Sashe 96
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Ai Tasleem ba ta san lokacin da ta yi wurgi da eyeliner din dake hannunta ba. Idanunta suka cicciko da hawaye. Ta hau girgiza kai murya na rawa ta ce.
"Ƙarya kike yi! Wallahi ƙarya kike! Ta sanya kayanta ne? Bari naje, nasan kin sauyamata wasu munafuka kawai!"
Tana kaiwa nan ta kama hanya za ta fita, Raihana cikin zafin nama ta tura ta baya har tana buguwa da gado sannan da sauri ta karasa ta rufe ƙofar da mukulli. Ba ta sa lokacin da ta soma zubar hawaye ba, lallai zatonta ya kasance gaskiya, dama ta san a rina! Da walakin goro a miya, shigarta falon Abban babu wanda ya gan ta sai Tasleem, ta ajiye kaya iyakar tunaninta ta tuna hancinta bai shaƙar mata wani ƙamshi ko wari na turare a sadda ta ajiye ba, sai daga bayan nan ta tuna tabbas mukullin a jiki ta bar shi bisa mantuwa ta fice kiran Humaira. Sai kuma yanzun ta gama tabbatarwa dagaske ba kokwanto zuciyarta ke yi ba, ɗazun a farko babu wani wari ko ƙamshin turaren da ta ji. Yanayin Tasleem ya fayyace mata komai.
"Kina zaton wani abu zai faru da Humaira ne idan ta sanya kayan da aka tanadar mata? Ko kuwa don kin fesa wani ƙaramin kayan asirinki kin yi tunanin za ta mutu ne ko kuma ta samu wata illar? Toh babu ɗaya Tasleem, babu daya da zai faru. Ko kin mance ita ɗin Allah ta sanya a gaba? Wajenshi ta ke kai dukkan kokenta? Kin mance tana tare da Mai Kariya daga dukkan sharri? Wallahi kin shayar da ni mamaki! Ban taba zaton son zuciyarki ta kai har haka ba da za ki iya gwada shirka don samun abin duniya! Waye Fadeel da har za ki kauce hanya ki rushe dukkan kyawawan ɗabi'unki saboda shi? Anya kina da hankali?"
Tasleem da ke kuka sosai, kukan baƙin ciki da takaicin yaudarar da Babandi ya yi mata ta juyo a fusace tana kallon Raihana cike da tsantsar tsana.
"Ke ce dabba jaka marar hankali da ba ki iya taya Æ´an uwanki kishi da son abin da suke so ba! Banza mai kwakwalwar kifi! Eh! Na so ace na illatar da rayuwar Humaira kuma koda ace aikina bai ci ba ai idan ta sa wata ba ta san wata ba! Raihana ki rubuta ki ajiye sai na illata rayuwar Humaira!"
Raihana a wannan gaɓar kalaman bakinta ma dakyar suke fita.
"Ke wace iri ce Tasleem? Ki ji tsoron Allah. Ba a yiwa Allah haka, har abada ba za ki ga daidai ba. Humaira ta fi karfinki da tsafinki har abada ba za ki yi nasara a kanta ba. Muna nan dake kina ji kina gani abubuwan alheri za su dinga faruwa gareta sai dai ko baƙin ciki ya kashe ki."
Wani wawan mari ta kai wa Raihana tana kuka itama Raihanar na kuka, ba don zafin marin ba sai don bakin cikin wannan masifu da take ta gani su na yawo a rayuwar Æ´an uwanta da ma mahaifiyarta wadanda son zuciyarsu ce kawai ta ke neman kai su ga kogon halaka.
"Banza yar iska da ba ta san ciwon nata ba! Daga ke har Humaira daidai nake da ku!"
Ta na kaiwa nan ta ja mayafinta ta bude dakin ta fice. Fitarta kuwa ta yi mugun gamo, don wata tsohuwar gwaggonsu ce ta ɓangaren Abba ta ji tana rangaɗa guɗa tana hamdala wai an ɗaura auren Humaira da Fadeel. Ai ba ta san sadda ta saki wani ihu mai ƙarfi ba da sai da mutanen falon hankulansu ya yi kanta sai ganinta aka yi ta zube ƙasa a sume. Nan fa aka shiga yarfa mata ruwa, ya yi daidai da faɗowar Mami gidan. Zuciyarta abubuwa uku ne ke dagule ciki, ga farincikin kuɓutar Jannat wacce suka sauka a can gidan Futuha don ta kimtsa kuma kada ta zo ta tarar da jama'a a yi mata caa, gefe fa Bala da ya kira ya tabbatar mata an samu an goge komai na wayar Wizzy an maido ta tamkar sabuwa fil kuma an mayar masa an ajiye kamar yanda itama a nata ɓangaren ta goge dukkan wani abu da ya shafi Wizzy har lambarsa babu ɗaya da ta bari ga kuma baƙin cikin albishir da Yassar ya kira ya yi mata cewar an ɗaura auren Humaira da Fadeel har sai da ta ɗura masa ashariya ta wayar. Shigowarta ta hangi Tasleem a sheme a ƙasa ana yayyafa mata ruwa a fuska.
Ta karasa kirjinta na dukan tara-tara.
"Lafiya? Meke faruwa ne haka?!"
Ta tambaya a hargitse tana tura jama'a tana nufar inda Tasleem din take.
"Ina zamu sani? Fitowa ta yi kawai a firgice sai ta saki ƙara ta zube." Cewar wata ƴar dattijuwa cikin dangin mijin Baba Amina. Tsaf Mami ta fahimci dalilin, kafin a yi abin kunya ta yi saurin cewa.
"Watakila mutanenta ne suka tashi, ɗan kama min ita zuwa ɗaki don Allah." Ta fadi tana duban dattijuwar, wasu dai suka hau ƴar dariya da kananun magana, a gefe kuma wata ta shiga rangaɗa guɗa tana cigaba da fadin wai ina Amaryar take ta fito. Har tana rerawa Humaira kirari. Mami ta bita da harara kamar ta shaƙo wuyanta, ta dai danne suka yi dakinta da Tasleem. Tasleem hatta da ajiyeta da aka yi tana ji ba ta son ma ta bude idanu ne gudun kar ta faɗi abinda za a ji kunya. Ba ta ma san ya aka yi baƙin cikin ya haifar mata da faɗuwar ba. Sai da ta ji ta kuma fahimci Mamin ce kaɗai a kanta sannan ta bude idanun, Mami ta bar jijjigatan da take faman yi gami da sauke ajiyar zuciya.
"Wane irin abin kunya kike son janyo min? Yanzun ma ya aka ƙare ballantana kin nuna baƙin cikinki a fili? So kike a tafi da mu a baka ana zaginmu?"
Jin haka ai sai ta ƙara sakin wani sabon kukan.
"Mami zan mutu wallahi. Fadeel shikenan ya auri Humaira. Babandi ya..."
Sai ta ji kamar an sa gam an ɗinki leɓɓanta, ta kasa ƙarasa abin da ta yi niyyar sanar da Mamin game da Babandi.
"Babandin me ya yi?"
Mamin ta tambaya kirjinta har wani lugude yake yi, ta tattara dukkan hankali da tunaninta ga diyarta don neman ƙarin bayani. Sai Tasleem ta kasa cewa uffan sai kukanta da ya karaɗe ɗakin. Mami ta ƙara jijjiga ta.
"Tambayarki nake!"
"Ba komai Mami. Aikin da ya bani ne bai ci Humairar ba."
Sai ta sauke ajiyar zuciya tana mai jan tsaki.
"Har kin tsoratar da ni. Toh ai dama ni na riga da na dawo daga rakiyarsa. Ganin kin damu ne ya sanya na bari mu ƙara gwada shi mu gani ko za'a dace. Amma yanzu ai bakin alƙalami ya riga da ya bushe. Sai ki cire komai a ranki ki mayar kan jarrabawarki kinga dai zangon ƙarshe ki ke. Wannan fadi tashin da nayi maku don ku samu karatu idan ita waccan (Futuha) ta watsar saboda romon baka na banza na ɗa namiji ke dai tunda kina ƙarshe gwara ki mayar da hankalinki. Sannan don Allah kada a gane kina cikin halin bakin ciki, nima kinga dai daurewa zan yi na dan shirya na fita a yi da ni. Kema hakan nake so, ki daurewa zuciyarki, idan ma ba za ki iya ba ki fice zuwa gidan Futuha, Antinki tana can tare da Anna sai dare idan an ragu za su dawo."
Tasleem dai ba ta ce mata uffan ba, ta dai ɗan ji sanyi jin Jannat ta kuɓuta amma tuna Fadeel da Humaira sun zama mata da miji yana baƙanta zuciyarta sosai. Haka tana ji da gani har Mamin ta miƙe ta shiga wanka. Ita kuwa wayarta ta hau lalubawa, ba ta fadi ba daga aljihun doguwar rigar atamfar dake jikinta ta zaro ta danna lambar Babandi da zummar ta ci mutunci sai dai kuma nan take reshe ya juye da mujiya.
"Ya aka yi Tasleem? Kamar kinsan ina shirin kiranki. Nasan zuwa yanzu kina tunanin kin yi rashin nasara a aikinki ko? Kar ki damu, ki shirya yanzu ki zo ina son ganinki komai zai yi daidai."
Sai ta kasa cewa komai bayan kalmar Toh. Ta miƙe jikinta har rawa yake yi ta yafa mayafinta ta fice daga gidan. Ba ta damu da taron jama'ar falon ba cikinsu kuwa har da Humaira da ke tsakiyar ƙawayensu da yan uwa ana hoto ana kuma tsokanarta. Ta bi Tasleem din da kallo yayinda itama ta kalle ta har ta a tuntuɓe. Ta kasa cewa komai ban da ta cigaba da tafiyarta, gani take yi ko mintuna kadan ida ta ƙara toh za ta ɓata ran Babandi kuma zai hana ta zuwa wajensa. Wani mugun tsoronsa take ji a zuciyarta. Ba ta ko damu da matasan da suka soma cika farfajiyar gidannasu ba ta fice.
***
Fadeel kuwa daga sadda aka ɗaura auren, ya samu wuri ya yi nafila raka'a biyu gami da nuna godiyarsa ga Allah da ya ba shi abin da ya jima ya kwana da wuni cikin bege da kaunarta. Duk yanda ya so ya keɓe domin ya yi kiranta abu ya gagara, jama'arsa ta ko'ina ga yan uwan Mahaifiyarsa ma daga Yola ta ko'ina. Babu damar wayar dole hakanan ya hakura har zuwa sadda aka dunguma don zuwa gidan su Humaira gaisuwar iyaye.
***
Cikin wani ikon Allah da kuma rabon a yi, ya yi shiga ta kamala ya bi tawagar Ango zuwa cikin gidan Amarya Humaira ba don komai ba sai don ya yi dacen É—auke gudan jininsa Ahmad koda kuwa cikin babbar rigarsa.
RANA DUBU NA ÆARAWO...."Masha Allah, ga nan Ango da tawagarsa nan shigowa."
Faɗin wata mata, nan aka hau gyara hanya, suka shigo da sallama dauke a bakunansu kowannensu cikin gayu. Matasa masu jini a jika ga ruwan arziƙi.
Ummita ta kauda kai daga kan Ridwan tun ganin da ya yi mata ya zubamata mayatattun idanunsa kamar ya haÉ—iyeta.
"Wancan guy din fa ke yake ta kallo, ke kuwa kin ƙi ba shi dama."
Raihana ta faɗi ƙasa-ƙasa, tuni ta gyara fuskarta ta fito, baƙin cikin halayyar yan uwanta ba zai sa ta kasa nunawa Humaira murnarta da samun miji ɗaya tamkar da dubu ba.
Harararta kadan Ummita ta yi.