← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 91 OF 101

Sashe 91

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Za ta so hakan amma fa ba za ta iya ba don ta tsorata da yanayin Abban. Ta sani mutum ne dama tun can mai zafi idan an taɓo shi sai dai kalar ɓacin ran yau da ta gani ba irin wanda ta saba ganinsa ciki ba ne a ire-iren lokutan da aka taɓo shi ba. Wannan ne dalilin da ya sa cikin sheshsheka ta ce.

"Aa Mami, zan koma amma na rantse idan Yakubu ya dawo sai ya bani takardata ba zan iya cigaba da rayuwa da shi ba."

"Don ubanki ni za ki watsawa ƙasa a ido?"

Futuha ba ta amsa ba sai kawai ta yi gaba ta fice da gudu gudu. Mami kam zama ta yi ta fidda dankwalinta tana yiwa kanta firfita saboda ji take ma iskar dake wulwulawa a dakin kamar feshin iskar wuta ce ba ta yi mata yanda ya kamata. Yau dai Abba da kansa ya iya kallonta ya faÉ—amata maganganun cin fuska son ranshi? Wato rigar mutuncin da ta ara ta yafa ya fiye mata alheri akan zahirin ita a idanunsa? Dama ba mallakarsa ce ta yi ba yake shakkarta kawai albarkacin wancan kyawawan halayyar da ta ke nunawa ta ci? Toh wai ita ba ta ma fahimta ba, aure yake nufin zai yi?

"Wallahi Isuhu ba ka isa ba! Ka yi kaÉ—an!!"

Ta yi furucin cike da hargagi da ɗaga murya, babu wani da zai ba ta amsa don haka ta kwashi jiki ta yi bangaren uwarta, yau ce ranar farko tun bayan aurenta da ta ji tana buƙatar shawararta wajen waɗannan ƙullace-ƙullacen da take yi. Shakka babu idan gininta na tsawon shekaru ya rushe ko kuma ya karasa rushewa za ta kwashi kashinta a hannu.

***
Fadeel ya yiwa Humaira duba na tsanaki, tana cikin wata damuwar da duk iyaka kokarinta na yin murmushin yaƙe sai da ya ɗago ta.

"Ka yi shiru." Ta furta a sanyaye ganin sun kwashi mintoci cikinsu babu alamun wani zai ce uffan. Ita tunanin sabuwar Mami da manufofinta ke dukan zuciyarta shi kuwa damuwarta ce ta haifar da ta sa. Tun da ya ga yanayin da Mami ta tarbe shi ya san akwai wata a ƙasa, ya kuma fi tunanin rashin nutsuwar Humaira saboda ganin Mamin cikin wani yanayi ne. Bai kawo komai bayan wannan ba.

"So nake ki gama tunaninki."

Ta girgiza kai.

"Ni ba tunani nake yi ba fa."

"Boddo please. Ko meke damunki kiyi hakuri ki cire shi a rai idan ba haka ba zan samu Abba da Alhajina yanzu kawai a daura auren na wuce da ke gidana."

Ya ba ta dariya dagaske, ta ɗan bishi da hararar wasa. Shi ma murmushin ya yi mata gami da ɗan ɗaga gira kaɗan. A ƙarshe suka sha hirarsu sosai da ta mantar da ita Mami da sabgarta. Sun ɗan jima kafin su yi sallama ya fice.

***
Anna ta muskuta tana kara tamke fuska, ai ita yanzu kam a duniyarta babu abin da ta tsana sama da Abba da wadancan yarannasa biyu da suka yi sanadiyyar kama autarta. Ta sanya gonarta ɗaya babba ta can Agadez a kasuwa yanzu haka an samu mai siya duk da akwai faɗuwa sosai a yanda aka taya amma ita dai burinta a samu abin cikawa a fiddo Jannat wacce mijinta ya yi ƙememe ya kuma rantse ba zai ba da ko biyar ba tunda ba shi ne ya sanya ta aikata ba. Dama yana cike da jin haushin yawon da ta ke yi bini-bini idan abu ya tashi sai ta matsa mishi za ta zo Nijeriya. Ga rashin ɗaukar yan uwansa da daraja, ganinsu take ƴan ƙauye futuk.

"Ke Maryam, idan za ki buÉ—e zuciyarki ki fito ki nunawa wancan sokon mijinnaki Maryam ce da ba a nunamata É—an yatsa ba ta karya ba. Ai ni da ace tun farko ma nasan wautar da kika yi kenan na wannan makircij da bai kai ki ko'ina ba da ba zan bari ba. Ai gwara mutum ya sanka da halinka amma yanzu zai dinga yi maki wani kallo saboda ba haka kika nunamasa a farko ba. Yanzu dai ki jira Æ´ar uwarki mu samu ta biya wadancan karnukan kuÉ—insu sai a san me za a yi."

"Yanzu Anna sai Jannat ta fito za ki duba matsalata?"

Mamin ta furta cike da takaici.

"Ke ba kya tausayinta ashe? Ita tana can a garƙame cikin yanayin a tausayawa ke kuwa ai naki mai sauki ne. Ki tashi tsaye ki ƙwatarwa yaranki ƴancinsu ta ƙarfin tuwo idan ba haka ba dama na fadamaki tun ba yau ba, Isuhu zai iya tattara rabi da kwata na dukiyarsa da sunan na Ummita ne yake juyamata."

Annar ta yi mata wani tuni mai ƙarfi da muhimmanci, tabbas akwai dukiyar Ummita a hannun Abba, duk kuwa da cewa shima Abban ya samu gadonsa a dukiyar ƙanin nasa. Tana tsoron Ummitar ta tashi aure ya ce zai tattara komai ya damƙa mata abinta da mijinta, idan kuwa hakane ita ya dace ta samarwa Ummita miji ba kowa ba. Mijin da za ta iya juyashi son ranta ba wanda zai gagareta sarrafawa ba. Mijin da ba zai zama ɗan da ta haifa da cikinta ba. Toh wa za ta samu haka?

"Ina magana kin yi shiru."

Kalaman Anna suka katse tunaninta. Miƙewa tsaye tana wani murmushi mai tarin ma'anoni.

"Zan san abin yi."

Daga haka ta fice ba tare da ta ƙara ba Anna amsar tambayarta na me za ta yi ba.

***
A kwana a tashi cikin hukuncin Allah har ranar sanya Humaira a lalle ya gabato. Ana gobe za a soma shagalin bikin sai ga yan uwanta daga Nijar sun dira a gidan. Mami duk shige da ficen da Baba Amina ke yi da ma wasu a ƴan uwan Abba da kuma Hajjo babu ko ɗaya da ta sanya hannunta ciki. Ita kuwa Humaira ta tattara batun Mami ta ajiye gefe bisa shawarar Hajjo da Baba Amina. Ta bi Mamin bi bana wasa ba amma Mamin ba ta ko sauraronta. Ga Tasleem a dakin da babu damar a yi wani abin sai ta tanka ta faɗi baƙa, a ƙarshe ma ta tattara ta koma ɗakin Anna da kwana. Hankalin Tasleem ya yi masifar tashi ganin dagaske dai bikin Humaira da Fadeel za'a yi, wannan na nufin za ta tashi a tutar babu kenan? Ta iske Mami hankali a mugun tashe tana kuka kamar ranta zai fita ita fa lallai Mamin ta san abin yi don zuciyarta ba za ta iya zama ta yi haƙurin ganin hakan ya kasance ba. Mami ta dafe kanta dake tsananin sarawa, kwana biyunnan ba ta iya bacci saboda damuwa.

"Don Allah Tasleem ki rabu da ni da wannan koke-koken naki. Na samu tabbaci daga Babandi aurennan fa sai an yi babu makawa. Wannan borin naki zai tashi a banza."

Tasleem ta dora hannu a kai wani sabon kukan na kwace mata har da majina. Ashe haka baƙin ciki yake? Haka radadin kishi yake? Toh ita yau duk biyun take ɗanɗana, ganin Humaira kamar wata sarauniya ya sanya ta ji inama ta kashe kanta ta huta saboda baƙin ciki da azabar kishi. Har ji ta yi wasu ƴan uwan Abba na ce mata ranki ya daɗe don hauka, acewarta.

Mami da ta ƙuramata idanu gaba daya sai ta ba ta tausayi, Fatima ta haifa mata baƙin ciki ta kuma bar duniyar ta bar ta da shi, gashinan tana ƙunsa. Can ta nisa ta ce.

"Toh ko za ki je wajen Babandi, dama ya ce ko bayan auren na fadi abin da nake son a yi musu amma saboda takaicin abin da naji gami da Abbanki da Maijidda sai idanuna ya rufe na ci mishi mutunci. Ki je ki ce nace ya yi hakuri ya dubi lamarinki ya samar maki da mafitar da ta dace. Zan biyashi ko nawa ne."

"Mami ki kirashi a waya toh."

Harararta ta yi ta ja tsaki.

"Kiran me zan mishi bayan na ce maki ga yanda muka yi da shi? Ke dai zan ba ki lambar da kwatance ki je."

Ta amsa da toh, a take kuwa Mami ta dauki waya ta turanmata lambar ta whatsapp dinta ita kuwa ta yi mata sallama ta fice bayan ta bi umarninta na shiga banÉ—aki ta wanke fuskarta.

A wajen Anna ta bar É—iyarta ta fice bayan ta sa facemask ta rufe hanci da bakinta yanda babu wani da zai gane ta a hanya.

***
Babandi ya kalle ta tsaf, ya buga wani murmushi mai tarin ma'ana bayan gama sauraronta da kuma jin daga inda ta zo wajensa.

'Kin tafka kuskure babba Hajiya Maryam. Kin kashe É—iyarki da hannunki.'

Ya yi furucin a ƙasan ransa.

*RUFAIDA UMAR*Ya nisa kafin ya ce.

"Haƙiƙanin gaskiya ba don ina ganin mutuncin Hajiya Lubna da ta zama silar haɗuwata da Mahaifiyarki ba, da babu abin da zai sa na ƙara karɓar wani aikin da ya shafe ta da ma wani nata. Amma tunda har ta fahimci ni Babandi ba za ta iya gudanar da rayuwa yanda take so ba tare da taimakona ba (Waiyazubillah) toh shikenan zan taimaka maki albarkacin hakan."

Tasleem ta saki wata doguwar ajiyar zuciya tana ɗan murmushin da ya ƙara kwaɗaitawa Babandi ita. Ya lashi leɓɓansa gami da mayar mata da martanin murmushi kafin ya hau buge-bugen ƙasarsa sannan ya ɗago ya dubeta

"Gaskiya Malama Tasleem yau dai kin zo a sa'a domin kuwa koda na ƙara bincikawa na tabbatar za a iya fasa auren Humaira da Fadeel, akwai kuma gagarumin sa'a da ke nuni da cewar za ki zama mallakinsa nan gaba. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, aikin da za ki yi hakan ya faru ba mai sauki ba ne.""

Da sauri ta tari numfashinsa.

"Na rantse kowane iri ne aikin zan iya yinsa muddin zan auri Fadeel."

Ya jinjina kai yana shafa gemunsa.
Chapter 91 · 0% Book details