Sashe 3
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Wanka ta yi gaba ɗaya ta ɗauro alwalar Magriba, koda ta fito wannan budurwar ta ɗazu tana zaune gefen gadonta tana waya, suna haɗa ido ta bita da harara ba shiri Humaira ta kauda kai. Idanunta ya kai ga akwatin kayanta, ƙarasawa ta yi ta buɗe sai dai gaba ɗaya ba'a nutse take ba sakamakon idanun wannan budurwar a kanta suke duk kuwa da wayar da take amsawa. Turanci zallah take zubawa har wani shagwaɓa take yi tana dukan gadon, kalmar I Lobiyun da ta ce yasa Humaira ta fahimci koma dai wane ne toh masoyinta ne. Ba ta ko ƙara kallonta ba gudun ganin abin da zai sosa zuciya, ta fiddo doguwar rigarta ta yadi ta warware ta zura. A gurguje ta ciro hijabinta, ta linke kayan da na cire na ajiye daga saman akwatin. Ba ta jima da tada salla ba sauran ƴanmatan nan biyu suka shigo suka cika ɗakin da hayaniya, rabin hirar tasu da harshen turanci suke yi. Koda ta idar ba ta iya nutsuwar jan addu'a mai tsawo ba, ta yi istigfari da hailala da salati ta shafa. Zama ta cigaba da yi anan ba tare da ta miƙe ba gudun ma kar ta yi wani abin ya jazamata baƙar magana. Hankalinta yana ga Abbanta wanda take da tambayoyi birjik da za ta yi mishi a kwakwalwarta. Eh yana sonta yana ƙaunarta, amma meyasa bai ƙara waiwayarta ba, meyasa ba ta taɓa ganinsa ba? Meyasa kuma koda a waya bai kira domin su gaisa ba? Dukkan wannan rashin kulawar nasa da ba ta samu ba, ace yana kaunarta ya kuma damu da itq? Ita kam tana son sanin amsar da zai fito daga bakinsa.
"Ke Indo."
Ta É—aga kai ta dube su kawa, suka kwashe da dariya.
"Kai Raihana ba ki da kirki wallahi, au ba ma za ki kirata Humairar ba sai Indo ko?"
Wacce aka kira da Raihana ta yamutse fuska.
"Aa, ina ce sunan Umma gareta, tunda kaka ce ai ko Indon ma da na ce ta gode min. Ku ni ba wannan ba, wallahi mu tashi mu yi magana fa tun kan a ƙaƙaba mana ita a ɗakinnan. Ni wallahi tsoro ma take ban. Mu faɗawa Granny ta yiwa Abba magana don Mami ba za ta goyi bayanmu ba."
Humaira ta kalle ta dakyau, doguwa ce kamar dai Abba, don ta fi Maminsu tsawo, Mamin ba ta da tsawo sai jiki kuma gajeriya ce. Fara ce tas itama kalar buzayen, gashinta da ya sha kalba ya sauka har gadon bayanta, riga doguwa ce ƴar kanti ta sa mai kama jiki.
"Kallon me kike yimin kamar wata mayya? Kar ki ji ance wai wani ke ƴar Abbanmu ce ki yi ƙoƙarin haɗa kanmu da ke, wallahi kar ki kuskura don bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne, atoh. Gwara ma Abban ya zo a yi meeting ɗin a bambance tsakanin aya da tsakuwa."
Duka wannan bayanin daga bakin Raihana su ke fitowa, Humaira ta sauke idanunta a hankali zuciyarta na zafi, dagasken dai ba ta samu karɓuwar kenan ba, zuciyarta na da ƙarfin jure abu idan har wanda ya fi ta a shekaru ne ya aikata gareta, amma ba ta jin za ta iya ɗaukar wannan rainin wayon.
"Futuha mene ne haka wai? Meyasa kullum burinku ku tozarta mutum?"
Maganar Ummita ya sanya Humaira ɗago kai, ashe wai akwatinta wacce aka kira Futuha ta nufa ta buɗe. Ita dai wacce ke faman waya tun ɗazun.
Ai kuwa kamar an mintsile ta haka ta miƙe tsaye a zafafe, ta ƙarasa daidai sadda Futuha ta ɗaga akwatin da niyyar doka shi da ƙas, da wani irin zafin nama ta ture ta, daga ita har akwatin suka faɗi, akwatin ya faɗa saman gado, ita kuwa ta yi rashe-rashe a ƙasan gadon bayan ƙugunta ya bugi katakon. Ai kuwa ta kurma ihu, Raihana da ɗaya budurwar da Ummita ta ambata da Tasleem suka yo kai Humaira gadan-gadan, Ummita ta tare su. Ita kuwa Humaira ko a jikinta ta nufi akwatin ta shiga harhaɗa kayan da suka zube tana maidawa lokaci ɗaya hawayen da ta fi zaton na ɓacin rai ne, su na kwaranya. Ya yi daidai da faɗowar Maminsu ɗakin wanda hakan bai wuce sanadiyyar ihun Futuha da ya mamaye ilahirin ɗakin ba. Jin muryarta da ta yi sai da gabanta ya faɗi, ta rasa dalilin da yasa take jin haka a kanta. Ta shiga ambaton sunan Allah a ƙasan ranta.
 "Lafiya? Me nake gani haka kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin kura? Ke Ummita sake ta, kyale su na ga gudun ruwansu. Au, don ku nuna mata rashin tarbiyyarku ba komai ba ne ba ko? Har kun soma yada halin?"
Tana maganar ne fuskarta a murtuke tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, ita dai Humaira sam ba ta tofa ba sai ci gaba da tsince kayanta da tayi tana harhaɗawa tana mayarwa ciki. Ba ta san ma'anar juya harshe zuwa wani can daban da ba ta sani ba, ta dai ji Mamin a cikin yare ta yi musu magana wanda ba ta fahimci koda harafi guda a ciki ba, sai gani kawai ta yi duka sun fice daga ɗakin idan ka cire Ummita da ta durkusa tana taya ta haɗi da ƙara ba ta haƙuri. Tana niyyar amsawa Ummita ta ji an shafa kanta, ta runtse idanu ba tare da ta ɗago kai ba don tasan Mami ce.
"Ki yi hakuri kin ji Humaira, su Tasleem su na da irin wannan halayyar na son yiwa baƙo shaƙiyanci. Kinga yau ki ka zo kuma kafin su karɓe ki za'a ɗan kwana biyu, a hankali idan sun gane ke ɗin ɗaya ce a cikinsu komai zai wuce kin ji ko? Ki ɗauke ni madadin Uwa, don mahaifiyarki mun yi zaman mutunci da nutunta juna da ita. Kema kuma nasan muddin dai kyawawan ɗabi'unta kika kwaso, ba za mu samu kowace iriyar matsala ba. Ina fatan haka?"
Jin bayanan Mamin sai ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, ta ji lokaci guda kaso saba'in na fargabarta akan Mami ya ragu, wannan furuci nata na madadin Uwa, ba ta jin za ta iya kwatanta daɗin da ya sanya ta. Kai ta gyaɗa alamar toh, Mamin ta maida dubanta ga Ummita.
"Sai ku hanzarta ku fito ta ci abinci daga nan zuwa bayan sallar isha'i, Abbanku na neman mu duka."
"Toh Mami." FaÉ—in Ummita cike da girmamawa. Daga haka ta fice ta bar mu. Ummita ta kalli Humaira da murmushi saman fuskarta.
"Sai fa kin yi hakuri sosai Humaira, da gaskiyar Mami, dama ya lafiyar giwa balle an jefe ta da kashi. Su Tasleem ba su da kirki, har gwara su Yassar a kansu, don su ba su kunyar ido, za su yi maka abin da suka so. Ki yi hakuri don Allah. Nima haka nake fama da su, don ma dai babu yadda suka iya da ni ne, Mamin na taka musu burki sosai a kaina."
Jin haka ta ji ta sosamata inda yake mata ƙaiƙaiyi. Aikuwa ta kasa shiru sai da ta furzar.
"Yauwa nikam Ummita, amma ba Mami ce ta haifeki ba ko?"
Ummita ta yi dariya.
"Kin gan ni ƴar baƙa ko?"
Sai kuma ta gyaÉ—a kai ta É—an sauya fuska alamar damuwa.
"Ba Mami ce ta haife ni ba kuma ba Abba ne mahaifina ba. Mahaifina ƙanin Abba ne, mahaifiyata kuwa ƴar asalin garin Bichi ce, gaba ɗaya sun rasu ne a sanadiyyar gobara. Ni kaɗai ce rai da aka fitar a gidanmu ko kwarzane tun ina da shekaru biyar a duniya, amma daga su har ƙannena jarirai ƴan biyu duka sun rasu. Tun daga wannan lokacin ne, na soma rayuwa a hannun Kakarmu sai daga baya ne Abba ya maido ni gidansa ya damƙa amanata ga Mami. Matar da ta riƙe ni har zuwa yau ba tare da ta nuna bambanci tsakanina da nata yaran ba, kusan ince a zamanin dai samun irin Mami abu ne mai wahala. Ga kirki da son mutane, ke ba don dai kar nayi hauka ba zan iya ce maki Mami ta fi nunamin ƙauna da so fiye da nata yaran domin hatta da ragamar kula da ɗakinta da na Anna ni ta damƙawa. Ke daidai da shawara wani lokacin da ni take yi. Sai ta ture shawarar nata yaran ta ɗauki nawa."
Jinjina kai Humaira ta yi, eh lallai kam Mami ta yi abin a yaba mata, a zamanin nan kafin a samu mai fifita ɗan wani akan nashi abu ne mai matuƙar wahala.
"Wace ce Anna?"
Humaira ta watsa mata tambayar. Ta miƙe ta shiga rufe akwatin a lokaci guda tana ba ta amsa.
 Â
 "Anna kakar su Tasleem, wacce ta haifi Mami. Ai anan gidan take rayuwa, a baya ma har da ƙanwar Mami da ba ta yi aure ba muka zauna. Amma yanzu Allah ya taimaka tayi aure tana zaune a can Misra da mijinta, ke kam ai Allah ya taimake ki ba za ki rayu inuwa ɗaya da ita ba. Don ta fi su Tasleem zafi da tsangwama, ke ta dai tsani duk wanda ba jininsu ba. Hatta da dangin Abba ba ta kaunar gani a gidannan, sai kuma Allah ya sa su ɗin ma ba su fiye zuwa ba."
Humaira ta buɗe baki za ta yi magana kenan sai ga wani ƙaramin yaro cikin yara ƙananu uku da ta gani ɗazun ya shigo a guje. Masha Allah yaron kyakkyawa duk kuwa da cewar bai ɗau hasken Mamin sosai ba, ya fi yin kalar Abba, amma kuma hakan ma sai ya ƙara mishi wani kyan na daban.
"Adda Ummi ku zo inji Mami."
Ya kai ƙarshe yana nuna su duka biyum da yatsa, alamun dai mu biyun ake nema. Sai ma ya ba Humaira dariya. Suka miƙe a tare zuwa falon. Ko ɗaya ba abokan faɗan nata a ciki, bada ɗayansu ba sa nan sai Mami da yaran, sai kuwa ɗaya a cikin matasan nan na ɗazu kwance saman doguwar kujera ya toshe kunnuwa da earpiece.