← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 92 OF 101

Sashe 92

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

"Sai mu'amala ta shiga tsakaninmu har na tsawon wata ɗaya kafin aurenki da Fadeel. Ita ko Humaira a yau zan fara aiki a kanta zuwa ranar da ki ka ce za'a ɗaura auren ina mai tabbatar maki ba zai yiwu ba. Idan dai kika ba da haɗin kai yanda ya dace kuma kika yi gum da bakinki ma'ana kika ɓoye cikinki hatta ga wacce ta turoki nan, toh shakka babu za'a dace. Za ki yi mamakin irin mahaukacin son da Fadeel zai soma yi maki har sai kin ce ya yi yawa."

Tasleem ta ɗan yi dum, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Tsaf ta karanci me yake nufi da mu'amala amma sai ta ji kamar dai hausarta akwai gyara a jikk wannan ya sanya ta ƙara neman ya yi mata ƙarin bayani. Nan fa Babandi ya buɗe mata komai ta tabbatar dai saduwar ita yake magana a kai ba komai ba. Ta ƙare mishi kallo, jibgegen ƙato mai mummunan fuska daidai gwargwado. Sai dai ga dukkan alamu yana amfani da manyan turaruka masu ƙarfi marasa dadin kamshi. Ba dai za ka ce yana tashin hamami ba.

'Kar ki sake ki cuci kanki, mene ne a ciki don kawai dai saduwa? Fadeel fa ne za ki aura ya zama a ƙarƙashin ikonki.'

Wani sashi na zuciyarta ke mata tuni, nan da nan ta ji ta yi na'am musamman da ta ƙara hasko kanta cikin wannan katafaren gidan da ta samu labarin ya danƙara na Humaira. Ga kuma kayan alfarma na lefe wanda zai dawo mallakinta. Duniya ta yiwa idanunta rumfa ruf, ba ta hangen komai sai ɗaukaka da shaharar da ke gabato ta. Wannan ya sa ta dubansa a tsanake.
 
"Na amince amma da sharaÉ—in sai na yi tsarin iyali gudun daukar ciki."

Ya yi wani murmushi na mugunta, a ransa faɗi yake. 

'Ashe ba ma fansar nayi niyyar ɗauka akan Hajiya Maryam ba. Ai sai kin haifa mata ƙaramar bokanya ko kuma boka.'

A fili kuwa sai cewa ya yi.

"Ke da kike gaban Babandi, ai ba ki da matsala akan tsarin iyali. Akwai layar da zan ba ki, muddin kika sanya a bakinki yayin komai, ina mai tabbatar maki babu ke babu samun ciki. Ba ma a kaina kawai ba, ko tsakaninki da sabon Angonki Fadeel idan har ba ki shirya ki haihu da shi da wuri ba wannan laƙanin zai maki aiki da ma wasu na sirri. Mallakarsa kuwa kin yi kan gama."

Wani dadi ya ratsa zuciyar Tasleem, ta kara samun ƙwarin gwuiwar da ta ji ko rai aka ce ta kashe akan ta samu cikar burinta za ta iya saboda kwaɗayin duniyar da kuma daukakr da ta ke hasasowa kanta muddin ya kasance Fadeel ya zama mijinta.

"Shikenan, Malam nidai na shirya komai ma a yi tunda za'a dace. Sannan nidai koda ace Humaira an raba ta da Fadeel, bana son ta auri mijin da ya fi shi ko nan gaba. Na fi kaunar ta auri ƙasƙantaccen da za ta dinga zuwa wurina da ƙoƙon bararta na neman taimako."

Babandi ya jinjina kai, ai barewa ba za ta yi gudu ba ɗanta ya yi rarrafe. Ya san ba a ƙas ta tsinci wannan muguntar ba.

"Burinki zai cika. Ina zuwa."

Ya miƙe ya shiga ɗakinsa kafin ya fito ya miƙa mata laya da umarnin ta tura bakinta. Ta bi umarninsa sannan ta mike suka nufi dakin kirjinta na harbawa amma hakanan ta daure, ba ita ta bar gidansa ba sai kusan goma da mintoci na dare. Babandi ya bi ta da kallo bayan ta fice ya kyakyace da dariyar nishadi, wa ya ƙi banza a rayuwa? Ai wannan lamarin karɓaɓɓe ne ba kuma ya jin zai bar rayuwarta ta sarara. Hakika Tasleem ta faɗi hannunsa. Daga nan ya mike ya gyara jiki ya bada umarnin kada hadiminsa ya bar wani ko wata su shigo ganinsa a sanar da kowa ba ya nan. Aiki sosai ya zauna yi na mallake Tasleem da kuma sa mata tsoronsa ta yanda ba za ta taɓa iya tsallake umarninsa ba saboda ba kadan ba ya ji ya kamu da matsanancin buƙatarta kuma yana son hakan ya ɗore ko don ya gwadawa Maryam ita ba komai ba ce.

***
Hankali tashe Mami ta ja Tasleem zuwa dakinta ta rufe. Dubanta take yi a tsanake. Jikinta banda ƙamshin turarukan da Babandi ke amfani da su babu abin da ke tashi. Ta kara shinshinarta sosai, Tasleem ji ta yi kamar ta saki fitsari a wando.

"Me ya yi maki?"

Ta tambaya cikin tsananin ruɗani.  Girgiza kai Tasleem ta yi. Ta tuna gargaɗin Babandi cewa muddin ta sake bakinta ya furta abin da ya faru ga kowa wane ne toh ta sa a ranta aikin ya lalace har abada kuma ba za ta samu koda rabin mutum  irin Fadeel ba balle a kai ga shi da kansa. Wannan ya sanya ta samarwa kanta nutsuwar dole ta fisge hannun Mami daga jikinta.

"Mami mene haka wai? Me kike tunanin ya yimin? Babu fa abinda ya yimin, kawai dai ya ban wasu turaruka na shafa ya ce na zauna ya dinga yimin wasu karatuka bayan ya kammala kuma ya ce naje na jira zan soma ganin sakamako. Gobe ma yace na koma zai ban wani garin magani da zan barbaÉ—a a makwancin Humaira."

Ajiyar zuciya mai karfi Mami ta yi har da kama jikin madubi. Sai bayan tafiyar Tasleem ta dinga tunanin anya ba ta aikata kuskure da ta tura ta wajensa ba musamman da ta tuno yanda suka kwashe. Ta kira wayar Tasleem din ya fi a ƙirga amma ba ta ko ɗaga ba hakanan na Babandi ma sai a ce mata a kashe. Tana niyyar zuwa da zummar kai mata yarinyarta dake faman kuka sai ga Tasleem din ta shigo gidan.

"Shikenan, ki wuce ki je kin bar yarinya tana ta kuka."

Itama ajiyar zuciyar ta sauke ganin Mamin ta yarda da zantukanta na bogi. Har ta kai ƙofa Mamin ta dakatar da ita hakan yasa ta waigo.

"Ki kula sosai da duk wani abu da Babandi zai sanya ki yi, idan har kanki ya ƙulle a kai ki sanar da ni kafin ki aikata."

Gyadamata kai kawai ta yi kafin ta juya ta nufi dakin Anna don gaba daya ma ta tattara kayanta daga ainahin dakinsu, ba za ta juri ganin wannan rawar ƙafar da ake yi akan auren Humaira da Fadeel ba.

***
Ɓangaren Humaira ba ta da ko ɗigon damuwa game da komai. Idan ka ga yanda ta yi kyau za ka rantse ba ta taɓa sanin wata aba wai wahalar rayuwa ba. Ummita ita kanta ta bar damuwa da yanayin kaddararta, gaba daya ma babu mai yi mata tuni a kai, yanda ƴan uwan Humaira ke haba-haba da ita da nunawa Ahmad kauna sai ta ƙara sakewa da su. A yanzu babu abin da ke damunta dangane da abin da ya faru da ita na baya sai ko yanzun da Ridwan ke neman takurawa rayuwarta da kira da ƙara fallasa mata zahirin zuciyarsa. Ga kuma Mubarak a gefe wanda ya ce babu gudu ba ja da baya don ya samu labarin Ridwan daga bakin ƴan uwansa. Ita kam gaba dayansu babu wanda ta ke jin ma kaunarsa a ranta sai tausayi da suke ba ta ganin su matasa su na neman daukarwa kansu abin da bai dace da rayukansu ba. A cewarta.

Safiyar ranar Juma'a su na zaune a daki, Humaira sai yatsine fuska take tana kallon kwanon da Baba Amina ta dire a gabanta na kazar da aka dafa da sinadaran gyaran mata.

"Ki kalla dakyau Humaira, hakanan za ki ci shi ko bakya so."

Fadin Baba Amina kenan, yanmatan dake dakin aka kwashe da dariya har Ummita da Raihana wacce ta saki ranta saboda murna da farin cikin ganin auren Fadeel da Humaira na niyyar tabbatuwa, abin da ta jima tana son gani.

"Nikam Baba idan ta ƙi ci a miƙomin yanzun nan na tashi da shi."

Cewar Raihana tana Æ´ar dariya.

"Aa Raihana, wannan kam na matan aure ne. Ki jira zai zo kanki ke da Ummita nan ba da jimawa ba kuwa sai mu gani ko cika baki ne ko kuwa dagasken za ki iya ci."

Aka yi dariya, Ummita ko murmusawa ta yi, ita ba ta fiye son ana sanya ta a layin waÉ—anda za'a aurar ba.

"Allah kuwa Baba cikina ya cika, dazunnan fa na gama shan wani..."

"Toh marar sirri, a gaban Æ´an uwan naki za ki tona abinda aka baki?"

Hajjo ta katse zancen Humaira, anan kuma sai Baba Amina duk ta sa aka fice a dakin aka bar Humairar sai ko Ummita da Hajjo.

"Kinga Humaira, wadannan abubuwan da nake sanyaki sha da ci, suna daga cikin abin da za su ƙara siyamaki daraja a wurin mijinki. Ba ki da wanda ya wuce mu da zamu tsaya don ganin rayuwar aurenki ta inganta da taimakon Allah. Abu kuma na gaba da nake son faɗamaki, bai wuce akan Maminki ba. Kar ki ga don ta sauko kamar ta sauya fuska ta shiga cikin sha'anin bikinnan na jiya ki yi zaton babu sauran ɓurɓushin hassada da bakin ciki a ƙasan ranta. Ta riga ta fiddomaki da kuma mu da zahirin wace ce ita wannan kadai ya isa ki kula koda bayan aurenki ki yi kokari kada ki bada wata ƙofar da za'a ji kanki keda mijinki. Ki godewa Allah, samun miji irin Fadeel a zamanin nan sai a tona. Mutumin da tun kina gwada masa tsana da kyara yake bibiyarki da nuna maki kauna ta gaskiya, wallahi Humaira koda wasa kika cutar da shi a zamantakewarku sai Allah ya yi masa sakayya. Kar ki yi amfani da wannan dumbin kaunar da yake gwadamaki wanda hatta a dangin Mahaifinki akwai wadanda suke nuna adawarsu da shi ki yi tunanin cutar da rayuwarsa. Ki yiwa kanki karatun ta nutsu, ki yi hakurin zama da mijinki kar ki yaɗa matsalar da za ki fuskanta da shi ga kowa ba ma fatan matsalar ake maki ba, amma ki kula ki san me kike yi."
Chapter 92 · 0% Book details