Sashe 21
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Zai yi magana da sauri Mami ta ɗaga mishi hannu, aikuwa abin da take gudu shi ya afku domin Anna faɗa ta hau yi kamar ta ari baki wai laifin na uwarsa ce da ta fifita bare a kan nata. Ganin dai abu ya ƙi ƙarewa Humaira ta miƙe tana mai jan hannun Ummita, itama ba shiri ta miƙe sun kama hanya tana ji Jannat ta kwalawa Ummita kira tana ba ta umarnin ta ja Hassan da Hussein ɗakin su Muhsin ta musu wanka. Ita dai Humaira a fusace ma ta karasa ɗakin don ta matsu ta daina jin muryar tsohuwarnan da ma Jannat din wacce ta ji tsanarta lokaci guda ya rufe ta. Me ake da wanda bai san daraja ta DAN ADAM ba?
Ita kadai a dakin ta yi ta mita tana tsaki. Ji take kamar ta je ta shaƙe wuyansu baki ɗaya. Sai kuma ta yi kwafa tana cije lebbanta, ita kadai ta san damuwar da take dannewa a ranta, amma a kwanakin nan abin yana neman fin karfin zuciyarta. Damuwar bai wuce Abba ba, mutumin da ya kasance bango majinginarta a gidan, wanda shi take yiwa kallon uwa kuma da uba. Wannan kauna da soyayyar da ya nuna mata a farkon zuwanta gidan yanzu ta rasa laifin da ta yi mishi ya sauya. Hira ma ya ƙi ba da fuskar ta ja shi da shi, idan har ita ɗaya ce a falonsa, nan da nan zai hau wasu ƴan aikace-aikacensa kamar gyara takardu ko kuma kiran abokan cinikayya, shaida dai ta cewar ba ya son ta ja wani dogon zancen. Ba dai za ta ce ba ya mata fara'a ba ne, sam a'a, sai dai babu ja a jiki balle har su shaƙu tamkar yanda ya nuna a farkon zuwanta. Toh wanda ma ka ke taƙama da shi bai wani damu da sha'aninka sosai ba ina kuma ga wasu can da har gobe sun ƙi karɓarta matsayin ƴar uwa ta jini? Kewa, kewar Dada da Kawunta duka suka mamaye ta, ba ta san cewar ta soma zubar da hawaye ba sai bayan ta sa hannu saman fuskar ta ji danshin lema. A hankali ta share su, ya kuma yi daidai da shigowar Raihana ɗakin. Ganin hawaye a fuskarta gaba daya sai ta ji ba dadi, ko ita ce ake yaren da ba ta ji tsarguwa yake sanya ta ballantana kuma wannan da dama din sun san ba da kowa ake ba sai su.
"Humaira kuka? Don Allah ki yi hakuri."
Ta fadi a sanyaye gami da zama a gefenta. Jin haka ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo lokaci guda tana gwale idanun da hannu tana share su.
"Ke ba fa komai, ba kuka nake ba. To me aka yi da zan yi kukan?"
Raihana itama murmusawar ta yi ba don ta yarda ba, ta sani Humaira akwai juriya da nuna jarumta, sai dai kuma itama ai Æ´ar adam ce, tana da zuciya ta kuma san meke ma ta zafi. KafaÉ—arta ta dafa.
"Na sani su Anna ba su ..."
"Raihana mu bar zancen, ya wuce wallahi. Ai komai mai ƙarewa ne. Lokaci ne." Cewar Humaira da sauri tana katse Raihana don a duniya yanzun idan da abin da ta tsana bai wuce a ambaci sunan Anna ba. Ta tsani mutum da ba ya ganin kowa da gashi. Tsohuwar sam ba ta riƙe girmanta.
"Kinga kuwa mutuminki koda wasa bai ƙara gangancin kirana ba?"
Maganar Raihana ya katse tunaninta. Cikin rashin fahimta ta ce.
"Wa fa?" Ta yi tambayar don har ga Allah ta mance, sai kuma bayan ta yi ta tuno da Musaddam din. Ta É—an É—aga gira.
"Au, É—an iska za ki cemin."
Suka ɗan yi dariya. A haka su Tasleem suka shigo ɗakin suka iske su. Zuwa yanzu Raihana ba ƙaramin haushi take ba su ba don haka daga kallo daya ba su kara bi ta kansu ba. Tasleem ta nufi sif din kayanta ta buɗe ta sa hannu a ƙugu tana kallo.
"Oh God! Ni wane kaya ma zan saka? Wallahi gaba daya na diririce."
Futuha da ta faÉ—a saman gadonta ta yi dariya.
"Atoh, sai ki ƙure a daka ko ba komai dai wannan ne first meeting ɗinku."
Raihana na jin haka ta mike da sauri ta karasa ga Futuha.
"Wai Hamza D ne zai zo?"
Harararta suka yi a tare, Tasleem ta ja tsaki.
"Ina ruwanki? Ai ke yanzu munafuka kika zama. Ba a sirri da ke."
Humaira ta yi tsam ta mike ta fice a dakin ba ta ko kalle su ba. Cin fuska ne ta san za a yi mata.
***
Rayuwar ta ci gaba da gudana, Humaira tun tana ganin ire-iren bautar da Jannat ke sanya su na ƙare ne abin dai ya ci tura. Daidai da wankin pant da rigar mama su take ba, Mami ke tsawatarwa a wasu lokutan shiyasa kawai su ke hakuri. Idan kuwa ta kai Humaira abin ya ishe ta rantsuwa take yi da ƙari cewar ita ba za ta wanke ba, sai Ummita ke tausarta ta karɓa ta wanke gudun samun matsala.
A wannan gaɓar kuma ba irin takurawar da Fadeel ba ya yiwa Humaira, iyakar ƙularwa ya yi mata, ta yi bakaken maganganun amma ko gezau, kusan kullum sai ya aiko mata da saƙonninsa da ke yiwa Raihana dadi. Ita ke karɓa ta yi ta karantawa har a wasu lokutan ta yi yunkurin ba shi amsa, Humaira ta nuna ba ta so.
Jannat ba ta bar gidan ba sai da ta yi wata É—aya cif. A sannan tuni Mubarak ya tattara ya koma, shima daf yake da kammala Masters. Yayinda Yassar da Dawud suka soma jarrabawar Æ™arshe na kammala degree dinsu a jami'a. Su Ummita ma tuni an koma karatu, Humaira kam ta yi nisa a fannin girke-girke don yanzu girki É—aiÉ—aiku ne ba ta iya ba, kama daga cimar fulawa har dai sarrafa shinkafa da sauran kayayyakin abinci. Girkin gidan zuwa lokacin ya koma kan ta rankatakaf don kowa burinsa ta girka ya ci. Ita kam ko a jikinta, za ta yi girkin ba son jiki amma fa ba ta yarda da wulakancin su Yassar da Tasleem masu cewa su na son cin wani abu daban.Â
Yassar su na dab da kammala jarrabawarsu ne suka tada hankalin Mami lallai sai ta tambayar musu Abba kuɗin da za su haɗa party da abokan karatunsu sai dai duk inda suka ɓullo Mamin ta ƙi asalima cewa ta yi su tuntuɓi Abban da kansu.
Yassar ya mike tsaye yana huci.
"Shikenan, idan Abban ya zo zamu yi mishi maganar. Mu dai gaskiya wannan karon ya sakar mana mu fita kunyar abokai. Wannan rayuwa har ina."
"Ni ban san irin Abba ba wallahi, Mami ke ma ba kya mishi magana, tun farko ai Anna ta fadi, ke kika ba da damar ba ya hidimta mana sosai. Nifa Allah kuwa har kunyar nace Babana mai kudi ne nake, saboda ba a gani a jikina."
Dawud ya fadi yana daga tsaye dafe da kujera. Mami ta yi mishi daƙuwa.
"Karɓi nan Dawud, shi uban naku sa'anku ne da ku ka tsaya ku na wannan ɓarin zancen a kansa? Kuna maganar kamar yau idan kun je gabanshi za ku iya maimaitawa? Kunsan Allah ku kiyaye ni, gaba daya zan tattaraku na kai kararku wajensa tun da dai shi kuna shakkarsa."
Suka ƙara tunzura, Humaira na gefe tana gogewa Mami mayafi bayan ta kammala goge nata kayan dalilin wutar nepa da aka kawo, biki ne Mamin za su je har da ita na ɗiyar mijin Anti Laila malamar girkinta. Katin gayyatar har ita aka ba da ta kuma tabbata saboda mutuncin da suke yi da Shema'un ne, sannan Anti Lailar ma ba ta da matsala ko kaɗan. Gaba ɗaya hirarsu babu wanda ba ya shiga kunnuwanta, tana mamakin irin wannan rashin tarbiyya na su Yassar da ba sa tauna zance kafin su furzar kan kowa ma. Haka suka yi ta mita a karshe dai kiran sallar la'asar ya sanya su tattarawa su bar falon.
"Allah ya shiryamin ku."
Humaira jin furucin da Mami tayi kafin ta wuce dakinta yasa ta amsa da amin, zuciyarta sai ta cika da tausayin Mamin. Matar dai na iyakar kokarinta a kansu. Ba zato ta ji an watso mata kaya saman kafafunta da ke miƙe a harɗe. Ta ɗaga kai ta dubi mai wannan aiki. Futuha ce tsaye daga ita sai vest da leggings. Gashinta a barbaje a gadon bayanta take duban Humairar fuska a yamutse.
"Ɗan dannemin kayan nan kafin su dauke wuta." Kallonta ba ta kara yi ba ta hadiye zafin da ta ji na wannan kalar rashin mutuncin na Futuha. Itama daga haka ta juya zuwa daki, ƙwafa ta yi ta kuma rantse ba za ta yi ba. Hakan yasa tana kammala na Mamin, ta hada da nata kayan da ta goge ta miƙe bayan ta ɗauke dutsen gugar a wajen gudun kar su Waleed su taɓa.
  Dakin Mamin ta soma shiga, sallah ta iske ta tana yi don haka ta ajiye mata a saman gadon kusa da wani haɗaɗɗen leshinta peach colour da ya sha adon duwatsu, ya hau sosai da mayafin. Humaira har sai da ta murmusa don tuni ta hango Mamin a ciki, karshen kyau ko ba a faɗa ba ta sani kalar da kuma kayan za su karɓe ta. Abar ka da farar mace.
Koda ta shiga É—akinsu Tasleem na tsaye tana fente fuskarta da hoda. Ita kuwa Raihana tuni ta shirya tsaf cikin wata maroon atamfa mai haske an yi adon yellow colour jikinta sai dai bai yi dau ba. Tana tsaye ta karkace sai hotuna ta ke yi a gaban window. Futuha da alama tana bandaki. Suka dubi juna da Raihana, da wani irin zumudi ta karkace hadi da É—an É—aga gira.
"Ya? Na yi kyau?"
Humaira ta yi mata murmushinnan nata mai fiddo da zahirin kyawunta.
"Kin fito tsab. Masha Allah."