Sashe 67
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Anti Amarya ganin ya yi shiru sai ta yi ɗan murmushin mugunta, ko babu komai dai alamu sun nuna kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta yanda Fadeel bai auri Murja ba ya yi sanadin barinta gidan, toh shima har abada sai ta raba shi da Humaira. Sai ta ga iya gudun ruwansa.
"Shikenan Antin yara, zan dai duba zancen. Mu yi addu'a mu kuma jira mu ga ta inda gaskiya za ta yi halinta."
Ta sauke ajiyar zuciya ganin ta yi nasara.
"Hakane, Allah ya bayyana gaskiyar."
Ya amsa da amin.
Æangaren Fadeel kuwa har tsawon kwanaki uku da al'amarin ya fasu yake cikin wani irin tashin hankali da baÆ™in ciki. Soyayyar da yake yiwa Humaira ta yi Æ™arfin da ko daidai da Æ™iftawar idanu ba ya zarginta da fasiÆ™anci balle kuma ya aminta da jita-jitar da ake yaÉ—awa. Wannan ya sanya a É“angarensa shima ya sanya aka soma bincike akan al'amarin don a gano bakin zarensa. Ga bikin babban amininsa nan da kwanaki uku amma hakanan damuwar yanayinnan ya gusar da murnar bikin a zuciyarsa. Ta yaya mutanen da aka ceto su cikin wani hali na maye da kuma muguwar rama da baÆ™i ace yawon duniya suka shiga? Har abada ba zai yarda da wannan ba. Da taimakon wani abokinsu na makaranta wanda yake babban ma'aikacin sirri na SS, bincikensu ya dinga zurfi. Ibb dai ya zuba idanu kawai yana Æ™ara mamakin wannan irin zazzafar kaunar ta Fadeel akan Humaira. Har shakka yake yi kada bayan aure ya zame mata mijin tace saboda shi kam abin ma ya shallake tunaninsa.
***
Tasleem tsaye tana safa da marwa a ƙuryar ɗakinta daga ita sai vest wacce ta ɗage mata saboda girman da cikinta ya yi sai ko ƙaramin short, waya ne a kunnenta, burinta kawai Antinta ta ɗaga domin ta ƙagu ta ji labari. Har sai da ta kusan katsewa sannan Jannat ta ɗaga muryarta a sake. Ko gaisawa ba su yi ba ta gangara inda yake ci mata tuwo a ƙwarya.
"Anti, ina ta neman wayarki a kashe na ƙagu naji daga bakinki. Kin ji labarin da ke yawo a media akan su Humaira ko? Anti hala aikinki ne?"
Wata dariya Jannat ta yi daga ɓangarenta tun ma kafin ta ce komai Tasleem ta samu amsar tambayarta, sai kuma ta magantu.
"Ni ce nan my daughter, ai ban fanshi marin da munafukar ƙanwarki ta yimin ba. Idan sunansu ya ɓaci a idanun duniya wa kike tunanin zai aminta da auren ɗaya a cikinsu? Ko a zatonki wancan sakaran Fadeel ɗin zai ƙara kallonta? Tasleem ki kwantar da hankalinki, yanzu na san na gama ɗaukar fansa akan Humaira don uwarta. Ita kuwa Ummita kinga cikin dake jikinta ya taimaka wurin da jama'a za su yi saurin aminta. Ke tun sadda al'amarin ya faru nake bibiyar kalaman jama'a ina dariya. Huumm muje zuwa."
Tasleem ta yi murmushi sosai.
"Na ji dadin rabuwar Fadeel da Humaira, na sani ko ya nace akan sonta zai wahala iyayen da suka san mutuncin kansu su yarda É—ansu ya aure ta. Amma Anti naji fa wai Abba zai sa ayi binciken wanda ya fara yaÉ—awa don a gano gaskiyar magana. Bakya tunanin idan aka kama shi asiri ba zai tonu ba?"
Tsaki Jannat ta ja.
"Nawa aka yi irin haka Tasleem, kin taɓa ganin waɗanda aka yi nasarar cafkewa?"
"A'a."
"Toh ki sa ranki a inuwa tawan, babu abin da za su iya. Yanzu ai na kira Abbannaku na jajanta masa har da kukan shegantaka, shi kuwa sai faman godiya da ban hakuri yake."
Suka yi dariya Tasleem har tana riƙe cikinta da ya ɗan motsa saboda dariya.
"Ina yinki sosai Antina."
"Nima haka yar uwa. Maminki ce dai ta matsamin da tambayoyi tun ranar farko shiyasa nake ta kashe waya, wai ita ga mai wayo, bugar cikina take yi don ta gane ko ni ce na sanya a yi amma na nunamata ban san komai ba sai ma da ta faÉ—amin. Kema ina jan kunnenki koda wasa kar ki kuskura kiyi maganar da kowa."
Tasleem ta amsa cikin jin dadi da walwala.
"Kar ki samu damuwa Anti. Ba ki da matsala da ni."
Daga haka suka yi sallama zuƙatansu cike fal da annashuwar ƙuntatawa bayin Allah.
***
  A kwana a tashi babu wuya cikin ƙudurar Allah, har dai jita-jitar da ake ga su Humaira ya kai watanni biyu, a wannan lokacin ƙura ta lafa sosai sakamakon shaidu daga D.P.O har ma da shi kansa Abba da ma waɗanda Abban ya yiwa tayin gidansa don ceto yaran nasa, likitocin da suka taimaki rayuwarsu da ikon Allah, da dai sauransu sun bayyanawa manyan gidajen jaridu abin da suka sani akan zancen har ma da irin gudunmuwar da suka bayar a lokacin. Wannan ya sanya jama'a suka gasƙata hakanan waɗanda suka aminta sai suka rinjayi masu kushe da ƙaryata zancen. Da wannan aka rufe babin Ummita da Humaira aka shiga kuma wani labarin daban ya zama abin tattaunawa a sosha midiya. Amma a ɓangaren Fadeel, magana ba ta mutu ba don yana nan a kan bakansa na sanya wa a binciko mai wannan aikin duniya ta san shi kuma ya ɗanɗani yadda ake ji idan aka ɓata wa mutum suna.
A ƙarshe ma da ya ga ba a samu haɗin kai daga jama'a ba, sai ya sanya kuɗi har dubu dari biyar ta hanyar tsohon abokin karatunsa ma'aikaci a SS, ga duk wanda ya kawo labari ko kuma ya ke da sanayya da wanda ya aikata laifin. Nan fa jama'a kowa ya yi ca, burinsu kawai su samu wadannan kuɗaɗe, a yanda rayuwar ta yi zafi sun san ba ƙaramin taimako zai musu ba.
Lokacin da Mami ta ci karo da wannan sanarwar a wani group dinsu na hamshaƙan mata wanda Hajiya Lubna ta buɗe, sosai ta ji hankalinta ya tashi. Ta ji ta ƙara tsanar Fadeel musamman da ya kasance zuwa lokacin Jannat ta gaji da ƙaryata cewa ita ta aikata a wajenta ta fito fili ta faɗamata cewar ita ce kuma fansa ta ɗauka. Ta sani, muddin ya kasance Fadeel sun ci galabar gano mai laifi to fa sunan Jannat zai ɓaci kamar yadda ƙimarta zai zube a wurin Abba.
Wannan ne yasa ta fita a whatsapp ta kira Jannat, ringing bai fi sau uku ba ta É—aga. Mami ba ta jira komai ba ta hau magana.
"Kin karanta labarin dake yawo?"
Cikin rashin ba abin muhimmanci ta amsawa yar uwar.
"Yes, na gani na karanta. Sai me?"
Mami ta danne jin zafin ire-iren magana gatsal da Jannat ke yawan yi mata a lokuta mabambanta ta ce.
"Sai ki girbi abin da kika shuka tun da ke ba kya shawara da uban kowa idan kika tashi ɓarna. Shi dai Fadeel da kike yiwa kallon tara saura gashinan yana shirin ba ki mamaki. Ko kina zaton ƙarfin kusancinmu ya kai ya hana shi daukar fansa a kanki?"
Tsaki Jannat ta ja.
"Ni babu wanda ya isa ya kama ni balle kuma ya ce zai yimin hukunci. ki ga kwantar fa hankalinki kawai, ni abin ya shafa kuma nawa hankalin a kwance yake don haka ba abin da zai faru."
Ƙwafa Mami ta yi.
"Shikenan, kiyi kuka da kanki duk abin da ya je ya zo."
Daga haka ta katse wayar tana sauke numfashi cike da ɓacin rai. Ta rasa yaushe Jannat za ta yi hankali. Ita komai ba ta iya bin sa da sauki ba sai ta yi garaje? Ai sai ta je ta ji da kunyatar da za ta yi a idon duniya da ma su Abba.
***
Yakubu ya dubi Futuha da murmushin yaudara bayan ta nutsu tana sauraron abin da zai ce ya soma magana.
"Na lura sam zamanki da Uwargida tun farko ba ra'ayinki ba ne, nawa ra'ayin ne. Hakan yasa na siya maki gida daban a can kusa da yar uwarki Tasleem. Kinga ke kadai abinki babu takura. Hakan ina fatan ya yi maki?"
Wani dadi ya kashe Futuha har ta kasa ɓoyewa ya bayyana saman fuskarta, dagaske aikin da ta sa aka yi ta hanyar abokiyar karatunsu Anti ba karamin ci yake yi ba tunda har gashinan ya soma tunanin kawo mata sauyi cikin rayuwa ta hanyar keɓance ta da abokiyar zamanta da nuna bambanci. Ta yi farr da idanu bayan ta rungumeshi ta sakar masa sumba a lebba.
"Hakan ya yimin sosai fiye ma da zatonka. Yaushe zan koma?"
Wani dadi da sanyi suka lulluɓe zuciyar Yakubu ganin ya shawo kanta cikin mugun sauki. Ya san da ace ta san dalilinsa na tashin wannan zancen sauya muhallin da ba ta fara aminta da hakan ba.
"Nan da sati ɗaya an kammala komai sai tariya. Yanzu ana aikin ƙarasa haɗa kayan wutar solar ne."
Dadi ya Æ™ara Æ™ume ta. Ta ji sosai kaunar Yakubu na Æ™ara mamayarta. Æacin ranta na hotunan auren Ibb da matarsa Dakta Salma da aka turo group din makarantarsu ya wanku a zuciyarta. Batun karatu dama tun tafiyarta Dubai da dawowarta ta watsar, Yakubu ya nuna ba ya so zai wadatar da ita da komai da take so, hakan ya sa ko a kanta ba ta damu ba balle kuma Abba da dama shima ya fi kaunarsu da zaman auren sai dai ya so ace ta kammala. Mami kuwa itama ganin É—iyarta na samun dukkan abin da ya dace na jin dadin duniya sai ta share zancen karatun.
"Allah ya kaimu lokacin."
Ya amsa da amin, daga haka ta miƙe ta na fadin bari ta kawo mishi abu mai sanyi, shi kuwa ransa ƙal ganin nan da sati biyu Ƴar Snow za ta zama mallakinsa matsayin matar aure.
***
_Sosai Ummita ke ihun daya cika kunnuwanta tana ambaton sunan Allah iyakar ƙarfinta, wannan ya sanya ta nufarta a guje ba ta damu da jinin da ke yawo a tsakar ɗakin ba tamkar ruwan famfo ta damƙo kafaɗunta tana jijjigawa tana fadin._
_"A'a Ummita kar ki mutu ki bar ni, zasu kashe mu idan suka riske mu a nan. Kinga ki tashi mu gudu!"_
_Rigarta Ummita ta damƙa da ƙarfi tana hawaye take fadin._