← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 52 OF 101

Sashe 52

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ta yi shiru, ita ba ta ce uffan ba balle ta yi wani yunƙurin kawai sai ta maida kai ta kwanta ta yi shiru. A karan kanta ba za ta ce ga abin da take ji game da Fadeel din ba, lamarin dai ba yabo balle kuma fallasa. Ummita na ji ba ta iya cewa komai ba, Raihanar ma ba ta sake magana ba sai ta miƙe ta rage kayan jikinta ta shiga wanka, ba ta son duk abin da zai takurawa rayuwar ƴan uwannata da ta ƙara sanin girman ƙauna da shaƙuwar da ke tsakaninta da su bayan sun yi mata nisan da ta zaci har abada ba za ta ƙara sanya su cikin kwayar idanunta ba.
  Ummita tana kai wa ƙarshen surar da take karantawa ta juya ta dubi Humaira.

   "Ki je ku gaisa mana."

Humaira ta yi mamakin jin wannan furucin naga bakin Ummita, tun bayan dawowarsu ba ta wani magana kwakkwara, ko hirar Raihana ke jansu da shi, sai dai ta basar ta yi shiru. Wannan murmushin da ba ya barin fuskar Ummita, babu shi babu labarinsa tun dawowarsu. Ita ɗinma ƙarfin hali take yi don faranta ran Mami da su Raihana ga kuma Ƙasim waɗanda gaba ɗaya suke nuna musu kulawa da ƙoƙarin ganin sun saki jikinsu.

"Kin ji?"

Maganar Ummitan ya ƙara katse mata  tunani. Tana so ta ja musu amma a yanzun duk duniya babu abin da ta ke so irin ta ga ƴar uwarta ta dawo tamkar yadda ta ke rayuwa a baya. Abu na  biyu kuma ta sani ba ta jin za ta iya ɗaukar waya ta kira shi da zummar godiya bisa hidimar da ya yi akan fitowarsu, don ko cikon da suka bayar na kuɓutar da su a hannun ƴan fansa ƙin karɓa suka yi da Abban ya maida musu, ta sani wannan ita ce damar ta amma hakanan ba ta son Fadeel din ya cigaba da shigemata shiyasa.

Abban har gidansu ya je ya ƙara godiya sosai shi da Mami wacce a sannan ne ta ga gidan da ya kere na Aminiyarta Hajiya Lubna.

Ganin Ummitan ta zubamata idanu ya sanya ta miƙewa.

"Toh, na ji Ummita."

Ta faɗi kamar ta fashe da kuka sai ta miƙe ta ɗora hijabi akan doguwar rigar atamfar da ke jikinta.

Suka ci karo da Mami a falon wannan ya sanya ta tsayawa.
Gidan yanzu duk an watse sai su kadai, Jannat ta tattara ta koma bayan dogon kiran da mijin ya dinga danno mata har abin ya kusan zame musu rikici sannan ta tafi ba don ta so ba. Tasleem kuwa tun fitowarsu da kwana biyu Hamza ya zo suka koma gida.
 
  Cikin sakin fuska Mami ta dubi Humaira.

"Ina zuwa haka?"

Ta sunkuyar da kai sannan ta ce.

"Wai Fadeel ne ya zo za mu gaisa."

Nan da nan fara'ar dake saman fuskar Mamin ya ragu.

"Zuwan me yake ta yi haka ne alhalin jinyar ta ƙare? Ina ce na muku iyaka da shi tun a baya?"

Humaira ta jinjina kai.

"Hakane Mami, kiyi hakuri. Ai gaisawa kawai zamu yi. Ya yi abin da ko maƙiyina ne ya cancanci na ƙara yi mishi godiya."

Mami ba ƙaramin mamakin furucin Humairar ta yi ba wanda daidai da fuskarta ta nuna. Sai kuma ta jinjina kai.

"Shikenan, ki je amma kar ki É—au lokaci."

Murmushi kaɗan Humaira ta yi sannan ta amsa da toh ta cigaba da tafiya. Ban da abin Mami, ita ba ta tunanin ma za ta yi auren, wane namijin ne zai aure ta bayan ta gama wulaƙanta duk masu kaunarta domin Allahn? Ta rasa dalilin da a ƴan kwanakin nan take jin sauyi a jiki da kuma kwakwalwarta. Wannan ne ya sa Fadeel samun rangwame daga wurinta.

Ɓangaren Mami kuwa ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu. Meke shirin faruwa haka? A duniya ba ta kaunar Fadeel ya raɓi Humaira kamar yanda bai raɓi Tasleem ba. Kai ba ma shi ba... Sai kuma tunaninta ya katse, ta haɗiyi miyau da ta ji yana mata zafi. Sai kawai ta nufi ɗakinta a gaggauce. Tabbas ta yi sake a kwanakin da suka shuɗe ba ta bayar an ɗoramata sabon aiki ba.  Wayarta ta fiddo ta shiga zarya a tsakar ɗakin tana jira a ɗauka daga ɗaya ɓangaren. Doguwar magana suka yi sai kuma ta hau murmushi hankali a kwance ta katse kiran ta shiga danna wayar karo na biyu inda ta tura kuɗi ga wani akawun lamba. Daga nan kuma ta ji wata irin nutsuwa ya saukar mata.

***
  Ya kwashi mintoci  masu yawa a zaune anan, shigowar su Waleed ne ma ya ɗauki hankalinsa suke hirar makaranta yana biyemusu. Ya gama fidda rai daga ganinta, gefe guda ga tsoron kada a koma ƴar gidan jiya, tunanin da ya sanya gumi tsastsafo masa a goshi duk kuwa da iskar dake kaɗawa a falon har tana kaɗa labule. Sai dai kuma ba zato ya tsinci sallamarta, cikin sauri ya kalli hanyar yana mai amsawa da rawar murya.
  
'Please Fadeel, Control.' Zuciyarsa ta ba shi shawara, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. Ya zubamata idanu, ta  fara dawowa ainahin Humairarsa, fuskar ta ɗan ciko ba kamar farkon dawowarsu ba. Hakanan ta yi haske fayau dama can a bayan har da rashin samun wanka ga uban cizon sauron da tabonsa ya yi ja a jiki da fuskarta.

  Ita kuwa kanta a ƙasa ta ƙarasa ta zauna ɗan nesa da shi, tana ji ya kaɗa su Waleed ciki akan su je su cire uniform dinsu.

"Barka da rana."

Ya yi furucin yana dubanta tamkar ya haɗiye ta. Sai a sannn ta ɗan ɗaga kai ta dube shi. Ganin yanda ya zubamata idanunsa ya sanya ta maida kanta ƙasa ta na jin wani yaam a jikin da ba ta saba ba a baya.

"Ina wuni, ya wajen su Baba?"

Fadeel da ke jin kamar an tsoma shi a aljanna ya faɗaɗa murmushin fuskarsa yana hamdala a ƙasan ransa. Dama komai ɗan hakuri ne, idan ka yi to fa zai wuce. Ya shanye wulakancin da zagin, yanzu ga shi nan ya soma cin galaba.

"Kowa lafiya kalau Alhamdulillah, Sisterna ma ta zo daga Adamawa. In sha Allah zuwa gobe za ta zo ku gaisa."

Sai ba ta watsa masa ƙasa a ido ba ta amsa da toh. Shiru ya biyo baya, a ɓangaren Fadeel ba ya so ya faɗi abin da bai yi daidai da ra'ayinta ba ta sauya fuska ta miƙe ta bar shi anan, ita kuwa godiya take son yi mishi don su yi sallama ta koma ciki amma ta rasa ma ta inda za ta fara sai can da ta ga ba shi da niyyar ce mata uffan sai aikin kallon da ba za ta ce yana ba ta haushi ko kuma faranta mata ba a lokacin, ta daure ta soma magana.

"Mun gode bisa dukkan ɗawainiyar da ku ka yi mana, Allah ya ƙara arziki."

"Ban yi abin da za ki godemin ba. Ke kika yi wanda zan godemaki. Nagode sosai and I..."

Sai kuma ya yi saurin haɗiye zancensa, ya san komai na tarihin Humaira a sannan daga bakin Raihana, ya san ba ta jin turanci amma kuma dai kalmar I Love You ko yaro ƙarami da bai je makaranta ba ya sani. Shirun da ya yi ganin zai yi taɓargaza ne, gaba ɗaya ji yake da ace Humaira za ta ba shi dama, zancen aurensu kawai za a yi. Ya sani hatta da Abbanta ya buƙaci a ba shi lokaci kaɗan yaransa su dawo cikin nutsuwa sai a haɗa auren Ummita da na su, shi ne a karon kansa ya roƙi alfarma a kyale Humaira ta amince da batun aurensa da kanta. Yana kuma ji a jikinsa hakan ce za ta kasance daga yanayin sauyin da ya gani tattare da ita.

"Shikenan?"

Ta katse mishi tunani, ya É—an lumshe idanu sannan ya buÉ—e su a cikin nata, ta kauda fuska ta yi shiru.

"Toh, zan koma bakin aiki, dama zuwa nayi na duba lafiyarku. Ki gaishemin da Ummita da mutan gidan. Allah ya ƙara lafiya."

Ta amsa da amin, cikin sanyin muryar ta ce.

"Zan fadamusu. Nima ka gaidamin Æ´ar uwarmu, sai ta zo goben in sha Allahu."

Ambaton ƙanwarsa Hannatu da ƴar uwarmu da ta yi ya sanya shi jin tamkar yana tafiya a iska tsabar mamaki da farin ciki. Ya ji dadin wannan lamarin sosai.

"Nagode."

Hakan ya furta kawai sannan suka miƙe kusan lokaci guda, sai da ya ga shigewarta sannan shima ya juya yana murmushin da har haƙoransa suka bayyana, ga duk wanda ya ga fuskarsa ya san yana cikin farin ciki da annashuwa.

***
Washegari Mami ta tashi da aikin girki na tarbar Futuha wacce ta yi waya ta sanarmata dawowarsu a ranar. Daga Dubai sai da suka je Saudia suka yi Umarah kafin su juyo. Humaira ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen shiga kicin ɗin din taimaka mata da aiki, zaman kaɗaicin babu abin da yake jefa ta ciki sai kogin tunani. Ummita ma ta fito falo kasancewar akwai wuta ta kunna tashar Saudia tana kallo.
Gaba É—aya samarin gidan sun dawo, Mubarak da ya kammala shima yana gida hakanan Yassar da Dawud wadanda sun fi sati da dawowa daga Camp suna nan tare da su. Anan Kano aka yi posting É—insu inda zasu yi service.
Daga Humairar har Ummita ba su ƙara samun matsala da su Yassar ba, musamman Humaira wacce a baya suke ƙi sosai, ita hakan ma har mamaki yake ba ta. Tsakaninsu gaisuwar mutunci, wasu lokutan har su ɗan tsoma ta a ciki idan suna ƴar hira. Har a lokacin ba ta saki jikinta da su ba don ba ta saba da hakan ba.

Suna girkin Ladidi na taya ta murnar yanda ta soma sakin jikinta tamkar a baya. Raihana ta shigo kicin din kamar an jefo ta har Mami na mata faÉ—a.

"Ku yi hakuri. Humaira, Yaya Fadeel ya kira Sister dinsa Hannatu tana hanyar zuwa."

Gaba ɗaya ta manta da wani batun zuwansu, Mami kuwa haɗe rai ta yi ba ta ce uffan ba har sai da Raihana ta ƙara magana.

"Ki je ki É—an sauya kaya don Allah. Kar ta ganki da Tshirt."
Chapter 52 · 0% Book details