← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 66 OF 101

Sashe 66

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Wasa-wasa sai ga zance ya yaɗu a duniya. Abinka da soshal midiya masu jran ƙiris sai ga labari salo-salo ana juyawa har da masu fitowa su na ƙara nasu gishirin su na ƙara yaɗawa. Abin mamaki da tsoron shi ne har asalin su Humaira da Ummita na kasancewarsu yaran riƙo a gidan da suke haka aka dinga yaɗawa ana faɗin watakila musguna musu ake yi ya yi sanadin shigarsu karuwanci yayinda a wani gefen wasu ke cewa mai yiwuwa son duniya ne ya kai su ga faɗawa halin da suka tsinci kansu. Har da kuma wadanda suka ce koda ace ba karuwancin suka fita da zummar yi ba, zai iya yiwuwa sun yi ne domin su samu maƙudan kuɗaɗe amm a ƙarshe abokan ta'addar nasu suka cutar da su ta hanyar yi musu fyaɗe. Labaru dai iri-iri akan bayin Allahn nan biyu Humaira da Ummita babu irin wanda bai yaɗu ba. Mafi rinjaye sun fi aminta da cewar da haɗin bakinsu aka sace su hakan ta kasance. Ƙalilan ne masu tsoron Allah wadanda ba su yarda da wannan labaran ƙanzon kurege da ake ta fafutukar yaɗawa ba.
  Tsintar wannan labari a wurin dangin Ummita da ma Humaira sam bai zo musu ta daɗi ba. Hankali tashe Anti Maijidda ta diro Kano, ko kaɗan ba su da labarin wai Ummita na da ciki, a hakan ma ba ta amince ba sai da ta zo don kanta ta ga Ummita da tulelan ciki, wannan baƙin ciki yasa har suma ta yi ta kuma tiƙe lallai sai dai Abba ya ba ta Ummita su tafi. Mami kuwa tashin hankalinta bai wuce na wayar da Wizzy ya ƙara yi mata bayan bayyanar labarun da ake ta yayatawa ba akan lallai Ummita na haihuwa ta ba shi ɗansa yana so zai kai wa gyatumarsa idan kuwa ta saɓa zai iya tona asirinta. Wannan dalilin ne yasa itama ta kafe akan Ummita ba za ta tafi ba.

Anti Maijidda ta fusata ainun ta dubi Mami da hawaye jage-jage saman fuskarta tana kai nunata da yatsa.

"Ke Maryam! Ni ba sakara ba ce ki dube ni dakyau! Idan idanun kowa ya rufe ba a ganin aibunki ni kuwa Maijidda ko ruwan teku za ki shiga ki wanke jikinki ki fito ba za ki taɓa sauyawa daga yanda nake kallonki ba. Don haka tun wuri ki fita idanuna na runtse, idan kuma ke kika yi naƙudar Ummita a yau sai ki hana ni tafiya da ita mu gani!"

Jin haka sai kawai Mami ta sa kuka sosai, Abba ransa ya ɓaci yayinda Ummita ta kwantar da kai a kafaɗar Humaira tana nata kukan.

"Hajiya Maijidda ina ganin ƙimarki kuma albarkacin Jamila da abin da ta haifa ya sa ban taɓa ɗaga idanu na faɗamaki maganganu ba. Ko ba komai kina ganina da wannan girman, amma fa ba zai yiwu ace koyaushe ki zauna kina kushe Maryama ba. Haba, duk ƙoƙarin da take yi akan Ummita bakya gani? Meyasa kike nema ki yanke zumuncin da ke tsakanina da ɗiyar ɗan uwana? Ke a ganinki idan ace yau Maryama na cutar da ita zan zuba idanu ne nayi shiru? Ni ga sakarai?"

Mami ta É—an dube shi ta gefen idanu kawai, yayinda Maijidda ta ji zafin maganganunsa.

"Alhaji Yusuf, na ji Maryam ba ta cutar da Ummita, amma yau idan har ni na isa da Ummita matsayin yaya ga mahaifiyarta ina neman alfarma a wurinka ka bar ni na tafi da ita Bichi. Ka ga dai yadda abubuwa suka rincaɓe, sunanmu gaba daya ya gama ɓaci, ba naku ba, ba kuma ga namu ba ƴan uwan mahaifiyarta. Don haka ina  roƙon arziki ka bar ni na wuce da ita."

Ummita ko kusa ba ta gane ɓacin sunan da Antinta ke magana a kai ba, sai ta yi tunanin ko don cikin dake jikinta ne kuma ga shi nan an soma sani a gari. Abba kuwa, ya yi shiru yana nazarin maganganunta, da alama sun yi tasiri a zuciyarsa. Ganin haka da sauri Mami ta dube shi.

"Yau kenan kana ƙoƙari ka nuna ba ni na haifi Ummita ba? Kokari ka ke yi ka sallamawa Maijidda Ummita ta wuce da ita ko? Kana son nunamin ba ni na haifeta ba, ashe Raihana idan ace ita hakan ya faru a kanta ba zamu yi hakurin duk abin da zai je ya zo ba mu bar ta karkashin kulawarmu ba? Lallai ka sani Yusuf, a yau idan ka amince da dauke Ummita daga hannuna toh ka sani cewa ta tafi kenan har abada ba za ta dawo wurina ba. Na kuma gode da nunamin iyakata da ku ka yi."

Tana kai wanan ta juya ta soma tafiya cikin zubar hawaye, wannan ya tashi hankalin Abba da ma su Ummitan.  Abban na kiran sunanta ta yi banza da shi, ita dai Anti Maijidda na tsaye riƙe da hannuwa a kirji tana kallon irin salon makirci na Mami mai ban mamaki. Ummita cikin sauri ta miƙe ta riƙo hannun Mami tana kuka  kamar ranta zai fita lokaci guda tana girgiza kai amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakinta. Mami ta dube ta cikin hawayen sai kuma ta shafi gefen fuskarta ta yi murmushin yaudara. Cikin karyar da murya ta ce.

"Kar ki damu Ummita. Da nan din da can duk É—aya ne."

Sai a sannan Ummitan ta magantu.

"Aa Mami, kiyi hakuri. Wallahi babu inda zan je, ke din tamkar uwa kike a gareni. Idan har a duniya za iya barin mahaifiyata toh kuwa zan iya rabuwa da ke. Kin rungumeni a sadda na buÉ—i idanuna babu iyaye, kin maida ni tamkar É—iyar cikinki, kin kaunace ni ta kowace fuska. Ni kuwa me zai sa na zama mai butulci a gareki? Kiyi hakuri da kalaman Anti Maijidda, ta yi su ne saboda tsantsar tausayi da kuma ganin kamar zan fi samun kwanciyar hankali a can, amma na tabbata ita kanta ta sani kina nunamin kaunar da ba don kar nayi wauta ba, zan ce ta fi na Raihana da su Anti Tasleem."

Anti Maijidda ta kasa cewa komai tayi gum sai kallo, Abba kuwa sai kalaman Ummita suka kashe mishi jiki, shakka babu gaskiya ta fadi kuma ba zai so a yiwa Mami butulcin nan ba. Ya dai so a farko ya amince da batun Anti Maijidda idan har sauya wurin zai dawo da walwala da farin cikin Ummita. Humaira sosai ta ji dadin kalaman da Ummita ta yi ga Mami, ta tabbata hakan ne kawai zai sanyaya zuciyar Mamin, sai kawai ta ji Anti Maijidda ta sire a ranta. Ita a duniya yanzu ba ta da maƙiyi irin mutumin da zai kushe Mami da ƙoƙarinta a kansu, abin da dai ta fahimta shi ne, ba a iyawa DAN ADAM, wannan sai mahaliccinsa. Ba ta san mene ne ribarta na aibata Mami ba.

Murmushi Mami ta yi tana dubanta kafin ta dubi Anti Maijidda da ta yi mutuwar tsaye. Sai a lokacin Anti Maijidda zuciya ta tunzurota ta soma magana tana duban Ummita.

"Yau kin watsamin ƙasa a ido ko Ummita? Ni kika nuna bani da wani matsayi ko ƙarfin iko a wajenki? Wa.."

"Anti please. Ki duba yanayin da take ciki mana ki rabu da zancen nan haka. Ina haÉ—a ki da Allah ki bar komai har ta rabu da abin da ke jikinta lafiya idan har dagaske farin cikin kike nema mata."

Mubarak ke wannan tun soma zancen ya shigo yana kuma sauraronsu. Ransa ya ɓaci ba kaɗan ba da yanda Anti Maijidda ke kushe masa uwa kuma mahaifiya amma ya fi jin zafin yadda take neman haifarwa da Ummita wai sabon ɓacin ran na daban. Jinjina kai Anti Maijidda ta yi, ta hadiye ɓacin ran nata kamar yanda ya nema. Dagaske ta fi kaunar samun lafiyar Ummita a yanzun da kuma kwanciyar hankalinta wannan yasa ta taka zuwa ga Ummita ta janyota ta rungume. Yadda Ummitan ke kuka hakanan itama take yi.

"Kiyi hakuri ya isa hakanan, shikenan magana ta wuce. Kiyi zamanki anan zamu dinga waya kin ji?"

Ummita ta gyada mata kai, daga haka kuma aka kashe zancen. Abba da Mubarak suka fita don haÉ—uwa da D.P.O don tsaurara bincike akan wanda ya yi wannan aika-aikar da ma neman alfarma gurin D.P.O akan ya fito gidajen yaÉ—a labarai ya faÉ—i abin da ya sani kan satar su Ummitan zuwa yanda aka kaya sadda aka je kwato su.

Mami kuwa ta ƙara jifan Anti Maijidda da murmushin cin nasara sannan ta juya ta bar falon zuciyarta fari ƙal yayinda ta bar Anti Maijidda da ɗumbin takaici da cizon yatsa. Ta sani addu'a babu abin da ba ya magani, za kuma ta dage da kai kukanta ga Allah, watarana halin Mami zai bayyana ƙarara a idon duniya.

***
Anti Amarya ta dubi Alhaji bayan gama nuna masa jita-jitar da ake yaÉ—awa akan su Humaira ta ce.

"Yanzu Alhaji wannan magana ko ƙarya ne a yanda sunan gidannan ya ɓaci fisabilillahi sai ka aminta da auren Fadeel da Humaira?"

Nan da nan Alhaji ya É—aure fuska ya ajiye wayar.

"Me kike son ki cemin? Sai na tauyewa ɗana farin cikinsa akan ƙaryar da maƙaryata suke yamuɗiɗi da shi?"

Ta tari numfashinsa.

"Saboda farin cikin ɗanka mu kuma za ka zubar da namu ƙimar gidan a idon duniya? Ka san wannan ɓacin sunan kuwa ba iyaka Nijeriya ya zagaye ba? Allah kaɗai ya san inda lamarin ya tsaya. Alhaji ya kamata ka buɗe idanunka sarai ka dubi lamarin da idanun basira, ni ban taɓa ƙin Humaira ba saboda ban ga abin ƙi tattare da ita ba kamar yanda babu wani aibu da ta taɓa yi gareni ba. Amma ana magana ne na haɗa zuri'a, idan ya kasance sai bayan mai afkuwa ya afku maganar duniya ta tabbata gaskiya sai ka sa hannu a kumatu ka ce za ka yi tagumi da nadama?"

Shiru Alhaji ya yi, maganganun Anti Amarya suka shiga tasiri a zuciyarsa. Dagaske yanzu idan har zancen duniya ya tabbata shikenan ya haɗa iri da ɓata gari?
Chapter 66 · 0% Book details