← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 7 OF 101

Sashe 7

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Shiyasa ai na ce a bi da mu ta wannan hanyar ba ta farko ba, kinga sai ki ƙara kalle garin sosai ko?"

Jinjina kai Humaira ta yi tana murmushi sannan ta jefo mata tambaya.

"Ni kuwa yar uwa su Abba su nawa ne a wajen Umma? Umman na raye?"

"Umman su Abba tun ina firamare, yaranta uku kawai Allah ya ba ta daga nan ba ta ƙara haihuwa ba sai ko yaran ƴan uwa da ta riƙe ta aurar. Kinga Abba shi ne babba sannan Babana, sai autar ɗakinsu Baba Amina, ita a can gadon kaya take zaune da mijinta. Kuma Kakanmu wanda ya haifi Abba shi ya riga ma Umma rasuwa, ita kadai ce matarsa har ya bar duniya. Kar ki damu kedai, tun da kika zo garin nan babu gidan da ba zamu je ki ga ƴan uwanki ba in sha Allahu."

Murmushi ya suɓucewa Humaira har ta ɗan lumshe idanu ta buɗe su, ranta ya yi fari sol, burinta ya cika. Yadda ta san kaf ƴan uwan Mamarta, yau Allah ya nufa za ta san na Abbanta. Haka suka karasa su na tafe Ummita na mata nuni da wuraren ƙayatarwa a garin.

***
   
Dattijuwar mace ce hakimce saman kujera ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Banda tsufanta da ya fito muraran, kallo ɗaya idan ka yi mata za ka ga tsantsar kamannin da ta yi da Mami har ta so ta fi Mami hasken fata. Ta gyara zama gilashinta gami da amsa sallamar da Mami ta yi mata ciki-ciki. Anna sam ba ta iya ɓoye abin da ke ranta wannan ya sanya a kallo daya Mami ta gane fushi take da ita. Da harshen buzanci ta ce.

"Anna yanzu zancen nan ba zai wuce ba? Ina ce na yi maki bayanin komai?"

Anna da sai a sannan ta dubeta ta ba ta amsa cikin yare don ba kasafai take yin hausa ba, kaÉ—an-kaÉ—an take ji.

"Ki ka ce bayani? Yanzu ke har kina tunanin zan gamsu da bayananki na wofi Maryam? Kina da masaniyar irin
wahalar da aka ci a baya? Wato ke dadi miji ko?"

Mami gaba É—aya ta dube ta fuskarta duk a jagule.

"Haba Anna, idan ban godewa bawan Allahn nan ba  bai kamata na watsa mishi ƙasa a ido ba. Mutumin da ya amince na zauna tare da ku, muke rayuwa. Duk da irin son abin hannunsa, hakan bai sanya shi watsi da lamarinki ba. Duk wata kulawar da mai shekarunki ya dace ta samu, babu ɗaya da ya taɓa nuna gajiyawarsa wajen yi. Toh mene ne aibu a ciki don ɗiyarsa guda ɗaya ta zauna a hannuna?"

"Shashashar banza da wofi, dama nasan ba alheri ne zai fito a bakinki ba. Wato dai gori za ki yimin ko? Dama nasan akwai ranar ƙin dillanci ai, dadin abin da baza  ta kike rawa. Shikenan zan sa maki ido na ga inda wannan rashin hankalin naki zai kai ki. Kin fi kowa sanin wahalar da aka sha a baya ai."

Mami dai ba ta ce komai ba, ta so a bar maganar a sanyo wata amma sam ba ta samu fuska wurin Anna ba dole haka ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, daidai ƙofa ta ɗan dakata kafin ta juyo ta sakarwa Anna wani murmushi da ita kanta Anna ya ba ta ɗumbin mamaki da baƙin ciki, to wannan sabon raini ne ya gifta tsakaninta da Maryam din ko kuwa dai kishi ya taɓa kwakwalwarta tun a shekarun baya? Haka Anna ta cigaba da saƙe-saƙenta da babu mai warware mata.

***
  A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har a yau Humaira ke cika sati uku cif a garin Kano. Abubuwa da dama sun faru na alheri a rayuwarta da suka rinjayi sharrukan ciki. Ɗaya daga ciki har da ƙarin suturu da ta samu, sai kuwa gadonta da sif din kayanta da Abba ya sa aka yi mata. A gefe guda Abba ya mallaka mata wata ƙaramar waya ƙirar Vivo sai dai tana yin whatsapp, kuɗin wayar dai dakyar suka  fito daga aljihun Abban nan ma sai da Mami ta sha fama har ta nuna ɓacin rai ƙarara, a duniya kuwa babu abin da Abba ya tsana kamar ganin Mami ta sauya mishi, nan da nan take cin galaba a ka sa muddin buƙatarta bai shallake tunaninsa ba.
  Ummita ta yi mata rakiya wurin dangin Abbansu na kusa, sun yi murna kwarai da ganinta. Sun kuma karɓe ta da hannu bibbiyu, babu abin da ya fi faranta ran Humaira irin shaidar kirki da suka yiwa mahaifiyarta. Ta kuma ji dadin hakan ba kaɗan ba. Rashin abin yi ne ya sa kusan koyaushe idan ba ta komai tana kan wayar tana danne-dannenta ganin ta riƙe abubuwan da Ummita ta koyamata tunda dai harshen turanci ne, ta kuma sani koda faransancin aka mayar ba za ta tsinci abin kirki ba. Abba ya sanya mata lambar Kawunta, sun gaisa sau ɗaya ta waya don ita kam ko whatsapp ma cewa Ummita tayi kada ta buɗe mata, ba ta ga wanda za ta yi hira da shi ba. Ta dai gwammace ta kunna rediyo ta yi ta saurare don hatta da waƙoƙi iri-iri na soyayya da Ummitan ta sanya mata ba ta damu da su ba.

  A wannan yammacin kamar koyaushe tana zaune a ɗakinsu gefen gado ta buɗe labule iska mai daɗi na dukanta, garin wuni aka yi cikin zafi yanzu kuwa sai ya ɗan huce. Rabin hankalinta yana ga farfajiyar gidan inda take hango Yassar tsaye da abokinsa wanda ta ji ana kira da Affan su na hira, a gefe ɗaya Muhsin ne da ball yana wasansa tare da Waleed, daidai nan Futuha ta buɗe gidan ta shigo, dawowarta kenan daga makaranta, Humaira na lura Affan na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba, daga yanayin tafiyarta za ka fahimci ba a nutse take ba, har ta gifta hankalin Humaira na kanta, ta san dai babu lafiya, tana kuma fatan ba gurguwar shawarar da ta ji jiyan wata aminiyarta Aina'u da ta zo tana ba ta ba shi ta gwada a yau ɗin, gabanta ya faɗi. Ba ta mance kalaman da suka fito daga bakin Aina'un bayan Futuha ta gama amayar mata da damuwarta akan mahaukacin soyayyar da take yiwa Ibb Gusau.

   _"Ke ki na ban mamaki wallahi Futuha, ki na da kyawun da babu namijin da zai kalleki bai ƙara ba. Da ace ni ce ke, wallahi babu abin da zai hana na kai wa Ibb Gusau kaina. Kina da sura irin wadda da zarar kin tallata mishi kanki zai ji nan duniya babu wata sai ke. Ke idan ma wannan bai yi ba, ki zo na raka ki wurin Malam Aci Bulus, na rantse maki ko me kike so za ki samu. Ke wallahi sai kin mallaki malamin nan kin juya shi kamar waina a tanda."_

Gaban Humaira ya yi wata iriyar faduwa, ta ambaci Allah a ranta, ta yi nisa da saƙe-saƙen zuci ta ji an banko ƙofar ɗakin an shigo, ta juyo da sauri, Futuha ce. Ba ta ko lura da ita ba ta kife a saman gadon Tasleem tana kuka har da sheshsheƙa. Humaira ta yi shiru, kafin ta lalubo abin faɗi duk kuwa da cewar ba shiga sabgar juna suke yi ba, Tasleem ta shigo ɗakin da sauri a bayanta kuma Raihana. Za ta soma magana amma idanunta na sauka kan Humaira ta fasa, cikin haɗe rai ta ce.
 
"Malama ba mu waje za mu yi magana."

Jin haka tsam, Humaira ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, bayan fitarta Raihana ta karasa ta rufe ƙofar har da sanya muƙulli sannan ta dawo. Futuha suka ɗago su na magiyar ta sanar da su abin da ya faru. Dakyar ta iya tsaida hawayenta ta shiga ba su labari.

"Ai na faÉ—amaku yadda muka yi da Aina ko?"

Suka gyaɗa kai duk sun ƙagu su ji komai.

"Shi ne..shi ne.."

Sai kuma ta yi shiru ta rasa me ma za ta ce. Tasleem ta zaro ido.

"Shi ne me Futuha? Kada dai ki cemin kin gwada aiwatarwa?"

Futuha ta runtse idanu gami da shafa gefen fuskarta tana kuka sosai. Sai a sannan idanunsu ya kai ga gefen fuskar, ya yi ja ya yi ruɗu-ruɗu alamun dai mari ta sha. Koda alama ma ba guda ɗaya ba.  Ba ta bari sun nemi ba'asi ba ta cigaba da maganarta.

"Na iske shi zaune a ofishinsa shi kaɗai yana aiki a system, koda na shiga bai ɗaga kai ya kalle ni ba, daga motsawar leɓɓansa na gane ya amsa sallamata. Duk da cewa gabana na faduwa hakan bai sa nayi ƙasa a gwuiwa ba na karasa ga teburinsa. Na sauke mayafina yanda rabin kirjina ya bayyana, na shagwabe murya ina mai batun ban gane abin da ya koyar a aji ba. Koda naga bai kalle ni ba, sai na yi gangancin kai hannu saman nasa, shi ne ya gaggauramin tagwayen maruka a kuncina. Ya kum rantse idan na ƙara shiga ofishinsa sai ya ɓalla ni kuma daga kaina masu tunani irin nawa za su dawo hayyacinsu."

Tana kaiwa nan ta ci gaba da kukanta. Tasleem da Raihana kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Raihana ta ja tsaki.

'Kema dai Futuha wataran kina abu kamar Waleed marar wayo wallahi. Ke kin manta tun farko itama Aina'un sonsa take yi wai? Ko don ta ɓata ki a wurinsa ku yi biyu babu kinga ai za ta ba ki gurguwar shawara. Ai mun faɗamaki amma ke idanunki ya rufe."

Tasleem ta amshe.

"Yanzu shikenan koda ace wannan mutumin na ganinki da mutunci kin ɓarar da shi, yadda za'a yi ki gyara ma nikam ban sani ba. Kada dai garin gyaran a ƙara jagula abubuwan shi nake tsoro. Ke!!! Wai don uwaki shi kaɗai ne namiji a duniya ma? Aikin banza kawai! Ga samari ƴan kasuwa da ƴan bokon su na matowa a kanki a instagram amma kin tsaya biyewa wani so, so, ke fa kike ban shawarar na shigewa Suhaima don na samu na yi mata koda snatching ne, amma ke nan kin tsaya ɓata lokaci akan wani kuturu gurgu."

Jin haka ran Futuha ya ɓaci, ta harari Tasleem kafin ta ja tsaki.
Chapter 7 · 0% Book details