Sashe 74
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
A ɗaki kuma ta iske wani tashin hankalin, wato Ummita ce cikin halin naƙuda, duk da ba ta san ya ake haihuwa ba amma daga yanda ta ganta tana ta juyi da rike riken baya tana kirarin mutuwa ya sa hankalinta ya yi mugun tashi. Babu wani abu da ya zo mata a lokacin sai mafarkinta. Ta shiga kwala ihun kira amma ina! Gidan an watse an tafi ga Abba don haka a guje ta fito zuwa sashen Anna neman ɗauki cikin rufewar idanu saboda tsabar tashin hankali.
©Rufaida Umar.Tana shiga ta iske Annan tare da Jannat su na ta hirarsu cikin yare. Ganin yanda ta faɗomusu sai da ta tsorata su. Cikin tsawa Jannat ta ce.
"Baki da hankali ne za ki faÉ—o mana É—aki ba sallama babu komai?!"
Humaira ta durkusa a gabanta tana kuka.
"Don Allah ki taimaka mu kai Ummita asibiti, haihuwa zata yi kar ta mutu."
Maganar ta É—an shigi Jannat, ko babu komai Ummitar ta yi mata bautar da wani a yaran Mamin bai mata ba, ta kuma fi Humaira yin biyayya a gareta. Anna ta yatsine fuska.
"Ke har kin gane haihuwa ce za ta yi? A ina kika san wata naƙuda? Watakila ma juyi ne."
Jannat ta dubi Anna cikin yare take ce mata ai Ummita cikinta ya haura takwas, daga nan ta bi bayan Humaira bayan ta yafa mayafi saman kanta da ko dankwali babu, Humaira dai da ta gaji da maganganunsu ne ta kuma fitowa don tunanin kiran wayar Mamk da ya faÉ—o ranta.
"Ke! Ina za ki je? Muje ki taimaka mata ta fito, bari na sanya a nemo mana abin hawa."
Tana kai wa nan ta fita farfajiyar gidan, motarta su Mami sun wuce asibiti wurin Abba da ita. Dawud ta yi karo da shi wanda shigowarsa kenan gidan bai ma san wainar da ake toyawa ba don wayarsa na kashe babu chaji.
"Yauwa maza nemo abin hawa Dawud, Ummita ke naƙuda yi sauri."
Ai jin haka a gaggauce ya juya, can kuwa Humaira na kukan halin ciwon da ta ga Ummita ciki ya zo ya kuma lafa mata kaɗan a haka ta daure ta zuramata hijabi ta taimaka mata ta miƙe suka fito ko takalmi Ummita ta kasa sanyawa sai salati take yi da kiran ta tuba a yafemata, Humaira ta nema mata gafarar kowa da ta ke mu'amala da shi. Wannan ba ƙaramin tada hankalin Humaira ya ƙara yi ba. Har sun shiga abin hawa Jannat ta maida ta tace ta dauko kayan da aka haɗa na tarbar haihuwa, itama sai lokacin ta tuna. Mami ce ta haɗa komai ta ajiye a ɗakinta saboda ba a son Ummita ta gani balle har damuwarta ya ƙara ninkuwa. Da saurinta kuwa ta fita ta koma ɗakin Mamin tana lalube saboda tsabar ruɗewa ba ta ma gan shi a gefen madubi ba a ajiye cikin karamin akwati, dole sai Jannat ce ta je ta dauko bayan ta balbale Humaira da masifar ruɗewar banzar da ta yi, acewarta.
A cikin ɗan sahun ma haka Ummita ta dinga salati da nanata kalmar a nema mata yafiya har Jannat ta gaji ta ja tsaki wai ta fiye raki da yawa. Dawud na gefe kusa da ɗan sahun shi kansa sai dai Ummita ta ba shi tausayi ya ji dama haka haihuwar take? Tun su na tafe Jannat ta yi waya ta sanar da Mami nan da nan ta ce su taho da ita asibitin da Abba yake don shima ya warware kawai dai maganin bacci ne bai sake shi ba acewar likita yana buƙatar hutu.
***
Gadan-gadan aka karɓi Ummita don har ta soma zubar da ruwan naƙuda, gaba daya ahalin gidan hankalinsu tashe idan ka jira Jannat dake ta chatting abinta. Tashin hankalin Mami bai wuce na fatan Allah yasa abin da za a haifa ya mutu ko don ta huta da bibiyar da Wizzy yake mata musamman yanzu da Ummita ta shiga watan haihuwar kusan koyaushe sai ya yi mata wani shegen gajeran saƙo a whatsapp cewar KAR KI MANTA. Wannan kalaman su kadai yake ce mata daga su ba ya ƙara koda harafi ɗaya. Ga Mubarak kuwa, babban burinsa Ummita ta rayu kar ya rasa ta. Gaba daya ya kasa sukuni sai safa da marwa yake yi, Raihana dai na gefe tana danna counter tana jan salati yayinda Humaira take zaune shiru.
 Kafin a kai ga fitowa a sanar musu ta haihu suka ji kukan jariri ya karaɗe inda suke, nan da nan duk suka nufi ƙofar suka yi cirko-cirko. Jimawa kaɗan ɗaya a cikin Nurses din dake ciki ta fito fuskarta a sake tana kallonsu ta ce.
"Alhamdulillah, ta sauka lafiya an samu É—a namiji."
"Nos ya Ummitan?" Tambayar da Mubarak ya cilla kenan.
"Tana cikin ƙoshin lafiya sai dai da alama ƴar shagwaɓa ce sai kuka take mana tun bayan da ta haifo santalelan saurayin."
Wani guntun tsaki Jannat ta ja, su kuwa babu wanda ya ce uffan kowa da kalar tunaninsa. Humaira dai ko ma mene ne, ko wane irin tabo ne da yaron ita ta godewa Allah da har Ummita ta sauka lafiya ta kuma rabu da cikin da ta tsana lafiya. Hakanan ma tunanin Raihana. Babban burinta na kasancewar lafiya yar uwarta ta sauka.
Ga Mami kuwa ba su iya sun fahimci halin da ta ke ciki ba sai dai ga dukkan alamu akwai wata damuwar da take ciki don gaba É—aya fuskarta ta nuna. Sun fi kyautata zaton kuma saboda lamarin haihuwar Ummita ne. Wa zai yi murna da haihuwar É—an da aka same shi ta fyaÉ—e? Babu shi kam, amma kaddara ce babu yanda suka iya.
"Ku je gida zan zauna a wurinta. Ke Humaira ki yo mata abu mai É—an ruwa da zafi wanda za ta ci ki kawo."
Ba ta so tafiya ba tare da ta ga fuskar Ummita da ba amma sai ta daure ta amsa da toh ganin kamar har a lokacin fushi sosai Mamin ke yi da ita ba ta huce ba.
Bayan tafiyarsu idan ka dauke Mubarak da Mami ta kora don dubo ko Abba ya farka, babu kowa a asibitin sai ita (Mamin). Tana zaune ta yi shiru cikin tunani, toh yanzu idan ta kasance za ta kai wa Wizzy jaririn nan wa za ta sanya wannan aiki? Kuma ma a ina za su haɗu? Ta dai san ba za ta taɓa iya raba Ummita da abin da ta haifa a asibitin nan ba saboda babban asibiti ne kuma mai tsaro sosai ga kyamarori (CCTV) ta ko'ina don haka sai ta zaɓi neman shawarar abokiyar shawararta a ire-iren waɗannan gaɓoɓin. Wato Hajiya Lubna. Miƙewa ta yi ta fice can farfajiyar asibitin ta danna mata kira, ringing hudu ta ɗaga ana biyar. Ko sallamar da dama ba ta wani ɗaɗa su da ƙasa basu yi ba Mami ta tare ta da sauri.
"Lubna ina cikin tashin hankali, ga dai yarinya ta haihu an sami namiji amma kaina ya ƙulle. Yanda yarannan suka sanya idanu a kan jaririn nan ta ina kuma ta wace hanya zan soma dauke shi na kai wa wancan ɗan shegiyar?"
"Kai Maryam, wannan ai abu ne mai sauki duk kin bi kin wani sanya ni fargaba. Kar ki yarda ki sanar da shi an haihu ki bari har sai an kwana biyu yanda idanu ba zai dawo kanki ba. Duk lokacin da kika samu wata wawakekiyar damar ba sai ki fiddo da shi ba ko da haɗin bakin wani amintaccen ma'aikacinku ba? A ɓoye dai aka fitar da shi ni na tabbatar ba za a zargeki ba, toh ke wa ma kike tunanin zai zargeki bayan wannan halin iya wuyar da kika gwada musu a rayuwa tsawon zama?"
Sauke ajiyar zuciya Mamin ta yi na samun ɗan sauƙi daga damuwarta.
"Shikenan, zan yi iyakar kokari na ganin bai samu labarin ba zuwa lokacin da zan aiwatar da shirina."
Daga haka suka yi sallama bayan Hajiya Lubna ta ƙara jaddada mata lallai ta yi kokarin aikata hakan ko ba komai ƙimar gidan nasu zai dawo idan ya so sai su san me za su yi a gaba don cimma sauran manufofinsu wadanda babu ɗigon alheri.
***
Dakyar Ummita ta iya tsaida kukanta, sun gyarata tas an kuma yi mata sauyin ɗaki amman ko ɗaga kai ta kalli abin da ta haifa da ya kwaso kamanninta tamkar an tsaga kara an karya ba ta yi ba. Ya yi kukan har ya haƙura ya tura yatsa baki yana tsotsa a haka ya yi bacci.
 Itama gajiya ta sanya bacci mai nauyi ɗaukarta. Koda Mubarak ya shigo haka ya iske su, ita bacci jaririn ma haka. Fuskarta ta yi wani fayau kuma ta ɗan sauka ba kamar ɗan kumburin da ta yi a fuskar ba kafin ta haihu. Ya kai duba ga jaririn, kamannin da yaron ya yi da Ummitan sai ya ji ya shiga ransa sosai. Tausayinsa kuma ya mamaye shi, ire-irensa su na nan birjik a faɗin duniya waɗanda ƙaddarar samuwarsu ta hanyar da ba ta sunna ba ta faɗamusu musamman ma a yanayi irin na Ummita ta hanyar fyaɗe. Amma hakan ba ya wanke tabon da suka riga suka goga daga ubansu, sai a dauki tsangwamar duniya a ɗora a kansu alhakin da ace son ransu ne su ma za su fi kwadayin a haifesu ta hanyar aure. Ya ƙara kai duba ga Ummita, ya tabbata ko ganin jaririn ba ta son yi saboda tsana, fatansa Allah yasa watarana zuciyar wannan Uwa ta russuna har hakan ya jawo mata kaunar ɗanta. A hankali ya sa hannu ya ɗauki yaron ya yi mishi addu'a har ma da yi mishi huɗuba bisa umarnin Abba wanda ya samu lafiya bayan Mubarak din ya shaida masa abin da ke faruwa ya sanya shi yiwa yaron huɗuba da suna Ahmad. Abba kuwa ya tsaya domin rama sallar da ta kubce masa.
Yana nan tsaye bayan ya shimfiɗa jaririn haka Mami ta shigo, ganinsa a nan sai ta haɗe girar sama da ta ƙasa, ba ta son abin da zai sanya Mubarak ɗin raɓar Ummita da ma abin da ya shafe ta gaba daya. So take kawai ya tattata ya bar garin zuwa Camp kafin ya ɓallo mata wani abin da ba za ta iya ɗauka ba.