Sashe 81
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Daga bisani suka yi sallama, tana nan zaune har ya yi saura bai fi mutum biyu motar ta cika ba sai idanunta ya sauka kan Fadeel dake tsaye ya yi shigar tshirt fara ƙal da maroon wando na Adidas. Sumar kansa idan ka ƙura idanu za ka fahimci ko tsayawa taza bai yi ba. Sai rarraba idanu ya ke yi a tashar, sai ya ba ta tausayi da kuma murmushi lokaci guda. Ta dan yunkura da zummar buɗe ƙofa ta fito idanunsa suka shiga cikin nata, da azama ya ƙarasa ita kuwa tuni ta bude murfin ƙofar. Ya sa hannu ya riƙe murfin gami da durƙusawa su na fuskantar juna, ta kauda idanunta ta maida ga kallon gaban motar.
"Barka da asuba."
Abinda ya fito daga bakinta kenan. Madadin ya amsa sai ya yi shiru yana ƙaremata kallo. Can dai ta juyo, daidai lokacin Rabe ya karaso.
"Ranki ya dade kin san shi ne?"
Fadeel ya kalle shi sai kuma ya miƙa hannu suka yi musabaha.
"Eh na san shi."
Sai a lokacin ya dan murmusa.
"Waye shi?" Ya tambaya, Rabe dai na tsaye kallon ikon Allah, ya dai fahimci ko waye daga yanayin kallonsa da nata, ita din cike da jin nauyi da kunya, yayinda shi kuwa kallonta yake morewa, ga duk wanda ya kalle shi kuwa zai gane ba ƙaramin nisa ya yi a kaunarta ba.
Ta É—an bishi da hararar wasa, Rabe kuwa ya yi Æ´ar dariya. Fadeel ya dube shi.
"Aurenmu nan da sati biyu in sha Allahu. Ina gayyatarka."
Nan da nan ya ƙara washe haƙoransa wadanda yawan yin asuwaki ya sanya ba su dafe ba.
"Sai Oga, ina taya murna. Allah ya nunamana lokacin."
Daga haka ya yi gaba ya bar su. Fadeel ya harareta kadan, ta yi mishi kyau, fatarta ta ƙara gogewa sakamakon mayukan gyara fata marasa haske da Baba Amina ta kawomata har ma da na wanka da take amfani da su.
"Kin yi kyau. Sai dai meke faruwa ne naji kamar Raihana na cewa an yi attacking É—inku? Ban fahimci komai ba."
Sai a lokacin ta tuna tashin hankalin da suka tsallake cikin ikon Allah. Tunaninta kuma ya tafi ga son gano yanda aka yi Raihana da ke zaune a gida ta san da wannan magana, toh waye? Ko dai na gida ne?
Ɗan ƙas da ya yi da yatsunsa saitin fuskarta ya maido ta hayyacinta.
"Kin wani zubamin idanu ina tambayarki. Kwana nawa ne zan zama mallakinki?"
Ya karashe da wani kalar kallo da ma murmushi. Ita sam ba ta ma san cewa idanunta a kansa ta tsayar ba. Sai ta É—an yi wuri wuri da idanunta tana kallon mazauna bayan motar, macen ma hankalinta na ga wanda ta ke da tabbacin mijinta ne su na kwasar hirarsu.
"Ki bani labari idan wani abin ya faru da ku a hanya."
Nan da nan ta labarta masa komai da ta ji kuma ta gani, ya dan yi shiru yana nazarin zantukan, akwai dai alamar tambaya babba.
"Antinku Jannat na gida ko ta tafi?"
Tambayar da ya watsa mata kenan, shi gaba daya yanzun bai yarda da Jannat din ba, matar da son zuciyarta zai sa ta yi yunkurin munana sunan wadanda ba su yi mata laifin komai ba, toh za ta aikata abin da ya fi hakan. Ga Humaira kuwa jin tambayar ta yi wani bambarakwai, da ace ma Fadeel din nada labarin takun saƙar da ke tsakaninta da Jannat toh za ta kawo dalilin da yasa ya ambace ta a wannan gaɓar kenan, amma sanin da ta yi koda wasa ba ta taɓa buɗa masa sirrikan cikin gidansu ba ya sanya ba ta kawo wani abu a ranta ba sai dai ta yi mamakin tambayar.
"Eh tana nan sai bayan biki za ta koma."
Ya jinjina kai.
"Alright, hakan ya yi daidai. Ba don Abba ba, ni da kaina zan kai ki wurin su Kawu. Amma babu komai, wannan ne tafiya ta ƙarshe da za ki yi ke ɗaya ba tare da ni ba a rayuwarki in sha Allahu."
Ta ɗan yi ƙasa da kanta tana wasa da zoben hannunta. Zuciyarta ban da soyayyar Fadeel babu abin da ke yawo cikinsa.
"Inda muke bai dace mu cigaba da hira a haka ba. Zan dinga kiranki har zuwa lokacin da wayarki za ta daina shiga sai dai please kina isa ki sanya layin can ni ki yimin koda flashing ni kuma zan kiraki. Kinji?"
Ya ƙarashe a raunane, ta ɗan kalle shi, rabuwa ko yaya take ba ta da dadi. Ta kawar da kai.
"In sha Allah."
Abin da ta ce kenan kawai, ya miƙe gami da fiddo ƙaramar envelop a aljihin wandonsa ya ɗora saman ƙaramar jakarta dake kan cinyoyinta.
"Bon Voyage."
Daga nan bai ba ta damar cewa komai ba ya rufemata ƙofar ya yi gaba. Ta bishi da idanunta da suka cicciko da kwalla, kamar ta ce masa tana sonsa ko hakan zai saukaka masa dumbin kewarta da take da tabbacin zai ji, sai kuma ta ji harshenta ya yi nauyi, a hankali kuma cikin zuciyarta ta furta 'Ina sonka sosai Fadeel.' Amma a fili juwa envelop din kawai ta ɗauka ta sanya a jaka ba tare da ta duba abin da ke ciki ba. Mintuna bai fi uku ba fasinjojin suka cika motarsu ta tashi bakinta dauke da addu'a.
***
Ummita ta fito daga banɗaki idanunta sun ɗan tasa sai dai ba su kai ga na Raihana ba wacce har lokacin kuka take yi tamkar ranta zai fita duk kuwa da wayar da ta amsa na Humaira ya ci ace ta samu sassauci amma ina abin ya fi ƙarfinta ya shallake dukkan tunani. Ta ƙarasa gefenta ta zauna.
"Ya isa haka Raihana, kinga ɗazu kin daure da Mami ta shigo ba ki yi wani abun da zai ɗagamata hankali ba asalima baccin gangan kika yi. Yanzun kuma kin kasa nutsuwa, tambayar duniya nayi maki akan ki faɗamin wanda ke kokarin kashe su Abba kuma a ina kika ji amma kin ƙi. Lafiya lau muka yiwa Humaira rakiya amma yanzu kin hargitse. Kin tayarmin da hankali, daure ki faɗamin ko ma me ake ciki please."
Raihana sai ta ji kamar Ummitan ta ƙara mata giyar kukanta, ta ina? Kuma da wane bakin? Kai wane hankalin ne ma zai dauka alhalin nata hankalin ma ya kasa, sosai take faman ƙaryata kanta amma wata zuciyar na kwaɓarta da ƙara haska mata al'amarin sakamakon kunnuwanta dake mata amsa kuwwa da muryar Mami wacce ke ƙara jaddada cewa a kashe Abba da Humaira. Toh idan ita ta kasa ɗauka, ta ya ya za ta fara yiwa Ummitan bayani ta gasƙata ta? Ta ya za ta ce mata ai Mamin da ta riƙe su matsayin ƴaƴa na cikinta ita ke barazanar kashe musu uba da kuma ƴar uwa?
"Shikenan Raihana, tunda ba za ki yi magana ba. Kuma ba za ki bar kukannan ba zan je na sanar da Mami, ba za ki bar ni cikin tashin hankali da canki canka ba."
Ummita tayi maganar cikin fidda tsammani da kuma yunƙurin miƙewa don aiwatar da abin da ta ce. Cikin sauri Raihana ta riƙo hannunta tana mai girgiza mata kai. Ummita ta fahimci ko mene ne ba ƙarami bane, za ta iya rantsewa rabon da ta ga Raihanar cikin wannan yanayin tun sadda suka kuɓuta daga hannun ƴan garkuwa. Kai ba ta jin ma tashin hankalin ya yi kamar wannan. Gaba daya fuskarta ta yi ja ga kuma jijiyoyin goshinta da suka fito raɗau, kuka sosai da majina. Cikin dusasshiyar murya ta ce.
"Kiyi hakuri zan fadamaki komai amma sai da iznin Abba. Ko kuma ki bari kya ji daga bakinsa. Kar ki faÉ—awa kowa komai."
Ta karashe tana ƙara fashewa da kuka, Ummita cikin hawayen ta ce.
"Shikenan, amma na rantse idan ba ki bar kukannan ba zan je yanzu na kira Mami."
Raihana jin zafin sunan Mami da Ummitan ke faman ambata ya sanya ta mikewa tsaye cike da jin wani ƙarfin da ta nema ta rasa a mintocin baya.
"Na daina, nace ki bar ambaton sunan kowa, kiyi hakuri Abba yace kada zancen ya fita. Bari na wanko fuskata."
Daga haka ta yi hanyar bandaki, ita kuwa Ummita bin ta da idanu ta yi baki a hangame, yanayin yanda ta bada amsa a fusace ne ya sanya ta kallonta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da share nata fuskar. Za ta yi hakurin ji daga bakin Abban ko mene ne.
***
Anna da Jannat su na kwance su na bacci jin an bankaɗo kofa da ƙarfi ya yi sanadin farkawarsu a ɗan razane. Tsaki Jannat ta ja ganin Mami tsaye sannan ta juya kai ta ƙara lulluba da ƙaton bargo.
"Maryama lafiyarki kuwa? Anyi wani abu ne za ki shigo a haukace?"
Mami wacce ke bin su da kallo cike da nazari gaba daya ta fita hayyacinta, ita dai hankalinta ya kasa kwanciya. Toh uban waye ya sanar da ƴan sanda ƙudurinta idan aka ce duk jama'ar gidan bacci suke yi?
Ta sauke ajiyar zuciya na wahala.
"Babu komai." Daga nan ta sa kai ta fice ta maida musu ƙofar ta rufe, kafin ta bar wajen sai da ta tsaya jikin ƙofar ta kasa kunne shiru tana son ji kodai za su ce wani abu amma ba ta ji komai ba wannan ne ya sanya ta nufar dakin samarin yarannata don nan din ne kadai ba ta leka ba.
Kwankwasa kofar ta yi niyyar yi sai ta fasa gudun kada wanda ya yi wani yunkurin ya ji motsinta, ta bude ta leƙa kadan, bacci suke yi daga Yassar har Dawud, hankalinta ya kai ga Kassim wanda ya juyawa ƙofar baya, ta ɗan yi ƙuri da idanu don son tantance abin da ya dauke masa hankali a waya yake kallo. Muraran ta hango mummunan abu na yawo a kan wayar, bidiyo dai na haramtacciyar zina na jinsi shi yake kallo, hankalinsa sosai yana ga abin da yake yi har sai da gigitaciyar ƙarar da ta saki ya farkar da Dawud da Yassar, Ƙassim kuwa da wani irin firgici da rawar jiki ya yi cilli da wayar.