← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 26 OF 101

Sashe 26

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
Tun faruwar wannan lamarin Fadeel ya shiga damuwa ainun, yana da tabbacin shi yake so ba a sonsa, ya kuma shirya rungumar wannan jarrabawar ya yaƙe shi. A gefe ga mahaifansu da suka soma matsawa akan su fito da matan aure shi da Ibb. Satinsa guda bai kira ta ba balle ya aika mata saƙo, jarrabawa ya yi domin ya ga ko zai iya yakice ta a rai bisa shawarar Ibb amma sai ya ji kamar yanzun ne ma ya soma kaunarta. Ba kuma ya jin zai iya haƙura da ita. Ya miƙe daga saman gadon da yake kwance wanda tashinsa kenan daga bacci mai cike da mafarkan Humaira, kamar daga sama ya ji ana kwankwasa ƙofar falon, agogon dake maƙale a bangon ɗakin ya kalla, ƙarfe goma har ta gota. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki, ya tuna yau suka yi da Alhaji zai soma zuwa kamfaninsa ya kama aiki, jin ƙarar kwankwasar yake har cikin kansa dake radadin ciwo, iya sati ɗaya zuciyarsa ta jigatu da rashin ji ko ganin Humaira, ta ina zai soma fidda ta daga rayuwarsa? Wannan abu ne da ba zai yiwu ba sam. A hankali ya miƙe daga shi sai vest da dogon wando ya fito falon.

"Waye?"

"Ni ce Yaya Fadeel, abin kari na kawomaka."

Guntun tsaki ya ja jin muryar Murja. Ƙofar kawai ya bude ya juya ba tare da ya ko kalle ta ba ya ce.

"Ki ajiye ki fice. Na gode."

Ta ji ciwon hakan amma da ta tuno da batun Malam na cewa idan har ya ci abinda ta girka da laƙanin da ya ba ta to fa ba makawa hankalinsa zai karkato gare ta. Ya yi mata gargadi akan lallai ta tabbata ya ci, idan kuwa bai ci ba to fa haka za ta kara narka uban kudade a yi mata wani sabon aikin. Don haka sai ta zauna a falon ta ƙi bin umarninsa, shi kuwa wanka ya shiga bayan sun yi waya da Alhaji ya buɗe mishi wuta akan rashin zuwansa ofis da wuri, hakuri ya dinga  a shi ya ce yana tafe. Suka yi sallama. Koda ya fito wankan a gaggauce ya shirya cikin kananun kaya, dark green din tshirt sai wandon jeans. Ya ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, ya gyara sumar kansa. Fitowarsa falon ya ga mutum zaune, nan da nan ya tamke fuska, ita kuwa Murja da rawar jiki ta ce.

"Barka da safiya, bari na haÉ—a maka shayin."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.

"No ki bar shi nayi latti, Alhaji na jirana. Ki je da su kawai."

Murja cikinta ya bada sautin kululu, ita dai ta shiga uku, wannan rashin sa'a har ina? Yanzu shikenan ta yi asarar dubu tamanin? Ita kuwa wa za ta je ya ba ta wasu kudaden a ƙara maimaicin aiki?

"Ba kya ji ne?"

Wannan karon ya yi maganar yana ji kamar ya É—auke ta da mari hagu da dama, abu É—aya da ya sa yake raga mata bai wuce na tunanin shi É—in ma fa haka yake fama da soyayyar wata ba ta sonsa.

Ganin yanayinsa sai ta maida kayan kwandon ta dauka ta fice har da kwallarta. Fadeel yana so ya kashe ta, yanzun ma ji take kamar ta faɗa wannan faɗaɗɗan kirjin nasa ya yi mata rumfa da hannuwansa, sai dai kash! Wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma kuma komai nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma sannu sannu ba ta hana zuwa, ta na ji a jikinta watarana haƙanta zai cimma ruwa.

***
Abba ne zaune fuskarsa cike da walwala, babu jimawa iyayen Hamza suka tafi bayan sun nemawa ɗansu auren Tasleem kuma ba musu ya amince ya ba su. Tasleem da kanta ta kira Hamza ta ce ya turo saboda bakin cikin abinda Fadeel ya yi mata, ga faɗan da suka yi da Futuha me  yi mata dariyar ta rasa shi, ita kuma don ta nunawa Futuha tana da mai sonta dagaske ba irin ita me bin Ibb ba ya sonta ba yasa ta kiran Hamza ta ce matukar dagaske yake toh ya turo a nema mishi aurenta a kwana uku, idan kuwa ya wuce haka to kaunar da yake mata a baki ne. Dama kuma shi abin da yake jira kenan, don haka sai kawai ya ba da kai bori ya hau.

Mami ta shigo itama fuskarta dauke da walwala ta zauna gefen Abba. Kafin ma ta ce wani abu ya riga ta.

"Maryama yau ina cike da farin ciki, ba ni da burin da ya wuce naga na aurar da yarannan mata lafiya kowaccensu ta tare a ɗakinta. Ina tsoron sharrin wannan zamani. Ita ma Futuha zan mata magana, ta fito da miji na haɗa aurensu baki ɗaya zai fi min. Karatun can su je su ƙarasa a ɗakin mazajensu, naji da kannensu masu tasowa."

Mami ta jinjina kai,

"Hakane Abban yara, in sha Allahu itama zamu yi magana da ita naji ko tana da tsayayye. Na san dai wani yaro da ta kwallafa rai a kansa amma shi bai san tana yi ba."

Abba ya É—an yamutse fuska.

"Ai kinji irin shirmen yaran yanzu masu biyewa soyayya, ban da shiririta ke ba manema kika rasa ba, mutane nawa ne suka tare ni akan suna sonki amma ki nacewa wanda ba ya so? Allah ya kyauta, lallai ki ce mata nace ta nutsu ta fiddo miji a haɗa aurensu da ƴar uwarta. Kina ji dai iyayen shi Hamza sun ce nan da wata shida suke so a yi komai a ƙare."

"Shikenan, zan mata magana." Mami ta amsa a sanyaye, fatanta Allah yasa Futuha ta cire ran da ta kwallafa akan Ibb ta kama wani.

***
  Futuha na zaune tana danne-dannenta a waya kamar koyaushe, bidiyo mai zafi ta ɗora tana bin waƙa, ta ci ado a bidiyon har ta gaji, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya da dankwalinta na leshi, karanta comments kawai take tana jin dadi tana zabga murmushi, wasu kuwa zagi ne da addu'ar nema ma ta shiriya. Irin wannan sai dai ta ja tsaki ta wuce. Ta ci gaba da kallon bidiyoyin jama'a nan ta ci karo da wani bidiyo da ya ɗaga hankalinta wacce wata Sa'a Ƴar snow ta yi a kanta, zagi ne na cin mutunci da sharri, wai Baby Futuha ta tiktok karuwa ce kuma tana da hotunanta da shaidu akan hakan. Tashin hankalin har da hotonta daga ƙasa gefen bidiyon. Ba ta san sadda ta kwalla ƙara ba a ɗakin bar ya farkar da Humaira me baccin sha biyu. Su biyu ne dama kaɗai a ɗakin, ita Humaira ma ba ta san Futuhar ta shigo ba domin gaba daya sun fita makaranta, kenan ta dawo ita. Kuka sosai Futuha ke yi hannunta har yana kakkarwa. Humaira ta ji hankalinta ya tashi, duk kuwa da cewar ba sa shiri ta miƙe ta ƙarasa gareta.

  "Anti Futuha lafiya?"

Ba ta ko kalleta ba ta wuce da sauri ta yi hanyar fita. Humaira dai na kallon ikon Allah. Toh me ya yi zafi haka? Ta watsar da batunta gami da buga hamma.
   *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

"Shi Fadeel din ya sani?"

Ta girgiza kai tana kara sunne wa kamar mai jin kunya.
Alhaji ya yi shiru sai kuma ya ce.

"Shikenan, ni dai b na yiwa yarana dole balle kuma namiji. Zamu yi maganar da Fadeel duk amsar da ya bayar za ki ji daga Antinki."

Ji ta yi kamar Alhajin ya harba mata mashi a ƙahon zuciya, da irin wannan amsar ai gwara kawai ya ce mata aa kansa tsaye. Abu ne da ya sani kamar yanda ta sani, zai wahala Fadeel ya amince da shi, ta yi zaton yanda Alhajin ke yabawa da nutsuwarta zai ce ya amince ya zaɓawa Fadeel din ita matsayin matarsa. Haka ta mike ta fice gwuiwa a sake. Bayan fitarta Alhaji ya yi shiru, ta ina zai soma ɓata ran ɗannasa wanda a baya ya sha baƙar wuya a dalilinsa da mahaifiyar Fu'ad? Ya musguna mishi, bai duba maraicinsa ba na rashin uwa ya yi watsi da shi. Karshe don kansa da ya gaji bayan ya yi hankali ya fice ya koma dangin mahaifiyarsa a can ƙasar Kamaru. Sai kuma bayan da ya kwashe dogon shekaru har kusan biyar ya dawo yanzun kuma ya hargitsa shi komai ya ƙara hargitse mai? Yaransa biyar kacal a duniya, Fadeel ne babba sai Fu'ad sai kuwa ƙanwar Fadeel uwa ɗaya uba ɗaya Hannatu dake aure a can Adamawa, sai yaran Anti Amarya biyu, Khadija da Abdulmaleek. Shi hakanan Allah ya yi shi ba mai yawan haihuwa ba, matansa babu me yin tsarin iyali.
  A ƙarshe dai ya yanke zai mishi maganar auren don shi kansa yana damuwa kwarai akan zaman yaran haka(wato Ibb da Fadeel) ba tare da iyali ba. Har ga ƙaninsu Fu'ad ya yi auren ya bar su.

***
  Fadeel ya nutsu a gaban mahaifinsa, bai katse shi ba har ya kai aya. Sai a lokacin ya yi magana.

  "Na ji bayananka Alhaji, ina neman addu'arka musamman a wannan wata mai alfarma da za mu shiga akan neman zaɓin Allah. Sai dai kuma ba na kaunar Murja, ba na sonta matsayin matar aure. Don Allah abar zancenta."

Jinjina kai Alhaji ya yi, ya É—an murmusa kaÉ—an.

"Shikenan, Allah ya sa hakan ya fi alheri. In sha Allahu zan tayaku kai da É—an uwanka. Ya kamata ku maida hankali."

Fadeel ya amsa a ladabce. Daga nan suka rufe wannan babin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan alheri na sadaka da neman lada da Alhaji ke yi duk shekara idan watan azumi ya kama. Kamar yin kunu da abincin sadaka, kyautar butoci, ruwa, dabino da ma sauransu a masallatai., daukar nauyin tafsir, sai kuwa idan sallah ta matso ya yiwa ƴan uwansa marasa ƙarfi da marayu da dama sutura. Da wannan suka rufe babin Murja da ma batun aure. Anti Amarya dake laɓe a bayan labulen ɗakin Alhaji, ta ji ciwon cewa da Fadeel ya yi ba ya son ƙanwarta. Ta yi ƙwafa, ai idan ya san wata bai san wata ba.
Chapter 26 · 0% Book details