ranta ya ɗan yi sanyi jin yadda Anti Jannat ke fadin kaddarar Humaira kai ka ce ita ta rubuta hakan. Batun cikinta ya ƙara jefata damuwa, dama ba da son ranta ta samu ba kuma Hamza ya rantse sai ya yi mugun saɓa mata idan ta zubar.
"Wallahi Anti idan har zan samu na auri Fadeel zan iya kashe ko nawa ne a yimin aiki a kan Hamza ya sake ni. Anti wai kin taɓa ganin Fadeel kuwa da irin yadda ya haɗu? Wallahi ba zan iya zuba idanu wata ta kwacemin shi ba."
Anna tsohuwar banza ta kwashe da dariya madadin ta yi kwaɓa akan wannan haramcin da ake aikatawa sai ma ta ce.
"Kina da Jannat Firdausi ai babu ke babu fargaba. Yadda aka yi wancan haka wannan ma zai kasance labari."
Suka yi dariya. Can kuma Jannat ta É—an jinjina kai.
"Ko wane ne wanda ya aikata wannan kidnapping din ya yi matuƙar burgeni, da ace ina da damar ganinsa sai na mishi babbar kyauta. Sai hakan ya zo mana da nasara kuma akan gaɓa, Boka ya tabbatarmin da cewa Humaira a can za ta haɗu da ajalinta. Itama Ummita babu tunanin za ta rayu balle har su samu damar kuɓuta su dawo. Kawai dai zan so dawowar ita Ummita, yarinyar ta iya bauta."
Tasleem ta yi murmushi.
"Nima dai Ummita ba ta yimin komai ba, ba ni da wani ƙulli da ita kamar Humaira. Wallahi Anti na tsane ta na kuma tsani duk wani mai sonta."
"Har da ni kenan!"
Suka juya don ganin mai furucin a razane.
®ï¸Rufaida UmarMurja ta jima tsaye jikin tagar falo tana hangen fitar Fadeel a gigice. Ranta idan ya yi dubu toh ya É“aci. Hankalinta kuwa idan akwai abin da ya fi gaban tashi toh ta ya yi wannan dalilin ne ya sanya ta komawa cikin daki da sauri-sauri ta É—auko gyalenta sai ko waya da jaka ta fice daga gidan a birkice har Anti Amarya wacce ta fito daga nata É—akin tana tambayar ko lafiya kuma ina za ta je amma babu amsa.
***
Kasancewar tare suka isa asibitin da ƴan sanda wannan ya sa a gaggauce aka karɓi Humaira da Ummita zuwa emergency. Abba ya kasa zaune balle tsaye, ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanunsa, ga jiri na kwasarsa yana ta ambaton sunan Allah kamar zai ciri baki. Daidai lokacin Fadeel ya shigo a birkice ya ƙarasa ga Abba.
"Abba sun fito? Su na ina? Me ya same su?"
Dukkan waɗannan tambayoyin ba a hayyaci yake yin su ba. Abban ma da ba a wani nutse yake ba sai ya kasa tanka mishi kawai sai ajiyar zuciya da kallo ga lebban na motsi amman ko harafi guda ya kasa fitarwa sai D.P.O ne ya karɓi zancen ya yiwa Fadeel bayani.
"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu babu abin da zai faru garesu. Likitan ya tabbatar mana ga dukkan alamu kwayoyi aka ɗura musu amman in sha Allah za su yi iyakar ƙoƙari a kansu."
Fadeel ya dafe kansa ya yi juyin, ya yi safar ya dawo ya kai marwar amma wannan kalmar ta ya kwantar da hankalinsa ya kasa samun matsaguni a zuciyarsa. Kwayoyi? Ya ma rasa inda zai jefa zancen a kwakwalwarsa ballanta ya samu ya yi aiki da shawarar D.P.O Salahuddeen.Â
***
A can gida kuwa, Tasleem tun sadda ta kai labarin tafiyar Abba fanso su Humaira, Jannat ta dauki waya hankali tashe ta kira Bokanta. Kaca-kaca suka yi sosai tana zaginsa akan ita fa ba su yi haka ba. Wannan ya sa Boka tun a wayar ya ci alwashin sai ta girbi wannan tozarcin da ta yi masa. Kasancewar idanunta sun rufe ruf sai kawai ta ja mugun tsaki ta katse kiran.