← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 12 OF 101

Sashe 12

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

"Sannu baiwar Allah, kiyi hakuri ba da gayya hakan ta faru ba. Direbana ne ya É—auki waya bisa umarnina ba kuma mu ankara ba hakan ta kasance. Akwai inda ke maki ciwo sai a karasa asibiti."

Ya karashe yana kai idanunsa kan gefen cikinta da take ta faman dafewa. Ganin haka sai ta saki cikin don ba ta kaunar taimakonsa saboda irin kallon da yake jifanta da shi, kwatankwacin irin kallon Kabeer. Fuskarta a daure tamau ta amsa.

"Na ce maku babu abin da ke damuna, lafiyata kalau. Nagode da taimakon."
Daga haka ta karasa tana cije lebba ta yiwa É—an sahun sannu kafin ta kai hannunta dake rawa don har lokacin ba ta dawo daidai daga razanin da ta shiga na hatsarin ba ta fiddo kudi za ta ba É—an sahun na hakkinsa dake wurinta amma ta kara tsintar muryar Alhajin nan wannan karon muryarsa har Æ´ar rawa take yi, kirjinsa kuwa bugu yake da karfi tsabar son da ya shiga zuciyarsa farat É—aya na yarinyar.

"Ki bar shi zan biya. A wane unguwa kike sai mu sauke ki?"

Jama'ar duk idanunsu a kansu, wadanda suka lura da yanayin mutumin ba su ga laifinsa ba don Humaira ta haÉ—u iyakar haÉ—uwa, sai dai a ganin wasunsu, girma ne zai fadi muddin ya bari ta gasa mishi magana. Aikuwa masu wannan tunanin ba su kai ga furtawa ba suka tsinkayi muryarya cike da tsiwa tana magana tana kara zaro manyan idanunta masha Allah.

"Baba ina mutunta furfurarka hakan yasa nake gargadinka akan ka fita a hanyata wallahi tun ban gasamaka wacce za ta hanaka bacci ba. Haba! Wannan ai shiga sharo ba shanu ne, ka kusan kaimu lahira na maka uzuri yanzu kuma me ya shafeka da kudin da zan bayar? Da kai ke biyamin kudin motar? Ina ruwanka da ni?" Daga haka ta ja dogon tsaki ta miƙawa ɗan sahun dubun gaba daya na motarta zuwa da komawa ba tare da ta jira chanji ba, daga haka ta juya daidai sadda wannan matashin ya kara miƙo mata ledar da shaf ta mance da batunsa, saƙon Mami zuwa ga Anti Laila. Sai lokacin ta ga ashe ma leshi ne sai atamfa. Godiya ta yiwa matashin a fusace ta bar wurin tana huci, ga cikinta inda ta ɗan bugu bai bar raɗaɗi ba. Kunya da tarin bakin ciki suka lulluɓe Alhajin, bai taɓa zaton yarinyar ba ta da kunya ba da tuni ya ɓoye zalamarsa a kanta.

"Sai hakuri Alhaji, yaran yanzu ba su da kunya."

Ya basar da zancen yana maida duba ga Ɗan sahun nan da ba da umarnin ya tashi su karasa asibiti ko kuwa dai ya sallame shi yanzun a nan, ɗan sahun ya aminta da hakan, nan take ya ba shi kuɗaɗe masu ɗan kauri gami da ƙara ba shi hakuri. Daga haka ya juya zuwa motarsa har lokacin bai daina jin kunya da ɓacin rai ba su sake shi ba. Ya kuma ƙudurta a ransa idan har haka yaran zamani su ke, to ya yi Allah wadai da ire irenta, ba kuma ya jin zai kara kallonta da sunan wata da ya taɓa gani har ya ji kaunarta cikin ransa.

***
A ɓangaren Humaira dakyar ta karasa gidan Anti Laila, ita sai da suka yi nisa ma ta tuno ba ta da chanjin da za ta sallami mai adaidaitan don haka ta ce ya jira ta kawo mishi. Wajen Anti Laila ta karɓa bayan ta mata bayanin hatsarin da suka yi, nan kowa ya hau ta da sannu. Anti Laila da kanta ta kira Mami ta shaida mata, hankali tashe ko mintuna talatin ba a yi ba sai ga Mamin da direban Abba. Daukarta ta yi suka nufi asibiti, koda likita ya duba ta ya tabbatar kawai buguwa ce. Magunguna ya ba ta sannan suka wuce gida. Maganin ta sha bayan ta ci abinci ta kwanta.

Abba har É—akinsu ya shigo ya duba ta, ganin da sauki bacci ma take ya sanya shi fita.

Sai da ta yi kwanaki uku ba ta leƙa ko farfajiyar gidan ba a rana ta hudu ta koma zuwa koyon girke-girke abin ta.

***
Rayuwar ta ci gaba da tafiya yau dadi gobe babu, rashin dadin a wajen Humaira bai wuce na yadda su Tasleem ke kara nuna mata kiyayya a fili ba. Har ta kai da an wayi gari watarana sun yi mata sharrin sata, domin an tashi Mami tana neman kudin har dubi ashirin da ta ajiye ƙasan filo, gaba daya ran Mami a ɓace yake, sannan ma ita Humaira ba ta nan kuma ita ce ta gyara ɗakin kafin ta fice gidan Laila. Ganin an duba ko'ina sai Futuha da su Yassar suka ba da shawarar a duba ɗakunansu. Mami a farko ta ƙi, sai da Ladidi ta ce ya kamata a duba ko'ina tunda dai nema ake kuma abin da yasa Ladidin faɗin haka ganin su na neman ɗorawa yarinyar kirki Humaira ita kuwa tana da yaƙinin idan har Humaira ce ba za a sami ko sisi na wani a kayanta ba. Tasleem da ta dage tunda Humaira ce ta yi gyaran ɗakin a soma duba kayanta ya sa Ummita cike da kwarin gwuiwar sanin wace ce Humaira ta shiga fiddo kayan Humairar daga sif dinta. Sai dai tun kan ta yi nisa Futuha ta zura hannu ta jawo wata doguwar riga.

"Kambu! Dama yarinyar nan ita ta ɗaukarmin wannan rigar? Tasleem ku dubi rigar da nake tunanin ta ɓata a wajen wanki?"

Mami ta kalle su, ta yi shiru da mamaki. Can kuma sai ga ɗan kunne da sarƙa sun faɗo. Raihana ta zaro ido tana ɗauka.

"Innalillahi, ku ga sarƙata da nake nema kwanaki? Ashe ita ta ɗauka?"

Kai kamar wasa jikin Ummita na sanyi da wannan sharrin, ba ta yi aune ba ta kai hannu kan takardun kuɗi, tsabar razanar da ta yi ya sa ta fiddowa da sauri. Ladidi ce ta karɓa tana salati ta ƙirga, aikuwa dubu ashirin cif ne wanda Mami ke cigiya, Ummita kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin.

"Wallahi Mami wannan sharri ne, Humaira ba ɓarauniya ba ce. Ko kwandalar mutum ta gani idan tana aiki ajiyesu take a wurin da ta gan su."

Mami dai ba ta iya magana ba domin kanta ya ƙulle, a sanyaye ta sa hannu ta karɓi kuɗin ta fice a ɗakin tana ji su Yassar na yiwa Ummita masifa wai sai ta faɗi wa ke mata sharrin amma ba ta ko iya tankawa ba. Ita kanta ta sani sata ba ya daga halayyar Humaira don ta sha ajiye kuɗin da suka fi waɗannan kauri ba ta taɓa su ba, amma ta sani mutum ka iya sauyawa. Bare ma a irin gidan nan na Alhaji Isuhu da ba a facaka da kuɗi.

Humaira ba ta dawo gidan ba sai yammaci bayan la'asar, da murnarta ta tura kyauren gate ta shigo bayan ta gaida Baba dattijo dake zaune a benci yana siyan rogo a wurin ƴar tallah. Farin cikin bai wuce na yadda suka yi snacks har biyu a yau ba, samosa da springroll kuma cikin ikon Allah ta yi ya yi kyau a ido ya kuma yi daɗi a baki har a foilpaper ta nannaɗe ta kawo don Mami ta ci ta ji. Muryar Ƙasim ta tsinta a kanta.

"Ɓarauniya ta dawo."

Kallonsa ta yi gabanta ya faɗi, a duk irin wulakanci da jefa-jefan mugayen sunaye da suke mata, babu wani cinikinsu a ya taɓa kiranta da ɓarauniya wannan ya sa ta ji wani irin sanyi har ta kasa mayar masa da martani yadda ta saba idan ya jefe ta da marar dadi. Ya ɗan ɗaga gira.

"Oh, bakin ta kanwa ya yi la'asar kenan saboda kin sani kin sata shiyasa. Dama ustazancin ashe na ƙarya ne, toh yau asirinki ya tonu. Ɗan adam butulu."

Ta dafa kirji idanunta da suka cicciko da kwalla tun soma maganarsa ta kafa mishi.

"Yaya Ƙasim sata fa ka ce? Ni na yi satar?"

Ya harareta ya wuce kawai ba tare da ya ce komai ba. Ta bishi da kallo har ya shige gidan, itama a hankali ta soma taka ƙafafuwanta da suka yi mata nauyi saboda mutuwar da jikinta ya yi ta yi cikin gidan kirjinta na harbawa.

***

Ma sha Allah, Alhamdulillah. Sai kuma bayan sallah in sha Allah. Allah ya karbi ibadunmu, a sanya ni a addu'a ina bararta don Allah. 🤲🤲 Fatan alheri.07

Tasleem, Dawud, Yassar da Futuha ne zaune cikin falon sai dai ba ta sha mamakin ƙin amsa sallamarta da suka yi ba, dama ya lafiyar giwa ballantana kuma an jefe ta da kashi? Su na ganinta Tasleem ta miƙe ta yi kerere gabanta hannuwa a ƙugu ta ce.

"Ɓarauniyar banza da wofi, kin dawo kina wani sum-sum kamar munafuka. Koda dai dama munafukar ce, Mamin da ta daukake ki tana maki kallon kamar wata waliyya ai gashinan kin watsa mata ƙasa a ido. Ke ni ba wannan ba ma, earpiece dina da na jima ina nema idan kinsan ke ce ɓarauniyarsa wallahi tun wuri ki fiddomin abina. Atoh, bari ma Abba ya shigo gidan, ko Mami ba ta faɗamasa ba sai mun faɗa."
Chapter 12 · 0% Book details