Sashe 39
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
***
A sati guda kacal, gidan gaba daya an watse sai mutan gidan. Mubarak ma wanda bai fi watanni biyu suka rage ya kammala karatu ba ya tattara ya koma a yayinda a gefe daya Yassar da Dawud ke shirin tafiya bautar ƙasa. Gidan ya zama gwanin dadi ga Humaira, babu wani da ke matsa mata yanzu balle kallon banza. Raihana da Ummita sun je gidajen amare ita kuwa ko leƙe ta ƙi yi. Ta dai yi musu cincin bisa umarnin Mami, an kai wa kowaccensu gidanta saboda tarbar baƙi.
Raihana da Ummita suka maida hankali a karatu don sun soma shirin jarrabawar fita aji SS2 zuwa SS3. Ita kuwa Humaira a sannan ta kammala darussanta na makarantar Anti Laila, hakan yasa koyaushe tana gida idan har ba wani aikin ta samu ba. Sai ya kasance ita ke girkin gidan, a cewar Mami, hakan zai É—ebe mata kewa. Ta kuma yarda da hakan dari bisa dari, ita kanta ba ta son zaman shirun don yana jefa ta tunani kala-kala.
Ranar ta kama laraba tana tsaye tana shanyar undies dinta a gefe kuma tana sauraron waƙar Ala mai suna Shahara. Jin waƙar ya tsaya ne yasa ta fahimci kira ne ya shigo. Ta ɗan goge hannunta da sauri ta dauka ganin baƙuwar lamba a ranta tana fatan ya kasance oda ne ta samu don dazu suke magana da Mami take nuna rashin jin dadin yanda kwanaki biyu shiru ba'a samu ba. Da sallamarta ta ɗaga. Aka amsa daga can, muryar mace ce. Suka gaisa a mutunce. Nan take shaida mata ta samu lamba ne daga ɗaya daga cikin kwastamominta, tana son a yi mata snacks na birthday din yaronta da za ta yi. Nan fa Humaira ta ji dadi sosai, ba ta kawo kowa a kwanyarta ba sai Hajiya Rukayya, ita ce mai kokarin haɗa ta da mutane. Suka yi magana ta lissafa mata kalolin snacks din da take yi, ita kuma ta zaɓi kala uku. Nan ta fadi adadi. Suka yi sallama da zummar za ta turo rabin kuɗin, rabi kuma idan an kai za ta cika. Ta bukaci Humaira ta turamata acc no ta text.
Da wannan farin cikin ta karashe shanyar da ta fara, ta dauki bokitin ta shige gidan ta kofar kicin ta baya. A falo ta hadu da Mami. Ta sanar da ita batun odar da suka samu, Mami ta ji dadi kwarai.
***
Ita kuwa Anti Amarya tana ajiye wayar ta dubi Fadeel da murmushi saman fuskarta ta ce.
"Yauwa mun yi magana. Zan tura mata kudin yanzu idan ta aiko."
Ya É—an murmusa.
"Ok Anti. Bari na wuce ofis, sai na dawo."
"Toh Allah ya ba da sa'a."
Har ya soma tafiya ta kira sunansa, ya juyo.
"Amma meyasa ka ce kar na ambaci sunanka?"
Ya yi murmushi cikin son nemo abin faÉ—i can ya ce.
"Saboda ba za ta gane ni ba, ba ni ke yin odar ba. Sister Rukayya ce ke yi mana. Idan kika ce Haj Rukayya za ta san ta."
Cikin gamsuwa Anti Amarya ta amsa. Daga nan shi kuma ya fice. Murja dake jin su tana daga dinning table a zaune, ta bishi da kallo. Yana fita ta yi saurin karbar wayar Anti Amarya, tana tambayarta me za ta yi, babu amsa. Sai da ta kwafe lambar Humaira fes sannan ta adana a wayarta.
"Me za ki yi da lambar?"
Ta dan sha mur.
"Ina tunanin ita ce budurwan nan tasa da yake mutuwar so."
Dariya Anti Amarya ta yi.
"Kin samu matsala Murja, me zai yi da ita toh? Nikam jikina bai ba ni hakan ba. Daga jin muryar wannan É—in ma kin girme ta. Ba na ji a gaskiya zai kula yarinya, yaron ba ya son raini tun farko idan kin lura."
Murja ta dan ji hankalinta ya kwanta, amma hakan ba zai hana ta bincikawa ba tunda dai ta kasa É—aukar wayar Fadeel, idan ma ta É—auka to ya sanya password ba ka iya shiga.
Tsayuwar mota suka ji a farfajiyar gidan. Murja ta leƙa, ganin Fu'ad tare da Matarsa Kausar wacce a yanzun take dauke da karamin ciki, ta ja guntun tsaki.
"Waye ne ya zo?"
Yamutsa fuska ta yi.
"Wannan dogon ne mana mai hankali a gwuiwa tare da matarsa. Ni na rasa wannan jaraba, mace da ciki sai shegen yawo."
Ta kara jan tsaki. Anti Amarya ta bude baki ganin wannan karfin hali na Murja, mutum da gidan ubansa sai a hana shi kawo matarsa? Za ta yi magana ta fasa ganin Kausar din ta shigo. Ta tarbe ta da fara'a suka gaisa ta karaso. Shi ma Fu'ad ya biyo bayanta hannunsa rike da jakarta na kaya. Bayan sun gaisa ne yake cewa Antin tafiya zai yi na kwanaki uku zuwa Abuja zasu yi meeting da shugaban kamfanin da ya ke aiki shi ne ya kawo ta gidan ta zauna dayake ƴan gidan su Kausar din sun yi tafiya Saudia. Anti Amarya ta karbe ta hannu bibbiyu, ta sa Murja kai mata jaka daki. Murja na kumburi haka ta ja akwatin kayan zuwa ɗakin da babu kowa ciki wanda a baya ya kasance na Hannatu ƙanwar Fadeel.
Kausar wayayyiya ce sosai kuma gogaggiyar ƴar boko da ba ta daukar raini koda na sakan, tun farkon zuwanta gidan ta ga take-taken rashin kunyar Murja wannan ne dalilin da yasa ba sa ga maciji. Ba ta shiga harkarta ko kadan. Murja kuwa ta tsani a duniya ta ga wanda ya fi ta iya kwalliya da komai ma a wuri, balle kuma kuɗi da uban Kausar ya ninka baban su Murja. Gaba da baya dai yarinyar ƴar gata ce kuma gatan da ta samu bai yi sanadin taɓarɓarewar tarbiyyarta ba. Tana da girmama mutane amma ba ta daukar raini. Hatta da wayarta sabuwar version ne na Iphone, hakan ya sa Murja ko kallonta ba ta yi idan tana dannawa tsabar bakin ciki. Wannan ne kuma ya kara mata son ganin ta mallaki miji irin Fadeel, ta san komai take so za ta same shi cikin sauki.
Koda Fu'ad ya bar gidan, Anti Amarya da Kausar sun taɓa hira kadan kafin ta mike ta nufi ɗakin da aka tanadar mata don sosai bacci ne a idanunts. Ciki ya sanya ta zama kamar wata kaasa. Murja ta bi bayanta da harara. Anti Amarya kuwa ta kalleta dakyau ta ce.
"Ke banza ce, ba ki da wayo ko na sakan, yanzu a gaban Fu'ad kike share matarsa? Ke da kike neman gurbi a zuciyar yayansa, to ta ina zai tayaki yaƙin? Ki cigaba da nunawa duniya ba ki da kunya, wallahi ina maki kashedi, ba a samun kan mutane sai an haɗa da kissa. Ai koda ace kina mata ƙin mutuwa bai kyautu ki nuna ba. Daɗina da ke sam babu wayo sai aukin ɓata rawarki da tsalle."
Murja gaba daya sai jikinta ya yi sanyi.
"Kuma fa hakane Anti. Ni wallahi abin ne ya soma yimin yawa. Wanda nake so bai san da zamana ba, na rasa ta ina zan soma Anti."
Wani murmushi Antin ta yi.
"Au, kin dawo hanya kenan? Da ba malamai kika ɗaura ɗamarar bi ba? Ke da ace na bi hanyar malaman za ki ganni a gidannan har i yanzu? Toh uwar Fu'ad abinda ya kashe ta kenan, ta nuna ƙiyayya da makircinta a fili karshenta kuma yanzu ga gidannan ya gagareta zama. Malama duk wata ɗabi'a mummuna watsi da shi za ki yi. Ki sauya salon shigarki zuwa na matan arziki. Wani matsewa ki fiddo sura ba shi ke burge Fadeel ba, idan kin lura yana son ya ga mace mai tarbiyya. Sai kin sauya sosai, ki kuma daina rawar ƙafa a kansa, a hankali nan gaba ko malamin ne sai a bi a shawo kansa. Amma kafin wannan matakin ke za ki sauya takunki."
Murja ta dinga gyada kai tamkar ƙadangaruwa, sosai darasin na Anti Amarya ya shige ta, sai dai ta ina za ta fara? Sun jima Anti Amaryar na ƙara wayar mata da kai tana ɗauka, a karshe dai ta saki ranta sosai ta kuma gane Antin nata ba ta wasa ba ce.
****LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Da taimakon Allah ta kammala aikin odar da aka bata. Kamar yanda ta saba, wannan karon ma waya ta yi akan a zo a karɓa. Aka ba ta lokacin zuwa karfe sha biyun rana. Bayan sun yi sallama ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin wani irin nishaɗi. Hamdala ta yi kamar koyaushe kafin ta fiddo manyan ledojin mai tambarin Deelsha's Delicacies ta sanya.
***
 Murja ta kammala shiri tsaf sai rawar jiki take yi ta je ta ga Humaira me snacks. Kausar na zaune a falo tana taya Khadija da Hanifa (Ɗiyar Saddika yaya ga Anti Amarya) hura balan-balan su na tarawa. Murjar ta fito. Kallo ba ta ishe ta ba, ta gefen ido Murja ta watsamata harara. Daidai lokacin da Anti Amarya ta shigo bayan ta dawo daga farfajiyar gidan inda mai decoration ke ƙawatawa don anan za a gudanar da birthday din Abdulmaleek na cika shekaru uku a duniya.
 "Ni na shirya zan wuce."
"Toh tsaya na baki cikon kuɗinta. Don Allah ki yi sauri kina karɓa ki wuce ki karɓo Cake din."
Ta amsa da toh. Anti Amarya na shiga ciki sai ga Fadeel ya shigo falon riƙe da Abdul yana mishi wasa. Nan da nan Murja ta ji ranta ya yi wani irin sanyi. Ta kuramasa idanu tamkar ta lashe shi musamman ganin yanda shigar jan t-shirt da baƙin jeans ya haskaka shi abinka da fari. Ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama kawai ta tsinci kanta a faffaɗan ƙirjinsa. Sai da ta ji suna gaisawa da Kausar sannan ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta ƙarasa ta zauna ita mai shirin fita. Murya cike da yanga ta ce.
"Yaya Fadeel barka da rana."
Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai, shi a yanzu sam ba ta burgeshi tun sadda Alhaji ya faɗamasa saƙonta.
"Yauwa."