Sashe 6
Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read
Humaira ta jinjina kai, tabbas haka ne don ta ga mijin Mammati wata ƴar uwarsu a Maine, shi ma babu bokon amma yanzu kaf ƙauyen nasu babu mai kuɗinsa. Idan ya zo hutu da yaransa kowa sai ya san ya zo saboda alherin da yake yi musu.
"Ki je ciki nasan zaman da kaÉ—aici ke kadai, ki sa Ladidi ta kunna maki kallo a wayarta sai ki yi."
Ta fadi hakan saboda babu wuta, Æ™a'idar Abba tun sha biyun dare ake kashe masa inji, sai ko idan aka ci sa'a Kedco sun hasko wuta. Humaira ta fice a falon bisa bin umarni.Â
Bayan fitarta Mami ta ƙarasa ga Abba fuska dauke da damuwa.
"Ya haka? Kana son ka karyawa yarinya zuciya daga zuwanta? Ko kuwa so ka ke ta riƙi mahaifiyarta da mugun zato a ranta alhalin ba ta ji ba ba ta gani ba? Don Allah kar ka fara, kar ka yi wannan kuskuren. Tabo ne da yaro kan yiwa gurguwar fahimta."
Abba ya numfasa.
"Hakane, sai dai ki sani ba karamin taimakona ki ka yi ba don ba ki da masaniyar abin da zan ce a sannan. Na gama iyakar nazari ban san ƙaryar da zan shirga don rufe zancen ba. Na gode maki mace ta gari."
Ya karashe yana jifanta da murmushi, ta rausaya kyawawan idanunta tana maida mishi martani.
"Nima na gode da wannan yabon, muje ka shirya lokaci na ƙurewa. Idan ka dawo ni kuma kafin nan na bincika wurin wacce ya dace a kai Humaira ta fara daukar darasi."
"Hakane, amma zan fi so ta gama shiga ta san Æ´an uwana. Kafin a durfafi wannan."
Mami ta É—an yi jim sai kuma ta amsa da toh. Bayan shigar su É—akin yana cikin shiri ta sanyo zancen kaya.
"Ka ga ya kamata a ɗan ɗinka mata suturu ko ba yawa, mutumin da ya zo daga ƙauye na tabbata ba wasu kayan kirki ne da ita ba."
"Ke dai wato burinki kawai na karya bakin aljihu, toh wannan na jikinta ba sutura ba ce? Kin fi kowa sanin ba na son kashe-kashen kuÉ—i ko?"
Ta yi Æ´ar dariya, an zo wajen. Ai idan har batu na fitar da kuÉ—i ne toh nan suke kai ruwa rana, a karshe dai hakanan ta ke cin nasara a kanshi, kafin ya botsare akan jima.
"Haba Abban yara, Humaira fa uwa guda ce, idan ba ka yi mata ba wa za ka yiwa?"
Ta ƙarashe murya a narke kamar wata matashiyar budurwa, hakan ya tuna mishi zamanin tashen soyayyarsu. Ya yi dariya gami da girgiza kai.
"Maryam kenan, ke kam ba a kayar da ke a magana. Shikenan idan na dawo zamu ga yadda za'a yi. Na fita ai ko?"
"Eh ka fita kam, Allah ya kara buÉ—i." Ta ba shi amsa tana dariyar itama.
Ya amsa da amin.
***
 Washegari kuwa Mami da kanta ta bada aka siyowa Humaira atamfa da leshin sai kuwa kananun kaya dogayen riguna duka dai ba masu yawa ba, hatta da takalmin shiga taro ƙafa biyu da mayafai kala uku sai da Mami ta siya mata, ba kuma ta tsaya anan ba sai da aka haɗo da kayan shafe-shafen mata da na kwalliya da kuma undies.
Abba ya kalli kayan sannan ya kalli Mami.
"Yanzu dukkan kayan nan a dubu talatin?"
Mami ta É—an bishi da hararar wasa.
"Au, ka yi zaton kowa irinka ne? Wannan dai ya fi ƙarfin abin da ka bayar, Mami ta cika ta siyawa ɗiyarta. Wanda ka bayar ma mun gode."
Ya yi Æ´ar dariya.
"Maryam mai halin girma, ai shikenan, wannan tsakaninku kun fi kusa. Allah ya saka da alheri."
Ta amsa da amin. Sannan ta umarci Ummita dake zaune wadda ita ce ta dauko kayan zuwa sashin Abban akan ta ɗauka ta ba Humaira na shafe-shafen, suturun kuwa ta sa a leda Humairar ga shirya su kai wurin telansu.
Ummita ta amsa da toh, sannan ta kwashi kayan ta fice.
A falon Mami kuwa, Tasleem ce zaune a gefe daga ita sai vest sai kuwa wandon makarantarta da ba ta cire ba, zaune take tana cin ɗan wake tana ba su Raihana labarin wata ƴar ajinsu Suhaima da kusan kullum ta Allah babu ranar da ba sa taɗinta. Sosai ta tsayawa Tasleem ɗin a ƙoƙon rai, a cewarta yarinyar ta fiye rawar kai, ga nunawa sauran ɗalibai kamar ta fi uban kowa ƙoƙari. Tasleem ta cusa loma a bakinta sannan ta dube su.
"Kun san yau wallahi ta ci arzikin Babandi da ya shiga tsakaninmu amma da sai na gwabje bakinta. Ƴar iskar yarinya ta dubi tsabar idona ta ce wai ina mata katsalandan a harkokinta saboda kawai tana yin tutorial din sanya kai na ce ita kanta ba ta gane ba shikenan fa ta tasomin, su kuwa ƴan korenta su Teema Small saboda na taɓa Hajiyarsu me zuwa da mota nan suka goyi bayanta."
"Ke dai Tasleem ina raba ki da nuna bakin cikinki a fili ga Suhaima, kin kasa ɓoyewa har sun harbo jirginki, ke ba ki iya kwantar da kai ba? Ai irinsu da sannu za ki shige mata har ta yarda dake ki zama aminiyarta, kika san wane Don ɗin za ki samu ta hanyarta? Ko kin mance cewa ubanta fa ya fi naki arziki, koda dai namun akwai sai maƙo." Faɗin Futuha tana ƙarashewa da murya a ƙasa gudun kar ta yi shuka a idon makarwa. Suka kwashe da dariya, shiru Tasleem ta ɗan yi sai kuma ta ce.
"Ke kuma fa haka ne wallahi, don ba ki ga wani arnen gaye da ya taba zuwa wajenta a makarantar ba, wallahi ƙarshen dai haɗuwa ya haɗu, ba wai kyawun fuska ba aa, motarsa ma kanta abin a kalla ce."
"Ahaf, to kin gani. Ai kinga kakarki ta yanke saƙa muddin ki ka samu irinsa. Bare ma yanzu da Abba ya yi sanyi da batun auren, da ace ban da Mami ta shawo kansa ya bari ai da yanzun mun haihu. Taɓ ni nasan da yarana biyu."
Suka yi dariya, hankalinsu ya koma ga niƙi-niƙin kayan da Ummita ta shigo da su daga bangaren Abba.
"Ke." Cewar Futuha. Ummita yarinya mai sanyi da hakuri, ta juyo ta kalle ta. Da yatsa ta nuna ledojin kafin ta ce.
"Wannan fa? Daga ina zuwa ina?"
Duk da tambayar ta rainin hankali ne, amma ta amsa.
"Aiken Mami ne, ta ce a kai wa Humaira."
Daga haka ta ci gaba da tafiya, dukkan su ukun ba wacce ta tanka sai faman furzar da hucin ɓacin rai da baƙin ciki. Can sai Tasleem ta ja tsaki tana ture kwanon da ta ci ɗanwake da ƙafa.
"Mami! Mami!! Wallahi ban taba ganin uwa irin tamu ba wacce ba ta damu da lamarin yaranta ba. Kunsan Allah, ba don kamanni da kuma Ann dake ƙara ba mu tabbacin cewa ita din mahaifiyarmu ce dagasken ba da zai yi wuya na yarda."
Cikin taɓe baki Futuha ta amshe zancen.
"Uhum, kema dai kya fada. Ai shiyasa nake so mu samu mazan kece raini da za'a kalla a ƙara kalla. Ko ba komai za mu huta da baƙin cikin Abba da Mami."
Tsaki Tasleem ta ja ranta na zafi, sai dai ta kasa magana karshe kawai ta mike ba ta ko kara kallon kwanon ba kuma babu niyyar ɗaukewa. Bayan wucewarta kallon Futuha ya koma kan Raihana wacce ta maida hankalinta ga waya tana murmushi.
"Ke kuma ke da wa? Mu gani."
Raihana kamar wacce aka tsikara ta mike tana ja baya da dariya.
"Toh sa ido, ina ruwanki da wayata?"
Futuha ta taɓe baki.
"Kya ji da gulmarki dai, kullum latse-latsen waya, wayarki ta munafukai babu wanda kika taɓa bari ya ga meke ciki. Ni ban san irinki ba, ko hoto za ki nunawa mutum sai dai ya kalla haka tana dunkule hannunki kamar wacce za'a sacewa."
Raihana na dariya ta yi hanyar waje gami da fadin.
"Eh ɗin dai, wasu ma ba a san me suke shukawa ba. Gwara ni ko failed ban taɓa samu ba sai ku masu C.O."
Futuha ta yi kwafa kawai tana huci, zafi biyu ya haÉ—e mata.
***
Murna sosai Humaira ta yi da wannan kyautar ban girman. Ta ɗaga wata riga ja mai adon fulawa ruwan madara tana mannawa a jikinta. Haƙora a buɗe ta dubi Ummita.
"Kinga kamar Mami ta auna, daidai da ni."
Ummita ta yi dariya.
"Eh mana, sai ki sa hijabi su na falon Abba kiyi musu godiya. Kinsan Allah, Mami tana ban mamaki. Wai fa har cikawa ta yi da kudinta ta ƙarasa yi maki siyayya, nidai ban taɓa ganin mace mai kirkinta ba."
Humaira ta jinjina kai tana murmushi cike da gamsuwa da zantukan Ummita. Tabbas itama a farko ta yiwa Mamin gurguwar fahimta, amma yanzu kam ta ga saɓanin tunaninta. Sai kuma da sauri ta dubi Ummita.
"Wai anya ban yi wauta ba? Kin ga ban je na gaida Anna ba tun da na zo."
Ummita ta É—an yi shiru alamar damuwa, har dai Humaira ta ce.
"Lafiya kika yi shiru?"
Girgiza kai ta yi.
"Anna fa ba ta wani murna da zuwanki, ta cewa Mami koda wasa kar ta sake ta turo ki ɓangarenta. Ki share kawai, ni nasan Mami za ta shawo kanta, kuma tunda kuna tare a gidan dole watarana ku haɗu ai. Zance ne kawai irin na Anna. Kinga jeki ki yiwa su Abban godiya mu wuce, yamma na yi."
Humaira ta gyada kai kawai ta numfasa, dama ba dole ne kowa ya ƙaunaceka ba. Ba tare da damuwa ba ta zura hijabin ta fice a ɗakin.04
Humaira ta ware idanu tana ƙarewa garin Kano kallo a hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai wa telan Mami dinkunan an kuma auna ta, sosai akwai bambanci da inda ta fito koda dai dama ita din a ƙauye take. Sai dai kuma hatta da titunan garin burgeta suke yi. Ummita ta kalleta ganin yanda gaba ɗaya hankalinta ke a waje, murmushi ta yi.
"Humaira kenan, idan dai garin nan ne har sai kin gaji da shi ina tabbatar maki."
Jin haka sai ta yi dariya.
"Anya kuwa? Nidai sosai ya burgeni wallahi. Ji nake tamkar kada mu koma gida."
Dariya Ummita itama ta É—an yi.