Sashe 87
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
***
Bayan dawowar Abba daga miƙa Nusy hannun hukuma inda akai akai ta faɗi wanda ya sanya ta ta ƙi, yana zaune yana amsa wayar Alhaji mahaifin Fadeel dake jajanta al'amarin Jannat da kuma kwantarwa da Abban hankali ganin dole ya shiga damuwa tunda kanwar matarsa ce, kasantuwar hakan kuma ya jawo kananun magana iri-iri a kafafun yada labarai kowa na cewa watakila ma ita ta sa aka sace su. Abba ya yaba sosai da samun surukin da ya rikiɗe ya zame masa abokin kuka a rayuwa ya dinga godiya. A haka Mami ta shigo falon ta iske shi. Ganinta bai sa Abba fasa wayar ba, tana ji yana bada labarin abin da ya faru bayan dawowarsu daga kotu amma sam ba ta fahimci da wanda suke wayar ba sai daga baya. Ta matsu sosai ta ji ya kai gaɓar da take so wato sanin hannun da Nusy take, ba ƙaramin girgiza ta yi da jin wai tana hannun Ridwan ba. Wata irin zufa ta karyo mata. Ridwan dai da Jannat ta zama karkashinsa a can ofishin SS, kai kai kai, ita kuwa ta san zai wahala Hajiya Lubna ta iya wani abin a kai amma dai za su gwada sa'arsu. Har Abba ya kammala wayar ba ta sani ba sai da ta ji ya yi magana.
"Hajiya Maryam lafiya?"
Ta É—an yi firgigit gami da dan muskutawa da tattaro dukkan damuwar duniyarnan ta É—ora saman fuskarta. Dama ya lafiyar kura?
"Ina fa lafiya Abban yara, kana tunanin zan zauna cikin nutsuwar ruhi bayan abubuwan da suke biyowa baya? Wallahi idan aka ce wani nawa zai cutar da jininka zan ƙaryata hakan. Wai Jannat dai da kanta ta aikata wannan mummunan abu ga yarannan? Haba Abban yara, ni gaba daya kunyarka nake ji. Don Allah ka yafemin kar ka hukuntani da laifinta. Tabbas ta aikata wauta."
Sai ga Mami ta soma kuka da hawaye, Abba ya ɗan yi shiru kawai yana kallonta. Ba don da kunnuwansa da kuma idanunsa ya ji ya gani tana bada umarnin a aiwatar da kisa a kansa da gudan jininsa ba, zai iya dafa Alkur'ani dukkan abin da take faɗi kuma take nunawa a zahirance da zuciyarta ɗaya ta ke yinsa. Sai dai ina, Maryam ta gama sirewa a ransa, kullum kuma kodayaushe cikin addu'a yake akan Allah ya kara buɗa idanunsa ya nunamasa gaskiyar matar da yake rayuwa da ita kuma ya rayu da ita tsawon shekarunnan cikin rufewar idanu da rashin sanin haƙiƙaninta.
Mami ta É—an yi turus jin babu wani sauyi ko kuma yanayin da zai nuna maganganunta ya shige shi a saman fuskarsa, ta dube shi da dan mamaki kirjinta na É—an dukan tara-tara, kada dai zarginta yake yi?
"Abban yara kodai kana tunanin da sanya hannuna cikin abin da Jannat ta aikata?"
Ya numfasa gami da girgiza kai da riƙo yatsun hannunta.
"Ko kusa Maryama, ni ba na zarginki da komai. Idan na zargeki na ce na zargi wa? Matar da muka rayuwa tsawon shekaru sama da ashirin cikin so da kauna ta gaskiya? Ko kuwa wacce ta riƙemin amanar gida da na yara har ma da wadanda ba ita ta haifa ba cikin kauna da aminci? Har abada ke ba abar zargina ba ce."
Mami ta ɗan yi yaƙe, a karan kanta sai ta ji tsarguwa, ba ta gamsu da zantukan Abban ba. Shi kuwa idanunsa ƙurr cikin nata, danne zuciyarsa yake yi sosai don ya fi kaunar tafiyarsu a hakan har zuwa sadda zai kama ta dumu-dumu.
"Kawai dai lamuran ke dauremin kai, waye ya aiko a sace Ahmad? Idan kuma ba aike bane, ita din wace ce da ta zo tafiya da shi? Akwai dai lauje cikin naɗi wanda na tabbata Ridwan zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya warware wannan ƙulli."
Kirjinta ya ba da dam! Bayan sunan Fadeel, a yanzu Ridwan shi ne suna na biyu da kaf duniya ta ji ta tsana. Wato shi ga ɗan iska, ya shigo rayuwarta don ya wargaza ta, toh kuwa bai isa ba. A fili kuwa jinjina kai ta yi cikin nuna damuwa ƙarara da mamaki.
"Tabbas nima abin ya É—auremin kai Abban yara, koma wace ce wannan yarinyar da ta kira kanta da Nusy, akwai wani sirri tattare da zuwanta da bincike kadai zai tona shi. Ka kwantar da hankalinka gaskiya za ta bayyana."
Murmushi ya yi sosai.
"Nima gaskiyar na fi son ta bayyana. Zan so abin da yake ɓoye ya fito fili. Na dai yanke shawara da zarar an kammala bikin ƴar uwarta zan maida ta hannun Hajiya Maijidda na ɗan wani lokaci mu gani. Ba don saboda bikin ba ma tun yanzun za ta wuce, toh amma ba na son na yanke mata wannan farin ciki."
Mami ta daure fuska tamau.
"Wace irin magana ce wannan kake yi? Wato ka raina dukkan kulawar da Ummita ke samu a wurina?"
Shima nan da nan ya É—aure nasa fuskar.
"Nayi zaton ke ce farkon wacce za ta yi amanna da wannan shawarar Maryama, idan har dagaske kwanciya da nutsuwar hankalin Ummita ki ke buri, toh fa babu abin da ya fi wannan samar mata nutsuwa."
Sai ta gane tana shirin kwafsawa da sauri kuma ta gyara zancen ta hanyar raunana murya da fuska.
"Na sani Abban yara, amma kewarta na fi tunani da zan yi. Shikenan dai Allah ya kawo karshen komai."
Abba ya amsa da amin, ba shi da tabbacin ko dagasken take yi akan lamarin Ummita, ya dai bi ta da hakan ne kawai.
Sai da Abban ya fice zuwa masallaci don gabatar da sallar la'asar sannan ta samu damar kiran Hajiya Lubna ta sanar da ita. Hajiya Lubna ta tambayi cikakke sunan Ridwan din, nan ta sanar da ita, sai kawai ta ja tsaki.
"Aikin banza kai, ai wannan ɗan Hajiya Fa'iza ne, matar Late General Mukhtar AbdurRashid. Sai dai yaron a yanda na san shi yana da wani irin kafiya akan ra'ayi da taurin kai. Za dai mu gwada sa'ar mu. Kar ki samu damuwa. Idan ma ya ƙi bada haɗin kai ai sai mu biyo mishi ta sama."
A farko zantukan Hajiya Lubna sun ɗan sa jikinta mutuwa, amma jin ƙarashen sai ta samu kwarin gwuiwa. Suka rabu akan duk yadda ake ciki za su yi waya.
Daga nan Babandi ta dannawa kira ta labarta masa komai, ya ce kada ta samu damuwa zai yiwa abin tufka. Sunan Ridwan kawai ya tambaya cikakke daga nan ya ce zai mata aiki a kansa.
Haka ta sallame wayar zuciyarta fari ƙal.
***
Matashin ma'aikacin dogo mai ƙira, baƙi ne, irin baƙin da hutu ya ratsa. Yana da cikar sumar kai, ya na sanye cikin ƙananan kaya ya tsaya gaban tebur gami da ƙurawa Nusy idanu babu wasa ko kaɗan a cikinsu. Ita kuwa tana binsa da kallo tamkar ta lashe shi, a baya tana yiwa Wizzy kallon wani haɗaɗɗe kuma jarumi musamman a fagen bariki, amma a yanzun da Ridwan Mukhtar AbdulRashid ke tsaye a gabanta sai ta nemi sauran ruwa a jikinta ta rasa. Sai dai ta sani wannan ba sa'anta ba ne, ko za ta mutu ba zai auri ƳAR BARIKI irinta ba da ba ta san adadin wadanda suka ci moriyarta ba.
"Idan za ki yiwa kanki adalci, ki faÉ—i gaskiya ki huta kuma hukuna ta huta. Ke din wace ce kuma mene ne dalilinki na shiga gidan Alhaji Yusuf da niyyar satar É—an mutum?"
Ta ji idanunta sun cicciko da ƙwalla amma ta yi shiru babu amsa. Idan ta fadi ba amanar Wizzy kadai ta ci ba, har da na kanta don ta tabbatar za ta yi biyu babu, wato dai babu auren Wizzy balle kuma samun wani ƴanci na rayuwa.
Ridwan ya É—an kwankwasa tebur, ta É—ago idanunta ta kara dubansa. Fuskarsa kaÉ—ai ta isa sanya matarsa samun nutsuwa da bacci mai dadi. Ko wace ce ta same shi ta huta.
"Ba ki shirya magana ba kenan? Ki sani Nusaiba akwai hanyoyi da dama da zamu sanya ki magantuwa, idan kin zaɓi ta hanyar tsananin hakan ce za ta faru. Idan kuwa kin shirya sanar da mu ba tare da ɓata lokaci ba, wannan ma kin kyautawa kanki."
Wani tunani ya faÉ—omata sai ta yi saurin magana ba tare da hango matsalar abin da take shirin faÉ—i zai jawo ba.
"Nidai ba satar ɗanta na je da niyyar yi ba. Babansa ne ya ke da buƙatar ganinsa ya nemi alfarma na kawomasa shi ƙofar gidan koda kuwa na mintoci ne sai na maida musu shi."
Ya ji zuciyarsa ta yi wani irin tuƙuƙi. Babansa? Shi dai da ya ke da alhakin keta alfarmar macen da a yau yake jin babu ya ita a zuciyarsa? Shi din dai da ya yi garkuwa da ita? Nan da nan jijiyoyin kansa suka fito raɗau, idanunsa suka kaɗa. Ya murza yatsun hannunsa suka yi ƙara ƙas ƙas.
"A ina zamu same shi domin mu tabbatar da abin da kike magana a kai?"
Sai kuma ta hangi wautarta, nan da nan ta soma zufa. Ya dakamata tsawar da sai da ta miƙe tsaye tsabar firgici.
"Ki sanar da ni!"
Wayarsa dake gefe ce ta katse shi, ganin mahaifiyarsa ce ya sanya shi saurin É—auka ba tare da ya É—aga ba ya fita a dakin da sauri, a duniyar Ridwan ba shi da abin girmamawa sama da ita. Mutum ne mai matukar gudun zuciyarta. Ya samu kyakkyawar shaida ta girmama uwa a wurin mutane. An kuma ci sa'ar da ya kasance ba ta fiye yi mishi katsalandan kan aikinsa ba.
A wannan karon da Hajiya Lubna ta shaida mata alfarmar da take nema na sakin Nusy bayan ta roƙi alfarmar ta sirranta sunanta. Sai ta yi kiran ɗan nata don jin taƙamaiman wace ce Nusy din.
Ridwan jin tambayarta ya yi mamaki, koda wasa bai sanar da ita komai game da Nusy ba amma lamari an Jannat da ma su Ummita babu wanda ba ta sani ba. Kasancewar ba su yi zaman hira ba ne ya sa koda wasa zancen Nusy bai haɗa su ba. Bai nata tambaya kan tambaya ba, sai ya zaɓi labarta mata dukkan komai. Hajiya Fa'iza ta amsa masa bayan gana sauraro.