← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 71 OF 101

Sashe 71

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 7 min read

Tana fadin haka ta ture ta ta yi gaba tana kwankwasa ƙofar itama ta bi bayanta tana dariya. Koda suka shiga da nishaɗinsu, tana ji Jannat na hirar ɓatancin sunan da aka yi musu amma ta yi banza da ita musamman ganin har da rainin hankali a zancen don tana yi tana dariya har da cewa wai wa ya sani ma ko dagaske ne tunda abu a duhu babu wanda ya san gaskiya sai su biyun da abin ya faru da wadanda aka kira da suna kidnappers din. Duk yanda ta shiga da walwala sai da Jannat ta rushe wannan farin cikin, shiyasa ta dinga kaucewa haduwarsu tun da aka ce ta zo amma yau gashinan zamansu inuwa guda ya janyo tana gasa mata zantuka marasa kan gado. Haka ta kai zuciyarta nesa ta danne. Tana ji su na hirar gidan Futuha inda Raihana ke ta labarta musu yanayin gidan, Tasleem me za ta yi ban da dariya? Ta dinga kyakyacewa son ranta har sai da Jannat ta yi mata magana. Raihana kuwa duk yanda ta kai da yiwa Futuha dariyar gidan sai da ta ji haushin farin cikin da Tasleem ta hau yi har da ambaton Allah ya ƙara. Jannat ba ita ta tashi tafiya ba sai dab da magriba, Humaira da Raihana har suka gaji ga tunanin Fadeel da zai zo bayan Magriba. Tuƙin ma yinsa ta dinga yi da gadara da yanga kamar ba ta so sai ka ce ta san da zuwan Fadeel din amma ko kusa ba su sanar mata ba. Don kanta kuma daga baya ta ware hannun sitiyari ta shiga gudu har suka isa gidan. A gurguje Raihana ta sanya Humaira shiryawa. Ummita na daga kwance tana kallonsu sai murmushi kaɗan a fatar bakinta. Inda ta ga da buƙatar gyara za ta yi magana. Duk da halin da take ciki ta yi farin ciki kwarai da wannan sauyi na Humaira akan al'amarin Fadeel.
Humaira ta kammala shiri cikin wani rantsetsan yadinta mai adon maroon da yellow ta yi kyau sosai musamman da ta yafa mayafi yellow sai tashin ƙamshi take yi. Raihana ta so ta yi mata kwalliya amma ta nuna ba ta ra'ayi, ita duk kaffa kaffar da take yi kada ta motsawa Ummita wani lamarin akan Sahabi, ba ta san cewa Ummita kwarai take jin dadin yanda ta sauya ba.

"Masha Allah kin yi kyau sosai."

Fadin Ummita tana dubanta. Ta maida mata martanin murmushin amma ba ta ce uffan ba can kuma ta dubi Raihana.

"Kinga ban sanar da Mami ba, na rasa ta yanda zan faÉ—amata."

Cikin basarwa Raihana ta ce.

"Kar ki wani damu, tana wajen Abba, ke idan ma ta tambaya zan fadamata."

"Toh." Shi ne kawai amsar Humaira ta ba.

***
Wannan karon madadin ta gan shi tsaye a farfajiyar gidan, sai ta same shi a ɗakin saukar baƙi na Abba. Ashe Mubarak ne ya kai shi can, shi suka yi karo ya sanar mata inda yake. A kunyace ta sunkuyar da kai ta nufi ɗakin kai tsaye.
Da sallamarta ta sanya kai ciki bayan ya amsa. Suka ɗan dubi juna ta kauda kanta, ya sha adonsa cikin yadinsa mai tsada fari ƙal ga kuma hula ya ɗora wanda ya yi matuƙar hawa da kayansa. Kallonta kawai yake yi ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba. Ta ƙaraso ta nemi wuri ta zauna can nesa da shi kaɗan tana gaishe shi. Ya amsa mata zuciyarsa tamkar ƙanƙara. Sai kuma ya rasa ta inda zai fara, sai ya ji kamar an ɗaure mishi bakin saboda tsabar shauƙi, ita kuwa ta baza kunnuwanta don son ta ji me zai ce. Can ta tsinkayi muryarsa a tausashe.

"Kin yi kyau."

Ta kasa cewa komai sai murmushin da ta É—an yi. Jin lamarin ta ke banbarakwai, wai ita ce ke yin zance. Abin dai kamar a mafarki.

"Boddo." Ya kira sunan da take matukar jin dadinsa amma koda wasa ba ta taɓa gwada mishi ba. Sai da ya ƙara maimaicin kira kafin ta amsa a hankali. Fadeel ya yi hamdala a ransa, tabbas babu wani abu mai girman da ya fi ƙarfin addu'a. Komai idan ka sanya Allah ciki kuma ka dage da addu'a to fa zai zo ya zama tarihi. Hakan kuma yake fata, wannan ƙiyayyar ta Humaira gareshi ta koma tamkar ba ta taɓa yinta ba.

"Nasan za ki ce Fadeel ya fiye naci da takura. Kiyi hakuri, haka Allah ya yi ni, yadda ban iya ƙin abu ba haka nake idan na so ba, ba na mishi son da nake jin zan iya haƙura da shi yau, gobe ko jibi. Kina daga cikin abu mafi girma da tsada da na taɓa samu a rayuwa, a zatonki zan bari ki suɓucemin?"

Ta kasa tankawa, jikinta ya yi la'asar, sai ta ji ya yi matuƙar ba ta tausayi kwarai har ta ɗago idanu kaɗan ta dube shi, kwayoyin idanunsu suka sarƙe, ya harɗe tafukan hannuwansa guri guda ya tallafa haɓansa gami da ɗan karkata kai kawai yana dubanta. Ta janye ƙwayoyin idanunta gami da sadda kai tana wasa da zoben azurfar yatsarta. So ta ke ta ce ka yi hakuri Fadeel, na sani ban kyautata maka ba ka yafemin. Amma ta ji ta kasa, da wane idanun ma za ta dube shi har ta iya bayan shafi-shafin rashin mutuncin da ta sauke a kansa.

"Aa Boddona, in sha Allahu sai mun kasance a inuwar aure. Sai kin zama mallakina nan ma ba da jimawa ba."

Ya ƙarashe zancen da murya ƙasa-ƙasa. Abin mamaki idanunsa a saman fuskarta, ko kallonsa ba ta yi ba balle ya tsammaci kallon hararar da ya riga ya yi sabo a shi. Wannan sauyin da take yi sai ya ji zuciyarsa n kasa ɗauka, ba kuma wai rashin aminci da shi ba. Ko kusa, sai dai kawai ya kasa sakin jiki yana ganin kamar na ɗan lokaci ne. Duk da haka yana kokarin tunasar da kansa cewa addu'a ce ta kai su ga wannan munzalin ba kuma ya tunanin akwai abin da zai sauke su a kanta. Ya miƙe ya ɗan matso kujerar da take kai ya zauna, tana can ƙarshe kujerar kasancewar mai zaman mutum uku ce, shi kuwa yana gefe ya ba da tazara tsakaninsu. Magana mai muhimmancin da ya kasa sanar da ita ne ya ke ganin ya dace ta sani yanzu. Kirjinsa na bugu saboda fargabar kada ta tada bori kan tsarin bai mata ba. Amma da ya ambaci sunan Allah sai ya samu ƙwarin gwuiwa don haka ya karya bille ya soma magana.

"Humaira, iyayenmu sun yi magana sun kuma tsayar da ranar aurenmu."

Ta ji tsiƙar jikinta ya tashi, ita da aure? Babu wani yanayi da ta ji da ya wuce na sanyin jiki kamar wacce aka yi wa duka. Har wani zufa ne ya yankomata, sai ta shiga maimaita sunan Allah a ƙasan ranta.
Shirunta ya haifarwa da Fadeel wata irin fargaba har sai da ya ji inama bai ce uffan a kai ba. Har ya fidda ran za ta tanka sai ta ƙaryata tunaninsa ta hanyar magana tana dubansa fuskarta na nuni da damuwa.

"Amma ta ya ya zan yi aure na bar Ummita cikin wannan halin?"

Ya sauke ajiyar zuciya jin abin da ta ce, cikin ƙarfafa gwuiwa ya ce.

"Kar ki damu Boddo, idan har wata ɗayan da su Abba suka sanya ya cika, matuƙar aka ɗaura babu wanda zai takuraki da zancen tariya har sai lokacin da kika aminta don kanki. Hakan ya yi maki?"

Ga mamakinsa sai ta gyaɗa kai da ɗan murmushi kaɗan a fatar bakinta. Ai sai ya ji inama yana da damar haɗa jikinsa da nata. Hakan ma da ta aminta da aurennasa ya yi mishi sosai, muddin dai ta zama mallakinsa to sauran duka mai sauki ne. Hakan ya ayyana a ransa. Bai ja ta da hira ba gudun kada kuma a zancen ta yi wani tunanin ta sauya ra'ayi don haka ya zaɓi su yi sallama a wannan gaɓar, yana da tambayoyin da zai so ace ya yi mata na dalilin ƙin shigar ta makaranta ta zaɓi girki da ma dai son jin duk wani abu da ya shafe ta amma ba ya son kwaɓarsa ta yi ruwa sai ya haɗiye kwaɗayinsa ta hanyar yi mata sallama ya miƙe, itama ta miƙe suka fito tare ta ja ƙofar ta rufe. Hannuwansa cikin aljihu ya ke dubanta kamar ya haɗiye.

"Sai mun yi waya. A gaidamin yan uwana."

Ta gyada kai. Har ta soma tafiya sai ta juyo, yana tsaye cak kawai yana kallonta da shanyayyun idanunsa so na fisgarsa. Ta É—an kauda kai daga dubansa ta ce.

"A gaidamin su Baba, idan kun yi waya da Maman Husna ace ina gaida ta."

"Ko na turo maki lambarta? Saƙonnin sun min yawa kada na manta."

Ta É—an murmusa.

"Shikenan sai ka turo."

Ta juya za ta tafi ya dakatar da ita.

"Boddo."

Tsayawa ta yi ta juyo, murmushinsa ya yi har gefen kumatunsa na lotsawa.

"Ina ji da ke."

Ta yi saurin juyawa ta nufi ciki, sai da ya ga shigewarta kafin ya fice zuwa inda ya adana motarsa yana shafar sumar kansa duniyar na mishi dadi.
Chapter 71 · 0% Book details