Sashe 9
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
A can kuwa Humaira duk ya takura mata, ita ba ta saba da wannan rayuwar ba. Kawai wani garjejan saurayi ya zauna yana jan ta da hira ba hadin uwa da uba, ita kam abin ya girmi kanta. Ta kula bai ko damu da jama'ar falon ba waɗanda su din ma kallonsu kawai suke jifa-jifa su na mayar da hankalinsu ga tv. Tambayoyi yake mata iri-iri, amma ba ƴar Mami ce ke ba? Yaushe ki ka zo? Karatu kike? Da dai sauransu ita dai eh ko aa kawai take ce mishi duk ta takura. Haka Mami da Hajiya Lubna suka sauko, ganinsu ya sa ya miƙe yana shafar ƙeya.
"Wai Kabeer ina aiken da na maka ne? Idan ba za ka je ba, ka fadamin na aiki Bala direba."
Hajiya Lubna ta faÉ—i rai bace tana watsa mishi harara, sarai ya gane manufarta, amma shi kam yana ji a ransa ko karatu Humaira take yi zai iya dakon jira ta kammala ya aure ta. Ya lura auren jari Hajiyartasa take so ya yi.
"Sorry Hajjaju, bari na tafi. Mami ku gaida gida, sai na tako har falonki na ƙara gaida ki."
Mamin ta yi dariya.
"Ai babu laifi Kabeer, ko da wacce ka zo ka shiryawa amsar da za ka samu."
Ganin ta É—ago shi ya fice yana Æ´ar dariya gami da faÉ—in.
"Na shirya Maminmu, amma dai ba zan ja baya ba."
Mamin ta ƙara darawa. Humaira ta miƙe suka kara yin sallama da Hajiya Lubna, har farfajiyar gidan ta rako su. Humaira dai har ta ɗan kwashe mintuna a mota ba su gama tsayuwarsu a bakin ƙofar falon su na tattaunawa ba, ba ta san me suke cewa ba dakyar dai Mamin ta taho ta shiga motar suka tafi.
***
 05
Humaira ce zaune a falo da safe, yaran gidan duka sun fice makaranta kasancewar sun soma jarrabawar zango na uku (Raihana da Ummita kenan), a yadda Ummita ta ce mata, daga jarrabawar to aji na gaba za su je.
Kallon tashar Arewa24 take inda ake hasko wani wasan kwaikwayo na marigayi Ibro. Ta shagala gaba daya tana tuntsira dariya ta ji ɗif, wuta ta ɗauke. Guntun tsaki ta ja, ita kam ba ta san matsalar wuta a nijar ba domin koyaushe akwai. Ba ruwanka da tayar da janareto. Ganin haka kawai sai ta miƙe da zummar komawa ɗaki.
"Humaira."
Muryar Ladidi ta katse ta, ta juyo ta amsa. Tire ne a hannun Ladidin ta karaso gareta. Fuskarta duk ta yi narai-narai alamun roƙo.
"Ki taimakamin don Allah ki miƙa sashen Anna, kinga suyar agadar Mami nake kada ya ƙone. Kuma Annar za ta sha magungunanta ne lokaci na tafiya."
Kirjinta ya ɗan buga dam, ta kasa magana. Toh akan me za ta cewa Ladidin ba ta taɓa shiga sashin Anna ba? A ganinta hakan su ta shafa. Ganin yadda Ladidin ke magiya yasa ta karɓa, godiya ta yi mata ta koma kicin. Ita kuwa ɗan hanyar da take ganin su Muhsin na yawan zirga-zirga zuwa wajen Annar ta zubawa ido sannan ta sauke ajiyar zuciya ta nufi wajen. Anna ɗin ai mutum ce ba aljana ba balle ta illata ta, za ta je ta ga me zai faru idan ta yi karo da ita. Koro ta za ta yi daga ɗakin ko kuwa dai duka za ta yi mata. Da haka ta tunkari hanyar.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin da sallama, jin shiru yasa ta maimaita. Wata murya ta amsa, ta tabbatar ba shakka muryar ta Anna ce. Shiga ta yi ta karasa ta ajiye saman ƙaramin tebur dake wurin. Anna dake zaune gefen gado ta soma magana tana laluben gilashinta.
"Ladidi sai yanzu ake kawomin abin karin? Yau me ya tsaida ki haka? Ina gilashina na jefa?"
Humaira ta hadiyi miyau, kenan dai Anna ba ta san ma wace tsugune a gabanta ba. Ta daure ta ce.
"Ina kwana. Ya karfin jiki?"
Jin baƙuwar murya ya sa Anna saurin sanya medicated glass ɗinta wanda da shi ne ta ke gani sosai ba dishi-dishi ba. Yarinya budurwa ce durƙushe a gabanta, fara sol. Kanta duk da cewar akwai hula, sumarta ba ta ɓuya ba don hatta da goshi da bayan ƙeyarta sumar ce kwance. Ta ƙuramata idanu tana ƙokarin tuno inda ta san fuskar. Sai dai a ɗan lokacin ba ta ankare ba don ita shaf tuni ta mance da wata wai Humaira a gidan tunda ba su taɓa karo ba. Ba ta damu da shiga sashin ɗiyarta ba, ya fi rayuwa anan dai ɓangarenta.
Daidai lokacin Mami ta shigo É—akin kamar wacce aka jefo, ta samu labari daga Ladidi cewar Humaira ta tura kai wa Annar kari. Shigowarta ya sa Anna mayar da dubanta gareta.
"Ina kika samu yarinya ha..."
Sauran kalaman Anna suka maƙale a fatar bakinta, shakka babu ta tuno komai. Ta tuna ashe akwai wani ran bayan jikokinta a gidan da aka ce tsatson Fatima ce. Ta tuna Humaira kamar yadda ta ji sunanta a bakin su Yassar masu yawon kawo ƙorafi a kan fifikon da Mami ke yi mata sama da su. Nan da nan ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Daidai lokacin Humaira ta ƙara gaidata wannan karon muryarta har ɗan rawa yake. Ta nuna Humairar da yatsa idanunta akan Mami.
"Me wannan abar ta zo yi wurina? Me na faɗamaki? Ban ce maki ba na son ganin baragurbi a wurina ba? Ke don uwaki wa ya ba ki iznin zuwa wurina, ko ni na haifi uwarki?!"
Maganar sosai ta daki Humaira, nan da nan idanunta suka cicciko da kwalla, uwarta kuma? Uwar dake kwance a kushewarta? Mene dalilin sanyo ta ciki? Ba ta jira umarnin Mami ba ta miƙe a zuciye ta kama hanyar fita daga ɗakin, Mami ta riƙe hannunta wannan ya dakatar da ita sai dai ba ta ko juyo ba. Daidai nan kuma hawayen suka sauka saman kuncinta. Da harshen buzanci Mamin ta yiwa Anna magana, Annar kuwa cikin harshen da Humairar za ta ji ta amsa a fusace cikin ɗaga murya.
"Au! Don na zage ta kike kirana marar adalci? Ni Maryama kike kallon idona ki ce ba na adalci? Toh anyi rashin adalcin. Idan maye ta manta ai uwar ɗa ba ta mance ba. Ke da kika ga za ki iya haɗiye duk baƙin cikin da kika risƙi kanki a baya, ki yi. Nikam ba da ni ba, kuma ke duk radda kika kuskure ki ka ƙara gangancin takowa ɗakin nan sai na sa jikokina sun nakastamin ke. Sauran yunwa kawai."
Humaira tuni ta janye hannunta a na Mami ta bar É—akin da sauri.
Kai tsaye ɗakinsu ta nufa ta zube saman kafet ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Ita fa duk abin da matar ta ce bai dame ta ba kamar sanya uwarta da ta yi a ciki. To me Mamarta ta yiwa Mamin da har Anna ke batun ba za ta mance ba? Wane irin zama suka yi a baya? Ita Mami da ma ƴan uwan Abba, sun yiwa Mahaifiyarta kyakkyawar shaida, amma me Anna ke nufi da kalamanta? Ko kuwa dai ita ke taya ɗiyarta kishin kamar yadda Ummita ta taɓa faɗi?
Ba ta ji shigowar Mami ɗakin ba sai ji ta yi an kama hannunta an ɗaga ta. Ta miƙe tsaye, Mami ta yi mata murmushi.
"Ki yi hakuri Humaira, kin san iyaye ne sai mun yi hakuri da su mu samu a rabu lafiya. Ki taya ni yi mata biyayya, kar ki kara zuwa ɗakinta har sai don kanta ta nemi hakan wataran wanda in sha Allahu nake fatansa nan kusa. Kar ki sa komai a ranki, ki kuma shirya anjima da kaina zan kai ki gidan koyon girki. Ki cire komai a ranki ki mayar da hankali, ni kuma anan gida idan kin dawo zan dinga iyakar ƙokarina wurin ganin an samar maki dukkan kayan girkin da ki ka koyo a can ki yi a nan mu ci mu ɗanɗana, kin ga daga haka hannunki zai miƙa. Wataran sai a wayi gari kina odar biki da suna har ma da wuraren party ko? Kin zama Hajiya."
Zancen Mamin ya sanya ta murmushin da har wushiryarta ta bayyana. Mamin ma murmushin ta ƙara yi. Daga haka ta fice a ɗakin. Humaira tuni ta share batun Anna ta tattara ta watsar.
***
Sun je gidan Anti Laila ƙanwar Hajiya Lubna tare da Mami, ta ba da form bayan sun biya komai, Mami da kanta ta cikewa Humairar. Anan aka ajiye ranar litinin matsayin ranar da za ta fara zuwa koyon girkin. Daga nan suka yo gida ranta fari sol.
Kai tsaye ɗaki ta nufa hannunta riƙe da na Waleed wanda zuwa yanzu daga shi har Muhsin sun sake da ita, fuskarta a sake, zuciyarta wasai. Ummita ce kaɗai zaune tana karatun jarrabawa, ganin haka Humaira ta dubi Waleed.
"Tafi wajen Muhsin ku yi wasa ka ga Adda Ummita karatu take yi. Anjima sai ka zo ka koyamin turanci ko?"
"Okay! Bye."
Itama ta amsa da bye din tana dariyarsa, ya dage a lallai zai koyamata turanci, haka za ta biye mishi tana É—an tsintar wasu abubuwan da ya iya. Ummita ta kalle ta tana murmushi.
"Yau dai fara'arki ta musamman ce. Kada dai ki cemin har kin soma shiga aji?"
Dariya Humairar ta yi daidai sadda take zama a gefenta.
"Aa fa, amma an gama komai an biya, litinin zan soma zuwa."
"Kai naji dadi wallahi. Allah ya nuna mana."
Ta amsa da amin, ta mike ta hau cire kaya da zummar shiga wanka. Ta dai kula kamar Ummitan ranta a jagule ya ke, ba ta ce mata komai ba har ta shiga wanka ta fito. Anan kuma ta ga ta amsa waya ta yi jifa da wayar saman gado tana ɗan goge fuska. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gareta ta zauna.
"Ummita, lafiya? Meyafaru?"
Ummita tana kallon littafin amma ta kasa karatun sai kawai ta girgiza kai tana shirin cewa ba komai amma tuni hawayenta ya zuba saman littafin. Humaira ta janye littafin.
"Don Allah meke faruwa? Anyi wani abu ne bayan fitar mu?"