← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 31 OF 101

Sashe 31

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Ta yi mata alama da yatsu cewa ta yi a hankali. Nan ta nunamata hotunan da ta aikawa Fadeel da kuma yanda suka yi a waya. Ummita duk sai ya ba ta tausayi.

"Allah Sarki Fadeel, nikam yana burgeni wallahi. Humaira ta tsinci dami a akala take wasa da shi."

Raihana ta yi ƙwafa.

"Rabu da ita, in sha Allahu ba ta da miji sai shi. Itama ai tana sonsa gulma ce kawai."

Girgiza kai Ummita ta yi.

"Bari faɗin haka, kar ki manta jinnu babu abinda ba su sanyawa, Ya Sayyadi ya ce har raba mata da miji su na yi saboda sanyawa ɗaya ƙiyayya da kuma hana zaman lafiya."

"Allah ya karemu da sharrinsu. Itama Allah ya yi mata magani."

Ummita ta amsa da amin.

***
Hajiya Kubra wacce suke kira da Maama, mahaifiya ga Ibrahim (Ibb) ta dubi Fadeel tana mai faɗaɗa murmushinta har ana ganin haƙorin makkanta mai sheƙi.

"ÆŠan Alhajinsa, ganinka sai an yanki tikiti."

Fadeel ya shafi ƙeyarsa yana murmushin jin nauyi, yau gaba ɗayansa cikin nishaɗi ya ke ji, babu hoton dake yawo a kansa sai hoton Humaira da ya gani tana murmushin da wushiyarta ta bayyana zahiri.

"Ina nan Maama, ai ko ba ku yanka ba ni fa É—anku ne."

Ta yi dariya aka ƙara gaisawa. Suka ɗam taɓa hira bayan an kawo mishi ruwa da lemu sai snacks ya ci. Ibb ba ya nan sun ɗan fita da Daddy. Maama ta gyara zama sosai babu alamun wasa a fuskarta ta ce.

"ÆŠana kamar yanda ka ce ni uwa ce gareka, ina son ba ka wata shawara kar kuma ka ce na maku katsalandan kai da abokinka."

Duk da cewa tuni ya ɗago zancen, tunda ai tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi sai ya tattaro dukkan hankali gareta ya ajiye kofin dake hannunsa.

"Maama kin isa da mu ɗin ne, uwa kuma da ta isa, ai ɗa ba ya taɓa wuce faɗa daga gareta ba ballantana kuma nasiha ko shawara."

Maama ta yi murmushi, hakika kalamansa sun burgeta. Ta jinjina kai.

"Wannan hakayake Fadeel, maganar ba wata mai tsawo ba ce sai ta buri da mafarkan iyayenku. Mun yi hakuri mun zuba idanu, daga kai har É—an uwanka kamar babu niyyar faranta mana. Kun fi kowa sanin bamu da burin sai na ganin kun fidda matar aure amma shiru kamar maye ya ci shirwa. Ba mata a garin ne?"

Ta ƙarashe da ƴar dariya, shi ma murmushin ya yi mai dauke da damuwa.

"Akwai Maama, ku yi hakuri, in sha Allah zamu yi. A taya mu neman zaɓin Allah. Mun fi kaunar farin cikinku sama da komai."

"Shikenan, Allah ya yi maku zaɓi mafi alheri da albarka."

Ya amsa da amin. Yana shirin tafiya sai ga Ibb ya shigo tare da Daddy. Shi ma fararen kayan ya sanya irin na amininsa. Nan kuma hira ta dawo sabuwa, Daddy ya hada su ya kara yi musu zancen aure. Ya jima a gidan kafin ya fito tafiya. Sai da suka karasa har bakin motarsa sannan Ibb ya dube shi.
"Wai lafiya? Yau kamar wanda aka yi ma albishir da aljanna sai fara'a kake yi. Akwai labari ne?"

Fadeel ya ƙara fadada murmushinsa. Hotunan Humaira ya nunamasa, da mamaki Ibb ya dube shi murna fal ciki.

"Dagaske ne abin da nake gani? Ita da kanta ta turomaka? Ah lallai dole ka yi fara'a, ka ce tsayuwar darenka a azumi Allah ya karɓa."

Fadeel ya É—an basar ta hanyar sosa kara hanci.

"No ba ita ce ta aikon ba, Raihana ce ƙanwarta."

Nan fa Ibb murna ta koma ciki, ya ja guntun tsaki.

"Allah ya yayemaka wannan makahon son Fadeel. Ka ture batun wannan yarinyar ka nemi matar aure ta gaske please. Ni dai dab nake da kawowa su Daddy matar aure."

Fadeel ya bude mota yana murmushi yana kallom hanya har wasu Æ´anmatan da suka zo giftawa suka maida mishi martani don a zatonsu da su yake. Ya kauda kai.

"Shikenan, ka ga na huta sai ka yi auren ka samar mana yara da wuri, su Alhaji idan su na ganin jikokinsu hankalinsu zai kwanta ni kuma na cigaba da jiran abar ƙaunata."

Ibb ya harareshi.

"ÆŠan iska, sai aka ce maka daga auren sai haihuwa ko?"

Fadeel dai dariya ya yi.

"Toh me ya yi saura idan har ba juya ba ne kai?"

Shima Ibb dariyar ya yi. Anan yake faÉ—awa Fadeel wata ce Salma, likita ce kwararriya ta mata. Sun jima su na abotar da ta juye ta rikiÉ—e zuwa soyayya a yanzun. Ya yi shiru ne don ya gani ko abin zai É—aure.

"Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da alheri." Cewar Fadeel.

"Ameen, kai ma Allah ya kawomaka mace tagari da za ta mantar da kai Humaira."

Ya yi murmushi ba tare da ya amsa ba ya shige mota abinsa. Ibb ya matsa shi kuma ya ja ya tafi. A ransa ya na auna addu'ar Ibb din, ba kuma ya jin mai tabbatuwa ce.

***
Murja ce zaune gaban Malam wanda tun a waya ta zayyane mishi komai, batun Fadeel da kuma Humaira wacce ta ke buƙatar a shiga tsakaninsu a raba su gaba daya, ya kasance son da yake yiwa Humaira kacokam ya dawo kanta. Malamin bayan ya kammala aikin da duk abin da ya kamata ya mata umarnin ta zo. Tun da ta zauna take cike da fargaba na tunanin me zai fito a bakinsa, malamin yayarsu ce tana yawan zuwa karɓomata saƙo wurinsa, ba ta taɓa zuwa don aikin kanta ba sai a yanzun da soyayyar Fadeel ke neman haukata ta.

"Akwai hatsari a kanki babba idan kika ce za ki raba waÉ—annan mutanen."

Ji ta yi cikinta ya kaɗa, ranta idan ya yi dubu ya ɓaci har wani duhu take gani ya mamaye idanunta.

"Akwai hatsari fa ka ce? Toh wallahi na shirya tunkararsa nidai, zan aikata ko mene ne duk tsananinsa don Fadeel ya zama mallakina."

Malam ya yi shiru yana dubanta gami da auna irin rashin hankalinta.

®️Rufaida Umar.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Assalamu alaikum, ina mika saqon taaziyyar rashin member makaranciyar Dukan Ruwa kuma masoyiyata ta don Allah, Aysha Salisu. Allah ya gafarta zunubanta. Ya sa aljanna makoma, ameen.

****

Malamin ya jinjina kai.

"Aa Murjanatu, kar ki zo gaba kiyi kuka da ni, jimawar da muka yi da da yar uwarki da irin alherin da nake samu a wajenta, ba zan yi abin da zai cutar da ke ba. Ki je nan da kwanaki uku ki kara nazari, idan kin shirya fuskantar kowane ƙalubale da zai biyo bayan aikin, sai ki dawo."

Murja ta yi jim, a yanda ta ke jin Fadeel gani take babu wani abu da ba za ta iya jurewa ba. Can ta nisa ta ce.

"Malam, idan har dai ba hauka ba ne ko wata nakasa naji na gani zan jure."

Ya yi wani murmushi.

"Kina da gaggawa Murjanatu, eh ba nakasa ba ne, amma rushe maganar wannan yarinya a zuciyar Fadeel ba zai amfaneki da komai ba sai halaka. Abin nufi, har abada kema ba lallai ki aureshi ba, idan kuwa aurenku ya tabbata toh fa har ki mutu ba zai kusanceki ba. Ke za ki kasance kare ma ya fiki daraja a rayuwarsa. Ki yi hakuri, ita gaskiya ɗaci gareta kuma kin fi kowa sanin ni Malam Tanimu ba na ɓoyewa mutum koda kuwa idan ya aikata abun zai haɗu da mummunan bala'i sai na sanarmaka idan ka ji ka gani a tafi a haka, sai a tafi. Kin yarda kin amince?"

Ta ji zufa na karyomata, ita da take burin rayuwa mai kyau da inganci da shi? Take burin ta mallake shi su ji dadin tarayyar aure? Kai sam ba ta yi imani da faɗar Malamin nan ba duk kuwa da sanin da ta yi mishi ba na yau ba don haka kawai sai ta ce ya ba ta lokacin shawara, daga haka ta miƙe ta bar wajensa da nufin sauya sheƙa. Wannan Malamin ba abokin tafiya ba ne, ba zai mata yanda take so ba.

***
Sun yi yawo sosai gidan ƴan uwan Abba, wannan kam ita da Ummita ne sai ko Raihana da ta jera da su. Si Futuha kuwa daga gidajen ƙawaye sai ko ƴan makarantarsu na sakandire da suka haɗa reunion aka ci aka sha. Sun je hawan sallah Humaira ta sha kallo, abin ya yi matukar burgeta. Ta dauki hotuna sosai a wayanta, ita kuwa Raihana babu kwalliyar Humairar da ba ta ɗaukarwa Fadeel ba, daidai da bidiyonta a wurin kallon hawa sadda take murmushi da haska bidiyon sarki ta ɗauka ta tura wa Fadeel. Sosai sallar ta yi mata dadi, ta kuma yaba da kalar wasannin da aka yi.

***

Zaune take a falo tana ta kallon yanda a hankali ta soma samun mabiya a shafin Instagram, hakanan hatta a facebook da Raihana ta budemata ta sanya ta a shafukan tallace-tallace na sana'o'i nan ma ta samu abokantaka da mutane da dama, sai dai babu wanda suka taɓa hira a akwatin sirri (inbox). Ita kaɗai tana ta murmushi ganin yanda hotunan girke-girken da ta yi yake samun likes da kuma comment. Jannat ta shigo falon da rawar jikinta, dawowarta kenan daga gyaran gashi. Su Futuha sun fice shoprite sun kai yara, Ummita ta je albarkacin yaran Jannat da suka sa rigimar su sai an tafi da ita don ba karamin shaƙuwa suka yi ba.
Humaira ta É—ago tana dubanta don har ta tsorata ta, sam ba ta tunanin ta yi sallama. Su na cikin sati na uku ga sallah, a yanda ta ji daga Ummita, bai fi kwanaki uku ya rage Jannat ta bar gidan ba wannan yasa take ta shirye-shirye. Kallo É—aya Jannat din ta yi mata ba ta ko amsa sannu da zuwan da take mata ba ta yi gaba, har ta É—an yi nisa ta dawo baya tana yatsine fuska.

"Ke, ki dafamin abu marar nauyi yanzu."
Chapter 31 · 0% Book details