← Book details Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt Local reading mode
READING PART 27 OF 101

Sashe 27

Dukan Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel.txt · about 8 min read

***
A daren ranar Lahadi gaba É—aya garin aka dau murnar ganin watan Ramadan. Lokacin Sahur gaba É—aya gidan suka tashi aka yi idan ka cire Tasleem wacce ba ta da sallah.
  Lokacin shan ruwa na kawo kai, Humaira da Ummita har Raihana ana kicin ana faman kai da kawowa, Tasleem ba ta shiga ba don langaɓewa ta yi wai mararta na ciwo. Ita kuwa Futuha tana tsaye kawai tana yatsine-yatsine da gwatsale wani abun idan Humaira ta yi wai ba haka ake yi ba. Ita dai ba ta tanka mata ba albarkacin watan da suke ciki na ibada. Sai da suka kammala komai sannan suka jera a tsakar falon bayan shimfiɗa ƙatuwar ledar cin abinci. Na Abba kuwa can ɓangarensa suka kai aka shirya komai. Itama Anna, Raihana ta kai mata komai ta bar ta tare da su Muhsin don a duniya Anna ba ta fiye son zuwa falon Mamin ba sai da kwakkwarar dalili.

  Sai a sannan Tasleem ta shiga kicin din ta ɗibi abinci ta dawo falon tana ci ta a yatsine fuska wai gishiri ya yi yawa. Ba ta ko jin nauyin yan uwanta maza dake zaune a falon su na taɓa hira. Haka aka sha ruwa aka yi zaman cin abinci bayan kowa ya yi sallah. Mazan suka dinga santin girkin amma da zarar sun yi ido da Humaira su watsa mata harara idan ka cire Ƙasim wanda tun wata rana da ya shiga ɗakin Mami zai ɗau kuɗi ta gan shi kuma ta rufamasa asiri ba ta faɗawa kowa ba, tun a ranar ya soma ganin ta da ƙima a idanunsa. Ya ke kuma jin kunyarta. Yassar kuwa faɗi yake ai ba basirarta ba ce, koyamata aka yi. Futuha  ta ja tsaki.
  "Wai kai kana wani zance, ina abin yake? Ni ba abin da ya kara ɓatan rai wai sai da Abba ya ce wani mu shiga kicin mu koyi girki wajenta. Don Allah ku ji wani abu."

Dariya suka yi idan ka cire Ƙasim dake faman cin sandwich da ya ji kaza da su cheese yana santi.

"So ya ke ki je ki yiwa Alhaji Yakubu kar a ji kunya mana."

Jin an ambaci Alhaji Yakubu nan da nan ta ɗaure fuska. A duniya yanzu babu wanda ta tsana irinsa, mutum dai kamar maye. Abu daya da ta sani shi ne, daga maganar zuwa kamawar watan da suke ciki na azumi ya yi mata ɓarin kuɗi sama da dubu ɗari, wannan kaɗai shi ne ya burgeta musamman ganin cewa Tasleem ba  ta samu hakan ba. Rabu dai da Hamza akwai kulawa a baki amma babu ko asi da ya taɓa kawomata. Wannan abu na yiwa Tasleem ciwo kuma yana fasawa Futuha kai, tana son ta ga ba ta son mutum yana bibiyarta kamar jela.

"Kar ka sa na tashi, har wani tsami na ji abincin ya soma yimin a baki."

Yassar da Dawud suka kwashe da dariya. Tasleem ta yamutse fuska ta ce.

"Gulma, a bakya so kike kwace Æ´an chanjinsa. Fuska biyu."

Futuha ta dire fork din hannunta da ta ke cin haÉ—in salad da shi, tun ba ta kai ga haÉ—iyar wanda ta ke tauna ba ta soma balbaleta da masifa.

"An kwata ɗin, ina ce albarkacin kaza dai ƙadangare ke shan ruwan kasko? Ko kin manta abin da Mami ta ce akan amfanin kudin?"

Tasleem ta hadiye zancenta, ta tuna Mamin cewa ta yi Futuhar ta saki jiki da Alhajin ta dinga nuna masa kulawar koda iyaka baki ne, muddin dai zai bayar da kuÉ—in ba za a ji kunya a auren ba tunda ba su da tabbacin samun yanda ake so daga wajen Abba. Wato na siyayyar kayan É—aki da sauransu. Maganar Futuha ta katse ta.

"Kuma ko banza gwara Yakubu tun daga nan an san zai iya riƙe mata biyu, wani kuwa da ko ɗayar ma ya kasa nunawa zai iya sai afkin waya da ƙalƙalar  turanci kamar tsatson sarauniyar Ingila." Suka kwashe da dariya. Ran Tasleem ta kai kololuwa a ɓaci, su Humaira na zaune su dai su na shan ruwa abin su daga gefe suna kallon ikon Allah. Raihana ce ta tofa.

"Kai Adda Futuha, ramuwar gayya fa akwai zafi kar ki kai Adda Tasleem bango."

Aikuwa tana cewa haka kamar ta kara zuga Tasleem sai kuwa ta yi caraf ta ba ta amsa.

"Kyale ta Raihana, ai mugun abu ya ƙare a gindinta tunda ko ba komai nidai auren soyayya zan yi, Hamza gani ya yi yana so a mutunce. Wata kuwa sai bayan an jefe ta da kalmar karuwanci, ƴar rawar Tiktok sannan ta yi na'am da Alhaji mai zubin moɗa."

Lallai, baki idan ya san me zai faɗi bai san me za a mayar masa ba. Aikuwa Futuha ta yi kukan kura har ta na cilli da bowl din salad dake saman cinyarta zuwa ƙasa, ta yi kan Tasleem da kokawa. Itama Tasleem kasancewar a wuya ta ke kawai sai ta biye mata suka hau jibgar juna. Dakyar Yassar ya shiga tsakaninsu gudun kar Abba ya ji.

Tasleem na  huci ta ce.

"Ni kuɗi bai dameni ba tunda zan auri wanda yake sona nake sonsa. Arzikin dai ai na Allah ne, kuma ko makaho ya shafa ya san Hamza ba talaka ba ne. Alhamdulillah ba a taɓa yimin wannan mugun ƙazafin na karuwanci  ba."

"Shegiya! Ni kike kira karuwa, ai gwara ni sharri ne, ke kuwa sau nawa kina yiwa Mami sata? Ko ranar da aka yi na Humaira, ina ce ke ce kika kawo shawarar a yi mata wannan sharrin don ki wanke kanki. Ke ce kika É—auki kuÉ—aÉ—en, ganin Yassar ya kama ki sai aka shiryawa Humaira tuggu don kar Mami ta zarge mu."

Humaira da ke shirin kai kofin kunu bakinta ta yi saurin ajiyewa, ashe ma ɓarayin biyu ne? Ba ma wannan kadai ba sai ganin yau dai Allah ya karɓi addu'arta gaskiya ta yi halinta. Tasleem gaba ɗaya ta yi wuri-wuri da idanu, ko kaɗan ba ta zaci Futuhar za ta yi mata wannan tonon sililin ba. Yassar ya dakamusu tsawa amma kasancewar girma ya faɗi ko a jikinsu, sai dai tsawar farko daga Abba ya sanya gaba daya suka yi tsit. Ashe yana tsaye a bakin ƙofar falon tun sadda suka soma kokawa, Mami na biye da shi a baya. Gaba ɗaya hankalinta a tashe, wato dai ya allura ta tono garma? Ba wannan ba ma, babu uwar da za ta so ganin yaranta kansu a rabe. Gaba daya falon ya yi tsit su Tasleem sai rarraba idanu ake.

Ya shigo tsakiyar falon ya wanke su ganin ba su duba girman watan da ake ciki ba na ibada su na yi mishi faɗa a falo. Daga nan ya nemi sanin abin da ya faru da Humaira a baya, nan fa Raihana kamar wacce ake tsikara ta ba shi labari. Humaira kanta a ƙasa tana hawayen farin ciki, wato da Allah ya tashi wanke ta sai ya sa Abba da kansa ya ji zancen ba iyaka Mami ba. A ranar su Yassar da Futuha sun ga tashin hankalin Abba, ya kuma ci alwashin saɓawa duk wanda ya ƙara jarraba musgunawa Humaira. Hatta da Mami mai kokari akan Humaira a ranar har da ita ya haɗa ya ce ai laifinta ne da ba ta tsawatar musu shiyasa suka samu sake. Haka Abba ya yi faɗan da ba su zata ba har Humairar daga nan ya fice daga falon. Mami ta bi yaran da kallo sai kawai ta juya ta bi bayan mijinta. Humaira ta mike ta kalle su fuskarta dauke da murmushi ta juya zuwa ɗaki.  Ranar jin ta take ranta babu ko ɗigon bakin ciki sai dai ba ta ji dadin dorawa Mami laifin su Yassar da Abba ya yi ba. Amma ta yi mamakin Abban, a baya tana tunanin ko sonta ne ya daina, ko ya manta ma da ita a lissafin ƴan gidan sai kuma abin da ya yi yau ɗin ta fahimci tana nan daram a zuciyarsa kawai dai ba shi da lokacin kansa balle na hira saboda yanayin kasuwa.  Banɗaki ta shige ta ɗora alwala ta dawo ta zura hijabinta ta shiga lazimi. Ta na nan zaune ta yi shiru, wani lokaci can take tunowa ita da Dada musamman a wata irin na azumi yanda suke zama bayan shan ruwa a yi hira kafin lokacin sallar isha'i.
  Ƙarar wayarta ya katse mata tunani, ta sa hannu ta ɗauka. Fadeel, shi ne  sunan da ya bayyana saman screen din, haka Raihana ta adana mata lambar ba da son rai ba. Albarkacin watan da suke ciki ya ci ta ɗaga da sallama. Ya amsa daga can ransa fari sol.
   "Ina fatan kin sha ruwa lafiya?"

"Lafiya kalau." Ta amsa a taƙaice. Shiru ya ɗan biyo baya, ya rasa me zai ce yana gudun ya yi furucin da zai sa ta katse wayar gaba ɗaya. Ya kasa hakuri balle ya danne don haka ya ce.

"Sai yaushe Humaira? Sai yaushe za ki samarwa wannan ɗan marayan gurbi a zuciyarki? Ba zan gaji da roƙo ba, ki ba ni dama Humaira. Wai kin san so kuwa?"

Nan da nan ta ji ya har ta soma harzuƙa a sanadin kalmar so da ya ambata, cike da gatse ta ce.

"Sai nan da shekara."

"Kin yi alƙawari nan da shekarar za ki amince ki yarjemin da batun aure?"

Ta dauki maganar a zancen banza, ta sani babu wahalallen da zai yi dakon shekara ya auri budurwar da ba ta ko son zancen auren balle auren. Don haka babu dogon tunani ta amsa.

"Eh, na yi muddin za ka rabu da kirana ka bar takuramin."

Shiru na wasu lokutan sai kuma ya sauke nannauyan ajiyar zuciya.

"Za ki same ni da bin umarninki, amma kiyi hakuri koda saƙo na dinga aikomaki ta waya. Ke kuma ki daure ko da sallama ki amsamin domin na san kina sane da ni."

"Naji."
Ta amsa gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili ba, ta ji zufa ta keto mata. Tsanarsa ta ke ji yayinda a wani gefe can a ƙasan ranta ta ke jin wani abu da ba ta tantance ba.
Chapter 27 · 0% Book details