← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 83 OF 101

Sashe 83

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Yallaɓai zamu wuce lokaci ya ja. Kiyi hakuri Ummita, za ta girbi abin data shuka maki kinji ko?"

Ya ƙarashe yana yiwa Ummita kallon da shi kadai ya san ma'anarsa. Daga haka wani ma'aikacinsu ya matso ya ba Jannat umarni akan ta yi gaba su je, nan fa Anna ta hau bori da ashariya duk cikin hausarta da bai irin na Bahaushe sak. Hatta da Abba sai da ta zage wai ya bari za'a tafi da autarta saboda ya nuna son kai. Abba dai mamaki bai bar shi ba, kenan duk wannan son da kaunar da suke nuna mishi da yarannan a fatar baki ne? Ya lura Mami sai kokarin janye Anna take yi tana mata yare akan ta yi shiru amma ina idanunta ya rufe ita za a tsfi da gudar jininta kuma mafi soyuwa a ruhinta.

Raihana ba ta ce uffan ba, zuwa yanzu lamarin na su Jannat ba ya girgiza ta, ko babu komai ta ga wacce ta fi su iya tsari da kuma makirci. Na su ba komai bane. Ana wannan abu kallon Mami kawai ta ke yi yadda ta dage har da jan Ummita a jiki tana rarrashi. Ba ta sani ba akan Ummitan ko abin nata ya kai zuci ko aa, kawai sai ta kasa aminta da hakan sai ta juya ta koma ɗaki saboda wani sabon kukan da ya yunƙuro mata.

Haka aka wuce da Jannat tana kuka da ihun a yafe mata don gaba daya kuma da ta ga al'amarin dagasken gaske ne sai ta shiga tashin hankali. Abba kuwa ana ficewa da ita ya fice zuwa dakinsa, tun a falon ya sanya mukulli ya kulle don ba ya buƙatar ji ko ganin Mami a wannan yanayin. Yana buƙatar samun hutun da zai yi tunanin da ya dace.

***
Duk wannan budurin da ya faru su Futuha ba su da masaniya a kai sai washegari labarin ya riskesu daga Dawud da ya yi waya ya zayyane musu komai da komai. Zo ka ga kuka da sheshsheka wurinsu musamman Tasleem da ta ji tamkar an tafiyar mata da wani sashe na jikinta don za ta rantse shaƙuwa da kaunar dake tsakaninta da Jannat ta shallake nata da na Mami. Ita mai shirin fita zuwa makaranta inda suke shirye-shiryen zana jarrabawar ƙarshe sai ta fasa suka ɗunguma har Futuha zuwa gidan. Ba su iske Mami ba don tun ranar da aka tafi da Jannat suke asibiti sakamakon faduwar da Anna ta yi, ita ta kwana a wurinta bisa iznin Abba don shi dama ba shi da buƙatarta yanzun. Ta riga da ta gama sirewa a ransa. Raihana suka soma cin karo da ita kwance a falon da casbaha a hannunta tana ja.

"Ke ina suka kai Anti Jannat?"

Tambayar da Tasleem ta soma jifanta da shi cikin zubar hawaye ko zama ba ta yi ba. Guntun tsaki Raihana ta ja a ƙasan ranta a fili kuwa dakyar ta ce.

"Nima ban sani ba."

"Uhum, nikam tun farko dama sai da na nuna rashin goyon bayana ga wannan.."

Idon da Futuha ta yiwa Tasleem ne ya sanya ta yin shiru, dagaske dai suɓutar baki ta so yi, sai ta ji tsoron kada Raihanar ta fahimci komai. Ita kuwa Raihana koda ta fahimtar ma ba ta nunamusu komai ba, ta fi damuwa akan al'amarin kashe ran da uwarta ta so a yi. Har yanzu ta kasa kwantar da hankalinta, abin ya jefa ta cikin matsanancin damuwa da tunane-tunane.

"Kin je asibitin wajen Anna ne?"

Cewar Futuha, girgiza mata kai kawai ta yi. Futuha ta ja tsaki.

"Duk dai abinki duk wani guje-gujenki ba ki da sama da Annar da kuma mu, aikin banza kawai. Wato wai ke an taɓa ƴan uwanki shi ne kika dauki gaba da uwar uwarki. Dakyau."

"Rabu da ita dai Futuha, duk dai lalacewar naka naka ne. Tashi mu wuce asibitin don ni ko wajen Abban ba zan shiga ba. Ai yana ji yana gani aka titsa ƙeyar Antin amma ya ƙi hanawa saboda ya nuna son kai da fifiko tsakanin wasu can da mu."

Tasleem ya fadi tana huci gami da gyara goyon da ke kokarin kunce mata.

Sai a lokacin Raihana ta mike zaune a zafafe ta shiga ba su amsa.

"Su din dai jininmu ne koda kun ƙi ko kun so. Kuma wallahi da ace ni ce ku zan ji da rayuwata ne ba na tsaya kallo da kushe ta wasu ba. Ke kuma da kike kiransu da wai ƴan uwana, to ki goge kalmar wai din, yes jinina ne su kuma wallahi sun fiyemin ku nesa ba kusa ba. Kin tsaya ganin kuskure a rayukan wasu, kina nan mijinki har lefe ya kai na Ƴar Snow zai aure ta. Mtsw! Nonsense!"

Tana kaiwa nan ta juya a fusace ta bar su a tsaye kamar an wawushe musu ƴaƴan hanji. Ba zagin da ta yi musu ne ya taɓa su ba don dama batun raini to fa Raihana ta yi musu shi, ko kadan ba ta wani ba su girma tun a baya, yanzun ma da ya ragu sun sani ko sun ƙi gaskiyar hakan ne albarkacin zama da su Ummita ne. Batun kai lefen Ƴar Snow da Yakubu ya yi shi ne ya fi komai sanya su cikin razana. Lefe gagarumin da suka gani yana yawo yau kusan sati kenan aka ce na Ƴar Snow ne, shi dai?

"Tasleem wai kodai ni ce ban ji daidai ba?"

Futuha ta fadi da wani irin ruɗani, ita kuwa Tasleem ta ɗan ji sanyi a ranta, kl babu komai idan har hakan ya tabbata ga Futuha zai kasance ba wai ita ɗaya ba ce ke shaƙar bakin cikin ɗa namiji ba.

"Kai ta ya za ki biyewa wannan mahaukaciyar? Kema kin sani dai don ta shaƙa maki baƙin ciki ne ta tayar da hankalinki."

Sai Futuha ta hau girgiza kai cikin mugun tashin hankali, Tasleem ganin haka ta ja hannunta suka fice tana fadin.

"Dallah Malama kar abin da ta fada ki bari ya yi wani tasiri a zuciyarki. Yakubun da ke Dubai yau kusan sati uku kike wani tunani na daban? Toh ina ce É—azun ma ya kiraki kun sha hira?"

Jin haka sai Futuha ta dan samu nutsuwa, sai kuma ta yi kwafa.

"Shegiyar yarinya kai, wallahi ta jefa ni cikin ruÉ—ani na É—an lokaci. Zan yi maganinta ne bari mu dawo."

"Atoh, ko kefa. Ni so nake Anti Jannat ta fito, don ba ma za'a kwaso kayana ba sai ta fito idan ya so na siyar mu haÉ—a kuÉ—in ta kai wa Teacher dinta ya karkatomin hankalin Fadeel."

Ta fadi Teacher gudun kar wani ya ji. Futuha dai jinta kawai take amma har a ƙasan ranta ta san da wuya aikin ya ci. Yaudarar kai dai Tasleem ta ke yi, amma da aiki na cin Fadeel da Ibb da tuni wani labarin ake ba wannan ba.

***
Mami zaune a gefen gado bayan ta gama ba Anna abinci dakyar ta yi loma biyar ba ta ƙara marmarin ci ba. Sai kuka take yi tana tsinewa Abba kai ka ce shi ne ya sanya a kama Jannat. A wannan yanayin su Tasleem suka shigo dakin, haɗa su tayi gaba daya ta rungume tana kuka wai an tafi da shalelenta. Mami kuwa sai ta mike ta bar musu gadon ta koma saman kujerar dakin cike da dumbin tunani. Toh wai waye ya sanya aka cigaba da bin ƙwakkwafi har aka binciko gaskiyar al'amarin? Ta san dai Abba tuntuni ya bar maganar. Sai ta ɗan ja tsaki, ita ba ma wannan ba, ta kasa gane wanda ya sanar da ƴan sanda har aka kai wa su Abba ɗauki, ga kuma wani sauyin da take fuskanta daga Abban, wannan kuma ta fi danganta shi da Jannat wacce asirinta ya tonu. Watakila fushin da ya yi da jin zancen ne ya shafe ta.

"Saki kuwa ni Hansatu?! Shi Hamzan ne ya sake ki?!"

Furucin da Anna ta yi ne cikin dafe kirji ya sanya Mami maido hankalinta ga hirarsu. Ta mike tsaye cikin mugun firgita tana duban Tasleem wacce ko a jikinta, haka ma mikewar Mamin ba ta wani razanata ba, ɗan shakkar Mamin da take ji a baya yanzu duka ya kau adalilin jin wacece ainahin Mamin da ta yi daga bakin Futuha sai ta gane cewa ashe ita da ma su Jannat ba su yi komai ba kuma ba za su taɓa shuka irin abin da ta shuka ba a rayuwa.

"Wa aka saki?"

Mamin ta ƙara tambaya don gani ta yi tamkar ba ta ji daidai ba. Tiryan-tiryan Tasleem ta ba su labarin abin da ya faru ta ƙara da fadin.

"Nifa Mami wannan abun ya yimin daidai kuma ya zo kan gaɓar da nake da buƙata. Ya je ya auri uwar Ramlatun ma ina ruwana. Ni yanzu Fadeel nake so na aura."

"Za kuwa ki mutu ba aure! Ke shashashar ina ce?! Waye ya faɗamami akwai ranar da tsinannen yaron can zai aureki?! Wallahi na rantse maki har abada ba za ki taɓa aurensa ba! Tun muna shaidar juna ki tashi ki koma ɗakinki ko kuma yanzu na saɓa maki!"

Ta turo baki.

"Nidai Mami bana son aurensa. Dama wallahi da nasan matsiyaci ne babu abin da zai kai ni ga aurensa. Ai kowa yana auren ne don ya samu gida hutun da zai ci karensa babu babbaka, idan ma mutum bai samu ba sai ya ɓullo hanyoyin da ya san hakansa zai cimma ruwa. Toh ni dai ba zan iya aikata abubuwan da kika aikata ba amma zan iya yaƙi da namiji har ya sauwaƙemin na fito na samu cikar burina."
Chapter 83 · 0% Book details