← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 101 OF 101

Sashe 101

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Kwanaki uku, abu dai kamar wasa ta ga dagaske ne, tsakaninta da Abba sai idan ta gaida shi ya amsa, babu sakin fuska balle har ta samu damar wata maganar. Zai shirya ya yi ficewarsa ko abincinta ba ya saurara. Jannat kuwa ta tattara nata ya nata ta bar gidan. Anna abin ya taɓa ranta ta kuma rantse sai ta yiwa Abba magana akai. Mami dai ta hana ta amma ina! A rana ta huɗu ne da tafiyar Jannat, ta tsaya a hanyar da ta san cewa dole ta nan din yake zuwa ya fice. Yana fitowa kuwa ya gan ta. Ɗan durƙusawa yanda ya saba ya gaishe ta a mutunce. Ta amsa tana cin magani gami da gyara tsayuwa sakamakon ƙafa da ta matsa mata.

"Isuhu, na yi shiru ne saboda ban sani ba ko Maryama za ta iya kokarinta wajen ganin ta sa ka janye dokar da ka kafawa Auta na zuwa gidannan sai na ga hakan ya faskara. Wannan ne ya sanya ni zuwa da kaina domin na ji ba'asi. Haba Isuhu, duk wani abu da yarinyar nan ta aikata sharrin shaiɗan ne, ta ba da haƙuri ta kuma nemi gafarar yarannan (acewar Annar kenan), toh na mene ne za ka hana ta zuwa inda uwarta take fisabilillah idan dai ba ni ɗin ka yi shirin kora ba?"

Abba sosai ya yi mamakin son zuciya irin na wannan matar, wato don ba nata aka yiwa ba? Kai shi yanzu dukkanin dangin Maryama ma tsoronsu yake domin su na shayar da shi mamaki. Yanzun ne ya ƙara fahimtar cewa ashe dai ba tsanarsu wasu a danginsa suka yi ba, ashe Hajiya Maijidda ba a banza ta tsani ganin Maryama ba. Ita din ta jima da sanin ainahin fuskar Maryama.

"Isuhu ka yi shiru ina magana?"

Anna ta buƙata a ɗan zafafe, abin da bai taɓa gani kenan a tare da ita ba. Koda dai ya sani cewa duk tafiyarsu guda.

"Kiyi hakuri Hajiya, ni dai Isuhu idan har wannan gida ikona ne, toh Jannat ba za ta ƙara shigarsa ba. Ban raba maku zumunci da ita ba tunda taku ce, amma idan dai a wannan gidan ne toh sai dai ku yi hakuri. Duk sadda kike da buƙatar zuwa wajenta in sha Allahu mota da direba ba zai gagareni samar maki ba."

Anna ta saki baki galala, yau Isuhu da kansa ke yi mata musu? Wato dai ba a shaidar É—an kuturu sai ya girma da yatsa.

"Ai shikenan, tunda dai hakanan ka ce nima yanzu dole zan haƙura da zaman gidanka. Allah ya bamu alherinsa."

Abba ko a jikinsa ya miƙe.

"A gafarceni Hajiya, amma ni dai na gama yanke magana. Ban ce ki bar gidana ba saboda ba ki yimin komai ba.."

"Aa, wannan dai kora da hali ne. Ba Auta kaɗai ka kora ba, nima dama watakila kana da niyyar kora ta tunda iyakar saninka ai ba zan rayu a gidan nan babu Auta ba. Nima dai watakila kana ƙullace da ni, babu yanda ka iya ne shiyasa."

Abba ya É—an yi murmushi mai ciwo jin abin da ke fita daga bakin ÆŠAN ADAM mai mance halacci, mai son kai da son zuciya. A yau dai Anna ita ke korar kanta daga gidansa saboda son rai irin nata.

"Ni dai Allah ya sani, ban kore ki daga gidannan ba saboda na dauke ki tamkar uwa a gareni. Ina mai baki hakuri bisa abin da na yi idan bai maki dadi ba. Ki yi hakuri hakan ba zai sauya komai ba."

Daga haka ya sa kai ya fice, yana jin Anna na salati da kiran wai dama can ya gaji da ciyar da ita amma bai ko juyo ba sai murmushin baƙin ciki da tausayin kansa da ya ke ji na zaɓen tumun daren da ya yi tun a farko. Kewar iyayensa ya ji na mamayarsa, ashe dai iyaye ba za a rabu da kewarsu ba musamman ma irin nasa nagari masu halayyar dattako. Ya yi musu addu'ar samun rahmar Ubangiji kana ya shiga mota. Madadin zuwa kasuwa sai kawai ya fice zuwa gidan ƙanwarsa Baba Amina.

***
Ya iske ta zaune, Raihana ba ta nan ta fice jarrabawa, hakanan sauran Æ´anmatan yarannata su biyu su ma sun fice. Ita daya ya iske. Tana ganin da yanayin da ya shigo nan da nan hankalinta ya tashi, ta kira sunan Allah a zuci da kuma fili.

Bayan ya zauna ta gaidashi. Kawai daga tambayarsa ko lafiya, ya soma zubar da hawaye. Baba Amina mace mai saurin kuka don har Abba na cewa su Humaira ita suka biyo, nan da nan ta soma kukan itama.

"Yaya lafiya? Ko mene ya yi zafi maganinsa Allah."

Ya jinjina kai. Ya ba ta labarin dukkan abin da ya sani a yanzu game da Mami har da yanda suka yi da Anna. Ya kara da fadin.

"Amina na yi zaɓen tumun dare."

Baba Amina zuwa lokacin kuka take yi sosai. Tausayin Abba da kuma tashin hankalin da ta ji na wai Mami na neman rayuwarsa ya sanya ta wannan kukan. Abban da ya zo don ya samu a rarrashe shi, sai shi ne ya koma rarrashin. Ta mike ta hado masa kayan shayi da abinci, ta yi mamakin yanda ya zage ya ci kuwa, tausayinsa kwarai ta ji, har ta kasa hakuri ƙarshe ta dube shi.

"Toh yanzu Yaya hakanan za ka yi zaman rayuwa da ita? Nikam hankalina sam bai kwanta ba, shikenan ka haramtawa kanka cimar gidanka saboda Maryam?"

Ya dan yi murmushin yaƙe bayan ya kora ruwan shayi mai dumi a cikinsa.

"Amina kenan, wallahi ganinta ma bana son yi. "

Takaici ya kama Baba Amina.

"Toh Yaya ka yi aure mana."

Ya É—an yi jim sannan ya jinjina kai.

"Tsoron matan nake Amina, ba zan iya auren kowa ba a yanzu."

"Ba duka aka taru aka zama É—aya ba Yaya, ni wallahi dama na jima ina yi maka sha'awar auren wata baiwar Allah, da ace za ka bani dama ni zan san yanda zan shawo maka kanta ta amince."

Ya yi murmushi.

"Wato dama kin dade kina so na yi auren kenan."

Ta yi murmushin itama.

"Eh toh, gaskiya kusan hakan ne. Tun da na soma gane wace ce ainahin Maryam na ji haka kawai ina son zamanka tare da wata bayan ita."

Abba ya girgiza kai.

"Mutum abin tsoro ne Amina. Kedai kawai Allah yasa mu dace."

Ta amsa da amin tana mai kara tausayawa rayuwar Yayannata. Haka ya yi mata sallama ya tafi bai ko damu da sanin ko sunan wacce ta zaɓar masa ba. Kusan ma bai dauki lamarin da muhimmanci ba. Ita kuwa ta dauke shi da matukar girma, ta kuma dauki ɗamarar dagewa da addu'a har kafin ta tunkari ɗan uwan mahaifinsu Baffa Tukur da zancen, tana son ta ga tabbatuwar lamarin ko don samar da farin ciki ga yayanta da kuma ganin yanda Maryam za ta ƙara bayyana munanan ɗabi'unta kowa ya ankara da shi. Ai tunda har Raihana da kanta ta bude baki ta ce dama Abbanta ya kara aure, ta san cewa lamarin babba ne.

***
Tafiya ta yi tafiya har aka kwashi watanni biyu, Humaira cikin ikon Allah ta samu juna biyu, wani irin tarairaya na musamman ta ke samu daga Fadeel, a wannan watanni Abba ya hana ta taka koda harabar gidansa da sunan ziyara, acewarsa ta yi hakuri da zuwa gidan zuwa wani lokaci. Ita kuwa zuwa lokacin ƙarshen damuwa ta shige shi domin so take yi ta ga Abbannata saboda ta sani tabbas yana cikin damuwa. Ta ji komai daga bakin Raihana.

Ganin wannan ne yasa Abba amincewa da zuwanta, ranar ko da ya kasance na zuwannata bai fita kasuwa ba, zamansa ya yi a gida. Yana zaune a falonsa Tasleem ta shigo gaishe shi, ya mance rabon ma da ya ganta don har mantawa yake yi ta a gidan, ya bita da kallo sosai ta sha zumɓulelan hijabi tana ta kare cikinta wanda bai kai ga fitowa ba amma hakanan take tsarguwar kada Abban ya ankare da shi. Shi kuwa ramar da ta yi yake bi da ido. Ya amsa gaisuwarta a daƙile ya kauda kai.

"Abba don Allah ina son É—an wani abu zan siya kayan sanyawa na ciki."

Ya ɗan yi jim, tabbas yanzun ya sani tana da hakki a kansa, idan bai mata ba yana tsoron ɓacin zamanin nan. Ya dan kara dubanta, sai ta ba shi tausayi. Yarinya ƙarama ta haɗu da zawarci saboda kishin banza da ta ɗorawa zuciyarta har ya kai ta ga marin uwar mijinta.
Hannu ya sa a aljihu ya fiddo kudi ya ƙirga dubu goma ya miƙa mata. Ta yi mamaki sosai don ba ta ma zaci za ta samu kamar hakan ba. Ta yi godiya, har za ta tashi sai ya kira ta, dawowa ta yi ta zauna jiki a mace. Zuwa yanzu ta gaji da zuwa wajen Babandi sai dai ta rasa dalili idan har ya dauki waya ya kirata toh ko me take yi ba ta kammalawa tana rawar jiki za ta je wajensa. Nasiha mai ratsa jiki Abba ya yi mata game da rayuwa da kuma faɗa akan rashin alfanun zaman mace babu aure. Ya nuna mata hakan ba zai ƙare ta da komai ba, yanzu idan babu shi a duniyar wa za ta tambaya? Abba dai sosai ya yi mata faɗa akan ta tsoraci Allah a lamuranta, kada ta bari son duniya da abin da ke ciki ya rufe idanunta. Tasleem jikinta ya ƙara mutuwa, ita fa dama yanzu ta gane dama kyau ba ya kawowa mace miji mai arziki balle kuma surar jiki. Kawai ta gane kaddarar mutum ce komai dake faruwa, yanzu ta bar yiwa kanta hangen miji irin na Humaira don ta san ba za ta samu ba, ita babban abin da ke ramar da ita bai wuce cikin Babandi dake jikinta ba wanda ta ƙi ta zubar saboda tsananin tsoron abin da zai biyo baya tsakaninsu idan ta zubar.

"Ƴar uwarki tana nan shigowa yau za ta kawomana ziyara. Ki sa Ladidi ta samar mata wani abin."

"Abba wa?"

Ya dube ta.

"Humaira."

Ta ji kwalla sun cicciko mata, ta sani Humaira ta zama hajiya, ko ba ta ganta ba ta san za a ganta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa ba kamar ita ba da ta rasa hakan. Gatanan ba wan ba ƙanin, ƙarfi da yaji ta zama kwartuwar Boka. Kullum cikin aikata zina take yi babu ji babu gani.

"Toh." Abin da ta firta kenan ta mike ta tafi.
Chapter 101 · 0% Book details