← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 54 OF 101

Sashe 54

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Humaira ba ta ce uffan ba, domin tun dawowarsu ta ƙara jin Tasleem ta fice a ranta, ta kuma ƙudurta ban da dai gaisuwa ta musulunci to fa babu abin da zai sa ta cigaba da tura kai ba kwarjini wurin waɗanda ba za su taɓa kaunarsu ba. Ko kaɗan Tasleem ba ta wani nuna farin cikin dawowarsu ba, ita kuwa me zai sa ta cigaba da shiga sabgar wacce ba ta yin ta?

"Allah Sarki, Allah ya kawomata da sauki."
Cewar Ummita sannan itama ta ja bakinta ta yi shiru.

***
Yanayin da Futuha ta shigar wa Mami ne ya sanya ta ɗago kai daga wayar da take amsawa har da hawayenta. Cikin wani sauri ta sallame wayar ta miƙe, Futuha ba ta kawo komai ba ta ƙarasa da sauri ta rungumeta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Mami wacce ta ji kirjinta ya yi wani irin bugu da ƙarfi ta ɗago kai da azama ta kalle ta har hannuwanta a rawa.
"Ke mene ne ya faru ne? Ina Yakubun?"

Gaba ɗaya ta ruɗar da cikin Mami wanda ta ji har wata ƴar ƙara ma yake yi.

"Mami ƙarya yake yimin, ashe matarsa tana gidansa cikin wata irin ƙasƙantacciyar rayuwa?"

"Toh ina ruwanki da ita! Ke ba kanki kika sani ba?!"

Yadda Mamin ta yi furucin a zafafe ya sa Futuha shiru tana kallonta da ɗan mamaki saman fuskarta, kamar dai ba Mamin da ta saba karo da ita ba. Sai kuma ta tuno labarin ƴanmatancin Mamin da Anna ta ba su, mace ce da a tarihin soyayyarta ba ta taɓa kallon mai mata balle ta ji zuciyarta za ta iya ɗaukar zaman kishi da ita ba, har tana jinjina mamakin zaman da ta amince suka yi da Fatima ta kuma ƙaunace ta. A baya dai Mami ba ta san kowa da komai ba sai kanta da kuma nata. Wannan tunanin da Futuha ta yi ne na tsohon tarihin Mamin ya sanya ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma mamakinta na farko ya gogu tas daga kwanyarta.
"Nifa ba wannan ƙaryar ce ta tada hankalina ba, tun kafin mu dawo likita ya bayyanamin ina da ciki bayan ƴar rashin lafiya. Na bar abin na ɓoye ban sanar mishi ba akan zan ba shi labari mai dadi, sai yau da muka dawo ne nake sanar da shi toh kawai sai ya sauya fuska. Ya kuma rantsemin shi bai aure ni don na haifarmasa, daga uwargidansa kawai yake da kwaɗayin samun yara. To fa shi ne da faɗa ya kaure tsakaninmu, ya ce na zubar ni kuma na ce ba zan zubar ba tunda ba shege ba ne, kawai Mami sai ya ja hannuna ya kai ni ɓangaren Uwargidansa. Nayi mamakin ganin ashe yaransa takwas har da budurwar da za ta yi sa'ar Raihana. Komai nata ya ci uwarsa a falon. Goyon ɗa take yi ma, a gabanta da na yaran ya nunamin yaranta sun ishe shi ba ya kaunar haihuwa daga kowace mace. Ya kuma aure ni don ya ci duniyarsa ganin da ya yi ni ƴar rawa ce wai a Tiktok na kuma san ta kan rayuwa sai ya ɗauka zan san dabarun family planning kafin aure."

Kawai sai ta fashe da kuka. Mami zuciyarta har wani tafarfasa yake yi. Ta ji kukan Futuhar tamkar yana ƙara tafarfasa ƙwaƙwalwarta don haka ta dakamata tsawa.

"Ya isa! Nace maki ya ishe ni haka! Haba! Da wanne ku ke son na ji? Da mummunan albishir din da Babandi ya faÉ—amin ko kuwa da hargitsinku?! Ke ba za ki iya cin uban shege ba?! Ba za ki iya yadda za ki yi ki ga kin fitar da yar iska daga gidanki ba?! Shashasha kai marar wayo!"

Tana kaiwa nan ta nemi bakin gado ta zauna kirjinta na dukan tara-tara tana maida numfashin gajiya. Futuha kuwa ai sai ta ƙara yin mutuwar tsaye don mamaki. Toh Mamin nan dai ta tabbata ita ce ainahin Mamin can baya lokutan yanmatancinta, ita ce Mamin da Anna ta yi mugun kewarta. Faɗa, zagi kuma duk akan kishi? Yau Mami dai da bakinta ta mata iznin daukar kowane mugun mataki ne akan kishiyarta da mijinta. Futuha ta juya cikin sassarfa tana kukan har lokacin ta fice zuwa ɗakin Anna.

Mamin kuwa sai bayan da kwanyarta ta ɗan samu nutsuwa, tashin hankalin dake ƙasan ranta ya ɗan lafa sai ta soma tunano irin maganganun da ta faɗawa Futuha. Ta lumshe idanu ta ja guntun tsaki. Ta san yarinyar dole mamaki ya kashe ta, amma ita ta san azabtuwar da take yi ko kuma ta yi a shekarun baya da suka gushe. Ta tsani kishiya tsana mafi munin gaske.

'Ciki har da Fatima?'

Wani ɓangare na zuciyarta ta watso mata wannan tuni. A fili ta ɗaure fuska tamau, idanunta nan da nan suka kaɗa tsabar masifa da kuma abin da ta tuna na daga rayuwar Fatima da Yusuf a baya.

"Har da Fatima." Ta furta a zahiri, can kuma ta miƙe ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta. Sai bayan ta dawo daidai ne sannan ta fito zuwa ɓangaren Abba. Ta iske shi zaune yana kallon labarai, itama wuri ta nema ta zauna da wani irin sanyin jiki.

Abba ya maido hankali gareta.

"Maryama, na ganki wani iri, Futuhar ba su dawo ba ne?"

Mami ta girgiza kai.

"Sun dawo, tana wajen Anna ma suna gaisawa."

"To ko jikin Tasleem din ne? Ni me ma ya faru ne da ita ta yi rauni?"

Ko kusa ba ta sanar da Abban gaskiyar abin da ya yi sanadin kwanciyar Tasleem din a asibiti ba. Ta sani muddin ya ji to faÉ—a zai yi wannan ya sa ta gyara batun.

"Zamewa ta yi ta faÉ—i a banÉ—aki. Amma ai da sauki tunda jinin ya tsaya."

Jinjina kai Abban ya yi.

"Allah ya raba su lafiya. Sai ta ƙara kula."

Ta yi shiru tana kallon gefe guda ta kasa amsa mishi, ya riƙo hannunta cike da kulawa murya a tausashe ya ce.

"FaÉ—amin, meke damunki?"

Ƙasa ta yi da idanunta sai hawaye, suka zubo saman hannun Abba da ya ɗora bisa nata. Nan da nan ya ƙara shiga tashin hankali.

"Kinsan bana son kuka ko? Taimaka ki faÉ—amin damuwarki Maryam. Zuciyata ba za ta É—auki wani sabon tashin hankalin ba bayan wanda na fuskanta kwanakin nan."

Ta jinjina kai ta dube shi.

"Abban yara tunanin yarannan ya kasa barin zuciyata ta huta. Tun dawowarsu zan iya ce maka Ummita har yau ta ƙi dawowa cikin nutsuwarta. Yarinya mai fara'a da son jama'a marar hayaniya, ta koma wata iriya. Babu doguwar magana balle hira, koyaushe zaman tunani da shiru. Wannan abu yana damuna matuƙa."

Shima Abban hakan da ta faɗi sai ya ƙara taso mishi da nasa damuwar.

"Hakane Maryama. Toh a shawarce me kike tunanin za'a yi? Mece ce mafita?"

Mami ta numfasa.

"Mafita a samar mata abin da zai dawo da walwalarta. Abin nufi, madadin lokacin da aka sa na aurenta da Sahabi, me zai hana a yi mishi magana idan sun shirya kawai ya kawo lefe a sanya bikin nan da kamar sati biyu?"

ÆŠan jim Abba ya yi cikin hali na tunani. Sai kuma ya ce.

"Kina tunanin idan an yi hakan ba a tauye ta ba kuma. Bana jin yarinyar nan ta samu nutsuwar da za ta karɓi aure a yanzu. Kada ki manta fa, keta haddinta aka yi ta ƙarfi. Aa Maryama, mu dai yi hakuri tun da abinda ya rage cikin shekarar bai wuce watanni biyar ba, ki jira mu ga abin da Allah zai yi a gaba."

Ba haka ta so ba sam, ba kuma ta taɓa tunanin Abban zai watsamata ƙasa a ido ba. Kai ta mance rabon ma da ta bada shawara irin haka dangane da abin da ya shafi yaran ya musanta. Ganin sauyin dake saman fuskarta ne ya sa Abban ƙara riƙo hannunta ya ɗan matsa.

"Kiyi hakuri Maryama, ba fa watsa maki ƙasa a idanu nayi akan al'amarin yaranki ba. Aa, ki dai daure na sani da zafi ka dinga ganin ɗanka cikin yanayi mai firgitarwa. Amma a shawarce, me zai hana ta je Bichi ko sati biyu ta yi kinga za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali."

Daure fuska Mami ta yi.

"Shikenan, ɗauke ta a yau ka kai ta sai Maijidda ta zuba ruwa a ƙasa ta sha tunda ta ga gazawata a kula da Ummita. Nagode."

Tana kaiwa nan ta zame hannunta cikin na Abban ta soma kokarin miƙewa tsaye. Ya yi saurin dakatar da ita.

"Haba Maryama, to kiyi hakuri naji na yi laifi a kalamaina. Ba zan kai Ummita ba face da izninki. Kiyi hakuri, shikenan? Yanzu me kike tunanin za'a yi don sama mata nutsuwa?"

Ta sauke ajiyar zuciya.

"Tunda har shawarar da na bayar bai yi ba, toh na fi tunanin ka bayar da kudi muje da su ukun nayi musu ƴar siyayya sai kuma ita Humaira da ka riga ka san matsalarta akan maza. Ganin wannan abu da ya afku ga Ummitan ya ƙara sanyawa ta tsani al'amarinsu. Daidai da Fadeel din da muke murnar ta soma sakin jiki da shi suna ƴar hira yanzun ko muryarsa ba ta wani son ji. Tun wuri gwara a yi mata maganinsa. Na kuma fadamaka labarin wani mai magani, idan har ka amince sai na kai ta a karɓo a gani ko za'a dace."

Abba ya kurawa Mami idanu, a duniya bai taɓa ganin matar da ba ta damu da nata ba sai na wasu. Ba ruwanta da damuwar yaranta sai abin ya ci tura. Matar da ɗiyarta ke kwance a gadon asibiti amma ba ta ko zancenta, burinta ta samar da farin ciki ga yaran wasu. Kaunarta ya ƙara mamaye zuciyarsa, ya riƙo hannuwanta ya sumbata sannan ya sakarmata murmushinsa da ya san yana daga cikin abin da yake ƙara dulmiyar da ita cikin kogin sonsa. Ita kuwa sai ta ɗan kauda kai tana murmushi.
Chapter 54 · 0% Book details