← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 63 OF 101

Sashe 63

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Tab! Mami kina da abubuwan mamaki sosai. Wallahi ba don ke da bakinki kike fadamin ba, da ace a wani wurin na ji dukkan wadannan zan ƙaryata ko waye ya faɗi."

Murmushi Mami ta yi.

"Ku ne ba ku san rayuwa ba, yanzu da ace wani mugun halin na nuna a zahiri, kuna zaton Abbanku zamu kai yanzu da shi ba tare da mun rabu ba? Ko kuwa kuna tsammanin a baya ida  kishi ya kwashe ni na kashe Fatima da hannuna yanzun zan cigaba da rayuwa a duniya? Ai hakan ba zai taɓa afkuwa ba, komai ɗan hakuri ne da bi sannu-sannu. Ka yi siyasa a komai, ka shanye komai ka danne sai ka ci riba. Ina dab da cin ribar kwace dukiyar Yusuf saboda na faranta maku, na ba yarana maza jari su huta daga maƙon da Yusuf ke yi musu, na kuma nunawa Anna ba Firdausi Jannat ce kaɗai ɗiya ba, nima na san yanda zan iya kwatar kaina a wurin miji, wannan ne dalilin daya sa na sanya aka sace yarannan, sai dai kuma kuɗaɗen su na dab da samuwa, komai ya rushe saboda zuwan ƴan sanda. Amma ban saduda ba, ban kuma karaya ba, har gobe ba zan fasa yunƙurin ƙwatarwa yarana haƙƙi ba tunda ubansa marowaci ne mai shegen maƙo."

Fuska a sake Futuha ta rungume Mami kafin ta saketa ta ce.

"Wai Mami ashe daman kina kaunarmu?"

Harararta ta yi.

"Wa ye ba ya kaunar nasa? Na fadamaki ai duk duniya wanda za ki ga ya nuna ba ya son nasa ya fi kaunar wasu toh ƙarya yake yi, munafuki ne."

Jinjina kai Futuha ta yi tana washe baki.

"Hakane, Mami na kara sonki wallahi. Kin wanke tunanin dake zuciyata na ganin bakya kaunarmu. Ni fa lallaɓa Humaira nake yi so nake ta zo gidana ta koyawa yar aikina girke-girke. Shiyasa kika ga ina ta janta a jiki da kissa."

Mamin ma dariya ta ce.

"Sai ki bada himma."

Sai kuma ta daure fuska sosai.

"Ina kara jaddada maki, koda wasa kika yi yunkurin sanar da wani ko wata labarinnan wallahi zan iya kashe ki."

Sosai furucin ya tsoratar da Futuha, ta yi saurin rike hannunta.

"Aa Mami, wallahi na rantsemaki babu wanda zai ji. Ai ina sonki, ba zan so hukuncin shari'a ko yaya ya hau kanki ba."

Sai anan ta saki fuska ta shafa kan Futuha. Daga haka suka bar zancen suka koma falo inda Tasleem suke zaune da su Mubarak ana cin abinci. Ko kallon Futuha ba ta yi ba, tsanarta take ji a zuciya, wato saboda tana da kudi shiyasa har wani shiga daki suke su rufe su na kwasar hira ita da Mami. A duniyarta ko a mafarki aka ce Futuha za ta samu miji wanda ya fi nata za ta ƙaryata. Ga Hamza yanzu ya sauya mata, zamansu gaba daya babu dadi hatta a bangarenta da uwar mijinta da ma yan uwansa. Albarkacin cikin jikinta kawai take ci ta san da wannan. Don ma dai Anti Jannat ta ce ta kwantar da hankalinta har ta haihu sannan su san yanda za su ɓullowa lamuran. Wannan ne kadai ya sa ake ganinta cikin nutsuwa, kuma ita dinma ba ta ragawa Hamzan.

***
  Da yammacin ranar daidai lokacin da su Futuha suka fito da zummar tafiya gida har da Tasleem wacce za ta sauke nata gidan sanadiyyar Hamza da ba  zai samu zuwa daukarta ba, sai ko Humaira wacce a dole ba don ranta ya so ba bisa umarnin Mami za ta bi Futuha gidanta ta yi zaman sati biyu kawai don ta koyawa yar aikinta girke-girke, su Raihana sun yo musu rakiya farfajiyar gidan. Humaira tana tuno Fadeel wanda ya ce yana hanya, tana son ta dakata ta jira shi amma wata zuciyar na kwaɓarta da nuna mata babu amfanin sauraronsa tunda ba aurensa za ta yi ba. Suna nan tsaye, tana sanye da yadi mai taushi maroon colour wanda ya fiddo tsantsar kyawunta da hasken fatarta, ta ɗora karamin mayafi a kanta golden colour. Babu kwalliya ko na ɗigo a fuskarta amma kuma sosai kalar ta karɓe ta, zama wuri ɗaya babu fita ya sanya har wani sheƙi fatarta ke yi. Daidai sadda Futuha ta bude ƙofa tana shirin shiga, daidai lokacin maigadi ya wangalewa Fadeel ƙofa ya turo da hancin motarsa ciki. Bisa umarnin Abba, Fadeel ya zama ɗan gida, duk sadda ya zo yana da damar da zai yi parking a farfajiyar gidan. Ya kuma shiga idan an mishi izni su gaisa da mutane. Shi din ne dai ya zaɓi rashin zuwan akai-akai saboda gudun kada ya baƙantawa Humaira ta ga kamar yana neman shigarmata hanci da ƙudundune alhalin gidansu ne.

"Wannan motar kuma fa?"

Fadin Futuha tana karewa motar kallo, lexus Ls blue black sai sheƙi take yi, daga gani ba a moreta sosai ba don ba ta nuna alamun tsufa ba.

"Wannan motar Fadeel ne. Na gane, ya taɓa zuwa da ita sau ɗaya wurin Abba."

"Fadeel?" Tasleem da Futuha suka nanata sunan a zahiri. Aikuwa kafin su rufe bakunansu haɗaɗɗen matashin nan mai sa numfashin yan mata tsayuwa na wucin gadi ya fito daga cikinsa. Sanye yake cikin maroon tshirt da baƙin wandon jeans kamar da hadin baki shi da masoyiyartasa. Ya rufe idanunsa da baƙin gilashi yana wani murmushi mai ruɗar da zuƙata. Duhun kayan da ma motar da yake jingine a jikinta sai suka kara fiddo da tsantsar farinsa na usulin bafalutani ɗan asalin garin Yola. 

Gaba daya Tasleem ta yi wani shock, suka yi mutuwar tsaye. Idanunta har wani ruwa-ruwa yake yi saboda tsabar kallonsa da ta shagala yi ga wani irin so da kauna dake fisgarta har ta mance da wasu igiyoyi masu ƙarfi da suke nannaɗe da ita suka yi mata shamaki da dukkan wani ɗa namiji da ba muharraminta ba. Shi kuwa Fadeel idanunsa a saman na Humaira har dai su Yassar suka karaso aka yi musabaha.

Humaira kuwa ta yi wani irin dauke kai daga kallo daya ba ta ƙara ba.

"Wajenki ya zo ne?" Futuha ta wurga mata tambayar tana ɗan murmushin yaƙe, a ranta kuwa jinjinawa Mami ta yi, tabbas ba karamin kokari tayi wurin danne abin da ke ƙasan ranta ba, akwai masifar wahala. Sosai itama ta ji kishin ace Humaira ce ta samu wannan kyakkyawan matashin kuma mai rufin asiri.

"Ban sani ba." Amsar da Humaira ta bayar kenan tana ƙara tamke fuska. Tasleem kamar ta shaƙe ta, yarinyar ta samu dama amma tana nuna girman kai. Ita da ace itace da wannan damar ai sai inda ƙarfinta ya ƙare.

"Assalamu alaikum."

Sallamarsa ta katse musu tunani, Raihana ta jingina jikin Humaira dab da kunnenta ta ce.

"Ki riƙe wannan bawan Allahn sosai idan kuwa ba haka ba ni zan maye gurbinki."

Ba ta san ya aka yi ba sai tsintar idanwanta ta yi da wurgawa Raihana wata muguwar harara mai nuni da tsantsar kishi, Raihana ta sa dariya tana riƙe kunnuwa gami da ɗan jujjuya kai alamun ta tuba. Tana kuma kara gasƙatawa Humaira na son Fadeel, ba kuma ta san abin da ya danne wannan soyayyar ba.

Tasleem ta amsa sallamarsa ciki ciki yayinda Futuha ta saki fuska sosai aka gaisa sannan ya dubi Humaira da shanyayyun idanunsa bayan ya cire gilashin.

"Boddo, barka da yamma."

Ya fadi yana mai ɗan dunƙule hannu da ɗan ranƙwafar da kai kaɗan tamkar wani basarake. Nan fa gaba ɗaya idanun ya koma kansu ana ganin ikon Allah.
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Ba ta ce uffan ba sai idanuwanta da ta sauke a cikin nasa. Ya ji kallon har a ƙasan ransa.

"Sauri fa muke yi." Tasleem ta furta cikin É—aure fuska, gaba É—aya wani irin mugun kishi ke cin zuciyarta. Fadeel bai ko kalle ta ba ya dubi Futuha.

"My sis, ko za ki ban aron ƙanwartaki for just 5mins?"

Murmushin da bai kai zuci ba Futuha ta yi.

"Ba ka da damuwa. Humaira jeki."

Humaira da ke jin kamar ta shaƙo wuyan Fadeel amma sai ta kasa yi mishi musu ta bi bayansa sadda ya yi gaba zuwa inda ya ajiye motarsa. A jikin motar suka tsaya su na hangen su Futuha da ke hira sai ko Tasleem da ta zubamusu idanu tamkar makauniyar da ta samu ido.

"Ka kirani kuma sauri muke za mu tafi."

Ya ji babu dadi daga yanayin muryar da ta yi mishi magana, ya dai daure ya haÉ—iye kamar koyaushe.

"Humaira kina addu'a sosai kuwa? Kina nafilfiloli da sallar dare? Kina mayar da hankali wajen yawan karatun Alkur'ani?"

Ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ta sani tana sallolinta biyar akan lokaci, tana kuma addu'a daidai gwargwadon yinta, amma yawan karatun Alkur'ani da kuma sallolin dare da ma nafila ba za ta iya buÉ—e baki ta ce mishi aa a kansu ba, kawai sai ta ji hakan ya yi mata nauyi a saman harshenta.

Ya tsinci amsoshin tambayarsa daga shirunta, don haka ya cigaba da magana a nutse ba tare da ya dauke idanu daga saman fuskarta ba.

"Salollin farillah wajibi ne Humaira, amma su Nafiloli neman ƙarin lada ne da kusanci ga Ubangiji. Za su buɗemaki ƙofofin rahma wadanda ba ki taɓa zato ba. Hakanan shi kansa karatun Alkur'ani, yawan tilawarsa da yin azkar safe da yamma zai ba ki kariya daga shaiɗanu da ma jinnu. Babu wani ko wata ko kuma wani abun da zai cutar da ke. Ina roƙonki ki yawaita addu'a, ina kuma ba ki shawarar yawan hailala, istigfari da salatin Annabinmu s.a.w. Ki ɗauka tamkar wani ɗan uwa ne gareki na jini yake ba ki wannan shawarar. Kin yarda kin amince za ki amfani da ita?"
Chapter 63 · 0% Book details