← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 88 OF 101

Sashe 88

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Ka cigaba da bincikenka, ina fatan Allah ya baka nasarar magance komai. Allah ya yi maka albarka. Ya nunamin cikar burina kafin mutuwata. "

Ya yi murmushin jin dadin wannan addu'a, ya sani ba ta da buri sai na son ganin aurensa, shi kuma ya sani kukanta ya zo karshe da yardar Allah don ya riga da ya gama samun wacce yake jin zai iya ƙare rayuwarsa da ita.

***
Labarin Jannat ya karaɗe ko'ina, mijinta ya samu zuwa ya kuma kawo sarƙoƙinta da aka nemi ya kawo, an siyar an haɗa da motarta amma duk da haka su na buƙatar cikon wurin miliyan hudu da rabi. Anna ta tattara nata ajiyar da bai cike miliyan ba ta bayar, Mami kuwa dakyar ta sanya dubu dari takwas inda ta rantsewa Anna su kadai gareta, duk da haka dai da sauran rina a kaba. Futuha ta bada dubu dari uku, Tasleem ko ba ajiye ba balle ta bayar, sarƙarta ɗaya ta gwal da ta mallaka ta yi shiru don ta san ba lallai ta samu ta mayar ba. Akan haka har Futuha sai da ta yada mata magana, wai duk tsananin kusancinta da Jannat ta kasa bada ko biyar da za'a haɗa a biya don a samu ta fito. Ita dai ba ta biyemata ba ta banzatar. Anna da kanta ta taka har zuwa gaban Abba da ya yi burus da batun Jannat sai shirin bikin Humaira da yake gudanarwa, roƙonsa ta shiga yi da kuka sosai akan ya taimaka ya sa hannu ko iyaka hakan a bayar don Jannat ta fito. Abba ya bata hakuri ya nunamata babu abin da zai iya yi a kai tunda dai magana ba a hannunsa take ba. A hannun hukuma da kuma yaran da aka ɓatawa yake. Wannan al'amari ya yi mugun dasa haushin Abban a zuciyar Anna. Ta kuma daɗa roƙonsa toh ya taimaka ya cika koda bashi ne idan ya so bayan fitowar Jannat din sai ta biya shi.

"Kiyi hakuri Hajiya, a yanzu dai ba zan ce akwai su ba, na tattara abinda ke hannuna na bada odar kaya na shaguna na, abin da ya rage kuma shi nake amfani da shi wajen fita kunyar jikarki da bikinta ke tafe."

Ina wuta Anna a jefa Abba don kiran Humaira da sunan surukarta da ya yi. Kamar ta dura masa ashariya haka ta ji sai dai ta daure ta haɗiye ɓacin ranta. Shi kuwa Abba miƙewa ya yi yana gyara zaman babbar rigarsa don ya kammala shirin fita kasuwa a ladabce cikin danne ɓacin rai ya ce.

"Ni na fita Hajiya, lokaci na tafiya. A yi hakuri za a samu mafita in sha Allahu."

Yana kaiwa nan ya sa kai ya bar falon sai ƙamshin turarukansa da suka bi bayanshi suka shige kofofin hancinta.

"Kai wannan Isuhu an yi ɗan duniyan ƙarshe, yanzu a dubi tsabar idanuna ya shirgan uban ƙarya duk don kar ya taimaki auta? Oh ni, yau naga abin da ya fi karfina. Aikuwa duk muguntarka sai yarinyarnan na fito tunda kai azzalumin mutum ne, sai baƙin mugunta kamar wani arne a cikinsa."

Ita kaɗai dai ta dinga bambamin nan har ta kai aya babu wani a falon da zai taya ta daga karshe ta yi kwafa ta miƙe ta bar falon.

***
A yau Raihana ta ƙudurta sai ta bincika wayar Maminta, duk irin kwaɓar da zuciyarta ke yi mata ta kasa hakura. So take ta ga da wanda Mamin ke waya har ta kai ga ba shi umarnin kashe Abbansu. Idan har ta yi nasarar samun lambar mai shi, toh kuwa ta yanke Abban za ta kai wa don ya bayar a kamo mutumin. Wannan ya sa a yammacin yau ranar Talata tana dawowa daga jarrabawar da suka soma na WAEC ta dinga fakar idanun su Tasleem da Yassar dake zaune a falo ana hira ta mike ta bi bayan Mamin zuwa dakinta da ta shiga. Ta kudurce idan har suka yi kiciɓus za ta wayance da tambayarta maganin ciwon kai wanda gajiya da kuma damuwa suka haifarmata, idan ko ba su hadu ba to wayarta za ta durfafa. Cikin iko na Ubangiji kuwa ko kyallin Mamin babu sai motsin ruwa da ta ji a banɗakin. Hamdala ta yi jiki da hannu na rawa ta dauki wayarta dake saman gado ta bude don ta san lock din. Kai tsaye ta shiga Call log ta hau dubawa har ta kai kan na kwanan watan da Humaira ta tafi, tana yi tana kallon ƙofar bandakin, har idanunta ya kai ga lambar da aka yi saving da WZY wanda lokacin kiran hya kasance da asubahi. Buɗewa ta yi ta karanta lambar har sau uku nan da nan ta ji ya zauna a kanta don babu laifi tana da hadda, da sauri ta fita ta kashe wayar ta bar dakin tana maimaita lambar a ƙasan ranta, Allah ya taimake ta su Tasleem ba su ankara da ita ba, kai tsaye dakinsu ta shiga su Humaira na mata magana ba ta amsa ba don kar ta mance lamba sai da zare wayarta daga chaji ta shigar da lambar ta yi saving sannan ta dago ta dubi Humaira.

"Yi hakuri kina magana hankalin yana nan, kaina ke ciwo kinga har yanzu bai bar sarawa ba."

Humaira wacce Hajjo ba ta jima da yi mata gyaran jiki ba fatarta sai kyalli take yi don tun a Nijar aka soma ta ce.

"Wayyo sannu, bari na samo maki magani wurin Mami."

Daga nan Humaira ta mike ta fice, dama tana son ganin Mamin su gaisa sosai, tun zuwanta har yanzun ba su wani gaisa ba. Sun dai gaisa da Hajjo itama sama-sama, ko me Mamin za ta yi a ganinta uwa ce a gareta. Tunda dai aure za ta yi gwara a rabu lafiya.

A falon ƙamshinta ne ya bayar da zuwanta, Tasleem ta kuramata idanu kamar ta shaƙo wuyanta ta mutu, cikin dogon hijabi take amma sai wani kamshi da kyalli jikinta ke yi. Ta gaishe da su Yassar wadanda a yanzu babu komai...

Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Allah ya yiwa Kakata rasuwa dazu. Ina barar addu'o'inku. Kuyi hakuri da ni na wannan takaitaccen kwanakin.

Ayi hakuri da typing errors.A falon ƙamshinta ne ya bayar da zuwanta, Tasleem ta kuramata idanu kamar ta shaƙo wuyanta ta mutu, cikin dogon hijabi take amma sai wani kamshi da kyalli jikinta ke yi. Ta gaishe da su Yassar waɗanda a yanzu babu komai tsakaninsu face mutunci. Kai ka ce ba su taɓa tsangwamarta a rayuwarsu ba.

"Ina kike tunanin za ki je?"

Ta ji muryar Tasleem a kanta, ta juya ta dubeta. Wani irin duba na ke a wa? Tasleem ta bude baki don mamakin hararar da Humaira ke yi mata, kafin ta samu abin faÉ—i sai kawai gani ta yi yarinyar ta sa kai a É—akin.

"Amma wannan yarinyar ta mugun rainamin wayo. Don uwarta har ina ma ta magana ta harare ni ta yi gaba?"

"Ke dai za ki ji tsoron Allah ki bar takura rayuwar ƴar mutane. Haba Tasleem, kina girma kina cin ƙasa. Nifa dama can kawai taya ɓera ɓari ne amma idan za a titse ni ba zan nuna laifi guda da yarinyarnan ta aikata gareni ba."

Cewar Yassar kenan. Tasleem ta kara kufula.

"Ai ba za ka gani ba saboda kai babu abin da ka sani."

"Sanar da mu."

Faɗin Dawud. Ita kuwa sai ta basar, ai da kunya ta ce musu wai kwacen saurayi Humairar ta yi mata, ita a karan kanta ta san zance ne kawai ba hakan yake ba. Su ma kuma sun san komai. Sai ta zaɓi waskewa ta hanyar nunamusu irin fifikon da Abbansu ke nunamata a kansu amma tamkar dai maganganunta ba su samu wani matsuguni ba. Shi Yassar idan dai bushasha da arziki ne, babu irin wacce ba ya yi a dukiyar Abba. Ya zama ɗan karya da kashewa mata kudi. Dawud ma yakan yafici rabonsa amma ya fi Yassar tsoro wannan ya sanya na sa bai fito fili ba. Toh idan dama don kudin ne suke jin haushi da ganin kamar an fi kyautatawa Humaira, ai dai yanzun su ma suna yagar na su. Wannan ya sanya ko a jikinsu.

***
Humaira da sallama a bakinta ta tura kai dakin Mami, ta iske ta tsaye riƙe da wayarta tana dannawa amma ganinta sai ta yi saurin juyowa tamkar wata marar gaskiya can kuma ta basar ta hanyar saita kanta ta ajiye wayar ta nufi gaban madubi don goge jiki.

"Mami ina wuni."

Ciki-ciki ta amsa.

"Lafiya."

Shiru ya ɗan biyo baya, ita ba ta ce uffan ba hakanan Mami dake shafa mai a jiki. Wayar Mamin ce ta yi ƙara Humaira ta mike da zummar ɗauka ta miƙa mata, amma kafin ta kai ga wayar ta ji Mami ta dakamata tsawa.

"Kar ki kuskura!"

Tana fadin haka ta taso da wani mugun sauri ta kai hannu ta dauki wayar, WZY ne ya kira. Humaira dai tana tsaye kamar an shuka icce tana kallon Mamin har lokacin kirjinta duka yake don ba kaÉ—an tsawar da Mamin ta yi ta tsorata ta ba. Mami ta É—an saci kallonta sannan ta katse kiran, a karshe ma ta danna Airplane mode yadda ba zai kara kira har ya same ta ba.

"Ina ruwanki da wayata? Bana son iskancin wofi, kin wani shigo kin min tsaye a ka, toh kin gaishe ni ba ina ce shikenan ba sai ki juya ki tafi?!"

Ta numfasa.

"Kiyi hakuri Mami, Raihana na zo karɓarwa maganin ciwon kai ya matsa mata kuma daga nan na..."

"Kiyi me?! Raihana ni baƙuwarta ce da ba za ta iya zuwa ta karɓa da kanta ba? Har akwai wani shamaki tsakaninmu ina uwarta mahaifiya?!"

Kalaman sun daki Humaira da har ba ta iya ɓoye mamakinta ba ta dubi Mami dakyau amma sai ta ji miyan bakinta ya kafe ta kasa cewa uffan. Tsakin da ta ji Mami ta yi ne ya maido ta cikin tunaninta.

"Kiyi hakuri nayi zaton da kai da kaya duk mallakar wuya ne, ban É—auka akwai bambanci tsakani ba. Amma zan kiyaye tunda an ankarar."
Chapter 88 · 0% Book details