← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 24 OF 101

Sashe 24

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

Mami ta saki baki galala tana duban irin kukan da Futuha take yi, lallai abin da zai sa ta kuka har haka ba ƙaramin abu ba ne. Tana da taurin zuciya a wasu lokutan, ita kanta zancen ya shige ta don ba ta mance yanda ta sha ba ta labarin wani Ibrahim ko kunyarta ba ta ji. Daidai da Anna ta san da zaman soyayyar da Futuha ke yiwa Ibb, sun kuma ji daga bakin Tasleem da ma su Yassar cewa mutumin bai damu da ita ba. Ta sauke ajiyar zuciya.

"Allah ya kyauta, shi ne akan wanda bai damu da ke ba za ki kashe yar uwarki? Kar ku kuskura na ƙara ganin wannan rashin hankalin."

Haka kawai ta fadi ta juya, madadin kicin ta wuce dakinta. Futuha ranta ya yi baƙi, wato ma abin da Mamin za ta ce kenan? Ita dai ta tsani halin rashin kulawar da Mamin ke nuna musu. A fusace ta yi sashin Anna har tana bangazar Raihanar. Ita dai Ummita ba ta ce uffan ba, toh ban da abin Futuhar ma, koda ace son Humaira yake, ta tabbatar ba zai samu fuska ba. Ita ta lura kowa ma Humairar ta tsana muddin zai furta mata kalmar yana sonta.

***
Anti Amarya ta ƙurawa Murja dake zaune tana faman jijjiga ƙafafu ido waya ta ke amsawa amma gaba daya fuska a jagule sai bayan ta kammala ta ajiye wayar, sannan Anti Amarya ta soma magana.

"Yanzu ke wannan Idris din kinsan matsayin babansa kuwa? Meyasa Murja ba ki da wayo da tunani? Kin maƙale akan yaron da idan ya shigo gidan nan kallo ba ki ishe shi ba? Komai kika yi ba ki iya ba, amma Idris tun haɗuwarku a bikin Fu'ad ya manne maki kuma dagaske aurenki ya ke son yi. Kinga ina raba ki, wannan fa shi ne saki reshe kama ganye. Kin gani sarai da idanunki yanda Ubansa ke ji da shi kamar ba shi da wasu yaran bayan sa, ko a haka ya dace ki fahimci babu wanda zai yi mishi auren dole. Ko da ace kuwa ba namiji ba ne, tun da ya sa ƙafa ya dawo ƙasar nan, Alhaji ke gudun abin da zai ƙara sanya wa ya yi nesa da shi. Toh kuwa ki kama kanki tun wuri ina shawartarki, soyayyar Fadeel ba za ta kai ki ko'ina ba. Ina kara faɗamaki wallahi ba ya sonki ba ya kaunarki."

Ta sani gaskiya ne tsagwaronta yayarta ke faÉ—i, amma ina, ta riga ta yi nisa da son Fadeel. Ta gama tsara yanda za su yi rayuwar aurensu wannan ya sa maganganun ke shigarta su na fita ta kunnen hagu. Ta furzar da huci.

"Shikenan, na yanke shawarar abin da zan yi."

A zaton Anti Amarya, ta dauki shawararta don haka ta murmusa.

"Ko kefa."

Ita kuwa murmushi ta ɗan yi, ta kuma ƙudurta a ranta za ta tari Fadeel kawai ta ce mishi tana sonsa. A yanda ta ga yana ganin mutuncin Antinnasa, ba zai watsa mata ƙasa a idanu ba.

***
BAYAN SATI ÆŠAYA...

A wani yammacin ranar Juma'a ne, Humaira na tsaye tana ninkin kayanta tana jerawa a sif. Futuha kuwa ta ƙure volume ɗin waƙar Kalmar So na breaker tana bi tana daukar bidiyo na kanta a tiktok. Riga gown ne a jikinta lemon green fuskar ta sha make up. Gashinta a waje ko ɗankwali babu, sai raye-raye take. Raihana da Ummita na zaune su na aikin lissafi na makaranta da aka ba su, su na ɗan taɓa hira jifa-jifa da Humaira. Su na yi suna kallon ikon Allah wajen Futuha da ta saita Camera ta waya sai raye-raye ta ke yi. Wannan karon ta sauya waƙar zuwa Warr na Ado Gwanja.
Kusan yanzun aikinta kenan, ta yi rawa ta ɗora a Tiktok da Instagram, babu laifi kuma ta samu mabiya sosai, wannan ya kara fasa mata kai, a farko hotunanta kawai take ɗorawa iri-iri a instagram, amma ba ta jima da soma Tiktok ba ta ga ta samu karɓuwa wannan ba karamin ɗauke hankalinta ya ke ba a yanzu. Su na a haka sai ga Tasleem ta faɗo ɗakin da gudu. Jiki na rawa ta karasa sif din kayanta ta bude. Futuha wacce ta kammala tana editing kafin ta dora ta dakata tana dubanta.

"Ke kuma lafiya?"

Ta juyo da wani irin zumudi.

"Kalau, babban baƙo zan yi fa. Kin tuna guy dinnan da na hadu da shi ranar bikin Shema'u? Abokin Ibb?"

Futuha ta gyada kai. Tasleem ta daka tsallen murna.

"Shi ne ya yimin waya ya kara neman kwatance, yau zai zo."

Ita kanta Futuha ta jiye mata dadi, amma haka nan ta ji É—an kishin yar uwar a ranta. Me Tasleem ta fi ta da har za ta yi kamu me zafi haka lokaci É—aya amma ita kuma ta kasa samun Ibb? Tun su na yara an sha cewa ta fi Tasleem kyau, balle kuma yanzun da suka girma. Kowa ita ya fi kira kyakkyawa a kan dai Tasleem. Wannan ma na daya daga cikin abin da ya fasawa Tasleem kai a yanzun, itama tana jin takaicin kusheta da yan uwan Mami har ma da na Abba ke yi a lokuta da dama su ce wai Futuha ta fi ta kyau. Sai Futuha ta kasa ce mata komai bayan "Inyee, na maki murna." Daga nan ta ci gaba da latse-latsen wayarta tana murmushin da bai kai zuci ba. Tasleem ta maida hankali ga duban sif dinta, ta san Futuha mace ce mai kishi, ta fi kaunar komai ta fi kowa, kuma sai gashinan nasarar a kanta take. Tashi guda ta yi kamun babban kifin da ya fi wanda Futuhar ke hari.

Raihana kuwa duban Ummita ta yi. Cikin sanyin muryar da ba lallai su Tasleem su ji ba ta ce.

"Kada dai ace Fadeel me son Humaira ne zai zo?"

Ita ma Ummita hakan ta ke zargi, Humaira na jin su ta yi kamar ba ta ji ba. Ta sani tabbas shi ne, sai bayan sun rabu ta kara tabbatarwa shi ne mai kiranta adalilin saƙon da ya turo mata bayan shigarta wurin bikin Shema'un, inda ya ce mata ta yi kyau kuma ya yaba da murmushin da ta yi mishi a lokacin. Sannan bayan sallar juma'a a yau din, ya bar mata saƙo inda yake shaida mata batun zuwansa gidansu a yau. Ya kuma roƙe ta kar ta ƙi fitowa. Ita kuwa a take ci kanka ba ta aika mishi ba balle ta kira ta dakatar da shi daga zuwan, ta fi kaunar ya zo ta jaddada masa ido cikin ido cewa ita ba ta soyayya, kuma ba ta sonsa ya rabu da ita.
Tunano hakan sai ta ji dariya ya kama ta, dakyar ta danne ta hanyar murmusawa. Wato dai yau din akwai kallo kenan. Ta kara duban Tasleem da ta sauya kaya zuwa wani leshinta ja mai ɗigon baƙi a jikinsa mai ɗan karen kyau, murmushin ta kara saki wannan karon har da sautin dariyar da ya sa su Raihana dubanta, suka kuma dubi junansu, sun tabbatar Fadeel ɗin Humaira ne a hanyar zuwa. Akwai dai matsala kenan.

©️Rufaida Umar.*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*

*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*

09034973645

Wayar Tasleem da ta ɗau ƙara ne ya sa ta saurin jifa da kwalbar turaren dake hannunta a saman gado, ta zari mayafinta da ya hau da leshin ɗan firit wanda ko kirjinta bai gama rufewa ba, ficewa a dakin ta yi bayan ta kara wayar a kunne tana fadin ga ta nan fitowa waje. Futuha ta mike ta bi bayanta wai za ta gani ko dagaske Tasleem din ta ke. Suna fita Humaira ta tuntsire da dariya har da faɗawa saman gado. Raihana da Ummita su ma dariyar suka shiga yi.

"Ni dama ya ce yana son nata dagaske ai da naji dadi, ko ba komai na huta da alaƙaƙai. Haba, ina dalili mutum ana korarsa yana mannewa sai ka ce mayen ƙarfe."

Ta ja guntun tsaki ta mike ta ci gaba da ninkin.

"Kai Humaira anya a duniya za ki yi aure kuwa? Wannan abu har ina wai? Duk kyau da kwalisa na saurayi ba kya sonsa? Meke damunki?"

Ummita ta ce tana duban ta, ji take kamar ta kai hannu ta buge ta tsabar haushi. Itama Raihana ta cafe

"Rabu da ita Ummita, ai kanta akwai alamar kuncewar notina. Da ace ma ni ce ke, ko don na nunawa Tasleem ita ɗin ba komai ba ce a wurin Fadeel ai wallahi da hannu bibbiyu zan tarbe shi, shima dai Fadeel din da ba shi da zuciya ya kyaleki ya ƙi, ya bari kina ta wulaƙanta shi son rai. Da ni ce shi ko?"

Ta yi ƙwafa amma ba ta ce komai ba, Humaira wacce tun soma maganarsu take kwaɗa musu harara, ta ja tsaki.

"Matsalarsa, ni dai ai ban yaudareshi ba, tun farko kuma na faɗamasa ya rabu da ni, ya ficemin a rayuwa amma ya ƙi. Aikuwa babu abin da zan ce mishi, ya je can ya ƙarata da Tasleem."

Ba su ce uffan ba sai kallon mamaki da suke mata, dagaske dai take ko a jikinta don ba su ga wani É—igon kishi a saman fuskarta ba.

A ɓangaren Tasleem kuwa, tana ƙarasawa falon ta ci karo da Mami a zaune tana amsa waya. Ganin ta da shirin fita ya sanya ta yi sallama da abokiyar wayar ta dube ta dakyau.

"Ke kuma sai ina haka?"

"Mami baƙo fa nayi, bari na shigo da shi falon saukar baƙi sai na zo."

Ba ta ma kara jin abin da zai fito a bakin Mamin ba ta yi wuf ta fice, Mami ta yi kasake tana duban hanya, fitowar Futuha ya sanya ta maida akalar tambayar a kanta.

"Wannan wane baƙon ta ƙara yi a yanzu ne? Duka-duka yaushe shi Hamzan ya zo da har zai ƙara zuwa?"

Taɓe baki Futuha ta yi cike da jin kishin ƴar uwarta ta amsa.

"Uhum, wai fa abokin Ibb ne yake sonta shi ne take wannan rawar jikin."

Wani É—an murmushi Mami ta yi.

"Wato dai ruwan ido ne abin nata kenan? Ya za ta yi da shi wanda ta yiwa iznin zuwa su gaisa da Abbanta?"
Chapter 24 · 0% Book details